MISHAL

Page 40

by @ayshagaladima22

MISHAL



By AYSHA GALADIMAđŸ€đŸż
***


BOOK 1 
Page 40

A wannan lokacin Zarah batasan ta yar da jakar hannunta ba , sai lokacin da taji fad’uwarta a ‘kafarta . 

Da ‘karfi ta furta “ Ouchhhh
” Tana tsugunnawa, hakan yasa suka kalleta , har da Mimi da zuciyar su take dukan 10-10. 

Ita da Ameerah sun zo zasu dubata Aya ta d’an shiga tsakanin wajan, murmushin fuskarta har lokacin bai gushe ba “ Karku damu kuyi tafiyan ku, I will help her 
” .

Mimi ta bud’e baki Aya ta sakar da fuskarta zuwa seriousness sai dai bata had’e face d’in sosai ba , idanuwanta ga baki d’aya akan fingers d’inta “ Mimi ku wuce abunda na fad’a muku, kar ku ‘bata musu lokaci , and yes zan dubata bakwa bu’kar damuwa . So now goo
” yadda tace go d’in cikin d’an kaushi kaushin murya tayi sa, hakan yasa Ameerah ta d’an ta’ba Mimi tana mata alama da suzo su tafi. 

Mimi ba tayi mata musu ba , ta juya suka soma tafiya , amma ko taku ashirin basuyi ba ga baki d’aya suka tsaya kusan a tare , kamar wad’anda suke karantar zuciyoyin junan su. 

A d’an tsorace Ameerah tayi ‘kasa ‘kasa da muryarta “ Mimi anya bawani laifi mukai ba ?
”

“ Lefi kuma ? Wana lefi mukai kodai wani aikin zasu samu?.”


“ Ameerah nima wallahi ban sani ba , amma wana abu mukai , ji yadda fuskar ki duk ta soma rawa, wallahi Ameerah kika tona mana asiri zaki ga rashin mutumcin da zanyi miki Allah kuwa .”

“ Aah Ahhh Mimi wallahi aka ritsani sai na fad’a uban wa yace kisa musha ice cream d’in?.”


“ Mts*** Mimi ta d’an ja tsaki tana hararan Ameerahn kad’an “ Dan kawai mun sha ice cream sai kice akan shi suke kiran mu, naga ai ba dole ice cream muka sha ba wallahi idan ma shine kawai muce shayin ice cream muka yi muka sha, chocolate kuma mukayi melting d’insa mun d’an dan gwala kad’an
..

Ai ba ko wace ‘karya ce haramun ba , idan mun dawo sai muyi istigfari, Allah ya yafe mana .”


‘Dan girgiza mata kai Ameerah tayi “ Wallahi nidai tsoro nake ji , baki ji yadda zuciyata take boom boom ba kamar zata fito waje?.”


“ Toh nima zuciyar tawa ai dukan boom boom, wallahi idan muka zauna anan wallahi zamu iya ‘bata musu rai , dallah ki nutsu ai de ba zasu doke mu ba , ni zuciyata na bani wani aikin zasu ce muyi musu , kuma Uncle Alameen na nan may be shine dalilin da yasa ma ake kiran namu wallahi.

Allah Ameerah ki nutsu banasan rashin mutumci
”

Numfashi Ameerah ta sauke da ‘karfi, tana dafe zuciyarta kafin ta kalli Mimi da itama tayi zaro zaro , itama kuma ta sauke ajiyar zuciya kawai sai suka kwashe da dariya suna cigaba da tafiya duk da sun kasa gane dariyar dad’i suke ko ta wahala , duk da fuskokin su ya nuna dariyar rashin mafita kawai suke . 

Suna zuna bakın door d’in Moh yau sai suka ganta abud’e kad’ai basai sun bud’e da kansu ba . 

Ameerah tayi wa Mimi signal akan ta soma shiga , itama kuma Mimi tayi mata signal d’in akan cewa ta soma shiga itama . 

Sunyi haka kamar sau uku kowa ya’ki ya soma takawa, sai Mimi ta d’an ‘kara matsowa kusa da Ameerah sabida ta fi jin abunda za tace “ Tsakani da Allah Ameerah kizo mu shiga , a shiga a tare tunda tare aka kira mu, yadda na taka ‘kafa d’aya kema haka zaki taka wallahi kin yadda ?”.

Itama Ameerah d’an matso da kanta tayi kusa da Mimi cikin rad’a rad’a ta furta “ Toh Dan Allah Mimi tsaya mu karanta Tabara ( SURATUL MULK) kinga in ma wani abun ne ai munyi addua ko?”


