Page 38
MISHAL
By AYSHA GALADIMAđ€đż
***
BOOK 1
Page 38
Hannayenta biyu tasa tana dâan tura kafadâan sa a hankali â Uncle Moh please ka sauke niâŠâ cikin rawar murya tayi maganar , hawayen da suka cika idanuwanta suna saukowa akan kumatun ta.
Baice mata komai ba sai finger dâinsa, da yasa ya dâan goge hawayen , idanuwansa ga baki dâaya akan fuskarta.
â Meyasa kike kuka ?â Yayi maganar cikin âkasan maâkoshi.
Ji tayi wani kukan yanaso ya taho mata, amma sai iya âkoâkarin mayar dashi take, ta hanyar sauke ajiyar zuciya, shiyasa âkirjinta yake sama , yana âkasa da sauri.
Ganin bashi da niyar sakinta ta dâan zabura da sauri zata miâke ya sake mayar da ita, fuskarsa babu faraâa ya furta â Keeee?.â Take Moh ya dawo original Uncle Moh dâinsa , babu faraâa kwata kwata.
Hakan yasa ta nutsu, ta dena âkoâkarin âkwace kanta da take yi.
â Good , so now tell me , kukan me kike?â.
Shiru tayi tana tunani, sai maganar Zarah ya sake dawo mata cikin kai, dâan taâbe baki tayi kadâan tana girgiza masa kai, babu abunda akai mun..â
âKarki bari na sake maimaita maganar da nayi mikiâŠ.â
â Dagaske Uncle Moh, babu abunda akai mun?â.
Hannunsa dâaya ya saka ya dâan ja hancinta, hakan yasa ta dâanyi murmushi kadâan tana san juyar da kanta amma yaâki bata damar hakan.
Sai ya saka hannunsa ya dâora kanta akan kirjinsa, hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya me dâan âkarfi a fili.
Sai da ya bari tayi relax sosai tukunna ya dâan sunkuyo da kansa dai dai kunnenta , yadda ita kadâai ce zata ji abunda yace â Mimi if youâre angry , just say itâŠâŠ so now tell me , me kike âboyewa a zuciyar ki?â. Yadda yayı magana so calm, yasa ta dâan dâago ta kallesa , sai ya dâaga masa girarsa guda dâaya , sai ta koma yadda take tana fadâin â Uncle Moh?â.
â Uhmm âŠâ ya fadâa ba tare da ya kalleta ba.
â Meyasa bakazo ka duba ni ba?â.
â Am not in town MimiâŠâ
Kanta ta sake jinjinawa, sai kuma ta sake fadâin â Aunt Aya tace zaka kira ni, kuma baka kira ni ba.â
â Ba gashi nazo ba , ai shine kiran , ko kinaso na kira miki itane?â.
â Itama ai tunda ta tafi ban âkara ganinta ba, tace min zata dawo amma har yanzu bata dawo ba .â
Hannu yasa yaja hancinta, har sai da tace aushhh, hakan yasa ya dâanyi murmushi kadâan , ita kuma ta dâan turo lips dâinta .
â Sheâs back , gobe zaki ganta .â
Da mamaki ta furta â Gobe ? Dagaske?.â
â Ko bakyaso ki ganta?â.
â Inaso , babu kowa fa yanzu Mamy sun tafiya, Aunt Shukura tana zuwa school sai ni kadâai fa âŠ.. like an orphanâŠ..â
â Then youâre not⊠you have a whole family and also here iâam âŠâ
Za tayi magana, ya miâke tsaye da ita , a hannunsa babu yadda ta iya sai dai ta saâkala hannuwanta a wuyansa sabida kar ta fadâi.
A haka suka cigaba da tafiya , har ya sauko âkasa da ita.
Falon âkasan babu wani haske sosai, itâs so dummy haka, ya wuce da ita har wajan dinning.
Kan dinning dâin kuma an shiryasa da different dishes , sai faman tashin âkanshi yake âŠ.
Sakar baki tayi tana kallan dinning dâin, tana mamakin yadda akai dishes dâin sukazo, tunda tasan babu kowa a cikin part dâin.
A kan kujera ya zaunar da ita , shima kuma ya zauna yana dâan nuna mata abincin da idanuwa.
Sai a lokacin taji ta soma jin yunwa , dan tun kukan da tayi akan maganar su Zarah bata kuma Ćaka komai a bakinta ba sai yanzu da taga abincin tsohuwar yunwar da take ji ya tashi.
