MISHAL

Page 39

by @ayshagaladima22

MISHAL



By AYSHA GALADIMAđŸ€đŸż
***


BOOK 1 
Page 39

Ruwa sosai ya soma cika Bathtub d’in nan .

Aylin da take ciki batasan abunda yake faruwa ba sai da ruwa ya soma shigar mata cikin hancinta tukunna jikinta ya soma motsi, har ta samu dabar bud’a idanuwanta.

Ruwan ya sigar mata hancı sosai , da ‘kyar ta iya run ‘kurawa ta mi’ke zaune tana dari da ‘karfi , jikinta yayi bala’in yin weak sabida abubuwan da tasha jiya , gashi ko mi’kewa tsaye ba zata iya yi ba a wannan condition d’in. 
Haka ta samu ta daddafa ta kashe ruwan , sannan ta fito daga bathtub d’in kamar tarwad’a dan dagangan jikinta take jan jiki, bawai mi’kewa tsaye tayi ba .

Lokacin da Ahmet zai fita daga toilet d’in ya riga ya janyo ‘kofar shiyasa bud’ewar tayi matu’kar yi mata wahala , har sai da ta d’anji ciwo a hannunta a garin bud’ewar . 

Da ta bud’e kuma bata gama dawowa sense d’inta ba ta fito daga toilet zuwa d’akinta.

Jikinta a ji’ke yake sosai da ruwa , ga kuma Ac shima da aka ‘kure, shiyasa sanyi da sanyi ya had’un mata waje d’aya , babu ‘bata lokaci ta soma rawar sanyi, babu kuma abunda zata lullu’ba , idan akwai ma ba zata iya d’aukowa ba a wannan hakin da take ci. 

Da ‘kyar ta kuma jan jikinta zuwa wajan da wayarta take , hannunta na rawa ta samu ta nemo number Ahmet. 

Ringing uku ya d’aga kiran. Murya a sha’ke ta furta “ help me please..” maganar a rarrabe ta yishi daga nan ta ajje wayar tana faman sauke ajiyar zuciya sabida yadda maganar yayi mata wahala .

Tana nan akwance kamar mintuna uku sai gashi ya shigo d’akin. 

Daga bakin ‘kofa ya tsaya yana kallanta, a yanayin da ya ganta ko damuwa baiyi ba , sai ma hannuwansa da ya saka a cikin aljihu yana ganin yadda take rawar sanyi. 

Da ‘kyar ta nuna masa Ac da hannunta alamar ya kashe sai yayi kamar be gane abunda take nufi ba . 

Ya soma tahowa inda take a kwance .

A hankali ya tsugunna wajan da take , ta d’an d’ago da fuskarta , idanuwanta da sukai ja ko iya bud’e su ba tayi kamar me bacci sabida da ta bud’e sai ta rufe, hakan yasa ya saka hannu ya d’an bubbugi face d’inta wanda hakan yasa dole ta dinga ‘ko’karin bud’e idanuwan. 

“ Kisan yadda zakiyi ki fita daga wannan haukan da kika jefa kanki, kada ki kuskura Anne tazo ta tarar da ke a wannan yanayin da kike ciki. 

Better be careful Aylin, kisan inda zaki dinga shaye shayen ki , not here in my house .” Ya saki face d’inta da ‘karfi , hakan yasa fuskarta ta koma ‘kasa sabida jikinta ya saki sosai. 

Mi’kewa tsaye yayi ya ciwo wani magani aljihunsa , guda biyu ya jefa mata , sannan ya d’auko bottle water shima ya jafa mata kusa da ita ba tare da ya kalleta ba ya furta “ This is all I can do for you..” daga nan ya fice daga d’akin.

Ta d’auki atleast 20 minutes kafin ta iya sake motsawa daga yanayin da ya barta , kafin ta d’auki maganin da ya bata zuwa bud’e ro’bar ruwan da ya jefo mata ya d’auke ta atleast wasu good 30 minutes har ta samu nasarar bud’ewa tasha daga kwancen da take , duk da ‘kwarewar da tayi, hakan bai sa ta dakata daga shan maganin ba . 