“ Lalle ma baki da hankali Ameerah sai mun gama full sural tare zamu shiga ? Wallahi ba zaki jazamun ba , kinsan yadda Uncle Moh ya tsani a ‘bata masa lokaci ,,, dallah taho mu shiga.” Mimi tad’an fincikota sukai gaba, amma suna zuwa daf da ‘kofar suka sake tsayawa, kamar wanda sukai gudu  duka suka d’ora hannu akan ‘kirji sannan suka sauke a hankali. 

Da finger Mimi ta nuna mata d’an wajan da yake abud’e ita kuma Ameerah ta d’aga mata gida d’aya sabida ta gane abunda take nufi. 


Dukan su suka je wajan da yake a bud’e suna dan saka idanuwan su ko zasu ga abunda yake cikin falon. 

Ba’a ganin komai suma d’in kuma babu abunda suke gani kawai tsa’bar guilt da ya kamasu sun ma ‘ki yadda da kansu haka suke ta faman turbuna ido ko zasu ga abunda suke san gani d’in. 

Suna a haka kamar mintuna 2 daga bayan su kawai suka tsinkayi muryar Alameen yana fad’in “ Me kuke nema toh?.” 
Daga Mimi har Ameerah baya sukai a tsorace , hakan yasa suka fad’a cikin falon babu shiri, ko wanne sai faman zazzare ido yake , gashi sunyi baje baje akan tiles alamar rashin gaskiya. 

Alameen d’in ne kuma a tsaye , hannunsa d’auke da wasu manyan fararan leda guda biyu , da car key a hannunsa , yasha ‘kananan kaya da p-cap , duk da dare ne kuma akwai ba’kin glass akan fuskarsa. 

Shi gashinan ba dariya yake musu ba , kuma ba murmushi yake ba , a tsaka tsakiya yake , kallo d’aya yayi musu ga baki d’aya ya karance su , ganin sun kasa magana balantana ma su tashi daga inda suke a zaune ya furta “ Ba kwajin sanyin inda kuke ne?”. Ya d’anyi maganar yana d’an nuna tiles d’in da suke zaune .

Cikin sauri suka mi’ke tsaye , bawai a kan ‘kasa suka zauna ba amma kuma suna d’an karkad’e jikin su , har da d’an juyawa su kalli cikin falon suna ro’kan Allah yasa Uncle Moh baya cikin falon, dan tabbas in yana ciki toh ya ga fad’uwar su kuma suma sun sani sarai kashin su ya bushe tasss.

Sun kasa tsayawa ma straight hakan yasa Alameen a karan farko yayi murmushi da ya fito da ha’kwaransa , tun lokacin da ya tsaya , aushe tun lokacin da suke tsaye a wajan part d’in yake tsaye kuma yaji abunda suke fama amma ko a fuskarsa hakan bai nuna ba kwata kwata . 

“ You guys kun dena magana ne ? Uhmm
.?” Yayi maganar yana kallan su ga baki d’aya at once . 

Da sauri suka d’an soma rawar bakin gaishe sa .

“ Uncle
 Unclee Alameen ina wuni?.”

Cikin falon da suke ciki ya nuna musu da fuska yana fad’in “ Get go inside 
.” Daga nan ya shiga cikin falon ba tare daya kuma kallan su ba .

Kallan juna Ameerah da Mimi sukai, ita Ameerah tana d’an jijjiga fingers d’inta alamar sun shiga uku, ita kuma Mimi fuskarta har ta soma tara ‘kwalla kamar ance musu sunyi wani abu. 

Da ‘kyar suka iya ‘kwa’kulo sallama sukai , kansu a du’ke suka ‘karasa shiga cikin falon, amma sabida ba’a amsa musu sallamar su ba , yasa duk suka sake shiga taitayin su , dan ita Ameerah already zuciyarta fall danasanin shan ice cream d’in nan take , sabida tasan babu lefin da tayi sai ice cream da Aya ta hanasu sha , ita kuma Mimi zuciyarta bai kawo mata wannan ba , tafi karkata akan may be wani aikin zasu saka su , tunda har Alameen yace a kira masa Ameerah , even though tayi mamakin ma yadda akai yasan Ameerah har yasan sunanta, amma sanin cewar yanzu ba shine me mahimmanci ba , yasa tayi saurin kawar da zancen ma ga baki d’aya, a zuciyarta.

A hankali Mimi ta sauke ajiyar zuciya a bayyane sabida ta sha’ko abunda take tsoran sha’kowa wato ‘kamshin turaran Moh, gashi tana matsowa ‘kamshin turaran yana ‘kara shiga hancinta, yana ‘karasawa ta zama very uncomfortable , a ‘bangaran Ameerah ma haka yake . 