Da idanuwa ta soma bin dishes dâin, bata masan wanne za tayi serving ba , sabida duka high note dishes ne.
Farfesun cowtail ta dâan zuba masa a bowl, tana tunanin mene ne next abunda za tayi serving dâinsa , sabida akwai su fried rice , creamy pasta , steamed vegetables, fresh fruit platter da drinks har kala uku ma.
Creamy pasta ta zuba masa da steamed vegetables, sai fruit juice da ta saka masa a cup, wani dâan bowl dâin kuma tana ibar masa fruit platter din wajan.
Ita kuma ta zuba fried rice da kuma grilled chicken, sai drink kawai..
Har ta gama serving dâinsa bai ce komai ba , kuma bai ci abincin ba sai da ya gama serving nata ta zauna , sannan ya soma cin abincin nasa gentle as always .
Ita kuma duk da tana cikin damuwa kadâan haka ta dinga cin abincin sabida kar ya fahimci wani abu, duk da time to time idan ta âkurawa abincin ido tana âkara tunano maganganun Zarah da Mommy da har âkasan zuciyarta tana addua Allah yasa mafarki take bawai gaske bane .
Shi ya soma ajje spoon amma bai tashi ba , kuma bai mata magana ba , na kamar mintuna 5 ganin har time dâin bata gama cin abincin ba , kuma yadda take ci kamar me cin maganiâŠ
â Mimi ? Ya kira sunanta .
Da sauri ta furta â Uhm UhmâŠ.â
â Your foodâŠâ ya kuma fadâa ba tare da yayi acknowledging yadda ta dâan diri rice ba .
Cikin sauri ta kalli plate dâinsa ganin ya gama cin abinci , itama ta mayar da hankali kan ta, ga baki dâaya tunanin da take , ta ajjesa a gefe , haka ta dinga tura abincin , har sai da taji zata yi amai tukunna ta haâkura ta dâan sha lemo amma taci abincin sosai yadda ya kamata.
Tana gamawa ta miâke zata tattara wajan, sai ta dâan tsinkayi muryarsa cikin low voice â Leave it there .â
Jiyowa tayi ta kallesa kamar bata gane me yake nufi ba , alamar tana neman âkarin bayani.
Shi kuma wayarsa da take kan dinning ya dâauka ya miâke , sannan ya riâko hannunta suka dawo falo.
Akan kujera ya zauna , hakan yasa itama ta zauna tunda hannunta yana cikin nasa .
Sai da suka zauna su duka tukunna ya dâan same hannunta daga nashi , bai ce mata komai ba , kuma bai sake riâke hannunta ba illa ma dâan matsawa ma da yayi kadâan , yadda zata fi sake wa .
After a long minutes of silent Mimi ta kallesa ganin idanuwansa a rufe , so take ta tanbayesa amma kuma tana tsoran yi masa tanbaya kar ya fahimce ta ba dai dai ba shiyasa ta dâan tsaya âkarewa face dâinsa kallo .
Tayi nisa a kallan fuskarsa ya budâe ido, karaf idanuwansu ya shiga na juna , kuma ta kasa janye idanuwanta daga nashin kamar yadda shima dâin bai dâauke idanuwansa ba .
Daga baya kuma taji idanuwanta na rawa sabida wani irin abu da take hangowa a cikin nasa idan wanda yasa mata jin tsoro da batasan ko na mene ne ba .
âKaramun smirk yayi , hakan yasa tayi saurin dâauke nata idon, tana juya tanbayoyin da suke zuciyarta , ba tare da tasan yadda zata yi masa su ba .
âAsked what you want to askedâŠ.â
Yayi mata magana ba tare da ya kalleta ba .
â Uncle Moh me⊠me .. me ..â sai tayi shiru ta kasa âkarasawa.
Sai da yace â Uhm?â. Tukunna ta samu courage dâin cewa â Meyasa kake kissing dâina ko kasani a cinyar ka , bayan babu kyau? Kuma Allah ya hana.â
â Are you asking me Mimi, or are you asking me to kiss you again?â.
â No Uncle Moh , am just askingâŠâ ta âkarasa a hankali.
â Then asked me in a proper wayâŠâ
Shiru Mimi tayi, bata fahimce sa ba and ba ta fahimci yadda zata tanbayesa in a proper way ba .
Tun daga nan tasan she can never asked him about Zarah ko kuma abunda su Zarah suka ce akanta , and beside that batasan yanke hukunci cikin sauri tunda har yanzu batasan actual dalilin su nayin haka ba .
