Page 1
SAWU BIYU
BY
KHADIJAH SULAIMAN
Young Talented Writers Association (YOTA)
Book 1
Page 1
2:15 AM
Dajin yayi tsit ba ka jin motsin komai sai na ƙwari da busassun ganyayyaki,cike da taka tsantsan sojojin ke cigaba da rarrafe suna ƙara kutsa kansu ba tare da damuwa da duhun dajin ba.
Wanda ke gaba ya gyara na'urar sadarwar dake kunnen sa ya yiwa sauran alama da hannu alamar su dakata.
"Falcon,this is Eagle Command. Do you copy?"
Yace"Eagle Command,Falcon. I copy. Go ahead."
Daga can ɓangaren aka ce"Change of direction. Move east immediately."
Yace"Copy that, Eagle Command. We're moving immediately."
Ya juya ya kalli sauran yace"Change of direction. We're moving east."
Ba tare da ɓata lokaci ba su ka fuskanci gabas,cike da ƙwarewa da sanin makaman aiki yake nazarin wurin.
Sun yi tafiya mai ɗan nisa yayi saurin dakatar dasu,ya ɗurkusa ya kai hannu ya shafa wurin,da mamaki ya kai hannun saitin hancinsa,jin abinda bai yi tsammani ba yasa shi saurin cewa"Falcon Team.HALT! Hold your positions!"
Yana rufe baki wani ƙara mai rikitarwa ya karaɗe wurin,da sauri ya juya,ganin wasu kwance a ƙasa ba rai yasa da ƙarfi yace"Falcon Team! Stay together! Do not scatter! Maintain formation!"
Yana gyara bindigar hannun shi yace"Return Fire".
Take dajin ya hargitse,hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yadda sojoji ke zubewa a ƙasa,da ɗan ƙarfi yace"Medic,attend to the injured".
Saukar bullet da yaji a kan damtsen hannun shi yasa yayi saurin dafe wurin yana cije baki.
Wanda ke kusa dashi yayi saurin riƙo shi yace"Sir,you're bleeding".
Ya ɗan lumshe ido yace"I'm fine,keep moving".
"Sir...".
A tausashe yace"i said I'm fine".
Cike da taurin zuciya ya cigaba da musayar bullet da waɗanda ko ganin su ba'a yi,duk yadda yaso ƙarfafa kansa hakan ya faskara, don lokaci ɗaya ciwon dake jikinsa ya rinjayi ƙokarinsa.
--------
A hankali yake kokarin buɗe idonsa har ya ware su tas yana bin ɗakin da kallo,cike da zafin nama ya yunƙura zai tashi,ya koma ya kwanta tare da cije baki jin zafin da ya ratsa har cikin kwakwalwar kanshi.
Sai da ya ɗan sami nutsuwa sannan ya tashi ya zauna yana bin hannun da kallo.
Jin ƙaran taɓa kofa yasa ya ɗago,kallo ɗaya yayi masa yasa hannu ya cire ƙarin jinin da ake masa ya mike tsaye,farin T shirt daya gani kusa da gadon ya ɗauka.
Ba tare da ya kalle shi ba yace"Ƙarfe nawa?"
Dr yace"this is after ten".
Ya cije baki da ƙarfi ya wuce shi ya shiga toilet,bai wani daɗe ba ya fito ya shinfiɗa darduma ya tada sallah.
Sai da ya gama duk adduoin shi sannan ya miƙe cike da dauriya ya nufi ƙofa.
Da sauri Dr ya ƙaraso kusa dashi yace"Lieutenant,you need to rest".
Ba tare da ya juyo ba yace"How many Casualties?"
"Sir..."
"How many?"
Yayi shiru ya kasa bashi amsa,ya gyaɗa kai ya buɗe kofa ya fita.
Headquarter tayi tsit tamkar babu mutane a cikinta,tsirarrun sojojin dake kai komo suka dinga bin shi da kallo.
Yana isa gaban office ɗin yayi knocking a nutse,sai da ya jira aka bashi izini sannan ya shiga.
Suna zaune kusan su uku ya gyara tsayuwa tamkar babu ciwo a jikin shi ya sara musu.
Brigadier General ya kalle shi da wani irin expression yace"Lieutenant Sadauki".
Cike da girmamawa yace"Sir".
"What are you doing here?"
Cike da nutsuwa yace"I came to give my report,Sir".
General yace"You were ordered to remain in the medical facility, yet you disobeyed that order and came here. Do you understand how serious your conduct is, Lieutenant?"