Tana gamawa kuma ta koma ta kwanta a wajanta duk da sanyin da take ji babu yadda za tayi, haka ta zauna sanyi yana faman asarsarar jikinta . 

Bayan kamar hour 2 da rabi , jikinta ya soma dawowa dai dai, abunda yake jikinta shima ya soma sakarta hakan ne yasa ta samu damar kashe Ac d’in tana jan wani dogon tsaki. 

Ta cire ji’ka’k’kun kayan jikinta ta watsar a filin d’akin, ta d’auko dogon duvet ta lullu’be jikinta dashi, tana kwanciya akan kujera tare da sauke dogon ajiyar zuciyar wahala , zuciyarta kuma fall tana tsinewa Ahmet dan tasan babu mai mata wannan wula’kanci kamarsa, sai kuma Emir dashi kome yayi mata bata d’auka a wula’kanci sai ma soyayya . 

Jikinta sosai yayi relax yadda take bu’kata , sai ta d’auko wayarta tana duba uban tarin message d’in da aka turo mata , da kuma missed call da suka cika wayar ta sosai. 

Wasu ta bud’e ta karanta abunda suke ciki, wasu kuma tayi skipping, har tai ta samu tayi wanka ta canza kayan jikinta zuwa riga da wando da suka kama jikinta. 

Lokacin da ta fito falo, Ahmet har ya gama breakfast yana ‘ko’karin fita ne . 
Koda ya ganta bai ce mata komai ba shiyasa tayi saurin tsayar da shi ta hanyar kiran sunansa . “ Abi.”

Kallanta yayi ba tare da yace komai ba , har ta ‘karaso wajansa “ Uhm Please Abi karka fad’awa kowa abunda ka gani a d’aki na please.”

“ Okay are you pleading me? Or you’re asking me to obey?”.

“ No ko d’aya babu Abi, just please dont tell anyone especially Anne . Please
”

‘Dan ta’be baki yayı, “that’s base on your performance
” yayi ficewarsa , yana barinta da hararan bayansa . 

Sai da ya fita tukunna ta saka hannu guda d’aya a bakinta tana taunar d’an yatsanta guda d’aya . 

Sai kuma ta hau sama da sauri tana le’kan window , sabida tanaso ta tabbatar da fitar Ahmet daga cikin gidan, bayan da tayi confirming haka , ta sauke ajiyar zuciya me ‘karfi. 

Tayi saurin wucewa d’akin Anne. 

Yananan a gyara tas tas kamar babu wanda yaka zama a cikinsa amma kuma akwai ‘kamshin turare sosai a ciki, kamar yanzu aka saka . 

‘Karewa d’akin kallo ga baki d’aya , ta sake fitowa ta kulle ‘kofar falo, sannan ta sake dawowa d’akin. 

Sosai ta soma binciken each and every loka da yake cikin d’akin, duk abunda ta ta’ba kuma sai ta tabbatar da ta gyara abunda ta ta’ba yadda aka ajiye , haka ta gama binciken part d’in Anne , tana jan tsaki sabida bata samo abunda take nema ba . 

‘Dakin Ahmet ta wuce shima yananan tsaf tsaf dashi kuma babu tarkace sosai a cikin d’akin, simple komai da yake ciki, ta rasa daga ina ma zata soma binciken a d’akin, haka dai ta soma bibbin cikawa and everything is empty babu komai. 
Da sauri ta gyara masa d’akin shima yadda ya ajjesa , tana zucewa d’aki. 

Da sauri tayi dialing wata number.
Ringing biyu akayi picking call d’in bata tsaya anyi magana ba ta soma nata maganar “ Har yanzu banga ni ba , duk na duba d’akin Anne , babu komai a ciki har d’akin Ahmet na duba shi still babu komai a ciki. Ko dai muna ‘bata lokacin mune a banza?.” 

