MISHAL

35_36_37

by @ayshagaladima22

MISHAL



By AYSHA GALADIMAđŸ€đŸż
***


BOOK 1 
Page 35_36_ 37.

Joy da take bakin ‘kofa tana ganin duk abunda take , amma ko kusa bata bari Mimi tasan tana cikin d’akin ba . 

‘Dan d’aga wayar hannunta sama Mimi tayi , tunani da yawa ßuna mata yawo a cikin zuciya , especially last abunda ya faru a tsakanin su , ya kasa fita a kanta , shiyasa tayi tunanin ganin sa lokacin da ta tashi, but yet she’s wrong, baya nan kwata kwata , har ta gama ciwan nata ta warke, and no single message or call for him. 

A hankali ta d’ora wayan akan ‘kirjinta , tana kallan ceiling d’akin, cikin sanyin muryar ta furta “ May be yana busy ?
. But atleast Uncle d’ina ne , zai iya samun free time ya tanbayi yadda nake , amma be yi hakan ba 
. Or maybe he doesn’t even know I’m awake yet?”. Ita kad’ai take wa kanta tanbaya , kuma take tunanin amsar tanbayar nata da kanta . 

Gudun kar a nemeta a ‘kasa , ta sawa ranta cewa har yanzu bai san ta tashi bane , shiyasa bai kira ta ya dubata ba . 

Da wannan tunanin ta mi’ke zata fita , har ta bud’e ’kofa sai kuma ta d’an tsaya , cikin ‘kasan mo’koshi ta furta “ Allah ya dawo da shi lafiya 
” ba tare da tasan dalilin yin addu’ar ba , ta fito daga d’akin zuwa ‘kasa .

A falo kuwa , Zarah da Ameerah suna zaune tare da sauran mutanen gidan, even though Zarah hankalinta ya rabu guda biyu sosai , zuciyarta sai faman tunanin me Mimi take a d’aki take . 
She just feels like tanasan tasan duk abunda Mimi take sabida ta haka ne kawai zata san yadda zatai ta raba Moh da Mimi kamar yadda ta ‘kudiri hakan a cikin zuciyarta . 

Ganin saukowar Mimin yasa ta sauke numfashi  tana fad’in “ Kin d’auko wayar?”. 

“ Yeah ..” cewar Mimi.

“ But naga kin dad’e ko waya kikayi ?.” Zarah ta kuma tanbaya. 

“ Not really , meyasa kika tanbaya ?.” Mimi tayi mata tanbayar tana zama akan kujera. 

“ No babu komai am just asking, naga kamar kin dad’e shiyasa nayi wannan tunanin , but tunda kin dawo ai shikenan.”

Daga nan suka d’an cigaba da hirar su , time to time kuma tana kallan wayarta . 

Already kuma Mommy Zarah 90% na attention d’inta yana kan Mimi , so duka hirar da suke da wayarta da take dubawa time to time , akan idon Mommy ne . 

Shiyasa ta d’ora wani kyakkyawan murmushi akan face d’inta tana kallan Mimin “ Mimi ko akwai call d’in da kike expecting ne? Naga sai faman duba wayan ki kike, akwai abunda kike so ne?.”

‘Dan ya’ke Mimi tayi tana ajje wayan “ No Mommy.”

“ Kin tabbata?.” Mommy ta kuma tanbayarta . 

“ Eh Mommy na tabbata .”

“ Okay Daughter na” da haka Mommy ta mayar da hankalinta kan ßu Mamy da suke magana. 

Ita kuma Mimi ta ajje wayar ga baki d’aya gudun kar wani ya sake mata makamanciyar tanbayar idan aka ga tana duba wayar. 

An d’anyi hakan da kamar minti 40 , Zarah ta d’an ri’ko hannun Mimi, ga baki d’aya ta dawo asalin Zarahnta da Mimi ta sani. 

“ Besty please no zamu iya yin magana mu kad’ai? Ina so na fad’a miki wani abu ne please?.”

“ As in me , you and Ameerah kike nufi?”. Mimin ta tanbayeta cikin d’an confusion.

“ No banda Ameerah , abun ai bai shafe ta ba , nidai please let me tell you something please.”

Kallan Ameerah , Mimi tayi , ita kuma Ameerah ta d’an d’aga mata kai , tana fad’in “ kuje i will wait for you.”

Hakan kuwa akai, dan Mimi tana mi’kewa ma Zarah ta ri’ko hannunta , kamar dai yadda saba a koda yaushe . 

Sun hau sama amma kafin su ‘karasa d’akin Mimi, Zarah ta tsaya tana sakin hannunta tunda already sun bar cikin mutane .

Sai da Zarah ta d’anyi shiru tana tunanin abunda zata cewa Mimin, ganin Mimi ta tsaya kallanta sai kawai ta d’anyi mata murmushi , deep down kuma tana faman ya’ki da zuciyarta ne .

“ Besty?.” Ta kira Mimin..

“ Hmm?”. Shine amsar kawai da Mimi ta bata .

“Uhm am sorry akan abunda nayi miki kwanaki, nasan nayi kuskure and tun daga wannan ranar nake so na baki ha’kuri amma na kasa, ranar da muka had’a gathering d’in nan, naso na baki ha’kuri a time d’in , sai kuma wannan abunda ya faru, but am really sorry akan abunda nayi miki, kinsan ba hali na bane , and it was a mistake , ko wana d’an adam kuma ajizine but we all make mistakes. 

So am sorry , hope you can forgive me ?”


‘Dan shiru Mimi tayi tana tunani sai kuma ta kalli Zarahn “ Me yasa ma kika taso da maganar nan? already ai mun wuce wannan abun , no need ki ma sake dawo dashi.”


“ Yeah na sani shiyasa ma nake baki ha’kurin, please dagaske nake miki, idan baki ce mun kin ha’kura ba , wallahi bazan ji dad’i ba , kinsan yadd taji da baki da lafiyar nan kuwa? Ji nayi kamar zanyi hauka wallahi.

Dan Allah Besty just say it , kice kin yafemun, zanji dad’i sosai, kinji?.”


“ Zarah?
.”

“ Please Mimi , idan baki fad’a ba sai nayi tunanin ko har yanzu kina jin haushi na akan abunda nayi ne , and bazan ma ‘kara kwatanta hakan ba just take it as my mad please Besty na .”


“ Shikenan Zarah na ha’kura , but karki ‘karamun irin haka , sabida ba zanji dad’i ba .”

“ Yeah bazan sake ba . Wai kinsan yadda naji lokacin da kike kwance? Hmmm kamar zanyi wani ‘karamun hauka , dan ma wannan guy d’in baya bari shigo a dubaki , but ni so nayi fa na koma can ga baki d’aya na dinga kula da take , amma kwata kwata basa bari.”

‘Karamun dariya Mimi tayi tana fad’in “ Zarah ? Are you kidding me ? Ina zaki koma ga baki d’aya ? Part d’in Uncle Moh d’in? Ba fa part d’in Mamy ba , part d’in Uncle Moh, cab karka ki bari suji wannan maganar naki, nima yanzu da na warke ba gashi na dawo nan d’in ba .”

“ Amma Mimi ai tunda ya bari kika kwana zaki iya zaman ki açan , why not baki zauna ba? Gaskiya part d’in Uncle Moh yana da kyau, kin ta’ba shiga kitchen d’insa? Ko kuma sama ? Nasan duk yafi falon ‘kasa kyau, gaskiya ka mata yayı a bar mu , muyi tour a part d’in nan ko na sati d’aya.”

Hannayenta biyu Mimi ta tafa mata a dai dai fuskarta tana fad’in “ Malama Zarah , stop your day dreaming, maganar part d’in Uncle Moh ake ba wani ba . Uncle Moh ! Uncle Moh ! You’re not okay , toh ba dani za’ayi wannan abu ba.”

