SAWU BIYU

Page 4

by @khadijahsulaiman406

SAWU BIYU 

BY

Khadijah Sulaiman 

Young Talented Writers Association (YOTA).

Book 1

Page 4

Some years back....

RAFIN DAWA, BAUCHI STATE.

Yara ne ke wasa cike da farin ciki a tsakiyar wurin,Sadauki na zaune ƙarƙashin bishiya yana bin yaran da kallo,da gudu Sani ya ƙaraso inda yake yace"mu je bakin rafi!" Sani ya faɗa yana dariya.
Sadauki ya girgiza kai yace"Umma ta ce kada mu je can da yamma."
Sani ya ce"To mu hau bishiyar tsamiya."
Da gudu suka nufi tsohuwar bishiyar tsamiya da ke gefen ƙauyen. 
Cike da ƙwarewa Sani ya fara hawa, Sadauki kuma yana ƙasa yana jiran ya jefa masa 'ya'yan tsamiyar.
Sani yace"yau ma a ƙasa zaka tsaya?
Sadauki yace"eh zan jira ka".
Yana tsaye Sani ya dinga jefo mishi tsamiyar ya na tarawa wuri ɗaya,har sai da ya tara da ɗan yawa sannan ya diro daga bishiyar kamar ɗan biri.
Sani ya cire rigar shi ya zuba tsamiyar a ciki suka nufi hanyar gida.
Malam Muhammadu dake alwala ƙarƙashin bishiyar kuka dake kusa da masallaci yace"daga ina ku ke?"
Da sauri duk su ka ja birki su na kallon shi.
Cike da faɗa yace"kun tsaya kallo na ne?ku wuce ku yi alwala idan mun koma gida za ku yi bayani".
Sadauki ya karasa ya ɗauki butar da mahaifinsu ya ajiye,sum sum Sani ya nemi gefe ɗaya ya juye tsamiyar yayi saurin sa rigar shi ya ɗauki buta.
Ana idar da sallah suka yi saurin mikewa tare da barin masallacin,sai da suka shanye tsamiyar sannan suka shiga gida, Sani ya shiga da gudu ya na dariya Sadauki ya bi bayan shi.
Da sauri Yalwati ta fito daga ɗaki jin muryar Sani ƴarta lami biye da ita.
Ta janyo rigar Sadauki ta dawo dashi gabanta ta riƙo kunnen shi na hagu tace"gidan uban wa ka kai shi baƙin munafiki?"
Lami tace"wallahi Inna yawo kawai yake kai shi,ɗazu na ga sunyi hanyar tafi".
Yalwati tace"wallahi idan ba ka fita hanyar Sani ba sai nayi maganin ka,shege ɗan iska sai nacin jaraba".
Sani ya ɓata fuska yace"Inna ba muje rafi ba ƙarya take".
"Za ka min shiru ko sai na dawo kan ka?yaro ana nuna maka annabi kana rintse ido".
Fatime dake gaban murhu juya miyar ta kawai take tamkar bata wurin.
Mallam Muhammadu ya shigo gidan da sallama, ɗaya bayan ɗaya ya gama ƙare musu kallo,ya dubi Yalwati yace"lafiya ki ka riƙe mishi riga haka?"
Ta hau jijjiga jiki kamar ƙaramar yarinya tace"gaskiya Malam ka shiga tsakanin Sani da Sadauki,ya daina kai min yaro yawo,ba na son alakar su kar ya koyo mugun hali".
Malam Muhammadu ya watsa mata wani kallo yace"kin yi kaɗan Yalwati,kin yi kaɗan ki shiga tsakanin Sani da Sadauki,idan ba za ki iya ganinsu tare ba ki rintse idon ki,maza sake shi kafin ranki ya ɓaci".
Cike da baƙin ciki ta sake mishi rigar tana gunguni ƙasa ƙasa,Sadauki ya nufi hanyar ɗakin mahaifiyar sa kamar zai fashe.
Yana shiga ya nemi gefe ɗaya ya zauna yana kallon gefe,bata kalle shi ba tace"ga tuwon ka".