Ba’a jin me ake ce mata a cikin wayar hakan yasa ta furta “ Shikenan zan sake dubawa .” Daga nan ta kashe kiran , ta shirya ta fita daga cikin gidan . 


______ 
Da yamma su Anne suka dawo gida .

Already sunci abinci kafin su dawo , shiyasa suna shiga cikin d’aki Nunu ta soma bacci . 

Ita kuwa Anne tana d’an hutawa ta shige kitchen , ta soma shirya dinner iri iri. 

A hankali kitchen d’in ya soma tashin ‘kamshin abinci, tana gamawa kuma ta wuce d’aki. 

Number Aylin ta sake kira , a yanzu tana ringing amma ba’a d’aga ba , hakan yasa ta ha’kura da kiran wayar ga baki d’aya ta shiga wata sabgar. 



______________
ABUJA

Da  magrib bayan sunyi sallar magariba suna zaune a falo suna hira su uku , sai ga shigowar Aunt Shukura hannunta d’auke da manya leda guda biyu. 

Mimi da Ameerah ne suka temaka mata wajan ri’ke ledojin suka ajje akan center , ita kuma ta zauna a kan kujera tana fad’in “ Wayyo Allah 
.”

“ Shukura , don’t tell me you’re tired ?” Aya tayi mata tanbayar tana kallanta da d’an mamaki akan face d’inta . 

“ Yeah Aya, wallahi na gaji, ko shigowa da wad’an nan ledojin ai ba ‘karamun abun bane , kalli yadda nake faman had’a gumi.”

“ No wonder Mimi bata iya training , you guys all bakwa motsa jiki, that’s why zaku gaji sosai .”


“Yanzu har wasu training d’in kike?” Cewar Shukura .

“ Yeah ! Amma ki soma zuwa ki shirya tukunna, idan kika huta sai ayi hirar .”

“ Okay ga abubuwan ku nan na taho muku dashi..” da haka Shukura ta mı’ke ta bar falon. 

Mimi da Ameerah kuma suka soma bud’e ledojin. 

Junk food ne da yawa a ciki, sai su ice creams da ta siyo kusan leda guda da different flavor, da excitement akan fuskokin su , suka soma fad’in “ Woow ! Our lovely Aunty Shukura .” Duk da sun san cewa ba zata jiyo abunda suke cewa ba tunda ta tafi d’aki. 

Aya sai da ta bari suka gama bubbud’e kayan, har sun fito da wasu uban junks da su ci a time d’in. 

Ita kuma tana tashi ta kwashe ga baki d’aya komai na wajan, bata bar musu single thing ba taje ta ajje su a fridge suka bita da kallo irin kallan mamaki da kuma sanin rashin abun yi next. 

Har say da Mimi ta kasa yin shiru ta furta “ Aunt Aya meyasa zaki kwashe ga baki d’aya kayan? Or baki kula da wanda zamu ci ba, it was a mistake abi?”.


“ Ba mistake bane Mimi, you’re not allowed to eat junked food all the times . 

Yanzu dare ne it’s not good for your health all , ku bari in a full day sai kuci , but between 12pm to 6pm. 

Idan ya wuce wannan time d’in you’re not allowed to eat any junked food okay?”

‘Dan dariya Mimi tayi sabida ji tayi maganar yazo mata unbelievable hakan yasa tayi dariya ma , har ta kuma cewa “ You’re Joking ko?”.

Itama Aya dariyar tayi kamar yadda Mimi tayi tana kallanta cikin idanu “ No Mimi am not joking 


Idan kuma dagaske kuna san ci, then you call Moh Moh and asked him, idan yace zaku iya ci, am good with that .”

Uhm Mimi da Ameerah suka sauke ajiyar zuciyan dan ko suna shaye shaye ba zasu ta’ba tun karar zuwa wajan nasa ba , hakan yasa Ameerah tayi saurin fad’in “ Ai yau da gobe duk d’aya ne , zamu jira zuwa goben idan yaso sai musha ko ya kika ce Mimi.”