Wani irin malulun abu Zarah ta had’iye da taji ya tsaya mata a ma’koshinta ga baki d’aya sai taji haushin Mimi ya sake ka mata , but she promise her self next time ita ce zata shiga part d’in ba Mimi ba , and Mimi ba zata sake saka ‘kafa cikin wajan nan ba, because everything belongs to her alone . 

Ba kuma ta so Mimi tayi tunanin wani abu akan haka shiyasa ta d’anyi dariya tana fad’in “ Me too am joking , waya isa ya shiga part d’in Uncle Moh, dan ma ke kina satar hanya kina shiga ne .”

Wani irin dariya ne yazo wa Mimi take fad’in “ Wace ce tayi satar hanya?”

Tsayawa kallanta Zarah tayi , jin yadda tayi dariyan. 
Sai kawai ta d’an ‘ka’kalo murmushi ta yafawa fuskarta “ Ke wasa nake . Shi wani dariya da kike , let’s go back kar azo ana neman mu, mu kuma munanan muna labari
” da wannan maganar Zarah ta kawar da d’aya maganar suka dawo falo, sabida bataso bakinta ya kufce har tayi wata magana da Mimi zata yi zarginta ko guda d’aya. 

Sun dawo falo aka cigaba da hira da surutu , kamar yadda aka saba duk lokavin da aka had’u. 

Sai wajan Azhar kowa ya watse ya nufi part d’in sa , masu tafiya office suma suka wuce aikin su. 

Falo ya dawo daga Mimi sai Aunty Shukura da kuma Mamy.


Mamy sai da taga kowa ya tafi ta kalli Mimi, “ Mimi zaki iya zuwa part d’in Moh ai ko?.”

Kanta Mimi ta jinjina mata tana fad’in “ Eh Mamy.”

“ Toh maza ya kamata kije ki duba Ɵu Aya , dan tunda kika kwanta suke faman jigilan aikin kula da ke , ko ni da na haife ki banyi wannan walahar da sukai ba and by Allah naji dad’in yadda suka kula da ke.”

Cikin amincewa da maganar Mamy , Aunty Shukura itama ta kalli Mimi “ Wallahi sunyi ma abunda yafi ‘ko’kari, bana tunanin ko bacci suna yi me kyau . Kinga Aya yadda ta rikice , ko ni da nake yar ki banyi rigicewar da tayi ba . Na yadda tana sanki Mimi, please be nice to her abunda tayi miki, babu me yi miki shi sai me ‘kaunar ki.”


“ Insha Allah , zanje na duba su yanzu , since na warke ga baki d’aya yanzu.”

“ Please daure Mimi na idan yaso , idan kika dawo sai kiyi sallah ki huta kema sosai kinji? Akwai kuma abunda kikeso na girka miki? Sabida test d’in bakin ki ya dawo sosai.” Mamy ce tayi maganar. 

Ita kuma Mimi ta girgiza mata kai tana mi’kewa tsaye “ I’m fine with anything Mamy gashi daman ba wani yunwa nake ji ba sabida naci break fast d’in nan da kikai mun sosai, na gode Mamy na, you’re the best 
.”

“ You’re also the Best Mimi na 
”

“ Iye Mamy abun ‘yar launin fata za’ayi , ni kuma fa ?”.

“ Abeg jareeeee
” cewar Mamy. 

Duk sai sukai dariya, har da Mamy d’in. 

________ Fitowa tayi zuwa part d’in Moh , tana shiga ta tarar dasu duk a tsaye , alamu ya nuna suma fitowar za suyi . 

Suna ganinta duk suka fad’ad’a fuskar su . 
Aya ce ma ta matso kusa da ita tana ri’ke mata hannu “ Little Mimi, lalle kin soma samun sau’ki tunda kika fito , yaya jikin ki? Hope komai lafiya , ko akwai abunda kike so?”.

“ No Aunt Aya na gode , daman nazo ne na duba ku and to thanks you for the care
.

Thank you so

”

“ Uhm Uhm Mimi rufa mana asiri, wannan godiyar ba mu zakiyiwa ba .” Cewar Alameen yana d’an dariya ‘kasa ‘kasa.

Sincerely speaking Mimi ta furta “ Toh wa zanyi wa godiya ?.”

“ Don’t worry lokaci zai nuna , yanzu dai ki samu ki huta sosai, because you really ! really need to rest kinji?.”

“ Insha Allah, Thank you so much, Uncle Alameen..”

“ My pleasure Mimi
.”

Kallan Aya tayi , za tayi magana “ No kar ma ki soma gode mun Little Mimi, if not zamu ‘bata dake..”

Murmushi Mimi tayi , still sai da tace “ Thank you Aunt Aya.”

“ You will never change 
.” Aya ta fad’a tana d’an dariya itama. 

“Daman Mamy tace na tanbaye ku , abunda za’a girka muku, or if you need something ku fad’a mun sai na fad’a mata
.”


“ No ! Kicewa Mamy mun gode sosai, yanzu fita ma zamuyi, but anjima insha Allah da daddare zamu zo gaishe da Mamy sai muci tuwo ba . 

But ai ke zaki dawo part d’in nan da zama kafin Moh ya dawo ko?”. Alameen ne yayi magana. 

Ita kuma ta ‘bata fuska “ No a d’akina zan zauna, ai na warke.”


“ Okay fine ! Kiyi yadda kike so Mimi , but you’re highly welcome duk lokacin da kikesan shiga , as always 
.” Cewar Alameen.

Ita kuma ta d’aga masa kai alamar Toh . 

Hannunta har lokacin yana cikin na Mimi suka fito daga part d’in.. 

Aya da kanta tayi insisting zata raka Mimi bakin part d’in su , kuma hakan akayi, Mimi ta koma ciki, Aya kuma suka fita tare da Alameen.

____ Haka ranar ta kasan ce cike da kulawa , duk wanda ya dawo sai ya soma tsayawa a part d’in Mamy ya duba Mimi. 

Zarah da Ameerah kuwa ba’asan wanda yafi wani zuwa dubata ba , har zuwa lokacin kuma babu wani call daga Moh, tun tana dubawa har ta ha’kura ta ajje wayar. 

__
Kamar yadda su Aya sukai al’kawarin zuwa , After isha’i prayer , sunzo sun sake duba Mimi, sunci abincin Mamy kuma, this time around har hira Alameen ya zauna sukai da su Baffa sosai. 
Da zasu tafi kuma Aya ta hau sama ta d’auko trolley d’inta , da mamaki duk suka kalleta , Mamy ce ta soma cewa “ Aya ina kuma zaki ji? Da kayan nan?”

“ Mamy akwai abunda ya taso mun which ake bu’kata na da gaggawa shiyasa zan tafi, but bazan dad’e ba zan dawo.”

Cikin rashin amincewa Mamy ta furta “Ba zaki zauna ki ‘kara mana koda 2 days bane? Atleast yadda kika dinga zirga zirgan nan ya kamata daka ke har Alameen ku zauna kwana biyu , babu shige babu fita har sai kun dawo da energy d’in ku sosai.”


“ Yes Aunt Aya ki zauna mana , daga warkewa na kuma sai kice zaki tafi kamar jira na dama kike na warke ki tafi?” Mimi ta ‘karasa maganar a shagwa’be.


“ Don’t worry Mimi, zan dawo ai ina kammala abunda zanyi zan dawo bazan wani dad’e sosai ba , bazan d’auki dogon time ba .
Take very good care of your self . Okay?”.


“ Insha Allah zan kula .”

“ Yawwa My dear Good night
”

“ Aunty Aya bari na rakaku har waje mana , sai na dawo
”


“ No Mimi , duka yaushe kika warke da zamu soma wahalar da ke? Kedai kiyi zamanki , Sai da Safe .” Cewar Alameen .


Batasan sake musu dasu shiyasa ta furta “ Shikenan Uncle Alameen sai da safe , Aunt Aya sai da safe..”


A tare both Aya da Alameen suka amsa mata da good night, su kayiwa su Mamy sallama sannan suka fita. 

