MISHAL

Page 42

by @ayshagaladima22

MISHAL



By AYSHA GALADIMAđŸ€đŸż
***


BOOK 1 
Page 42 

“ Moh you’re not nice at all , ji yarinyar nan yadda ta gudu , sai kace wani monster , nasan yanzu kallo na zata dinga yi kamar wani mugu mugu ko?.” Alameen yayi dariya lokacin da yayi maganar. 

Moh kuwa ko uffan bai ce masa ba, yana position d’insa akan kujera , hannunsa biyu yayi folding d’insu a ‘kirjin sa, idanuwansa kuma a kulle kamar me ‘bacci.

Girgiza kansa Alameen yayi “ Won’t you say anything? Ka barni ina magana ni kad’ai , ko kuma halin ne ya motsa? Mr Moh?”.

“ Alameen tashi ka tafi gidan ka .” Shine first word da ya fito daga bakin Moh ba tare da ya bud’e idanuwansa ba , maganar kuma ta kasance ‘kasa ‘kasa yayı ta, shima Alameen dan ga baki d’aya hankalinsa yana kansa shiyasa ya iya gane abunda ya fad’a . 

“ Babu inda zani Moh! Ka gama abunda kake so kayi ai dole ka kore ni, toh babu inda zanje , better open your eyes
. and let’s talk 
”


“ So noisy
.” Cewar Moh , yana bud’e idanuwansa akan Al’ameen d’in.

“ Ko me zaka fad’a ai sai dai ka fad’a , it’s better ka dena mun wannan mulkin naga and let’s talk, we need to talk , like damn seriously kasan de abunda yake fuskanto ka ko? And  kalli yadda kayi relax kamar babu abunda ya dameka ma kwata kwata.”

“ Okay me yake fuskanto ni?”.cewar Moh yana d’an gyara zaman akan kujera.

Finger d’aya Alameen ya d’aga masa , fuskarsa ta d’an nuna mamaki even though he’s not that shock “ No Man ! Kar kace mun you’re just okay 
. No no no
”

“Alameen na fad’a maka you’re just putting so much headache on me
 ko kayi mun shiru , ko ka tafi gidan ka , baka gajiya da magana ne ?”.

“ Moh ai dole ka fad’i haka mana, and you can say whatever
.. but me ? Babu inda zanje ni kad’ai, kasan ya kamata ku ‘karasa abunda muka d’auka a kwanakin nan, please let’s go mana kaji?”.


“ Why ? You can do it alone , dan haka kaje kayi what you need to do.”

“ No Moh! Please wannan kamar abun da banbanci , dole muje both of us and kasan da hakan ko? Just let’s go and fresh up and do what we need to do !!!!!  Please Man

”

“ Hmmm 
.” That’s the only answer the Moh ya bayar .

Shi kuma Alameen ya ciro waya a aljihu ya d’anyi danne danne , yana d’an d’agawa Moh girarsa guda d’aya . “ But before that ! You have to see this Moh
.” Ya mi’ka masa wayar. 

Kar’ba Moh yayi yana kallan abunda yake ciki na wasu ‘yan mintuna, hankalinsa sosai ya mayar cikin wayar, gashi ba’a ta’ba gane expression d’insa , balantana ko mutum ya fahimci abunda ya gani cikin wayar .

Bayan kamar mintina biyar ya mi’kawa Alameen wayar yana mi’kewa tsaye , tare da fad’in “ Let’s go
.”

Alameen bai ce masa komai ba ya mi’ke suka fita a tare , shi yana driving , Alameen kuma yana d’aya side d’in, suka fita daga gidan , lokacin kuma dare yayi sosai , dan fitilun kowana part a kashe yake alamar an kwanta sabida kusan past 1 lokacin. 


~
‘KARFE 2:59am na dare lokacin da mafi akasin mahalu’ki na cikin gidan nan sun kwanta sai wad’an da suka hana idanuwan su bacci ko makamancin hakan. 

A ‘bangaran Mimi itama sosai tayi nisa cikin baccinta, kuma da alama tana jin dad’in baccin da yake daga yanayin kwanciyarta , dan har duvet d’inta ya zame daga jikinta ya koma iya cikinta , ‘kafafuwanta duk suna waje yana bacci rungume da pillow abunta . 

Fuskarta looking so very innocent and cute kamar wata ‘yar yarinya, duk da d’akin nata babu wani haske sosai dan ta mayar dashi dummy amma hasken dare da kuma wata yana d’an haskowa ta çıkın d’akin har ake iya ganin fuskarta ma da take bacci. 

A hankali aka murd’a handle d’in ’kofar d’akin Mimi, ko sound d’aya na bud’ewar ‘kofar babu sabida yadda akayi ta a hankali cikin ‘kwarewa . 

Koma wane ne ya bud’e ‘kofar akwai ba’kar safa a hannunsa da ta rufe ‘yan yatsun hannunsa ga baki d’aya , da kuma wata doguwar riga ba’ka itama , fuskar a rufe ba’a gane koma wane ne yake shigowa d’akin. 