Itama Mimi kanta ta jinjina mata tana fad’in “ Yeah Allah ya kai mu
”


Mi’kewa tsaye Ameerah tayi tana kallan su “bari naje part d’in mu na duba su Mama sai na dawo kafin mu kwanta”.

“ Ameerah you can go with Mimi, nima zan fita wajan Alameen.”

“ So that means you’re going out?” Cewar Mimi?.

“ Yess.” Itama Aya ta bata amsa . 

Murmushi Mimi tayi tana fad’in “ Okay ! I will follow her now , amma yaushe zaki tafi?.” 

Kallan Aya tayi na d’an seconds , even though ta gane dalilin farin cikin Mimi, amma sai tayi kamar bata gane ba, ta ‘kara wani lallausan murmushi itama akan face d’inta “ Mimi am going out now ! If you guys are ready ma , let’s go , in na shiga mota , ku kuma sai ku wuce part d’in su Ameerahn, when am back sai ku dawo, or anytime you want tunda Shukura ma tana nan , but atleast tunda ta gaji, ku barta ta huta sosai da sosai. 

I think hakan yayi ai ko?”. 


“ Yeah
” cewar Mimi, tana kallan Ameerah da itama ta jinjina kanta. 
But kafin su fita sai da Mimi taje zata fad’awa Shukura fitar su , sai ta tarar da tana bacci, tana fitowa ta fad’a musu bacci take , shiyasa suka fito. 

Har wajan mota suka raka Aya , Mimi yau har da d’aga mata hannu, itan ma kuma ta d’aga musu hannu kafin ta kunna motar ta fita daga gidan ga baki d’aya .

“Mimi wannan farin cikin da yake kan fuskar ki ta mene ne haka? Da naga har kin soma ‘bata fuska amma daga ji zata fita fuskar ki ya çıka da annashuwa kuma .”

“ Uhm Ameerah you’re even asking me?let’s go back kafin muje part d’in naku.”

Kafin Ameerah tayi magana Mimi ta sake jan hannunta suka wuce part d’in su, suna shiga kuma kitchen shiga , Mimi tayi saurin d’auko leda tana bud’e fridge d’in. 

Da sauri Ameerah ta kalleta tana fad’in “ Me zakiyi kuma da leda?”

“ Lalle Ameerah you’re even asking me , toh junks d’in mu zan iya inyaso sai muci a d’akin ki. 

Haka kawai sai kace ‘yan 50 years ace wai sai an saka mana time da zamu dinga cin abu sai kace wasu masu sugar ko kuma diabetes?”.

“ Amma bakya tsoran ta dawo ta gani? Wallahi  wani lokacin Aunt Aya tana bari tsoro , duk tausaya idan tana wajan ajje sa nake amma ke kin iya d’auko Leda ma ko , zaki iya junks food idan ta gani ta fad’awa Uncle Moh ya zamuyi?.”

“ In sha Allahu ma ba zata gani ba, kedai akwai idan zaki sha toh , idan kuma ba zaki sha ba ni na d’ibi nawa kuma kar ma ki soma cewa na baki kema .”

“ Uhm Uhm fa Mimi..”

“ Uhm Uhm ko? Ameerah zaki ci ko ba zaki ci ba?”. 

“ Hhhhh why not zanci amma please me d’iba iya wanda zamu cinye kar ma ta gane .”

Mimi bata kulata ba , ta d’aukar musu manyan ice cream guda biyu , da su popsicles , su chocolate abubuwa dai da dayawa wanda da ‘kyar idan zasu iya cinye wa tunda da yawa Shukura ta siyo, haka suka d’auki wayoyin suka bar part d’in zuwa part d’in su Ameerah .

Allah ya temake su babu kowa a cikin falo, sukai sauri suka wuce d’akin Ameerah suka ajje ledar .