Suna shiga cikin mota Aya ta kallesa “ Alameen you guys are making things too hard for her .” 

Sai da ya kunna motar tukunna ya d’an kalli Aya “ Kema kinsan we’re not, just may be it may hurt at first , but ya kamata ta saba da kanta.”


“ But yet you guys please , I know you, karku soma wannan play play d’in, definitely da ban bar gidan nan yau ba , bazan iya zama na ganta haka nan ba , likeeeee damnnnnnnn Nooooo.”

“ Oh really? Yayi maganar ba tare da ya kalleta ba.

Itama ta amsa masa da “ Yes mana
.”

‘Dan ‘karamun dariya yayi mata “ Then ai kin fi sanin wanda zaki fad’awa wannan maganar, it’s not the innocent me Al’ameen
”

“ Alameen you’re not nice Serously”.

Shima ya amsa mata da “ Yeah na sani.” Da haka suka fita daga gidan suna  having conversations a tsakanin su.

___Mimi kuwa da ta koma Mamy ta zaunar da ita a kusa da ita “ Mimi akwai abunda kike so? Ko akwai abunda kike so?”.

“ Aa Mamy wallahi babu abunda nake damuna , kece kawai kike ganin kamar akwai wani abu , and I’m perfectly fine Mamy na
.”


“Shikenan na yadda yanzu ki koma d’akin ki , ki huta tunda tun d’azu kike zirga zirga , ke da baki da isash shiyar lafiya ma .”

“ Okay Mamy na , Good night
”

“ Good night dear
 idan akwai abunda kike so , you can text or call me , kinji?”. 

“ Okay Mamy
” daga nan Mimi ta nufi d’akinta , tayo alwala ta zauna akan bed tana sauke numfashi, she don’t even abunda yake zuciyarta gata gatan kawai, a karan farko da zuciyarta take jin tayi missing wani abu, duk da tana ‘ko’karin yakice tunanin amma ta kasa . A haka tayi bacci so moody, bacci ma kuma bawai dad’i yayi mata ba .


WASHE GARI 

Wajan Azhar tana zaune a d’aki , Ameerah da Zarah suka shigo sake dubata , tunda tun safe basu shigo ba sai yanzu


Zarah tana zuwa ta fad’a kan Mimi tana hugging d’inta “ My Bestyyyyyyy yau nayi missing d’in ki wallahi.”

‘Dan dariya Mimi tayi “ Abeg ni d’agani karki ‘ballani da kinyi missing d’ina ai da tun d’azu zaki zo duba ni , sai yanzu zaki zo kice kinyi missing d’ina? Abeg jareeee.”

“ Rabu da ita Mimi, trust me babu wani missing d’inki da tayi, how far ya jikin ki?
”

Murmushi Mimi tayi wa Ameerah tana d’an ri’ko hannunta kamar yadda itama Ameerah ta ri’ko hannunta “ Ameerah am fine , thank you , thank you ! Thank you so much for the care.”

“ Mtswww ji beki, kamar wacce nayi wani abu me girma kike mun irin wannan godiyar please stop it
” Ameerah ta ‘karasa maganar tana samun wajen zaunawa .

‘Dan kallanta Zarah tayi,tana wani d’age kira “ Ah su Ameerah anyi hankali, kamar bake ce kike fad’awa Mimi maganar duk da tazo bakin ki ba , amma yanzu naga ga baki d’aya kin wani canza , me ya faru?”.

Wani murmushin gefen baki Ameerah tayi tana kallan Zarah sosai “ Zarah wai kin manta da wa kike magana ne? Ameerah ce fa? Ko kin manta Mimi was my best and only friend kafin ki fara this Besty Besty things of yours ? Zarah?.”

Kafin Zarah tayi magana Mimi tayi saurin shiga tsakiya tasan halin ko wannan su especially Ameerah yanzu zata fad’awa Zarah manyan magana , kuma batasan hakan ya faru ta dalilinta . 

“ Dan Allah dukan ku , kuyi ha’kuri wannan abun duk bana tashin hankali bane . You guys are all my Besties to chill please, kar kuyi wasu magana all because of me , I won’t be happy gaskiya .”


“ So Mimi , is better ki fad’a mata, ni zuciyana bata da sanyi sanyi irin naki, just do me , I do you ne kawai , nothing more 
.” Cewar Zarah
.

Kallansu duka Mimi tayi “ Nidai nace muku dan Allah kuyi ha’kuri , duka fa is not a big deal and Wlh your guys are my besties no one will replace you all
.”


Kallan Mimi , Zarah tayi cikin zuciyarta kuwa fad’i take “ Allah ya tsare na zama Bestie d’in ki, am just waiting for the perfect moment, zaki gane baki da wayo, sai na sa kinyi da nasanin sani na , in your whole life, because I hate you, banza kawai
” Amma a fili sai ta d’an ta’be baki tana fad’in “ Shikenan , saboda ke dai zan ‘kyaleta
”

Ameerah kuwa “ Hmmmm” Kawai tace ba tare da ta sake cewa komai ba . 


From there suka cigaba da hirar su perfectly, even though wani lokacin bakinta yana ‘ko’karin sakin layi, sai tayi saurin waskewa . 

Zuwa wani lokaci me tsaho kowa kuma ya wuce part d’insa , d’akin yayi saura Mimi kawai, gashi d’akin ya soma zama mata so boring tunda babu Moh, kuma bata kuma ganin Joy ba, tunani ne kawai ta ko ina yake shigar mata kai



____ Zarah tana shiga part d’in su ta tarar da Mommy bata falo, sai ta wuce bedroom d’inta lokacin waya take. 
A gefen bed d’inta ta zauna har zuwa lokacin da ta gama wayar da take . 

“ Aa Zarah ya naga kin shigo ranki a ‘baci wani abu ne ya faru?”.

“ Mommy mene ne ma bai faru ba , sincerely speaking Mommy ina ta faman danne kai na akan abunda Mimi take mun amma na kasa ha’kuri wallahi ko me za tayi yanzu sai naji na ‘kara jin haushi. 

Musammman idan na kalleta . Mommy ta fini kyau , ta fini komai na rayuwa , kowa yana santa amma ni kenan kullum zan dinga zama a ‘kasanta ne? Mommy na gaji , ko da yaushe ni zan dinga binta ita ba zata dinga bina ba . Wallahi na gaji Mommy, kiyi wani abu kawai akan wannan abun. 

Nima inaso ta d’an d’ana irin abunda nake ji, and here is Ameerah , she’s busy defending her , itama haushin ta nake ji, ko ganin abunda Mimin take mana ba tayi , na kula yanzu ta soma dawowa santa . 

Mommy abunda kikai wa Ameerah wallahi ya soma sakinta, yanzu na kula ta soma dawowa san Mimi kamar yadda take a da. 

Mommy kar Ɵu juya mun baya, nidai kisan abunda za kiyi dan Allah Mommy
”


Tsaki Mommy tayi “ Matsalata da ke Zarah kin fiya garaje kwata kwata baki da ha’kuri, ko me za’a fad’a miki ba zaki d’auka ba sai dai ki dinga yi wa mutum taurin kai sai kice kin fisu .

Kin fini sanin abunda ya kamata nayi ne? Ke kin sanni kuwa? Ameerahn banza Ameerahn hufi , ita ta isa taja da abunda nayi niyar yi ne?ko ubanki ance miki haka na ‘kyalesa ne? Da ace banayin abunda nake yanzu ance miki za’a ma same ki ne? Toh banasan rawar kai . 

Idan kuma ba zaki nutsu ki saurari abunda nake fad’a miki ba , toh shikenan zan ‘kyale ki sai ki je can ki ‘karata, tunda ba kya ji kwata kwata.”


“ Mommy ai naga abun ne baya sauri na d’auka kamar yadda kikai wa Ɵu Ameerah shima haka nashi nasu yake amma kuka sai naga komai yasha banban.”