Haka ya shigo ga baki d’aya , sannan ya rufe ‘kofar nan ma babu wani sound da yake fitarwa ko kad’an .
Rufff aka rufe ‘kofar d’akin Mimi, ita kuma tana bacci batasan abunda yake faruwa ba da alama baccin nata yayi nisa sosai a wannan time d’in.

Wani abu aka ciro kamar dutse , tare da wani ‘karamar kwalba cikinsa farin abu ne kamar ruwa . 

Haka wanda ya shigo ciki ya bud’e ya sha wannan abun, ragowar kuma ya zuba a cikin abun hannunsa mai kama da dutse , yana murtsukawa a hankali, yana kuma tafiya dai dai gadon Mimi, daga farko har zuwa gefen inda zaka wuce haka ya soma tafiya yana murtsuke wannan abun.

Anyi haka kamar sau uku sai aka d’auko siriri abu me kama da ‘kyalle , ko kuma igiya aka d’aura a hannun hagu
 

Aka sake d’auko wani siririn afu fari tassss sabida yana da d’an tsaho a hannun mutumin shiyasa har ake iya ganinsa sabida kamar wani sharp object har kyalli yake dashi. 

Nunkawa akai gida biyu , ja d’an ja abun a hannunsa kad’an , take safar hannunsa ya d’an yanke alamar koma mene ne yake hannunsa is very sharp tunda zai iya yanka abu cikin ‘kan’kanin lokaci 


Koma wane ne yake tsaye , kallan Mimi yayi na kamar minti d’aya cif , sannan ya soma matsowa kusa da inda take , ko wana taku anayinsa a hankali cikin kulawa da kuma taka tsantsan, a haka aka ‘karaso inda Mimi take a kwance. 

Aka saka hannu aka d’an yaye duvet da yazo yanzu har wuyanta, kanta kuma a d’an sunkuye yake , shiyasa wuyanta be fito sosai ba , pillown da take kwance akai aka d’an ja kad’an, hakan yasa Mimi ta gyara kwanciyarta cikin bacci. 
Wanda yake tsaye ko tsoran ta farka ba yayi ko ba tayi, sabida ko motsawa bai yi ba ko batai ba daga inda take . 

Ganin wuyan Mimi kad’an ya fito aka d’aga wannan abun, zuwa dai dai saitin wuyanta , saura kad’an abun ya ta’ba fatar wuyan Mimi, kawai sai ga Mimi ta d’aga hannu ta d’an buga akan pillow da ‘karfi, hakan Yasa wacce take tsaye tayi saurin d’an ja baya daga yanayin position d’inta tana kallan Mimi. 

Sai kuma jikin Mimi da ya sake mirginawa kusan sau biyu akan bed, idan da ace farkon dare ne , mutum sai yayi tunanin Mimi tana sane tayi wannan abun yanzu.

‘Dan ja baya kamar taku biyu wacce take tsaye tayi, da alama kallan Mimi take , tana observing yanayinta . 

Knock ! Knock akai knocking ‘kofar Mimi, cikin sauri ta mayar da abun hannunta cikin rigarta da ta d’auko , tana kuma ja baya cikin taku. 
Takun ‘karshen ne kamar bata san tayi wanda sai da ta d’an dakata na wasu seconds tukunna tayi su, tare da barın inda Mimin take ga baki d’aya tana komawa wani side d’in. 

Sai kuma ragowar hutar part d’in tunda ba duka ake kashewa ba ta d’auke ga baki d’aya , har ta window Mimi ana iya ganin duhun part d’i , sannan kuma knocking d’in da ake ak dena shi. 

Cikin sauri ta koma bayan ‘kofa , tsawan mintuna 15 , tana sauraran yanayin waje, babu movement ko guda d’aya a wajan, sai ta saka hannu akan handle d’in na ‘yen seconds kafin a murd’a a hankali abud’e ’kofar . 

Yanzu ma cikin observation sosai, aka ‘karasa bud’e ’kofar sannan aka fita daga d’akin Mimi , ana sake rufo mata ‘kofa a hankali. 

Daga cikin d’akin Joy da take gefe d’aya ta fito da jikinta sosai, duk da tana nesa da inda Mimi take . 

Bata ‘karasa wajanta ba , sai dai tayi murmushi kawai yana kallan yadda  take bacci cikin kwanciyar hankali abun ta . 

Daga waje kuma lokacin da wacce ta shiga d’akin Mimi ta fito, bayan ta soma sauka ‘kasa a hankali Aya ta fito daga cikin corridor d’in da take tuntuni, jikinta sanya da ba’ka’ken kaya, da kuma face mask, da idanuwa da yanayin gashin kanta kad’ai mutum zai iya gane cewa ita ce shima sai wanda yayi mata farin sani sosai, dan kayan da ta saka duk ya rufe mata jiki, har ‘yan yatsunta ba’a gani. 

Kallan wacce take sauka daga stair case d’in Aya tayi, kafin ta saka hannu ta d’an zade face mask d’inta , fuskarta sam babu fara’a kamar ba Aya ba , daga inda ta tsaya kuma ita tana ganin me sauka amma ita wacce take saukar ba zata ta’ba tunanin akwai mutum a wajan ba , har ta fita daga part d’in ga baki d’aya .



_________________

To be continued
 đŸ”„


Aysha Galadima đŸ€đŸż
***

***