Kallan time Moh yayi , dare yayi sosai and takasan cewa komai.
Finger dâinsa dâaya yasa ya taâba goshin ta ita kuma ta dâago kai ta kallesa da sauri.
Da hannu ya nuna mata upstairs â Dare yayi , go and sleep MimiâŠâ
Cikin sauri ta jinjina masa kai sabida daman tana san komawa dâaki, daga lokacin da tace masa â Good night ..â zaka fahimci cikin excitement tayi maganar , har saida ya dâago ya kalleta .
Bata kalli hanyar sama ba , âkofar fita take kalla , dan duk tunaninta dâakinta yake nufi , ganin zata wuce ya kuma fadâin â Mimi?.â
Kallansa tayi tana fadâin â Naam Uncle MohâŠâ
âHaka nace ki kwanta a dâaki na .â
Zaro ido Mimi tayi zata yi magana , yayi mata wani irin kallo , babu shiri ta hadâiye maganarta . Simi simi ta wuce saman, tana shiga dâakinsa ta soma safa da marwa tana tunanin yaya zaâayi tayi bacci a cikin dâakin bayan dâakinsa ne .
Idan kuma ta kwanta a dâakin shi kuma an ina zai kwanta?. Ga baki dâaya taji ta kasa samun nutsuwa a tattare da ita , tana cikin safa da marwa dâin nan , Joy da tun dâazu take kallanta , ta fito sosai yadda zata ganta .
â Wannan kai da kawowar da kike na mene ne? Ko kina tunanin zai miki wani abu ne ?â.
Da sauri Mimi ta juyo ta kalli Joy. Tsawan sati bata Ćaka ta a cikin idanuwanta ba sai yanzu . â Haba Joy sai yanzu zan ganki? Kusan sati dâaya kin âki zuwa ko nayi miki wani abu ne kike fushi?â.
â No Mimi ba haka bane , dole ne yasa baki ganni ba , ba dan na so ba amma gashi yanzu kin ganni⊠kai kawon me kike haka?.â
â Joy taya zan kwana a dâakin Uncle Moh? Ni ga baki dâaya ma wani iri nake ji sai naji kamar an canza sa ne , not exactly kamar yadda na san Uncle Moh, ada ko kallo na ba yayi , and ba zai taâba riâke hannu na ba , amma yanzu fa ? He can even kiss me , kuma na fadâa masa babu kyau babu kyau , amma kamar baya fahimta na kwata kwata .
Ya zanyi Joy?â.
â HhhhhhâŠâ Joy ta dâanyi dariya har sai da Mimi ta dâan âbata fuska.
Hannunta Joy ta kama ta zaunar da ita akan dâaya daga cikin kujerun da suke wajan, amma ita bata zauna ba , tana dai kallan Mimi har lokacin.
â Mimi wani lokaci bada zahiri ake an fani ba wajan fahimtar abu.
Wani lokaci da zuciya da âkwaâkwalwa ake anfaniâŠ.. ki zauna kiyi tunani , wane ne shi, meyasa yake haka, kuma taya zaki gane maâanar hakan .
Karki bari tsoron da take zuciyar ki yayi galaba a rayuwar ki Mimi.
Wani lokaci tsoro makami ne , idan kika juyasa ta zama makami.
Wani lokaci tsoran ki zai iya fadâar da ke idan har baki yi yaâki dashi ba.
Akwai lokacin da tsoro yake da mahimmanci , akwai kuma lokacin da fuskantar wannan tsoran shine abu na farko da zai canza maka rayuwar ka ga baki dâaya , Ciki kuma har da tunanin da kike akan ZarahâŠâ
Sosai Mimi ta kalli Joy, duk da batayi mamakin yadda tasan abun Zarah ba , sai dai maganar yazo mata unexpected, hakan yasa ta furta â Joy me kike nufi?â.
â Mimi bani da hurumin fadâa miki wannan maganar kiyi haâkuri, ki zauna dai kiyi tunani sosai , kuma ki fahimci abunda ya kamata ki fahimta , ki ajje soyayyar kowa a gefe ki fahimci ainahin abunda yake zuciyar kowa kafin ki sakar musu zuciyar ki MimiâŠ
Ki zama mai kafin tunani, me basira , me kula sosai da abu, koda wannan abun ya kasance âkanâkani ne MimiâŠ
Bani da lokaci sosai Mimi , ki samu ki huta , tunda yace miki ki kwanta kiyi bacci, ya kamata ki kwanta , karki makara, kuma kiyi âkoâkarin goge tunanin da suke zuciyar ki , ki bar komai a muhallin da ya dace kinji?.â
Cikin sauri Mimi ta budâe baki za tayi mata magana , amma Joy ta âbace ba tare da tabata wannan chance dâin ba.