“ Hmmmm Zarah kenan, saurin me kike? Ki tsaya mana , ki bari nan da kwana biyu duka abubuwan nan sai kin sha mamakin su, nice fa kuma kowa yana gani babu wanda ya isa ya ja da abunda mukai niyar yi, ki tsaya kawai kiyi kallo , idan kin bada had’in kai , idan kuma abunda kika saba ne wato rashin ha’kuri, toh nidai babu ruwa na gaskiya .”


“ Mommy na bari tunda kika fad’a bari dai kawai na wuce d’aki na, zan jira nan da 2 days d’in muga abunda kike cewa Mommy
” da haka ta fice ta bar Mommy a tsaye tana faman nasari, sai kawai tayi dialing wani number ta kira .


__A part d’in su Ameerah kuwa Mama tana zaune a falo tana jin karatun al’kurani kuma tana hutawa , shigowar Ameerah yasa ta d’an d’ago tana kallanta . “ Har an dawo?”.

Kanta Ameerah ta d’aga mata tana samun waje ta zauna , tayi shiru kamar me tunanin wani abu, har sai da Mama ta furta mata “Tunanin me kike , kika zauna haka babu uhm babu uhm uhm ke d’aya?”.

“ Hmmm wallahi Mama wani abune ya soma bani mamaki, Mama kinga yadda Zarah take wa Mimi idan ta ganta, amma yanzu na lura cikin kwanakin nan sai ta dinga wani abubuwa
”


“Kamar ya ?” Mama tayi tanbayar tana samun waje ta zauna sosai. 

“ Mama yau idan nice nake wajanta babu Mimi , nunawa take kamar Mimi tana damunta ko kuma tana d’an jin haushin ta , amma a gabanta sai kiga kamar zata cinyeta sabida so, Besty sama besty ‘kasa , Mommy wannan fa munafurci ne wallahi , and I times sai naji kamar na fad’awa Mimi abunda take mata, but kinsan Mimi ba lalle ta yadda ba sabida Zarah ta sa mata so much trust akanta har yanzu kuma ban dena jin abunda nake ji a rai na ba , kawai sabida dai ina danne zuciya na ita ta addua shiyasa amma da banayi nasan kullum da munyi fad’a da Mimi sabida Indai muka zauna waje d’aya sai naji inaso na fad’a mata mugayan kalaman da zasu zauna a ranta but am not doing it intentionally wani lokacin ma sai na bar wajan ta sai na dinga danasanin abunda nayi.”


“ Hmmm Ameerah kenan, babu abunda zance miki da ya wuce ki kama Allah , kuma ki ri’ke Allah , duk wanda yayi ba dai dai ba akwai Allah kuma yana madakata, akwai ranar sakayya, abu d’aya kawai zakiyi shine kullum ki dinga adduo’in da na baki, kuma ki cigaba da neman tsari daga sharrin me sharri. 

Da kinji wannan abun yana taso miki a zuciya ki cigaba da maimaita Lahaula wala ‘kuwata illa billah , da kuma rabbi inni lima anzalta ilayya min kairin fa’kir, Allah zai duba lamarin ki , tunda kin bar komai a hannunsa , kinji?.”


“ Naji Mama , na gode sosai.”

Murmushi Mama tayi mata “ Ya jikin Mimi kuwa?”.

“ Mama Mimi yanzu kam ta warware tas babu abunda yake mata ciwo kuma , na tabbata daga nan dai zuwa gobe zata zama normal sosai insha Allah . 


____________________
A d’akin Mamy da yamma , Shukura tana zaune da ita da Mimi da Mamyn ßuna hira . 
Aunty Shukura ta kalli Mamy, sannan ta kalli Mimi sai kuma ta sake mayar da kallanta wajan Mamy.

“‘Mamy ni kam ba za’a gano wanda yayiwa Mimi wannan abunda ? Duk da dai abunda yana mugun d’aure mun kai idan na zauna tunanin babu wanda zai yi wannan abun a cikin ‘yan gidan nan , and ni har maid d’in gidan nan na yadda dasu , babu wanda zan iya zarga gaskiya , wani lokaci kuma zuciya na sai ya dinga cewa kodai it was by mistake . 

Gashi nan dai ga baki d’aya , na rasa wana tunani zanyi guda d’aya da zai gamsar dani
.

Mamy wai me Baffa yace ?.”


“ Hmmm Nima abun mamaki yake bani, nama rasa wani irin tunani zanyi, amma har ga Allah babu wanda nake zargi cikin zuciya na . 

Baffan ku kuma bai yi magana ba har yanzu duk da dai bayan ßallar isha’i yace zaiyi magana da ku dukan ku, abun shi dole yafi dukarsa sabida ‘yarsa akai wa wannan abunda , idan wani abu ba fata ake ba ya faru fa? And a long side mutanan gidan nan fa family d’insa ne , familyn ma na jini which is blood , ta yaya zai zargi a halin ‘yan uwansa ? Shukura abun akwai rud’arwa ne . 


Kallan su Mimi tayi ga baki d’aya dan ita abunda bai shiga kanta ba tana ganin hakan ma bazai ta’ba faruwa ba , shiyasa ma ta katse musu wannan tunanin na zuciyar su “ Mamy please ku dena wannan tunanin da kuke , ni gani nake ma duk bashi da wani amfani, wai ku har kun yadda da Dr din nan?

Bayan ga food poisoning ga abubuwa kala kala , haba mana dan Allah ku dena wannan maganar ma kar tsautsayi yasa wani daga ciki yaji. 

Ni ko da gangan akai mun, or by mistake ni wallahi na yafe , no need ma akuma taso da maganar nan tunda har ta riga ta wuce kuma am perfectly fine now , Alhamdulillah.”

‘Dan dariya kawai Mamy tayi “ Mimi kenan, wannan decision d’in ba naki bane , ki bari dai mu soma jin abunda Baffan naki zai fad’a kafin muce komai tunda mud’in duka a 
‘kar’kashinsa muke ai.”

Cikin amince wa da maganarta , both of them suka amsa mata da shikenan Mamy . Sai suka canza hirar zuwa wata daban , hira dai irin banter d’innan tsakanin uwa da yaranta.

Lokacin sallar magrib kuma yanayi, kowa ya wuce d’akinsa , before time d’in da Baffa zai dawo. 


After isha’i kamar yadda Mamy ta fad’a Baffa yasa a kira masa Mimi, bayan ya jiki da yayi mata da kuma d’an hira da sukai na d’an lokaci kad’an , Baffa ya dawo serious, yana dai dai ta zamansa sosai. 


Mimi bata kusa dashi a lokaci amma still ya nuna mata kusa dashi yana fad’in “ Mimi na dawo kusa dani na dinga ganin ki sosai kinji?”

Tashi Mimin tayi taje ta zauna kusa dashi tana masa murmushi ganin yadda yake ta kallanta kamar yau ya soma ganinta “ Sannu Mimi na , kinji jiki sosai


Murmushi Mimi tayi masa tana d’aga Kai “ Alhamdulillah Baffa, yanzu kam naji sau’ki sosai, babu abunda yake damu na kuma.”

“ Alhamdulillah” Baffa ya fad’a yana sauke wani numfashi , kafin ya d’anyi shiru na ‘yan seconds yana kallanta, sai kuma ya d’ora da “ Kin tabbatar babu wani abu da kike ji? Kada ki dinga cewa kina lafiya idan har kinsa ba haka bane ko kuma baki tabbatar ba Dr ta zo ta ‘kara duba lafiyan ki.” 

“Baffa wallahi babu. I’m perfectly fine now.”

“Good, Mimi na 
” ya kuma ambatan sunansa , ita kuma ta amsa masa da “ Naam Baffa na.”

“ Rashin lafiyar da kikayi , ta d’aga mun hankali sosai ba wasa ba . Babban tashin hankalin kuma abunda Dr ya fad’a a kan dalilin haka.”

“ Baffa
” ta kira sunansa amma yayi saurin dakatar da ita “ No bari na gama tukunna. 