Ya ɗan dago ya kalle ta jin abinda tace,ya san dama babu abinda za ta ce.
A hankali yace"Umma,kin ji Inna ta kira ni shege ɗan iska".
Ta zauna a kan tabarmar dake shimfiɗe a ɗakin tace"kayi hakuri,ba zan gaji da baka hakuri ba,watarana sai labari".
Yayi shiru yana kallon ta.
Umma ta dinga bin shi da kallo,can tace"ka yi sallar isha?"
Ya girgiza kai da sauri,ta watsa mishi harara tace"tashi ka fita,kar ka dawo min ɗaki sai kayi sallah".
Ya mike ya fita a ɗakin sai bin ɗakin Inna Yalwati yake da kallo ko zai hango Sani,sai dai har ya fita bai ji muryar shi ba.
Bayan sun idar da sallah malam Muhammadu yace"ina ɗan uwan ka?"
Sadauki yace"ban gan shi ba".
Ya gyada kai yace"yayi kyau".
Dauke da sallama ya shiga ɗakin Umma,ya ɗan zauna kusa da ita yace"Umma zan yi wanka".
Tace"ka duba kan murhu akwai ruwan zafi,idan ka ɗiba ka cika min tukunyar".
Ya miƙe ya fita ya ɗauki bokiti ya ɗebi ruwan zafin ya cika mata tukunyar kamar yadda ta umurce shi ya shiga banɗaki.
Tana zaune inda ya barta ya dawo daƙin bayan ya canza kayan jikin shi,ta kalle shi tace"ka ɗauki abinci ka ci".
Sadauki ya cigaba da zama tamkar ba da shi ake ba,share shi tayi kamar ba ta san dalilin shi ba,can tace"idan ba zaka ci tuwo ba sai dai ka kwana da yunwa,ba zan iya da wannan aƙidar ta ka ba".
Muryar Mallam ya sa ta yin shiru,ya ɗaga labulen yana binsu da kallo,a hankali tace "sannu da zuwa Mallam".
Yace"yawwa,lafiya na ga yayi shiru haka?"
Ta ɗan taɓe baki tace"ka san halin sa ai,shi ba zai ci tuwo ba,sai dai ya kwana da yunwa don bani da abinda zan basa".
Mallam Muhammadu ya sake labulen ya shigo ɗakin yace"Sadauki,ka na da abinda za ka ci ne idan ba ka ci tuwo ba?"
Umma ta kalle shi ta ɗauke kai,ta rasa irin Sadauki,shi ba ɗan wani ba amma ya iya zaɓe iri iri,yace ba zai ci kaza ba sai kaza,ga shegen tsafta,idan bai yarda da tsaftar ka ba ko abin hannun ka ba zai ci ba.
Sadauki ya sunkuyar da kai yana sauraron faɗan mahaifinsa.
Malam Muhammadu na gama faɗar shi ya juya ya fita,ya mike a sanyaye zai bar ɗakin tace"ga shinkafa can cikin kwanon samira,ka ɗauka ka je ka ci,gobe idan anyi tuwo sai dai ka nemo abinda za ka ci".
Cike da farin ciki Sadauki ya ɗauki kwanon samirar dake rufe yace"nagode Umma".
Umma ta dinga bin shi da kallo harya fita,ya karasa ƙarƙashin ƙaton bishiyar Kukar dake gidan ya ajiye samirar ya wuce ƙofar dakin Yalwati yayi sallama.
Ta fito tana gyara ɗaurin koɗaɗɗen zaninta tace" ɗan anace lafiya?"
Sadauki ya sunkuyar da kai yace"Sani ya zo mu ci shinkafa".
Cike da masifa tace"wai wannan Sanin ƙanin uwar ka ne ko na uban ka,haba wannan masifa da me tayi kama,za ka bar ƙofar ɗakin nan ko sai na watsa maka mari?"
Mallam ya yaye labulen ɗakin shi ya fito yace"Yalwati ki shiga hankalin ki da ni wallahi,Sani ba ɗan uwan sa ba ne,ke kin isa ki shiga tsakanin su ne?ko ki fito da Sani ko ranki ya ɓaci wallahi".