“ Mimi wallahi da Mama ta ganmu da wannan ledar ba zata bar mu musha sanyin nan ba , dan itama ta tsani taga all the time in shan abun sanyi sai kiji ta soma idan sanyi ya kamaka ya kake so ayi da kai, Alhamdulillah ma bata gan mu ba.”

“ Toh kin gani, since we’re safe ai shikenan, yanzu ki bari ma tunda ba’a san da shigowar mu ba , mugama cin abunda zamu ci idan yazo daga baya sai mu fita , lokaci ai mun riga da mun gama sha, ko?”. Cewar Mimi.

Ita kuma Ameerah ta nuna ‘kofa “ So na kulle ‘kofa kenan?”

“ Yeah kulle mana sabida mu tabbatar we’re safe .”

Haka Ameerah taje ta kulle ‘kofa , suka bud’e ledan nan , kamar shazu ma mai , haka suka dinga shan chocolate suna hira, ga uban ice cream duk girmansu sai da suka sha sosai , ko tsoran ha’kwaran su suyi sanyi ba sayı . 

Ahaka dai suka d’auki dogon lokaci. 
Abubuwan da basu gama sha ba suka saka a fridge d’in Ameerah da yake d’akin, ledojin kuma suka d’auko su, suka sake fitowa compound, sabida kar Mama ta ga ledojin sai suka yanke shawarar yadda da ita a dust bin d’in compound. 

Kuma successfully sun yar babu wanda ya gan su. 

Da suka jiyo ne Ameerah ta soma tanbayarta “ Mimi ina zamuje yanzu? Part d’in naku ko kuma namu? Or muje part d’in su Zarah? Tun d’azu da safe fa ban ‘kara ganin ta ba and bata kuma dawowa ba unlike before kamar wacce aka canza kwanakin nan.”


“ Uhmm”kawai Mimi tace . 

“Why are you humming? Ko baki ji abunda nace miki ba?”. 

“ Naji Ameerah ai tana da ‘kafa , tunda kika ga bata zo ba she’s not interested ne
”

“Anya Mimi babu abunda ya had’a ku? Kuke bari na a duhu?”


“ Ko d’aya from my side but ban sani ba ko daga nata side d’inta , but you can asked her if you want .”

“ Amma tare zamu je ko?” 

“ Nope” cewar Mimi tana d’orawa da “ Babu inda zani, if you want I will wait for you apart d’in mu, because am not going , and please just go if you want to go , stop asking me such questions haka da yawa.”

“ Okay I will asked her later 
 zamu koma part d’in namu ne tunda bamuga Mama ba da muka zo d’azu.”

“ Yeah muje mana.”

Da haka suka wuce part d’in su Ameerah , Mama har yanzu bata fito ba sai da Ameerah ta shiga d’aki ta kirawo ta tukunna ta fito falon . 

Tana ganin Mimi ta sake fad’ad’a murmushinta sosai da sosai “ Ah ah Mimi zuwan yaushe ?.”

‘Dan sosa kanta Mimi tayi tana hararar Ameerah da take mata dariya “ Mama bamu dad’e da shigo ba , ina wuni , ya aiki.”

“ Lafiya ‘kalau Mimi ya kike kema?.”

“ Ina nan lafiya Mama.”

“ Masha Allah haka ake so, ga abinci nan gama , idan kuna jin yunwa maza maza ku zauna kuci kar ku zauna shiriritar ku da kuka saba.”

Wani irin dariya Ameerah ta ‘kyal’kyale dashi har tana d’an ri’ke cikinta , kusan lokaci d’aya Mama da Mimi suka harareta, hakan yasa wani yariyar ya sake zuwar mata amma ta danne tana fad’in “ Haba Mama wannan hararar da kuke mun fa? Nifa babu abunda nace kuke ta hararata .”

“ In banda iskanci irin naki ina magana kina mun dariya , abokiyar wasan kice ni?”.