Da suka shigo cikin falon sosai da ‘kyar Mimi ta d’an iya bud’e baki ta furta “ Assalamu Alaikum
” Tana shiru itama Ameerah ta d’ora nata “ Assalamu Alaikum.” 

Alameen ne ya amsa musu, sabida muryarsa suka ji, amma kuma gaze d’in da suke ji a jikin su yafi na Alameen d’in . 


Cikin d’an wasa Alameen ya furta “ Mene ne kuke faman sun kuyar da kanku wai ? Are you guilty or what kunyi wani abu ne ?”. 

Kusan a lokaci d’aya suka had’a baki wajan fad’in “ Babu abunda mukai..” 
saura kad’an kuma Alameen yayi dariya akan respond d’in ßu amma kuma ya share . 

‘Dago idanuwanta Mimi tayi a hankali tana ‘ko’karin kallan side d’in Alameen da take tunanin yana zaune a wajan. 

Ai kuwa d’agowar ta ta yayi dai dai da lokacin da shima ya d’ago fuskarsa daga kan phone d’insa , hakan yasa idanuwan su ya shiga cikin na juna , ma’ana sukai Eye contact ba , ita ce tayi saurin d’auke kanta tana fad’in “ Uncle Moh
 Ina wuni?.”

Bai amsa ba , itama kuma Ameerah jin ta gaishe dashi , itama tayi saurin fad’in “ Uncle Moh ina wuni.” Still basu jin muryarsa ba , kuma kansu a du’ke yake shiyasa ba zasu gane ya amsa musu ko bai amsa musu ba . 

Mi’kewa tsaye Alameen yayi , yana d’aukar d’aya daga cikin ledar daya shigo dashi falon, sannan ya nuna wa Mimi waje “ Mimi zauna kuyi magana mana da Uncle Moh..” sai ya kalli Ameerah “ Ameerah ke kuma let’s go , nima I want to discuss something with you.” A  nanne zuciyar su ya d’anyi sanyi duk da ba sosai bane, alamar basuyi laifi ba kenan. 

Akan dinning Alameen ya zauna , sannan ya nunawa Ameerah kujerar da take facing d’insa alamar ta zauna akai .

Babu musu jiki na rawa taje ta zauna, tana jiran maganar da yace zai yi da ita, amma kuma sai taga ya had’e fuskarsa ga baki d’aya , kamar ba shine yayi murmushi ba , yanzu fuskar ga baki d’aya ya mayar da ita seriousness babu wani wasa kwata kwata a kanta, ledar da ya taho da ita ya ajje mata a gabanta and ledar tana da girma fa , da farko ba ta gane me yake nufi ba sabida bai mata ‘karin bayani ba , sai da ya d’an kalleta tukunna ya sake nuna ledar da hannun sa “ Finish everything Ameerah
” 

Lokaci d’aya taji ta ‘kware da yawu sabida batasan mene ne a ciki ba kuma a bata ‘katuwar leda ace ta cinye komai da yake ciki, dole yasa mutum ya   ‘kware ai . 

Ji tayi tana so tayi masa tanbaya akan ledar, sai taga yayi mata ‘karamun murmushi , at the same time murmushi kuma yana ‘bacewa , yana komawa wani irin gaze “ Ameerah ba’ayi mun musu , dan haka do what I asked you to do, okay!”. 

Jikin Ameerah sosai yayi sanyi, ji tayi hannunta kamar ba’a jikinta yake ba , sabida tama kasa motsa shi sosai , amma a hakan kuma tayi ‘ko’karin soma bud’e ledar. 

Wani had’iyar yawu tayi tana zaro ido sabida manya manyan robar ice creams da suke ciki, da kuma chocolate kala kala kunya bana wasa ba. 

Ita kanta sai da taji ‘kwalla tana shirin tarar mata a ido sabida kawai ta yadda cewa Alameen so yake ya kasheta , shiyasa zai bata wannan abun yace wai ta cinye kamar wata mayya. 


A wajan Mimi kuwa, tana tsaye ita bata zauna ba kuma bata bar wajan ba sabida ta rasa me za tayi , tunda ta gaishe sa bai amsa mata ba .
Shi kuwa sai da ya gama abunda yake da wayansa , lokacin har ta d’an gaji da tsayuwa , d’an yun ‘kurawa yayi ta d’an ka ma wani abun zai mata sai kawai taga ya matsar da center table d’in gabansa, ya ajje ledar da take kai a ‘kasa , da ido ya nuna mata ta zauna a can carpet d’in. 