Sadauki yayi shiru ya kasa bashi amsa, Brigadier ya miƙe tsaye cike da ɓacin rai ya jefa masa file ɗin hannun sa kan table,nan take idon shi da su ka canza launi su ka sauka kan abinda ke rubuce a file ɗin
Personnel involved :47
Killed :6
Wounded :11
Uninjured : 30
Mission : failed
Hostages : not recovered
Ya ɗauke kai daga kan file ɗin yana jin yadda kanshi ke wani irin sarawa kamar zai rabe biyu.
Brigadier ya buga table ɗin gaban shi yace"ka san abinda kayi kuwa,ka san abinda carelessness ɗinka ya jawo mana?sojoji shida sun rasa rayuwarsu,wasu sun samu raunuka duk ta dalilinka,mission ne mai ƙarfi da aka jima ana targetting amma duk ya tashi a banza saboda kai".
Ya lumshe ido jin yadda jikin shi ke wani irin rawa tsabar ɓacin rai,yayi ƙoƙarin controlling kanshi yace"Sir, I followed the information transmitted to my team".
Da ƙarfi ya sake buga table ɗin yace"don't give me excuses,ka bar route ɗin ainihi ba tare da umurni ba ka nufi wani wuri daban,ka jefa sojoji da yawa cikin hatsari wanda hakan ya lalata ƙoƙarinmu na dogon lokaci".
A hankali yace"Sir,nayi tunanin information ɗin was genuine".
Brigadier ya mishi wani kallo yace"ka yi tunani?ai kaga inda ka sami problem Lieutenant, believing isn't enough,you verify".
Ya jawo file ɗin gaban sa yana sake karanta abinda ke rubuce,kallo ɗaya za ka masa ka hango tsantsan takaicin dake rubuce a fuskarsa,ya ɗago ya kalli Sadauki da kanshi ke ƙasa yace"an zaɓe ka ne saboda Colonel Musa yayi recommending ɗin ka,so tell me,ka na da abinda za ka faɗa masa right?"
Har lokacin Sadauki ko motsi bai yi ba,ya koma ya zauna ya janyo wani takarda yayi rubutu yayi signing ya tura mishi yace"Lieutenant Umar Muhammad Sadauki,bisa la'akari da abin da ya faru da kuma bukatar gudanar da cikakken bincike, daga wannan lokacin an dakatar da kai daga duk wani aiki har sai an kammala bincike."
"Za ka miƙa kayan aikinka, ciki har da uniform da makamin da aka ba ka.
Ba za ka yi amfani da wani iko ko damar da matsayinka na soja ya ba ka ba, har sai an sake duba matsayinka."
Idon shi a ƙasa yace"Yes, Sir".
Yana fita ya nufi Unit Administrative Area yayi handling Uniform ɗin shi da bindigun shi yayi signing ya fita.
A hararbar wurin ya hango Bilal dake ƙoƙarin shiga ciki,yana ganin shi ya ƙaraso kusa dashi fuskar shi ɗauke da damuwa.
Sadauki yayi tapping bayan shi ya nufi inda yayi parking.
Bilal ya buɗe mishi kofa ya koma ya shiga driver seat,babu wanda yace komai a tsakanin su sai muryar Sheik Sudais dake tashi cikin motar cike da nutsuwa.
Sadauki ya kwantar da kanshi kamar mai bacci,ba tare daya buɗe ido ba yace"Su waye suka rasu a daren jiya?"
Bilal ya sauke numfashi yace"Ola,Kayode,Daniel,Bello,Chinedu da Yusuf".
Da wani irin tashin hankali ya juyo,Bilal ya kasa juyowa ya kalle shi,ya san dole ya shiga tashin hankali.
Ya koma ya kwantar da kanshi ya shiga maimaita "innalillahi wainna ilaihi raju'un".
Suna isa ƙofar gida Bilal ya sauko ya sa key ya buɗe gate ɗin sannan ya koma ya shigar da motar ciki.
Da wani irin sanyin jiki ya buɗe kofar ya fito,da sauri ya dafa murfin motar jin jiri na ƙoƙarin zubar dashi.
Da taimakon Bilal ya ƙarasa parlour,ya gyara mishi pillow a ƙasa ya kwanta ya lumshe ido.
A hankali tace"ina wayata?"
Bilal yace"me za ka yi da waya yanzu?"
Ya buɗe ido da ƙyar yace"na san wayar a kashe take,bani Please".
Bai ce komai ba ya ciro wayar shi a aljihu ya miƙa masa,yasa hannu ya karɓa ya kunna wayar ya ajiye kusa dashi.