Na kasa d’aukar abunda sau’ki Mimi, makamancin hakan bai ta’ba faruwa ba . Bazanyi saurin gaggawar d’aukar mataki ba har sai nayi bincike na tabbatar da duk abunda ya faru , tukunna zan yanke hukunci , ba zan yanke hukunci cikin  fushi ko gaggawa ba , amma duk wanda yayi miki wannan abun tabbas ba zan ‘kyale sa ba , sai na d’auki mummunan mataki akan koma wane ne. 

Babu wanda zai ta’ba mun ‘ya na ‘kyalesa, kiyi ha’kuri Mimi na kinji?”.


Murmushi sosai Mimi tayi har sai da ha’kwaranta suka fito waje “ Shikenan Baffa na , Nagode 
.”

“ No need for wannan godiyar  yanzu dare tayi ma , ke da kike kwanciya da wuri ya kamata kice ki samu ki kwanta , Allah ya tashe mu lafiya .”


“ Ameen .” Mimi tace tana mi’kewa tsaye , kafin ta fita sai da tayi wa su Mamy “ Good night” suma , already taci abinci, wanka kawai tayi, ta kwanta, tana d’an tunanin da ta fara a kwana d’ayan nan , kafin bacci ‘barawo ya zo ya d’auketa. 

Tayi bacci da kamar hour 2 Joy ta shigo d’akin tana kallanta, fuskarta da murmushi, har wajan gado tazo ta shafa kan Mimin “ Allah sarki Mimi, kiyi ha’kuri, na d’an lokaci kad’an ne , amma ina miki fatan ki fahimci abunda ake so ki fahimta , ko kya samu wani sassaucin.” Daga nan ta d’an shafa kanta , ta gyara mata abin lullu’barta , sannan ta ‘bace daga d’akin. 



__________
‘Karfe 3:30am na dare , lokacin da kowa yake bacci , a wannan d’akin duhun, matan nan ne guda biyu a ciki , yau ma sanye da ba’kin kaya ba’a ganin su , sai muryoyin su da ake ji. 

Ta hangun ce ta dafa ta damar kafin ta furta “ LAMY wannan  had’uwar ta gaggawa ce na tabbata yaushe kike so a gudanar da komai , a bisa yadda aka tsara mana .”

Wacce aka kira da LAMY ce ta d’an motsa tana tafiya a cikin d’akin, sai kuwa ‘karar kacau kacau d’inta da ake ji, tsanin ko awarwaro ko kuma sar’kar ’Kafa ne yake sawa yake wannan.”

Sai kuma ta d’an juyo tana fuskarta wanda ta kirata da LAMY d’in. 
“ SAMY ai komai yana hannun mu yanzu , kamar yadda muka tsaya , tunda har aka kwana aka tashi baizo ya ganta ba , abun mu ai yana tafiya dai dai yadda ya kamata. 

A wannan kwanakin, dole mu aiwatar da abun mu, sabida zamu samu daddad’an labari da muka dad’e muna san mu sani. 

SAMY burin mu zai cika, zamu zama manyan Hajiyoyi, burin sai cik na shiga d’aya daga cikin manyan ‘kungiyar duniya ..

Dole mu ‘karasa cika aikin mu dan akan yarinya ‘karama ba zamu ‘bata rawar mu ga baki d’aya ba .

SAMY burin mu zai çıka , burin mu zai cika sosai SAMY.”

Wani irin dariya SAMY tayi, itama kuma LAMY d’in tayi , sai suka matso suka rungume junan su cikin ba’ka’ken kayan nan , daga nan suka soma magana cikin wani yare me wuyar fahimta da iya su kad’ai suka san me suke cewa



_____________ 
Mintuna sun cigaba da tafiya , yayinda a wanni suke canzawa suna kwanaki. 
Haka lokaci ya soma tafiya , yanzu kwana hud’u kenan da warkewar Mimi, ta dawo normal babu wani rashin lafiya 
 life goes on , sai dai abubuwa da ta saka a ranta yanzu , duk da bata fitowa fili ta nuna, amma idan ta kasance ita d’aya tana shiga wannan damuwar. 

Tun tana duba wayarta da sa ran Moh zai kirata har ta fidda rai ga baki d’aya tama dena duba wayan ko tsammanin kiran sa . 

Kuma tun tafiyar Aya da Alameen bata sake jin wani labari ko zuwan d’aya daga cikin su ba, kamar ma babu wanda yayi existing a cikin su, haka Joy, itama tunda Mimi ta kwanta rashin lafiya bata ‘kara bari Mimi ta ganta ba amma duk dare tana zuwa ta dubata
.

Ameerah da Zarah kuwa , amintar su da Mimi ya ‘Kara ‘karfi duk da a yanzu Ameerahn tafi yawan kasancewa da ita , ba kamar Zarah da zata dinga kawo excuse ba , amma inda tazo kuma sai ta nuna babu kamar ta wajan san Mimi da ‘kaunarta. 

Da more take kawo excuses d’in nan bata san cewa da more Mimi take ‘kara kama kanta ba , musamman wasu d’an halaye da Zarah take yi yanzu , duk da bata fito fili ta nuna ba , amma wani lokaci tana jikinta yana d’an subucewa tayi a aikace duk  yadda taso danne wani abun kuma , ba ya iya dannuwa, har hakan ya ‘kara janyo more closeness tsakanin Mimi da Ameerah . 

Yau tana bacci wajan ‘karfe 6:15am , Shukura tayi knocking d’akin, tana shigowa . 

Mimi tana lullu’be tana bacci , Shukura ta d’an kira sunanta “ Mimi..” 

Shiru Mimi bata ce komai ba dan bacci take da alama baccin nata ma ya soma nisa . 

Sai da taje ta d’an tatta’ba ‘kafanta kad’an tukunna Mimi ta d’an motsa idanuwa tana kallan Shukura da take sanye da Abaya ba’ka, alamar fita za tayi. 

Idanuwanta da cike da bacci haka muryarta , ta d’an d’ago daga pillow tana kallan Shukura.

“ Aunty Shukura?”
. 

“ Yes Sleepy Princess , baccin ya isa haka 
”


“ Haba Aunty Shukura ‘karfe nawa? Gari ko haske ma bai gama yi ba . 

“ Ai gwanda tun yanzu ki wartsake , Mamy da Baffa zasu tafi , idan baki sauko kunyi sallama ba , wallahi zasu tafi kina nan kina bacci.”

Da d’an sauri Mimi ta tashi zaune tana fad’in “ Kamar ya?.”

Da mamaki Shukura ta tsaya tana kallanta “ Kina nufin Mamy da Baffa basu fad’a miki batun tafiyan su ba?”

“ Wai wana tafiya kike nufi ne dan Allah Aunty Shukura , na kasa fahimta abunda kike fad’a fa .”


“ Uhmmm ki sauko ‘kasa ai ßuna jiran ki, idan kika ‘kara 5 minutes zaki zo ki tarar sun tafi
.” Da sauri Shukura ta fita daga d’akin , sabida bataso ma Mimi ta cikata da tanbayoyi. 

Da sauri Mimi ta sauko daga kan gado, ta wuce toilet ta wanketa, cikin sauri ta saka takalmi ta sauko ‘kasa da sauri saurinta. 

A falon su ta tarar da akwati na medium guda biyu, amma babu kowa a cikin falon, cikin gudu gudu sauri sauri ta wuce falon su Mamy . 

A tsats tsaye ta tarar dasu suma sun shirya ßuna magana , daga bakin ‘kofa ta tsaya tana kallansu cikin mamaki, sabida gidin da tayi numfashinta yana fitowa cikin sauri har sai da ta d’an dafe ‘kirjinta. 

“Mamy
 Baffa
” ta kira su a hankali.

Mamy ce ta fara juyowa, tana ganin Mimin sai murmushin fuskarta ya ‘karu sosai. 
Da hannu tayi mata alamar tazo, hakan kuwa akai Mimi ta matso kusa da ita . 
Hannunta Mimi ta kama tana fad’in “ Mimi na kin tashi? Na d’auka ai sai munje tukunna za muyi waya . 