Duk da she’s little bit suprise haka dai ta zauna akan carpet ta tan kwashe ‘kafarta tana jiran abunda zai ce , sai ya kawai taga ya matso mata ledar ga banta, murya a kausashe ya furta “ Finish it all Mimi
” take taji waji rasssss gabanta ya fad’i duk da dai bata ma san mene ne a cikin ledar ba amma tunda yace ta cinye komai tasan ba abun alkairi bane .

Kuma yadda yayi magana bai bada wani second chance da za’ayi masa musu ba tunda cikin umarni yayi maganar. 

Haka tana tsoro ta bud’e ledar , ice cream ne da chocolate kamar yadda yake na Ameerah itama nata hakan yake, haka ta cuccuro komai da yake ciki, ta ajje a gabanta amma kuma ta kasa ta’ba komai sabida tasan dai bazata iya cin wad’an nan abubuwan ba dan dagaske cikinta a cike yake , wanda suka ci ma bai gama narkewa ba , balantana ma ace su kuma shan wannan ai ba zasu iya bacci yau ba . 

Cikin sar’kewar murya ta furta “ Uncle Moh
” bata ‘karasa abunda zata fad’a ba , ta kuma jin saukar kausash shar muryarsa kamar bashi ba kuma bama ita yake kallo ba “ Karki bari na sake maimaita miki magana ta Mimi! Finish it all .”


“ Ni bana jin yunwa , bazan iya cin su ba wallahi .” Duk da a tsorace tayi maganar , amma sincerely speaking , gaskiyar ta kenan ta fad’a sabida d’azu ba ‘karamun musun shan ice cream d’in nan sukai ba , har da na Allah ya isa sai da suka sha shiyasa ko waccen su cikinta yayi full sosai . 


“ Karki bari na sake maimaita maganata
.” Yanzu a hankali yayi maganar yadda ita kad’ai ce zata ji me yace.

Da sauri ta mayar da ‘kwallar idanuwanta sabida a yanzu kam ji take kawai zallan mugunta ne wannan yake mata tunda tace ta ‘koshi amma kuma ya’ki acknowledging hakan.

Strawberry ice cream d’in da yake gabanta ta soma janyowa , ta d’auki spoon d’in shan ice cream d’in, akaro na farko da ta saka a baki , sai taji ice cream d’in ma bai mata dadi ba ga baki d’aya , har wani d’aci d’aci taji harshenta yana mata.

Kallan ice cream d’in tayi, sai kuma ta kallesa ko zai ce ta barshi, amma bai ma san tanayi ba sabida fuskarsa ga baki d’aya bata wajan ma .

Haka ta kuma d’aukar wani spoon d’in tasha , duk da taji kamar za tayi amai amma haka ta had’iye . 

A spoon na hudu da tayi ne taji ba zata iya ‘karasawa a bakinta ba , yasa ta d’an tsaya tana zaune numfashi , dan ji take ko wana irin lokaci ma zata iya amayar da wanda tasha 

.

A ‘bangaran Ameerah ita ko ta’ba kayan ba tayi ba ta kalli Alameen “. Dan Allah kayi ha’kuri shine maganar da ta soma fito mata bayan shi kuma babu wani abu da tayi yun’kurin cewa .

Babu yabo babu fallasa ya furta “ Kar na sake miki magana akai , finish everything thing .”

Haka ta janyo ice cream itama ta bud’e tana sha kafin ta d’an tsaya, gwanda ita ta ‘ko’karta tayi spoon 10 ba kamar Mimi da tayi ba , kuma tana shan na goman ta ajje spoon tana fad’in “ Allah ba zan iya sha ba , idan nasha wannan abun amai zanyi wallahi.”

Without any care a kan face d’in Alameen ya furta “ Haka zaki shanye sa , ko kina so ko bakyaso, you guys love sweet thing ai ko? Am helping you , so maza jigaba da sha
.” Yayi maganar yana tsareta da idanuwa , haka dan dole ta soma tura ice cream bakinta , ga sanyi gashi kuma taji ya dena yi mata dad’i . 
Spoon 3 ta sakeyi ta ajje spoon d’in tana sun kuyar da kanta ‘kasa .