Ko minti biyu bai yi da kunnata ba ya fara jin shigowar saƙonni,vibration ɗin da yaji yasa shi lumshe ido,a hankali ya ɗago wayar, ganin sunan Mami yasa bai ɓata lokaci wurin ɗagawa ba.
"Faruq,tun ɗazu nake kiran layin ka a kashe,yanzu nake jin labarai,kana ina yanzu?"
A hankali yace"ina gida Mami".
Tace"gani nan zuwa".
Bata jira cewar shi ba ta kashe wayar,ya zubawa wayar ido ganin yadda kira ke rige rigen shigowa,babu wanda ya ɗaga a ciki sai na ƙarshen da aka rubuta Colonel.
Ya tashi ya zauna yana cije baki,daga can ɓangaren aka ce"Sadauki".
A hankali tace"Yes Sir,Good morning Sir".
Colonel Musa ya sauke numfashi yace"na sami labarin abinda ya faru,ka kwantar da hankalin ka har a gama bincike,ya jikin?"
A hankali yace"da sauki".
Colonel yace"Allah ya ƙara sauki".
Ya amsa da Amin ya kashe wayar,ya ɗora wayar kan kujera ya miƙe ya shiga bedroom ya cire kayan jikin ya shiga toilet,bayan kusan minti sha biyar ya fito da alamar wanka yayi ya shirya cikin riga mara hannu sai dogon wando ya fito.
A bakin kofa ya tarar da Bilal,kafin yayi magana Mami ta shigo Zarah biye da ita.
Ya zauna kan carpet don jikin shi babu wani ƙarfi yace"sannu da zuwa Mami".
Ta zauna kan kujera tana bin bandage ɗin hannun da kallo.
A hankali tace "Ya jikin?"
Yace"Da sauki Mami".
Ta sauke numfashi tace"Allah ya tsare ya kiyaye gaba,na ji kusan mutane shida sun rasu,Allah ya gafarta musu".
A hankali yace"Amin".
"Kun yi magana da Daddy?"
Ya girgiza kai yace"a'a,zan kira shi zuwa anjima".
"Amma me yasa ka bar asibiti da ɗanyen ciwo haka Faruq,bullet ba ƙaramin abu bane,ya kamata ka sami at least sati ɗaya under proper medical care kafin a sallame ka".
Ta juya wurin Zarah dake kallon TV tamkar bata wurin tace"zuba mishi abinci,kin gaishe sa kuwa?"
Bata kalle shi ba tace"ina kwana, ya jiki?"
Mami ta watsa mata harara tace"wani banzan hali ne wannan Zarah,mutum babu lafiya kin zauna ko kallon sa ba ki yi ba?zan yi maganin rashin kunyar ki wallahi,tashi ki zuba masa abinci ya sha magani kafin in ɓata miki rai".
Ta miƙe ta ƙarasa wurin basket da ta shigo dashi ta fito da plate da fork ta zuba mishi chips and egg sai tea da already Mami ta haɗa ta zuba mishi cikin cup ta ajiye kusa dashi.
Yana danna wayar shi harta gama ta koma ta zauna.
Mami tace"Bilal ya shiga ciki ne?shima ya zo ya karya na san ba lallai yayi breakfast ba".
Ya ajiye wayar hannun shi yace"zai fito Mami".
Mami tace"ka ci abinci don asibiti zamu tafi yanzu,ba za ka zauna da wannan ciwon a gida ba".
Yayi murmushi yace"kar ki damu Mami,zan iya kula da kaina".
Mami tace"sai dai idan ba Faruq dana sani ba,ƙaramin aikin ka ne yanzu idan aka ce akwai wani aiki ka kwashi jiki ka tafi,babu abinda za ka faɗa da zai yi convincing ɗina Faruq,ka cinye abincin nan mu tafi".
Babu yadda ya iya don ba zai iya mata musu ba ya gyara zama yayi bismillah ya fara cin abincin.
Bai wani ci da yawa ba don bakin shi babu taste kuma ba zai iya ce mata a'a ba shi yasa kawai yaci,ya ture plate ɗin ya janyo tissue ya share bakin shi,Mami dake danna waya tace"ba dai har ka gama ba?"
"Na gama Mami,bana wani jin yunwa".
Mami tace"babu zancen ba ka jin yunwa,sai dai idan abincin ne ya maka nauyi,mu tafi asibitin zuwa anjima sai a samo maka wani abin mai sauƙi".
Bai ce komai ba ya wuce ɗaki ya sake gyara jikin shi,Bilal dake kwance a gado yace"ina zuwa?"
A taƙaice yace"asibiti".
Bilal ya miƙe yace"ok,mu tafi".
"Akwai breakfast a parlour".
Ya girgiza kai yace"babu wani yunwa a tare dani,muje kawai".