Fuskar Mimi kamar za tayi kuka sabida tafiyar Joy.
âDan shiru tayi tana tunanin maganganun Joy, so take ta fahimci me Joy take nufi , amma ta kasa sai ma ciwan kai da taji kanta ya soma , dan dole ta ajje komai, ta kwanta a kan kujerar , kafin kace wani abu bacci ya dâauketa .
1 and half hours later ya shigo dâakin ganin tana bacci akan kujera , sai ya kalli bed dâin, sannan ya kalleta .
Baice komai ba yazo ya dâauketa daga kan kujerar ya kwantar da ita akan bed , ya lulluâba mata duvet , ya kashe mata hasken dâakin sannan ya sake fita daga dâakin.
WASHE GARI
Washe garı , âkaran kiran sallah ne ya soma tashin ta . Da fari bata motsa ba sai da kiran ya soma tashi a karo na biyu tukunna, ta dâan motsa tana dalilin wayarta , ganin bata taâbo wayar ba , ta soma miâka da hamma, tana miâkewa zaune.
Hannu ta saka tana muntsike idanuwanta, kafin ta budâe su ga baki dâaya .
Kallan dâakin da take ciki tayi da idanuwanta masu bacci cike da mamaki.
âKara sa hannu tayi tana shafa idanuwanta , tana âkara bin dâakin da kallo ganin inda take .
âDakin tane . Yes dâakinta ne dai nata da yake part dâin Mamy kuma akan gadon ta bayan tasan ba anan ta kwanta ba jiya.
Mamakin hanakan yasa baccin da yake fuskarta dâaukewa ga baki dâaya tana âkara kallan dâakin da kallo, har sa da taji kamar lokacin sallah yana âkoâkarin wuce ta , tukunna ta wuce toilet tayi alwala, tazo tayi sallah , Azkar da kuma karatun al-qurâani.
Ta gama da kamar mintuna 15, aka dâanyi knocking âkofar dâakin.
Kallan âkofar tayi , kafin ta yunâkura aka sake âkwanâkwasa âkofar.
Cire hijab dâinta tayi, ta nufi âkofar , tana budâewa wacce ta gani ya sata tsayawa so speechless , ta ma rasa wana reaction za tayiâŠ.
Murmushi Aya da take bakin âkofa tayi, tana kallanta â Na koma ? Ko bakyasan gani na .â
Mimi batasan lokacin da tayi murmushi ba tana fadâin â Aunt Aya ?â
Hannuwanta biyu Aunt Aya ta budâe mata ta murmushi , babu musu Mimi ta matso kusa da ita tana hugging dâinta â Daman dagaske zaki dawo?â.
âDago da ita Aya tayi tana kallan fuskarta âHow can i leave you Little Mimi?â.
â I thought ba zaki dawo ba fa , all this days.â
â And here Iâm. Can i ?â Aya ta nuna dâakin Mimi da hannu, cikin murmushin da har yanzu bai fita daga fuskarta ba ta furta â Why not âŠâ ta matsa mata hanya ta shiga.
Babu musu Aya ta shiga tana fadâin â Itâs been long, but i missed you terrible! Little Mimi.â
â So ki zauna anan kar ki bari Uncle Alameen ya âkara tafiya da ke âŠâ
Jiyowa Aya tayi tana kallanta â That man? Na gaji dashi, heâs so annoying atimes, i wonder yadda budurwarsa za tayi controlling dâinsaâŠâ
âHmmm âŠâ Kawai Mimi tace sabida batasan me zata ce mata next ba , sabida ba wai zama suke suyi hira sosai ba , tunda .
Ganin tayi shirun ne yasa Aya ta furta â Oh yeah ! Ameerah tana âkasa tana shirya mana breakfast, nima yanzu nazo na dubaki ne, banasan barinta ita kadâai a âkasa .â
â Ameerah ?â Mimi ta tanbaya da mamaki.