“ Cikin ki ya çıka ko?” Yayi mata tanbayar yana kallanta . 
Da sauri ta jinjina masa kai alamar “ Eh 
” sai ya mi’ke tsaye yana rufe ice cream d’in, Ameerah ta sauke ajiyar zuciya a tunaninta ai ya ha’kura ne , har yaje yasa ice cream a fridge, sai a time d’in Ameerah ta d’an samu chance d’in duba Mimi, ganin ta zaune da robar ice cream wani dariya yazo mata , amma kuma bata bari tayi dariyar ba ta had’e abunta sabida Moh da yake wajan . 

Tana cikin had’iye dariyar Alameen ya fito ya kalleta “ Let’s go Ameerah..” yayi maganar yana nufar hanyar fita , amma bawai ta main door ba , ta backdoor d’in part d’in . 

A tunaninta  shikenan an gama da ita , tayi saurin mi’kewa tana fad’in “ Nagode .” Bai ce mata komai ba kuma bai AMSA mata ba , suka fita backdoor.

Wajan so silent ne , sai kaga kamar wani gida ka shiga da ban sabida wajan akwai compound babba me kyau , yana da fad’i sosai da sosai, iska tana faman kad’awa wajan so dummy akwai haske amma bawai irin can sosai ba . 

‘Dan tsayawa Ameerah tayi sabida batasan hanyar da zata bi ba ta koma part d’in nasu shiyasa cikin rashin sani ta furta “ Uhm uhm Uncle Alameen ban.. bansan wajan ba..: taya
” sai tayi shiru ganin ya kalleta . 

Lokaci d’aya yayi mata murmushi “ Bakisan wajan ba ko?.” Tayi masa murmushi tana d’aga masa kai cikin confusion
.”

“ And kin ‘koshi sosai ko?” Ya kuma yi mata tanbayar ita kuma ta sake jinjina masa kanta alamar eh . 

Wani murmushi Alameen yayi yana nuna mata compound d’in “ Don’t worry yanzu zaki dawo dai dai trust me. 

So now abunda zaki soma shine jogging , trust idan kika gudun 10 minutes zaki ji cikin ki yayi normal .”

“ Jogging kuma?” Kamar za tayi kuka tayi tanbayar .

Shi kuma ya jinjina mata kansa “ YES or ba zakiyi ba?,”

Shiru Ameerah tayi babu bakin magana hakan yasa ya furta “ Then start . Kafin na canza shawara.”

Karo na farko da Ameerah take so ta fad’i abunda yake ranta tun d’azu , ga kwalla da suka soma sauko mata a zuciya , idan ta kalli idansa tace za tayi masa musu sai taga bata da wannan zarran hakan yasa ta goge kwallanta , ta soma gudu a cikin compound d’in.


Mimi kuwa tana zaune tuni ‘kwalla ya soma durowa akan fuskarta dan ba zata iya shan wannan ice cream d’in ba , bai ce mata komai ba , ya gama danne dannen da yake wayarsa kusan 25 minutes, tukunna ya ajje wayar. 

Ganin yanzu hankalinsa zai dawo kanta ta soba zubar da ‘kwalla duk dan sabida ya ha’kura da maganar shan ice cream d’in . 

Kallan ice cream d’in da ya soma melting yayi, kafin ya kalleta , gashi itama d’in shi take kallo irin kallan tsoran nan da rashin mafita. 

Gaze d’insa ya canza,hakan yasa tayi saurin saukar da idanuwanta ‘kasa tana d’an wasa da hannunta.

“ Mimi
.” Ya kira sunanta , ba cikin cold ba sannan ba gentle ba . 
Da ‘kyar ta iya fad’in “ Naam
”


“ Do what I asked you to do, 20 minutes na baki
.”


Cikin sauri ta had’e hannayenta biyu alamar ro’ko tana zama akan ‘kafafuwanta “ Dan Allah kayi hakuri Uncle Moh, wallahi ba zamu sake ba 
.”

Kallo d’aya yayi mata ya d’auke kansa, yama jinginar da jikinsa a kan kujera yana lumshe idanuwansa , hakan yasa taji kuka yanasan zuwan mata , rai a ‘bace ta d’an goge hawayen, ta d’auki robar ice cream bata ma d’auki spoon ba ta soma shan ruwan da yayi melting. 
Tana tsakiya da sha tari ya d’an ‘kwace mata , shiyasa ta ajje da sauri, ga kuma aman da yake ‘ko’karin tahowa. 
Da sauri ta mi’ke tsaye , ta wuce d’akin da aka kwantar da ita lokacin da bata da lafiya tunda a ‘kasa ne, ta wuce tai amanta , kuma sosai tayi aman, tana gamawa ta gyara wajan , ta wanke face d’inta sosai da bakinta tana ajiyar zuciya, tukunna ta bud’e ‘kofa zata fito. 