“ Mamy ina zakuje haka ? Naga har da akwati a waje? I don’t get it.”

“ Mimi tafiya ne zamuyi, shiyasa bamu fad’a miki ba , nasan halinki yanzu da mun fad’a miki jiya sai kice zaki bimu , kuma duka 1 week zamuyi, ba wani dad’ewa zamuyi ba .”


“ Amma dai atleast Mamy ai sai ku fad’amun , yanzu da Aunty Shukura bata zoba kenan shikenan tafiya zakuyi ku barni? Toh ya zanyi na zauna anan wajan?.”

‘Dan jan kumatunta Mamy tayi tana dariya “ Shikenan, sarkin shagwa’ba ai bamu so mu ‘boye miki, kawai dai wannan tunanin naki ne banaso kiyi tayi dan zamu tafi shiyasa kawai bamu fad’a miki ba. 

‘Dan turo baki Mimi tayi “ Amma dai da kun sani kun tashe ni
” ta ‘karasa maganar a shagwa’be. 

Murmushi Baffa yayi “ Yi ha’kuri ’yar Baffanta, ba wani dad’ewa zamu yi ba , nan da 1 week kawai zamu dawo kinji?”.

“ Toh yanzu Baffa ni d’aya zaki dinga bari a part d’in nan ? Aunty Shukura fa tana zuwa makaranta , kuma ba da wuri take dawowa ba , sai dai ni na dinga zama ni kad’ai 
 Dan Allah ku  tafi dani Baffa.”

Murmushi Baffa ya sake yi, yana zama akan kujera sannan yayi may nuni da ta zauna a kusa dashi. 
Zama Mimi tayi tana d’an turo bakinta da marairaice fuska , duk dan sabida Baffa ya yadda ta bisu. 

“ Mimi” ya kira sunanta. 

“ Naam” Baffa ta amsa masa .

“ Yanzu 1 week kawai zamuyi mu dawo , kamar yau ne ai , zanyi wa Daddyn ku ( Daddyn Zarah ) da kuma Uncle Bashir su turo miki Ameerah da Zarah sai ku dinga zama tare idan Shukura bata nan. And nasan zata dinga dawowa gıda , yanzu for your sake ma , ko Shukura?.”

Shukura da take tsaye kusa da Mamy ta jinjina masa kanta “ Insha Allah Baffa , zanyi ‘ko’karin haka kudai ku barmun amanarta kawai.”

“ Kai Aunty Shukura sai kace wata yarinya , har amanata za’a baki?”

“ Toh mece ce idan ba ita ba ?.”

Mimi ta bud’e baki za tayi magana Mamy ta furta “ Aa fa , wannan surutun naku bazai ‘kare ba , idan kuka soma magana , Indai kune, yanzu flight d’in mu ma sai mu ne mesa ma murasa . 

Ku tashi ku raka mu , idan yazo in kun dawo sai ku cigaba da maganar ku.”


“ Mamy ai nice zan kai ku, Mimi kam sai dai ta raka ku wajan mota tunda ina sauke ku zan wuce school kuma babu damar na tafi da ita ko na bata key tunda ba ‘kwarewa tayi ba
 ko zaki jira har mu gama lectures sai mu dawo tare ?”.

“ By which time zaku gama lectures d’in.?”.

“ As always 6pm
”

“ No am not going
” Mimi ta fad’a da sauri har sai da ta sa dukan su dariya, haka dai suka tashi suka fito, already an saka akwatin su a cikin mota , idi driver ya matso da motar dai dai part d’in su. 
After the rungume rungume da akai , Mimi kamar za tayi kuka , haka aka lalla’bata suka tafi, ita kuma ta koma cikin part d’in su, tana feeling more and more lonely ganin kowa ya tafi sai ita kad’ai apart d’in. 

Daga kan kujera ta kwanta , tana kallan center d’in falon. Ita kanta batasan me take tunani ba . 

Wajan 2 bayan ta yi sallah ta sake saukowa Hauwa kulu ta zo wajanta tana fad’in “ Aunty Mimi, nayi abinci amma bansan me zaki ci ba, shiyasa kuma lokacin naga kin shiga d’aki najira baki fito ba , akwai abunda za’a girka miki? Ko kuma Aunty Shukura ?”. 

‘Dan ya’ke Mimi tayi mata, sabida yadda yayi losing appetite d’inta yanzu bata tunanin akwai abund zata iya ci kuma “ No Hauwa kulu karki , tunda already kin girka muku abunda zakuci it’s fine, idan Aunty Shukura ta dawo if tana bu’katar wani abu, she will let you guys know , kunji.”

“ Toh Aunty Mimi
 Sai anjima”

Murmushi Mimi tayi mata , ba tare da ta kuma cewa komai ba . 

Daman fita za tayi compound, ada idan ta fito part d’in su Zarah take soma zuwa amma a yanzu sai taji tana san zuwa part d’in su Ameerah. 

Tana shiga kuwa ta tarar da Mama da Ameerah suna hira, ganin Mimi da sukai duk murmushin su ya ‘kara fad’ad’a . 

“ A’a sai yanzu ake ganin ku? Ko Mimi?”

‘Karamun dariya Mimi tayi “ Tuba nake Mama 
”

“ Ai banma ga laifin ki ba Mimi ke da baki da lafiya , ya jiki? Mimi sunyi tafiyar su , sun bar autar su a gida , tunda basa so mu muna so, daman ina da shirin zuwa ai in tafi dake..”


“ Mama ai gwanda da kika fad’a mata haka , na tabbata da badan su Mamy da suka tafi ba , Mama yau ba zaki ganta a part d’in nan ba .”Ameerah ce tayi magana 

Harararta Mimi tayi “ Ina ruwan ki? Ba dake fa ake hirar nan ba.”

“ Eh koma dai me zaki ce naji d’in ki fad’a amma sai nayi magana haka kawai a’ki bari nayi magana .”

“ Allah ya shirye ki Ameerah , Mama tayi magana tana tsaye , wannan surutun naki , zan ga ranar denawarsa.”

“ Yo Mama nida baki na?.”

“ Ni kike cewa ke da bakin ki?.” Mama tayi kamar zata kawo mata bugu, ita kuma tayi saurin mi’kewa a wajan tana dariya, a haka Mama ta bar musu falon , ita kuma Ameerah tazo ya zauna a kusa da ita tana fad’in “ Yan mata how far , ko har kin soma missing d’in Mamy da Baffa?”.


“ Yeah Ameerah ! I little bit amma
.”


“ Hmmm kedai ki fad’a mun gaskiya fuskar ki bai nuna kina missing d’in su ba , but something something ko nace someone else 
 dai .”

“hmmm Ameerah kenan, someone else like who?”.


‘Dan kallan falon su Ameerah tayi , ganin babu kowa ta d’an ‘Kara ‘kasa da muryarta “ Like Uncle Moh
”

Da sauri Mimi ta d’auke kanta tana fad’in “ You’re not serous
.” 


“ No Mimi it’s not like that , wallahi dagaske nake miki. 

I notice you fa , kina yawan duba wayar ki, and the way yadda kike shirun nan, ba kamar yadda kika saba ba.”


‘Dan basarwa Mimi tayi tana fad’in “ Nope it’s not like that , may be dai wani abun ne but me yasa zanyi missing d’insa? Uncle Moh d’in? Please kima bari.”

“ Mimi wai kin san me? Wallahi tallahi kinyi missing Uncle Moh , kema kuma kinsan da hakan , kawai kina ‘boyewa ne and ni banga dalilin da yasa zaki ‘boye bama , it’s normal da kin damu dashi .

Mimi wai san Uncle Moh Kike? Please tell me mana.”


“ Ameerah please ki bar maganar nan idan ba so kike na tashi nayi tafiya na ba .”