â Yeah Ameerah ! Jiya Moh Moh ya dâauke ki, so tayi bacci a dâakina , tace ta kira ki baki picking call dâin.â
â So Aunt Aya , youâre here since yesterday?.â
â Yeah ! Tun kafin Alameen yayi disconnecting wutar gidan âŠ.â Aya tayi maganar tana kashe mata ido dâaya.
Da mamaki Mimi ta furta â But why?â.
âDan murmushi Aya tayi tana nufar âkofa â You can ask him your self ⊠for now kiyi sauri kiyi wanka ki sauko âkasa , Ameerah is looking for you âŠâ daga nan ta fice daga dâakin ba tare da ta waiwayo ba .
Bin âkofar tayi da kallo, a tunaninta jiya wutar ce ta samu matsala , not knowing Alameen ne yayi disconnecting dâinta , and she have no right to asked him why , hakan yasa ta ajje tunanin nan , ta wuce toilet dan tayi wanka .
Bata dadâe sosai ba , ta fito ta shirya cikin âkananan kaya , but kayan basu kamata ba , sai ta saka hula akanta , ta dâauki wayarta zuwa âkasa .
Tana jiyo muryar Ameerah a kitchen suna hira , ta nufi haryar kitchen dâin kenan tajiyo muryar Shukura da ita fitowarta kenan, ta shigar cikin maroon dâin abaya alamar fita za tayi.
â Mimi?.â
Kallanta Mimi tayi tana fadâin â Naam Aunt Shukura ? Ina kwana?â
â Lafiya âKalau Mimi , Sorry jiya kinyi bacci da wuri na dawo late and Aya tace mun kina dâaki kina bacci, and kuma banaso na tashe ki a baccin shiyasa .
How are you? Hope youâre not lonely?â.
â Hmm A little bit Aunty Shukura , kinyi waya da Baffa ko Mamy? Bana samun number dâin su.â
â Nima bana samun su, but Baffa ya turo mun message yace there fine , idan sun kammala abunda suke zamu ji su , and they even asked me to greet you for them.â
â But Aunt Shukura dagaske sai sunyi week dâin nan kafin su dawo? Har na soma jin part dâin nan baya dadâi wallahi tun tafiyar su.â
â Toh ya muyi Mimi? 1 week kamar yau ne , if your lonely you can go out with Aya since sheâs back , ga kuma Zarah da Ameerah nasan zasu dâebe miki kewa , you wonât be lonely for long.â
âKaramun yaâke kawai Mimi taji mata jin ta ambaci sunan Zarah , batasan jan maganar sosai shiyasa ta canza maganar zuwa â Are you going out?â.
â Yeah Mimi , zanje school ne ..â
â Okay take care , nima school naga nan da 2 weeks zaâa koma , har na soma missing dâin gida ma wallahi , gasu Baffa basa nan atleast su zauna kullum na dinga ganin su.â
â Iye sannu dadâi gida, mu da muke zuwa school kullum baâa san mu kenan? Abeg karki sa na makara , su Aya ne a kitchen ko? Naji kamar muryarta.â
â Yeah sune , nima kitchen dâin zani fitowar ki ne ma ya dâan tsayar dani.â
â Okay muje kitchen dâin kafin na wuce.â
Daga nan suka wuce kitchen dâin tare âŠ.
Ameerah da Aya suna tsakiya da girki sai ga su MimiâŠ
â Chef Aya and Chef AmeerahâŠâ Mimi ta kanne musu ido guda dâaya.
Fari Ameerah tayi mata tana juya idanuwanta waje dâaya â Yes my lady, me kike buâkata?.â
â Anything Dear .â Mimi ta bata amsa , hakan yasa duka sukai dariya .
Ganin Shukura da dressing alamar zata fita Aya ta furta â Youâre going out?.â
Shukura ta jinjina mata kai ..
â Mun kusa gama breakfast , ki zauna kici kafin ki tafi mana?â.
â No Aya , thank you ! Yanzu ma na kusa makara ne , nace bari nazo mu gaisa kafin na tafi⊠Ameerah how far..â ta âkarasa tana mayar da kallanta kan Ameerah.
â Aunty Shukura ina kwana.â
âLafiya âkalau Chef dâin mu, am going out , see you all . Idan akwai abunda kuke so you can tell me sabida may be yau na dawo gida da wuri but am not sure .â
â See you Shukura , ina gida they wonât need anything, just take care of your studies okay? All the best.â Aya ce tayi maganar , hakan yasa Shukura ta jinjina mata kai, tana musu waving hannu kafin ta tafi.
Kitchen dâin yayi saura su uku.