‘Kırgınsa da yake wajan ne ya d’an tokareta, bata san yana wajan ba har sai da ta d’an buga kanta da jikinsa, tana saurin komawa baya kad’an da mamakin ganin sa a wajan. 

Amma sanın  cewa ta dalilinsa tayi aman haushinsa ya kamata , ta ra’ba zata wuce , yasa hannu a ‘kugunta ya dawo da ita cikin ban d’akin. 

Again ta kuma ‘ko’karin wucewa za ta fita , sai bai ri’ko ta ba , ya bari ta fito daga cikin toilet d’in, sai dai hannunta da ya ri’ko, ya d’an janyo ta kad’an yana jinginar da ita da jikin bango . 

Take zuciyar Mimi ya soma bugawa boom boom boom
..

“ ‘Dago ki kalle ni.” Yayi maganar kamar cikin rad’a . 

‘Dan d’agowa tayi ta kallesa, zata janye idanuwan amma ya tsayar da ita ta hanyar shigar da nasa idanuwan. 

Sosai ya ‘kure ‘kwayar idanuwanta da kallo na wasu mintuna, lokaci d’aya wani murmushi ya d’an sauka akan la’b’bansa wanda ta kasa ganewa ma’anar murmushin, sai kuma ya kama hannuwanta guda biyu yana kallan tafin hannun nata  , nan d’in ma wani dirty smile yayi , sannan ya kama hannun zai kai baki, ma’ana zai yi kissing d’in hannun sai tayi saurin janye hannunta tana ‘boye su duka a bayanta , yadda bazai ‘kara kamawa ba .

“ What? Hannun naki ne bakya so nayi kissing?”

Yau da confidence d’inta ta furta “ Yes ai ba miji na bane kai kuma kasan Allah ya hana wannan kuma zunubi ne , idan kayi
” bata ma ‘karasa ba yayi mata peck  a baki , ita kuma tayi saurin d’auke fuskarta , tana d’aukar hannu zata saka a bakın, cikin sauri ya janye hannun yana d’an d’ago wuyanta da ‘karfi har sai da taji zafi sabida aush d’in da tace .

“ Ni zanyi kissing d’in ki , ki saka hannu a baki? Me zakiyi? Don’t you dare try that , if not you will regret it.”

“ Uncle Moh wai ya kake so nayi, taya za’ai dan Allah ka d’inga kissing d’ina bayan ni da kai munsan hakan haramun ne , ni wallahi banaso ka dena , banaso Allah yayi fushi da mu, nidai ka bari Allah banaso.”

Shiru yayi for second, tayi tunanin ko be ji abunda tace sosai ba , shiyasa ta d’an d’ago da fuskarta tana kallansa, aushe shid’in ma kallanta yake kuma har ta saukar da idanuwanta ‘kasa bai dena kallanta ba . 


“ Mimi can you wait for another 7 days ?” Kamar Wanda yayi magana a zuciya haka yayi maganar, ita kuma bata jisa sosai ba sai tace Uhm?”. 


“ in the next 7 days your birthday right?”.

Ta d’aga masa kanta alamar “ eh .” 
“ Then you can asked me anything you want to know and I promise to tell you everything! I mean everything
”.

Batasan lokacin da ta furta “ But why?”
.

Sauko da face d’insa yayi dai dai face d’inta , ya d’an d’ora goshinsa akan nata , sannan ya d’ora karan hancinsa akan nata , hakan yasa suke iya sha’kar numfashin junan su sosai. 

Hakan da suke ya furta “ Don’t worry , ki soma counting  in the next 7 days but you will pay a huge price
. Let go back , ki shanye ragowar ice cream d’inki
” ya d’an matsa yana ri’ko hannunta ita kuma ta’ki motsawa hakan yasa ya kalleta .

Kamar za tayi kuka “ Uncle Moh wallahi bazan iya shaba , idan nasha amai zanyi sosai .” 

“ Then sai ki yi aman, but you most finish it 
. That’s your punishment.” Bai ma bata wani chance d’in magana ba ya soma tafiya da ita , ita kuma sai faman ‘bata fuska take amma babu abunda ya canza zani a hakan, ya dawo da ita falo ya d’auko ice cream da da ya saka a fridge ya mi’ka mata , ita kuma ta d’an marairaice masa fuska tare da turo lips d’inta , shi kuma a maimakon yayi acknowledging yadda tayi da fuska sai ya saka hannu yana shafa lips d’in , har sai da taji wani iri ta mayar dashi. 