“ A’a Mama kiyi ha’kuri amma yanzu muka ci abinci, ki bari zuwa anjima idan muka ji yunwa sai muci, ko yanzu ma ki zuba mana a warmers idan yaso ko da ace su Aunty Shukura ma zasu ci sai muci ga baki d’aya lokaci guda . 

Ai abincin yana da yawa ko?” 

Hararar Mama tayi kad’an tana fad’in “ Bansani ba” sai kuma ta kalli Mimi “ Bari na zuba muku a warmers kinji Mimi?.” 

“ Toh Mama mun gode .”

Mi’kewa Mama tayi ta shiga kitchen ita kuma Mimi ta d’auki pillow da yake kusa da ita ta jefowa Ameerah.

Ameerah tayi saurin kaucewa tana fad’in “ Wallahi idan bakiyi wasa ba sai na fad’awa Mama abunda muka ci, dan ma kin samu na rufa miki asiri shine zaki wani jefo mun pillow?”. 

“ In baki fasa ba .” Cewar Mimi.

Ita kuwa Ameerah ta bud’e baki tana ‘kwalla kiran sunan “ Mama .” Da ‘karfi yadda za taji , cikin sauri Mimi ta kalleta “ Wai mene ne haka Ameerah?”

Kafin Ameerah tayi mata magana Mama ta fito daga kitchen tana fad’in “ Ameerah , wannan kiran suna na da kike kamar wani abu ya faru? Me yake damun ki ne wai?”.

“ Sorry Mama . It was a mistake ..” cewar Ameerah tana d’an d’agewa Mimi gira .

“ Allah ya shirye ki.” Shine kawai abunda Mama ta ce ta koma kitchen .

“ Wallahi Ameerah kin cika mara mutumci kuma bashi kika d’auka wannan abunda kikayi Allah .”

“ Oho dai , yarinya ta gwadani ta ga yanzu idan ban kira Mama ba . Kuma har Aunt Aya d’in ma zan fad’awa kinga asirin namu ya to nu da hujja .”

‘Kwafa Mimi tayi tana shareta . 

Suna zaune Mama ta fito da jakar abinci guda biyu tana ajje wa daga ‘kasa “ Gashi nan na tabbata wad’an nan zasu ishe ku, idan ma basu ishe ku ba , ku dawo sai na zuba muku wani .”

“ No Mama dun ma isa tunda bamu da’de da cikin abinci ba .” Cewar Mimi, ita kuma Ameerah ta jinjina mata kai tare da d’aukar jakar abinci guda d’aya .

“ Mun gode Mama .” Cewar Mimi.

Itama Ameerahn desame abunda Mimi ta fad’a itama ta fad’a wato “ Mun gode Mama.”

Amaimakon Mama ta amsa musu godiyar tasu sai ma cewa da tayi “ Ku wuce ni ku bani waje 
 ni zaku zo ku dinga yiwa godiya ?.” 

Haka suka d’auki abincin nan suka fito, suna tafiya suna hira , basu ma kula da Zarah da take tsaye a part d’insu ba kamar me jiran wani. 

Ita kuma da ta gansu sai tayi tunanin ko suna sane suka d’auke fuskokin su shiyasa ta nufosu tana fad’in “ Kuka d’auke fuskar ku kamar baku ganni ba? Me nayi muku haka ne wai?.”

Sau d’aya Mimi ta kalleta ta d’auke face d’inta , Ameerah kuwa har da gyara tsayuwarta “ Kamar ya muka d’auke face din mu? Ko ni ko Mimi kin ta’ba gani wani ya ganki ya d’auke fuskarsa, ji wata irin magana da kike .”

“ Shikenan dai , tun d’azu nake faman jiran fitowar ku naga lokacin da kuka shiga part d’in ku ai Ameerah.”

“ Lalle na yadda akwai wani abu akanki Zarah, part d’in namu ne yake miki wahalar shigowa ko kuwa wani abu? Tunda kin ganmu me ya hanaki zuwa part d’in , har ma ki jira mu a nan , anya kuwa?”. 