â So now ladies , me zan taya ku dashi?â
â No Mimi , you donât need to worry your self , nida Ameerah ma mun isa , and weâre almost done , yanzu zamu gama babu wani aiki, kawai ki jira mu a falo, if youâre bored ki danna wayar ki or relaxed kadin mu fito.â
â But Aunt AyaâŠâ
Aya ta katse ta â No but Mimi .. just go.â
â Okay ..â Mimi ta fadâa tana komawa kan kujera.
Har ta shiga instagram, sai kiran Zarah ya shigo wayarta , kallan sunan kawai tayi ta cigaba da scrolling dâin IG dâinta.
A karo na biyu Zarah ta kuma kiranta, but nan dâin ma batai picking ba ta cigaba da harkar ga banta sai ga message dâin Zarah ya shigo wayarta â Mimi kizo inji Mommy.â
âDan shiru tayi tana nazarin maganar, taje ko kar taje.
80% na zuciyarta yana cewa kar taje while 20% yana cewa taje , tunda batasan me zata ce mata ba.
Wani kiran Zarahn ne ya sake shigowa , a wannan karan Mimi sai tayi disconnecting call dâin tayi relax tana cigaba da chart dâinta.
Ta manta ma da kiran Zarah , sai kawai ga Zarah ta shigo falon sim sim kamar wata mara gaskiya .
Sau dâaya Mimi ta kalleta ta dâauke idanta.
Ita kuma Zarah ta sauke wani ajiyar zuciya sai da ta kalli falon ta tarar da babu kowa a cikin sa sai su biyu tukunna ta âkaraso inda Mimi take a zaune.
âKaramun gyaran murya tayi, kafin ta furta â BestyâŠ.â
Wani irin kallon mamaki Mimi ta bita dashi, sai dai bata fito ta nuna mata ba , kawai dai sai yanzu ne ma ta soma mamakin audacity dâin Zarahn da har take iya biyo ta bayan abunda ta gama fadâa akanta.
â Besty âŠâ Zarah ta kuma kiranta tana dâan matsowa kusa da ita kadâan.
âKaramun murmushi Mimi tayi , ta ajje wayarta akan cinyarta sannan ta dâora both hannayenta akan âkirji tana kallan Zarahn da itama a yanzu ta âkura mata idanuwa sosai .
â Zarah kenan, itâs better ki ajje pretending dâin nan , this Besty stuff of yours I think ai lokaci yayi da ya kamata ki ajje su a gefe .
You can call me Mishal Or Mimi, any one.â
â Am not pretending Mimi , kinsan cewa bani da kamar ki , youâre my best friend, kawai abunda kika ji ba haka bane , baki fahimce ni ba kuma jiya ina ta kiran ki sabida nayi miki bayani amma kin ki tsayawa, and nazo har part dâin nan sabida na ganki anâki hanani ganin ki..
I think we can settle this, kuma zan iya miki bayani yadda zaki fahimta sosai, abunda kika ji ba haka bane , itâs just a slip of tongue.â
âDan lumshe ido Mimi tayi tana sake budâesu akan Zarahn.
â Zarah if youâre done please you can go, all your explanations bana buâkatar su and am not interested on them so , thank you , you can go now.â
â Haba Mimi wannan ai wulakanci ne , ina âkoâkarin yi miki bayani amma kamar korata kike .
Kinsan da gangan bazan cutar da ke ba and i will never do something similarly of that , kowa yana da secret dâinsa and i donât see why ma da jiya zaki hawo har wajan dâaki na bana nan, I never done that, da kika ga babu kowa wajan why not ki jira ni na sauko or something like that da duk hakan bata faru ba , but youâre here playing the victim.
Bayan ni ya kamata nayi haka , why please! Why ?â.
â So now Zarah idan na fahimce ki, youâre the victim here ? After all what you just said yesterday?.â
Ba tare da second though ba , Zarah ta furta â Yes ..â
Mamaki ne ya çıka Mimi , she never thought haka halin Zarah yake sai yau , yadda take magana , bama ta dâauka cewa tayi laifi sai ma ganin laifin ta da take gani sabida ta hawo saman dâakin su.
Idan zaâa ce mata Zarah can do that she will never believe that, ba zata taâba yadda ba ko wane ne ya fadâa mata, but gashi nan da kunnanta taji maganar Zarahn , and bata taâba kawo Zarah tana da hidden agenda ba irin wannan.