“ Don’t try what you did again Mimi

 if not , I won’t forgive you Mimi kinji?”. Da sauri ta d’aga masa kai alamar tohm .

Sai ta juya zata bar wajan, ya dakatar da ita ta hanyar sake ambatan sunanta “ Mimi?.” 
Ta d’an waigo ta kallesa .

“ You can go
.” Ya fad’a yana d’auke kansa, ita kuma tayi saurin fad’in “ Good night..” .

Da kai kawai ya amsa mata ba tare da yace komai ba, ita kuwa da sauri ta bar wajan sabida kada ma ya tsayar da ita , yana ganin irin saurin da take kuma amma sai yayi kamar bai ganta ba , har ta fice daga sashen. 

Sai a lokacin  ya d’an d’ago face nashi ya kalli hanyar da tafi “ Mimi will you really take what’s coming?”. Yayi maganar cikin low voice da duk ‘kwa’kw’kwafin ka ba zaka gane me yace ba . 


Mimi tana fita kuwa ‘kafa kif mai naci banbaka ba , ya gudu part d’in sun. 

A nan ta tarar da Aya da kuma a kwati guda biyu, Aya d’in kuma tana tsaye , da waya a hannunta , hakan ya nuna waya take.

‘Dan tur
 Mimi tayi tana kallan jakun kunan da mamaki duk da dai bata fito tayi magana ba , har abunda Moh yayi mata yanzu  yaso kauce mata ma. 

Aya da take waya kuma da hannu tayi mata nuni da part d’in Mamy.

Babu shiri Mimi tayi saurin ajje ice cream d’in ta nufi part d’in Mamy a guje .

Tana zuwa bata ma tsaya ‘Kwan’kwasa ‘kofa ba kawai ta bud’e ’kofar , wad’an da ta gani a tsatstsaye ne yasa ta ‘kwalla wani ‘kara ta nufar su za tayi hugging d’in su . 
Mamy ne da Baffa suka dawo sai Shukura da take tare dasu .

Gabaki d’aya dariya ma suke mata sabida abunda tayin yanzu,

Baffa ne ma ya furta “ Oh ni Mimi na har yanzu dai batasan ta girma ba , ko dai mu koma bakiyi kewar mu ba?”. 

Turo baki Mimi tayi “ Haba Baffa wallahi 2 days d’in nan da kukayi nayi missing d’in ku sosai , ka tanbayi ma Aunty Shukura , zata sheda hakan wallahi naji dad’i da kuka dawo , thank god ma da bakuyi kwanakin da kuka ce za kuyi ba .”

“Toh Allah ya shirye ki Mimi , tunda ba zaki bari mu huta ba kafin ki soma complain d’in nan naki Mimi
.” Cewar Mamy tana d’an hararar ta.

“ Baffa , kaganta ko ?.” Tayi maganar cikin turo lips .

“ Rabu da ita Mimi, kisan halin Mamyn nan taki , bata so taga muna rahanmu sai tayi kishi, ya kike Mimi na ? Hope you enjoyed your day
”


“ No Baffa gidan is so Boring wallahi da bakwa nan , but why did you guys change your mind? Like kunje zakuyi weeks a think.”


“ Dole kema kinsan zamu dawo ai sabida school d’in ki , and muma mun kasa zama sabida bakya nan, wajan so boring Mamy har cewa tayi dama mun taho dake.”

Kallan Mamy, Mimi tayi ganin ta d’auke face d’inta tana d’an ‘ba’b’bata rai na wasa yasa dĂŒk kowa yayi dariya Mimi kuma ta ‘karasa wajanta tana rungumeta tare da fad’in “ Mamy na
. My mozaa
..”


“ Yanzu Mamy ni bakuyi kewata ba sai Mimi , ni da nake zuwa school atleast ai ya kamata ku bani duk attention d’in ku, ku ‘kyale Mimi haka .” Cewar Shukura.

Kafin kowa yayi magana Mimi tayi mata gwalo “ Eh d’in waya ce ki ‘ki zuwa a ‘yar auta .”

Fito Shukura ta d’auko zata ‘kwala mata Mimi tayi saurin ‘buya bayan Mamy tana fad’in “ Mamy kin ganta ko?”


“ Wallahi daga dawowar mu Mimi ba zaki soma sani magana ba , naga lokacin baccin ki yayi , kema Shukura lokacin karatun ki yayi duk kowa yaje yayi harkan ga bansan bawai kuzo kuyi ta samu magana ba , ku in magana  baya damun ku , toh mu yanayi ya kamata ku bar Baffa haka ya huta 
”

“ Kai Mamy
.” Kusan time d’aya Mimi da Shukura suka had’a baki, hakan yasa Mamy ta mi’ke tsaye, duk sun san halinta kuma shiyasa sukayi saurin yi musu good night suna fitowa , a time d’in ne ma Mimi take cewa Shukura “ Aunty Shukura daman kin san zasu dawo shine kika ‘ki fad’a mun?.”