“ Hmm shikenan nayi shiru tunda dai bakyason maganar 
. So yanzu ya zakiyi da bacci ko zaki dawo nan da kwana ?”.

“ Nope Baffa yace mun wai ke da Zarah zaku dawo part d’in mu kafin su dawo , sabida kar a bar part d’in Empty haka .”

“ Eh toh kuma haka ne , kunyi magana da Zarah ne ? Ko ita ba zata kwana ba?.”

“ Nope bamuyi ba . Daga part d’in mu nan nazo , ko zaki zo muje can ne?”.

Girgiza mata kai Ameerah tayi “ No Mimi, kidai je ki dawo?”.


“ Kamar ya ko kunyi fad’a ne da Zarah?”

“ Wallahi ko d’aya Mimi , yau dai kawai , I just feel like not going shiyasa banje ba , badan wani abu ba , you know me ai , ko fad’a mukai am not afraid I will tell you, ke dai in zakije kije kawai , anjima kad’an zaki ganni part d’in ku inyaso ku dinner sai muyi tare ko ya kika ce?”.


“ Thank you so much Ameerah
” 

Tsaki kad’an Ameerah tayi “ Mtsww ai kuma sai kiyi tayi 
”


Bayan murmushi da Mimi tayi bata kuma cewa komai ba ta fito daga part d’in su Ameerahn. 

Sau d’aya ta kalli part d’in Moh, ta d’auke kanta, ta nufi part d’in su Zarah. 

Babu komai a cikin falon , sai tayi tunanin ko Zarah tana d’akinta , shiyasa ta nufi d’akin. 

Kafin ta ‘karaso, sai ta soma jin kamar magana ‘kasa ‘kasa , bata kawo komai ba ta cigaba da nufa hanyar d’akin Zarahn.

Sai dai da more tana kusanto d’akin, the more take jin muryar yana ‘kara sama, ga wani mixed feeling da take ji cikin zuciyarta , wanda ita kanta batasan ko na mene ne ba.

Tana zuwa ‘kafar d’akin, har ta saka hannu zata murd’a handle d’in , karaf muryar Zarah ya sauka a kunnanta lokacin da take cewa “ Wallahi Mommy bakisan yadda na tsani Mimi ba yanzu. 

Duk yadda naso nayi pretending amma yanzu  abun yana so yafi ‘karfi. 

Banda mu ba wallahi ko yau ta mutu, idan har zan aura Moh d’ina.” Wannan maganar da take fad’a ne yasa Mimi tayi saurin d’auke hannunta da ya soma rawa babu shiri. 

Bama hannunta kad’ai ba , ga baki d’aya jikinta rawa yake , har tana ‘ko’karin loosing balance d’inta , sabida wani jiri da ta soma ji yana ‘ko’karin kifar da ita. 


Batasan ya akai hawaye ya soma saukowa akan fuskarta ba , ita dai kawai taji kanta yana mata nauyi ne , ga wani azababban ciwan kai da ya soma saukar mata , lokaci d’aya . 

Tama manta a inda take, sai kawai ta jinjina da ‘kofar , hannunta ya bigi handle d’in hakan yasa ‘kofar ta bud’e saura kad’an Mimi ta fad’i ‘kasa . 

Sabida cin karo da Mommy da Zarah da tayi . Suma d’in a d’an firgice suka kalleta, dan daga yanayin face d’in ta da suka gani, sun gane taji abunda suke cewa .

Mommy za tayi magana Mimi tayi saurin janyo ‘kofar ta rufe , a garin gudu saura kad’an ta kifa akan staircase d’in wajan. 

Suma da sauri sukai ‘ko’karin bud’e ’kofar amma ina har ta sauka ‘kasa . 

A tsorace cikin kuka Zarah take faman ‘kwalla kiran Mimi ! Mimi
 Amma ina Mimi ko juyowa ba tayi, hawaye sauko mata kawai yake a fuska d’aya na bin d’aya , hannunta kuma guda d’aya gashi ta dafe kanta dashi. 
Jikin ta gaba d’aya rawa yake , numfashinta kuma da wani irin sauri yake fitowa . 


A d’an tsorace Zarah kuma ambatan sunanta “ Mimi.” Sai dai ba da ‘karfi tayi maganar ba sabida Mimi ta riga ta fito daga part d’in su  kuma ba zata so kowa ya fahimci abunda yake faruwa ba . 

Mimi kuwa tana tafiya , maganar zarah yana sake dawowa mata kamar a lokacin ne take fad’an su ma . “ WALLAHI BAN SAN YADDA NA TSANI MIMI BA SAI YANZU 
” ji take muryar Zarah yana dakar mata kunne. 

Sai kuma maganar da take cewa “ BANDA MU BA WALLAHI KO YAU TA MUTU, IDAN HAR ZAN AURI MOH ‘DINA.”

Cikin sauri Mimi ta rufe bakinta, da hannuwanta tana ‘ko’karin hana kukan da yake san kubuce mata . 

A hankali  ta furta “ Ya Allah
” Lokacin da take shiga part d’in su. 

Bata tsaya ‘bata lokaci ba ta wuce bedroom d’inta , sannan ta sawa ‘kofar lock.

Ko zama Mimi ta kasayi sabida rawa da jikinta yake , ga baki d’aya hankalinta ya riga da ya tashi. Wani irin bum bum taji zuciyarta yana mata . 

“ Uncle Moh? Uncle Moh ! Uncle Moh shine Moh d’in Zarah? Daman Uncle Moh soyayya suke da Zarah har take cewa gwanda na mutu ? Zarah why ? Me nayi miki haka da zafi haka? All this love ? All this care and friendship duk na ‘karya ne kike mun daman?.

Zarah me nayi miki haka kike mun fatan mutuwa ? Sabida soyayya ? Soyayyar ma ta Uncle Moh?.”

Kawai sai taji kamar lokacin na Zarah take cewa “ Moh d’ina
”

Zamewa ‘kasa Mimi tayi , tana had’a gwiwar ‘kafarta waje d’aya, wani kuka da batasan asalin ko na mene ne ba , yana zuwan mata sosai da sosai , kuma dagasken kukan take , muryarta har ya soma dusashewa, ga wani irin suya da taji ‘kirjinta shima yana yi mata. 

Sai da tayi kuka sosai, muryarta ya riga ya gama sha’kewa tukunna ta soma magana a hankali cikin rauni. 
“ Kenan komai ‘Karya ne , all the love Zarah duk bana gaskiya bane ? Bakya ‘kaunata ko kad’an? All the Besty stuff, all the I love you part it’s a lie haba mana Zarah. Why . Why why
” sai kuma ta ‘bata fuska
.


“ Kenan shiyasa baizo ya dubani ba kuma me kira ni ba sabida ni bayaso na ko? Hmmm
”  ta d’an goge hawayenta duk da wani na bin wani. Sai kawai ta sake saka wani kukan. 



PART DIN SU ZARAH

A part d’in su Zarah kuwa , babu abunda Mommy da Zarah suke sai safa da Marwa a cikin bedroom d’in Mommy. 

Kana kallan fuskar su zakaga zallan tashin hankali ne kwance . 

Zarah sai kuka take kamar wacce aka yanka. 

“ Mommy yanzu yaya zamuyi tunda taji abunda nake cewa ko zata je ta tona mana asiri ne? Mommy
”

Shiru Mommy tayi mata , bata ce mata komai ba hakan yasa ta kuma cewa “ MOMMY
”

Tsawa Mommy ta dakata mata “yi mun shiru Zarah , da ace bakya wannan surutun da haukan nan
naki zata ji abunda kike cewa ne? Kiyi mun shiru , yau yau d’innan zan samo mafita ba wai sai gobe ba , Allah ya tsare ni ‘karamar yarinya ta tona mun asiri, wallahi ko uwar ta bata haifa ba . Zo kiji..”

Da sauri Zarah ta matsa kusa da Mommy , wani magana Mommy ta rad’a mata, a d’an tsorace take kallan Mommy “ Mommy anya wannan beyi risk da yawa ba kuwa? Kin tabbata babu wani abu idan mukai haka?”