â Zarah you can go , if youâre done please.â
â Am not done Mimi, yanzu ma Mommy take kiran ki, na kira ki baki dâauka ba and na tura miki message shima baki bani reply ba atleast you can respect her as a mother , kije kiji abunda za tace.â
â Hmm okay muje.â Mimi ta miâke hakan yasa wani murmushi ya fito akan laâbâban Zarah da ya âki âboyuwa .
Zama su fita daga falon su Aya suka soma fitowa da abu a hannun su .
Ameerah ce ta kalli Zarah â Zarah yaushe kika shigo?â
âDan yaâke Zarahn tayi mata tana fadâin â Yanzun nan na shigo .â
â Okay to ki zauna muyi breakfast mana , mun gama .â
â No Ameerah Mommy ce take kiran mu, ki wari wani lokacin idan nazo.â
â Take kiran ku? Iya ku biyu kuma?â. Ameerah ta sake tanbaya .
â Yes..â itama Zarah ta bata amsa tana kallan Aya da ko inda take bata kalla ba , hankalinta yana kan Mimi da take kallo.
â Little Mimi, har mun gama breakfast , letâs go yanzu zamu shirya dinning dâinâŠâ
â Uhm Uhm daman Mommy ce take kiranta âŠâ Zarah tayi maganar a dâarare tana kallan Aya kamar me tsoran magana .
Ba tare da damuwa ba Ayan ta kalleta sannan ta furta â And so? Babu inda zata , zaki iya zama in kinaso , and zaki iya fita idan kin gaji , the choice is yoursâŠâ ga baki dâaya dâakin akai shiru , ita kanta Mimi tayi shock da irin reply dâin Aya duk da tun ba yau ba ta gane Aya âyar I donât care ce , she donât care and bata tsoran ta fadâi magana agaban kowa idan taso magana .
Kuma duk cikin su babu wanda yaga fuska da zai ja da abunda tace , hakan yasa Zarah ta kalli Mimi ko zata ce wa Aya dâin wani abu.
Sai taga Mimi ta share , ta bi bayan Ameerah da Aya da suka wuce dinning .
Sosai Zarah tasha jinin jikinta , Ameerah da Mimi kuma suka zauna akan dinning , lokacin da Aya zata kuma wucewa , wani mugun kallo da ta jefawa Zarah , sai da Zarah ta kuma dâan ja baya kadâan , dan ta tsorata da kallanta .
Aya tana barin wajan , kallo dâaya tayi musu both Ameerah da Mimin , tayi saurin ficewa daga part dâin.
Tana fita Ameerahn ta kalleta â Mimi wai whatâs wrong with Zarah ? Daga jiya zuwa yau na kasa gane mata , infact a cikin kwanakin nan tanayin wasu abubuwa so strange , especially jiya da nace mata tazo muje part dâin ku, tace ba zata je ba zata zauna a wajan Momy, on like before da babu abunda take âkaunar ji kamar tazo part dâin ku.â
â Ameerah may be she have her own reason neâŠ.â
Kallanta sosai Ameerah tayi , yanzu kam sun dena bata mamakin ma su biyu, zata yi magana Aya ta sake fitowa shiyasa Ameerah ta fasa fadâan abunda take san fadâa dâin.
Zama sukai , sukayi breakfast dâin su sosai.
Da suka gama suka mayar da abubuwan kitchen suka dawo falo, sabuwar kira ya âbarke a tsakanin su , anan ne Mimi take sake fahimtar Aya , is a simple and loving person.
_____________
ISTANBULâŠâŠ.
âKarfe 5:40am na safe Ahmet ya fito daga dâakin sa , yana kallan hanyar dâakin Aylin, amma bai ce komai ba ya fito falo ya zauna , idanuwansa ga baki dâaya akan âkofar shigowa falo kamar me expecting wani abu.
Gidan yayi tsif babu hayaniya ko kadâan.
Wayarsa ya âdâauka ya duba time , sannan ya soma duba messages dâin ciki na few minutes ya miâke zuwa sama .
Direct dâakin Aylin ya shiga .
Sau biyu yayi knocking , âkofar dâakin amma bai ce komai ba .
Jin babu motsi kwata kwata ya bar wajan zuwa dâakinsa .
Wanka yayi ya shirya cikin suit .
Lokacin da ya sauko âkasa , Anne ta shirya ta fito itama tare da Nunu da take sanye da uniform dâin school itama .
Tana ganin Ahmet ta soma dâaga masa hannu.