“ Ke nima bansan zasu dawo ba , kawai gani nayi Aya ta shigo dasu , aushe already tasan da dawowar su ? Kuma kika tafi shan ice cream ke da Ameerah? Dan naga Zarah yau sabida shim
She’s less busy kawai sai naga tana sharan part d’in nan bayan all maid da suke cikin gidan nan but ace za tayi sharan falo da daddare ? Wai ‘kafarta ciwo yake , and ku kuma kun tafi shan ice cream , ina ma kuka je?.”

A maimakon Mimi ta amsa mata sai ta jefa mata nata tanbayar itama “ Zarahn ce ta zauna shara kuma da daren nan?.”

Kai Shukura ta jinjina mata duk d itama tayi mamaki , da sauri Mimi ta furta “ Ina zuwa Aunty Shukura 
” daga nan tabar wajan da sauri bata bari ma Aya ta tsayar da ita ba ta wuce part d’in su Ameerah , lokacin tasan Mama tana part d’in Uncle Bashir tunda taga motar sa alamar ya dawo shima. 

‘Dakin Ameerah ta nufa tana zuwa ta ‘Kwan’kwasa sau d’aya sannan ta bud’e ’kofar . 

A kan gado ta hango Ameerah tayi nashe nashe ko motsin kirki ma bata yi . 

Ganinta da Mimi tayi a haka ta wani ‘kyal’kyale da dariya tana ‘karasowa wajan nata . 

Hannu ta sa ta d’an d’aka mata duka cikin wasa , ita kuma Ameerah ta d’ago da fuskarta ta harareta tana ‘kara komawa kwancen da take . 

Cikin dariya Mimi ta furta “ Haba ‘kawalliya , wannan hararar ta mece ce ? Bani na kar zoman ba fa.”

“ Toh idan bake bace wacce ne? Aushe wannan guy d’in mugu ne , sai yayi ta faman yin murmushi kamar na Allah aushe ‘kasun gumin mugu ne . Har da Jogging fa ya sani, Wlh inayi sau d’aya nayi sumar ‘karya shikuma ya juya zai d’auko ruwa tuni na arcs duk da bansan hanya ba haka na samu na dunga zagane har na gano hanya wallahi babu ni babu biye miki. 
Ke kin riga kin saba da mugancin Uncle Moh ni kuma ban saba ba Allah dai ya isa na , wallahi abokin Uncle Moh d’in nan mugu ne .”
 Wani dariyar Mimi ta kuma ‘kyal’kyalewa dashi har da hawaye tana fad’in “ Aa fa , kar muje ayi irin na novel ku fad’a soyayya daga baya .”

“ Allah ya tsaye , wallahi babu me rabani da Abdul d’ina ( Her boyfriend)
.”

“ Lalle yayi miki kyau me boyfriend
”

Ameerah bata ce mata komai ba sai da ta soma janyo hannunta ta zauna “ Mimi kinga Zarah kuwa yanzu?”.

“ No why?.”

“ Lokacin da na fito fa naganta zata je part d’in su sai na tsayar d Ita , wallahi wani irin harara ta bankamun tana ja mun tsaki kamar wacce tayi mata wani abu.
Kamar irin taga wata ma’kiyarta , naga dai lafiya muka barta .”

Hannu Mimi ta bud’e cikin halin ko ina kula ta furta “ Thats her own cup of tea 
”



📱 LITTLE ANNOUNCEMENT đŸ€đŸ“š

Book 1 zai ƙare a Page 50 đŸ„č📖

Duk wanda yake son ci gaba da karanta Book 2 & 3, farashin yanzu shine ₩800.

Once Book 1 ends, the price will be ₩1,000.

So idan kina/kana son ci gaba da journey ɗinmu, ₩800 offer ɗin nan yana nan har zuwa Page 50. đŸ€

Payment Details:
🏩 Bank: ZENITH BANK
đŸ‘€ Account Name: AISHA UMAR 
💳 Account Number: 2681892316

Bayan kin biya, ki turo proof of payment + sunan ki domin a tabbatar da payment ɗin. ❀

Thank you so much for all the love and support! đŸ„čđŸ€đŸ“š



_________________

To be continued
 đŸ”„


Aysha Galadima đŸ€đŸż
***


***