“ Uhm Ameerah duk ma ba wannan ba , mu ajje wannan maganar a gefe Mommy ce tace na kira ku.”

“ Mommy?” Ameerah ta kuma tanbaya , ita kuma Zarah ta amsa mata da ka. 

Kallan Mimi da bata ce komai ba tayi, sai kuma ta furta “ Muje toh Mimi.”

Da fari shiru Mimi tayi tana tunanin zuwa , idan ita kad’ai Zarah ta fad’awa ana kiran su ba lalle taje ba , but da taga akwai Ameerah sai kawai ta jinjina mata kai , suka soma tafiya Zarah har da saurin tsayawa a side d’in Mimi.
Mimi kuwa nunawa tayi like she never exist ga baki d’aya . 

Suna shiga cikin falon su Zarah , Mommy da take zaune sai faman fara’a take ta mi’ke tsaye sabida shigowar su Mimi, har zuwa a yi hugging d’in su, d’aya bayan d’aya tana fad’in “ Daughter d’ina ya kuke
..”


Mimi was speechless amma kuma nan ma mamakin na ta ya kau tunda Zarah zata iya nuna abunda tayi ba komai bane , tabbas Mommy in ta nuna ba wani abu bane. 

Har hannunta Mommy ta kama ta zaunar akan kujera tana fad’in “ Tun d’azu nake neman ku, kamar munyi muku laifi yau ko part d’in namu bakwasan zuwa.”

Ameerah da batasan wainar da ke faruwa ba tayi mata murmushi “ Aa Mommy daman muna da niyar zuwa ne
”

Hakan yasa Mommy ta kalli Mimi tana mata wani murmushi “ Mimi ke kuma fa ?.”

Shiru Mimi tayi tana kallanta har sai da Ameerah ta d’an ta’bo ta , ita kuma Mimi ta mi’ke tsaye tana kallan su ga baki d’aya “ Mommy bari naje na ajje wannan jakar su Aunt Shukura Ɵuna jiran mu , zamu dawo ko Ameerah?.”

Ameerah dai kawai ta d’aga mata kai itama kuma tana mamakin abunda Mimi tayi , tunda zuwa yanzu ta riga ta fahimta kamar akwai wani abu a ‘kasa amma batasan tsananta bincike tunda basu fad’a mata ba su duka . 

Kallan jakunkunan hannun su Mommy tayi “ Toh ga Zarah nan ku je tare mana , amma ku tabbata kun dawo sabida akwai maganar da zanyi daku ku duka kunji ko Daughters d’ina?”.

Ameerah da Zarah ne suka amsa da “ Toh MOMMY.” Mimi kam har tayi hanyar fita , Ameerah da Zarah suka mara mata baya .

Suna fitowa waje motar Aya ta shigo , sai suka d’an tsaya dan ita Zarah jikinta yayi sanyi sosai, su kuma Ameerah da Mimi suka d’an tsaya kallan kallo sabida tuno abunda sukai d’azu . 

Aya tana fitowa daga mota fuskarta cike da murmushi, itama tana kallan su ganin yadda suke d’an matse fuska kamar basu san abunda sukai ba ya ‘kara sa Aya yin wani murmushin da ita kad’ai tasan ma’anar abunda tayi . 

Ta kalli jakunkunan hannun su, na hannun Mimi ta amsa ta mi’kawa Zarah , babu musu Zarah ta amsa tana kallanta, tana fad’in “ Mimi ! Moh Moh na kiran ki
.” Booooomm zuciyar Zarah ya soma bugu saura kad’an ta yar da jakar hannunta . 

Aya again ta amsa jakar hannun Ameerah tanayi mata murmushi itama “ Kema Ameerah ki bita Alameen yana neman ki
.”itama taji booom zuciyarta ta buga 




( 😂😂😂😂 Bari nayi dariya kawai
)



_________________

To be continued
 đŸ”„


Aysha Galadima đŸ€đŸż
***


***