Murmushi yayi mata yana amsar ta daga hannun Anne .
â My NunuâŠ.â
â My MemetâŠâ itama ta amsa masa .
Kallan Anne yayi â Good morning Anne .â
â Good morning Abi, fatan ka tashi lafiya.â
â Iâm good Anne , ya kuka tashi?â
â Same as always AbiâŠâ
â Let me prepare something for you Anne âŠâ
â No weâre good , already nayi order a hanya kawai zamu amsa mu wuce school , ko Nunu?
Kanta Nunu ta jinjina masa tana maâkale hannuwanta duka biyu a wuyansa , tana fadâin â MemetâŠâ
â Yes Love⊠Good MorningâŠâ ya fadâa yana dâan shafa bayanta .
A hankali ta kuma fadâin â MemetâŠâ
Shima kuma ya kuma fadâin â Yes LoveâŠâ
Muryarta a rarrabe ta furta â BU BU.â
Shiru Ahmet yayi mata , sai kallan Anne da yayi, ita kuma Anne ta dâauke idanuwanta daga kansa tana barin wajan.
Ganin hakan yasa jikinsa yin sanyi kadâan yana dâan dâago da ita sai yaga hawaye kan face dâinta .
Da sauri ya soma goge mata hawayan, ganin wani yana saukowa ya sake hugging dâinta â itâs Okay , idan kuka dawo school zan kira miki shi kinji?.â
â Yaushe zai dawo?â.
â Kwanan nan Bubu zai dawo so stop crying in baki dena kuka ba ai bazai zo ba.
Stop crying okay ?â.
Kanta Nunu ta dâaga masa da sauri tana dâan turo bakinta .
Wajan Anne suka nufa , kallo dâaya tayi musu ga baki dâaya sai ta amsa Nunu dâin tana kallan dâakin Aylin.
â Ahmet please kafin ka fita ka tabbatar da inda Aylin take kaji?.â
â Sure AnneâŠâ
â And please nasan halinka , kar ka biye mata idan tayi maka wani abu , nasan halinta da rashin kunya kai kuma baka dâaukar wannan abun but please, banasan fadâan ku.â
â Yeah Anne , karki damu you can just go âŠ. Ki bar komai a hannuna .â
Anne har ta juya sai kuma ta sake waigowa wajan Ahmet â Ahmet karka fadâawa Emir kaji?.â
âDauke kansa Ahmet yayi yana murmushi , sai dai baice mata komai ba , ya dai dâaga mata kansa kawai .
Anne bata ce komai ba suka fita daga falon Nunu kuma ya dâaga masa hannu , shima kuma sai da ya dena ganin su tukunna ya sauke hannunta yana âkara kallan dâakin Aylin dâin.
Bayan kamar 20 minutes yana tsaye a falon , lokacin ya tabbatar da cewa su Anne sun fita daga gidan gabaki dâaya .
Ya shiga dâakinsa ya dâauko wata âyar âkaramar jaka yana sake knocking dâakin Aylin.
Jin shiru ya dâauki wayarsa yana dâan danne danne , sai ya dâauko wani abu ya saka a jikin âkofar , ya cigaba da danne dannen sa kamar na mintuna 5 , sai fit.
Wani âkaramun sound ya fito daga âkofar da kuma budâewa da tayi kadâan alamar lock dâinta ya budâu.
Komai da yayi anfani dasu ya kamar cikin jaka , sannan ya budâe dâakin.
âKarewa dâakin kallo yayi , yana kallan how messy it looks like âŠ.
Da kuma abun allurar da yake âkasa , da magunguna.
Sai da ya saka hand glove tukunna ya soma dâaukar magungunan dâaya bayan dâaya yana karantawa , sannan yayi snapping.
Yayi Snapping Aylin da take a kwance tun jiya kamar gawa .
âKafarsa dâaya ya saka ya dâan taâbata , bata motsa ba kamar wata gawa .
âKara âkarewa dâakin kallo yayi , sai ya nufi toilet dâinta , shima itâs not that clear ,kowama dâakin yayi daman har zuwa lokacin bai cire Handglove dâinsa ba , yana zuwa kawai ya jawo kanta kamar wata kayan wanki zuwa toilet dâin , haka ya saka ta a cikin bathtub dâin, sannan ya kunna mata ruwa, yana fitowa daga toilet without looking backâŠ..
_________________
To be continued⊠đ„
Aysha Galadima đ€đż
( Black Queen)
***
***