Bai ce komai ba su ka fita,a waje suka tarar da Mami,tana kallon Bilal tace"abincin fa?"
Ya shafa kai yace"zan ci zuwa anjima Mami".
Ta taɓe baki tace"daga kai har abokin ka ba ku son cin abinci,ayi ta fama da mutum kamar a cikin wani za'a zuba".
Bilal yayi murmushi ,Sadauki ya ƙarasa ya buɗe mata back seat ta shiga Zarah ta zauna kusa da ita.
Suna haɗa ido ta ɗauke kai da sauri,ya ɗan bi fuskarta da kallo ya ɗauke kai ya koma wurin Bilal dake tsaye.
A hankali suka dinga bin motar su a baya har su ka isa asibitin dake matsayin na Mami.
Babban private hospital ne mai ɗauke da kusan hawa uku,tunda suka shigo ake gaishe su cike da girmamawa.
Ta tsaya gaban nurses dake reception tace"a gyara min VIP 1 Ina da patient".
Sadauki ya dafe kai jin zancen Mami,Allah yasa dai duba shi kawai za tayi ya koma gida don bai shirya zaman asibiti ba gaskiya.
A office ɗinta su ka zauna har aka gama su ka haura sama,tunda su ka shiga Zarah ta shige can cikin office ɗin Mamin mai ɗauke da gado ta kwanta,bata wani ɗade da kwanciya ba bacci ya ɗauke ta.
A can sama Mami tasa aka kawo mata kayan aiki ta sake duba ciwon,ta ɗan gyara inda zata gyara tunda bai nutsu wuri ɗaya ba ta rufe tasa mishi drip ta bar ɗakin.
Tana fita ya lumshe ido jin yadda bacci ke ƙoƙarin ɗaukar shi,ya juya wurin Bilal yace"Mami na son stocking ɗina a asibitin nan".
Bilal yace"maganin ka kenan tunda ba ka san zafin jikin ka ba".
Bai sami sararin bashi amsa ba bacci ya ɗauke shi.
Bai tashi farkawa ba sai ƙarfe uku na rana,yana buɗe ido suka haɗa ido da Emmanuel.
Ya tashi daga inda yake zaune ya ƙarasa wurin shi yace"sorry Falcon,ya jikin?"
Ya tashi ya zauna tare da kai duban shi kan hannun ciwon yace"I'm feeling much better".
Idayat dake zaune kusa da Adebayo tace"Allah ya ƙara sauƙi".
Ba tare da ya kalleta ba ya amsa da Amin suka gaisa da Adebayo.
Ya sauke ƙafafuwan shi ƙasa ya sanya takalman shi dake wurin ya miƙe ya shiga toilet.
Bilal ya ɗauko mini bag dake ɗauke da kayan da ya koma gida ya ɗauko ya kwankwasa kofar ya miƙa mishi.
A shirye ya fito ya shinfiɗa darduma ya rama sallollin dake kanshi.
Yana nan zaune aka turo kofar ɗakin, Zarah ta shigo riƙe da basket Sudais biye da ita.
Ya miƙawa mazan hannu su ka gaisa ya zauna kan wani empty chair dake kusa da Sadauki yace"ya jikin?"
A hankali yace"Alhamdulilah".
Sudais yace"Allah ya ƙara sauƙi".
Zarah ta ajiye basket ɗin hannunta ta gaida yan ɗakin ta kalle shi tace"ina wuni".
Ya ɗan ɗago ya kalleta yace"Lafiya".
Ta tsaya tana wasa da yatsun hannunta don gabaɗaya a takure take,Idayat da gabaɗaya hankalinta ke kan Zarah ta ɗan taɓa Adebayo tace"is she not that his sister?"
Ya gyaɗa mata kai yana danna wayar hannun shi.
Tayi murmushi tace"Come and sit next to me,what is that your name?"
Zarah ta ɗago idanuwanta ta kalleta jin kamar da ita take,ganin tana kallonta yasa a hankali ta buɗe baki tace"Fatima".
Idayat tayi murmushi tace"nice name Fatima,come and sit here".
Ta girgiza kai tace"thank you".
Sudais ya miƙe tsaye ya miƙa mishi hannu yace"zamu tafi,Allah ya ƙara sauƙi".
A nutse yace"Amin nagode".
Kamar yadda Mami tace sai da yayi sati ɗaya a asibitin,a matuƙar takure yake don ji yake tamkar ya gudu ya koma gida amma ba zai iya ba.
Haka dai ya haƙura har ta sallame shi ranar da ya cika kwana takwas.
***
Oum Rijalain