Tsaki Mommy tayi “ Ban sani ba Zarah , kinji nace bansani ba , ki fita daga ido na wallahi kinji na rantse miki
”

“Mommy
.” 

“ Zanci Ubanki Zarah wallahi . Zanci ubanki kinji na gaya miki.”


________
A d’akin Mimi kuwa sai wajan la’asar ta dena kukan da take , idanuwanta har sunyi luhu luhu abunka da me kyawun ido. 

A gaban mirror ta tsaya tana ‘karewa fuskarta kallo sai kuwa ta share hawayenta, tana fad’in “ Look at you Mimi, yaushe har kika damu da wanda bai damu dake ba uhm?. 

Haka kika damu dashi Mimi? Why bayan bama take yake ba?”. 

Ita kad’ai ta gama surutunta a gaban mirror , sannan tayi alwala tayi sallah , akan daddumar ta kwanta, lokacin da taji saban kuka yana zuwan mata. 

A kwancen ta soma kukanta, har bacci ya d’auketa




___ Sai after Magrib tukunna ta farka daga baccin da take , tana kallan time taga 7 har ya wuce , da sauri ta tashi, dan har kanta ya soma ciwo ma. 

Sallah tayi tukunna tayi wanka, ta saka simple dress . 

Tasan anymoment from now Zarah ko Ameerah wani daga cikin su zai iya zuwa nan, and she’s not ready to face anything or anyone for now
 .

Hijab d’in sallah d’inta ta d’auka , tayi sauri ta fito daga d’akin, Allah ya taimaka babu kowa a falo, cikin sauri ta fice , tasan waje d’aya ne kawai zata iya kasancewa  safe duk da a yanzu tana ganin bai kamata ta dinga shiga ciki ba , amma bata da choice sai da tayi wa kanta al’kawari from now har zuwa lokacin da abun nan zai fita daga kanta zata ko’karin tai avoiding zuwa. 

Tana shiga part d’in sai taji kuma yayi mata wani iri ba kamar yadda ya saba shiga ciki ba 
. 

At first zuciyarta har ya soma bata kawai ta koma amma kuma batasan me Mommy da Zarah suke ciki ba , d’an juyawa tayi zata d’auki phone d’inta , sai taga babu wayan ma ga baki d’aya, a time d’in ne ta nuna , tana gefen bed d’in d’akinta. 

Gashi she’s not a fan of watching movie , kuma bata da wani mood d’in kallo d’in ma safe


Haka ta zauna , ba uhm ba uhm uhm ita kad’ai , har ta daidai tu time d’in sallar isha’i tayi sallahr ta , sannan ta kwantar da kanta a gefen kujera tana lumshe idanuwanta kamar me bacci, amma kuma ba bacci take yi ba. 

Tunanin da yake zuciyarta take ‘ko’karin avoiding ga baki d’aya . 

Tana zaune a wajan har 9 tasan a wannan time d’in ko kowa bai nemeta ba toh Ameerah zata neme ta gashi bata taho da wayanta nan d’in ba. 

Tana cikin wannan tunanin kawai taji diffffff abunda bata ta’ba gani ba , a iya zuwa part d’in nan da take wato wutar part d’in ta d’auke ga baki d’aya, babu haske ko guda d’aya, haka kuma babu abunda zata kunna taga haske , ita d’aya a cikin wannan building d’in.

A d’an tsorace ta mi’ke tsaye, tana dafe dafe ko zata samu hanyar wucewa ta bar wajan amma babu abun dafawa sai kawai taji zuciyarta ta yanke ta fad’i wani tsoran ya sake shigarta , babu yadda za tayi sai dai ta samu bayan kujera guda d’aya ta raku’be jikinta , tana jiran lokacin da wutar zai gyaru ita kuma a lokacin sai ta samu damar ficewa daga part d’in. 

Sai dai har 30minutes tayi babu wuta babu alamar wuta, ita kunnanta ma har motsi ya soma jiyo mata a falon, bata ßanı ba ko dan tana tsorace ne take jin wannan yanayin oho
.

Bayan kamar 20 minutes ta soma
ji kamar taku, ai kuwa da sauri ta mi’ke zata bar wajan, taji an ri’ko hannunta, a razane ta bud’e bakin da Allah yayi mata zata kwarara ihu taji wani d’umi a bakinta . 

Kafin ta ankare kuma anyi sama da ita . 

Da sauri ta soma kokawar ‘kwacewa amma ta kasa sai ma ji da tayi an ‘kara matse ta , abunda ta soma
ji a hancinta ne yasa zuciyarta bugawa da ‘karfi duk da tana ‘ko’karin ‘kin yadda da abunda take ji d’in. 

Tayi tayi ta ‘kwace kanta ta kasa, har hannuwanta take so ta ‘kwace amma ta sabida yadda aka ri’ke mata hannuwa ga baki d’aya ana tafiya da ita kuma taji kamar stairs suke haka, batasan lokacin da ta san kuka ba duk da kukan baya fita sosai sabida bakinta da yake haka ya cigaba da tafiya da ita , har zuwa d’akin da yake saman. 

Tana ji lokacin da aka rufo ‘kofar d’akin, aka cigaba da tafiya da ita , ba zata babu tsammani aka ajjeta akan bed amma kuma ba’a sakar mata baki ba . Sai agogon hannunsa da ya d’anyi haske , a haka ya kai d’aya hannun ya danna button, ita kuma ta samu damar ‘kwace hannunta .

Da iya ‘karfinta ta daddage tana so ta turesa amma ko gezau kamar babu abunda tayi, ganin hakan yasa ta saka both hannuwanta tanasan ‘kwace bakinta amma ya had’a duka hannayen guda biyu zuwa sama, ya ri’ke su da hannu d’aya, both kafafuwanta ya ri’ke su da dashi ‘kafar, d’aya hannunsa dai dai stomach d’inta da yake d’an shafawa kad’an. 

Ita dai kuka kawai take da iya ragowar muryar da Allah yayi mata.

Booom sai light ya dawo, karaf idanuwansu ya had’u a cikin na zuwa , kuma har time d’in bakın ßu yana waje d’aya ya’ki bata damar sakin bakin. 

Tana ganinsa hawayen idanuwanta ya ‘karu sosai, ta soma kokawar ‘kwace jikinta , tana rufe idanuwanta amma sai da ya ‘kara mintuna uku a haka tukunna ya zare bakinsa yana kallanta . 

Ita kuma ta juyar da kanta gefe tana kuka. 

‘Daya hannunsa ya saka yana juyo da fuskarta , amma ta’ki yadda ta kallesa ma sai idanuwanta da ta runtse sosai .

Fuskarsa ya kawo dai dai saitin wuyanta , ya d’an hura mata iska kad’an har sai da ta motsar da wuyan sabida wani irin abun da taji a wajan. 

Cikin husky voice d’insa ya furta “ Are you angry?”. 

Mimi ta’ki kulasa , tana ‘kara juyar da kanta gefe sosai , yanzu da ya tashi juyo da face d’inta ri’ke da yayi a cikin hannunsa , ya’ki bata damar d’auke face d’in “ Say something
” ya kuma maganar kamar me rad’a. 

Cikin kuka ta furta “ Nidai ka sake ni
”.

“ Then look at me!” Yayi maganar cikin cool voice har sai da ta d’an sauke ajiyar . 

Sai kuma ta’ki kallan nasa , shi kuma ya matso da face d’insa dai dai tata sosai , zaiyi kissing ta kallesa , batasan lokacin da ta hararesa ba hakan yasa ya d’an murmusa gefen lips d’insa kad’an yana sakin hannunta .

Ta yun’kura zata mi’ke ta bar masa wajan, shi kuma ya d’agata ga baki d’ayanta ya d’orata akan cinyarsa
..


_________________

To be continued
 đŸ”„


Aysha Galadima đŸ€đŸż
( Black Queen) 
***


***