Yalwati tace"gaskiya ba'a kyauta min wallahi,naga dai ni na haifi abina ba wani ya haifa min ba,so ake a koyawa ɗana mugun hali,a ƙauyen nan waye bai san zuri'ar uwarsa mafarauta dangin matsafa bane?to wallahi dole ya fita harkar Sani ko yaƙi ko yaso".
Malam yace"shikenan ki jira ni in fito".
Ta watsawa Sadauki wani mugun kallo ta koma ɗaki,Sani ya fito daga ɗakin sai kumbura baki yake.
Sadauki ya kama hannun shi suka nufi ƙarƙashin bishiyar.
Malam ya sauke labulen ya koma ɗaki.
Bayan sun zauna Sani yace"tun ɗazu nake son fitowa Inna ta hana ni".
Sadauki yace"na sani".
Sadauki ya miƙe ya wanke hannun shi ya dawo yana kallon Sani yace"ka je ka wanke hannu".
Bai ce komai ba ya miƙe ya wanke hannun ya dawo suka ci abincin tare.
Har karfe tara su na zaune a wurin, Umma ta yaye labulen ɗakinta ta tsaya daga bakin ƙofa tace"ku wuce ku kwanta sai da safe".
A tare su ka shiga ɗakin su dake can ƙarshen gidan, suka kwanta kusa da juna su na hira ƙasa ƙasa.
Da asuba Mallam ya shigo ya ta da su suka wuce masallaci,bayan an idar da sallah suka tsaya karatu sai karfe bakwai su ka shigo gidan.
Umma na sharar tsakar gida ya shigo,ya duƙa kusa da ita yace"ina kwana Umma".
Tace"lafiya kalau,ya karatun?"
Sadauki yace"lafiya umma".
Ya karɓi tsintsiyar hannunta ya cigaba da sharar.
Bayan ya gama ya ƙarasa bakin rijiya ya fara ɗebo ruwa yana zuba mata a randar ta.
Umma ta haɗa mishi ruwan wanka ta ajiye mishi soso da sabulu ta koma ɗaki.
Yana gamawa ya ɗauki bokitin ya shiga wanka,bayan ya fito ya shiga ɗakin su ya nemo riga da wando ya sa ya fito yana kallon ɗakin Inna Yalwati.
Umma ta cika mishi kofi da koko ta ajiye kusa dashi ta cire ƙulƙuli guda biyu ta miƙa mishi.
A hankali ya dinga shan kokon,sai da ya shanye sannan ya miƙe ya fita ya wanke kofin ya dawo.
Ya ɗan kalle ta yace"Umma zan je rafi".
Ta kalle shi tace"me za ka je yi a rafi da sassafen nan?"
Sadauki yace"wanki za muyi tare da Sani".
Umma tace"ku kula ɗan Allah,ku dawo kafin rana ta ɗaga,ka buɗe robar can akwai sabulu".
Yace"to Umma".
A can ɗakin su ya tarar da Sani,suka haɗa kayan wankin su wuri ɗaya suka bar gidan.
Sai kusan ƙarfe takwas da rabi suka isa,rafin cike yake da yara mata da maza.
Sai da suka sha wasan su har kusan karfe goma sannan su ka fara wankin,Sadauki na wanke kayan Sani na ɗauraya.
Bayan sun gama wankin sun shanya suka cigaba da wasa tare da sauran yaran dake wurin banda Sadauki don bai cika shiga sabgar kowani yaro a ƙauyen ba.
Yana zaune ƙarƙashin bishiyar mangwaro yana binsu da kallo,sai da kayan suka bushe sannan su ka nufi hanyar gida.
A gaban masallaci suka tarar da maƙocin su Malam lawali ya na sadakar fura da nono,Sani ya juya cike da farin ciki yana kallon Sadauki yace"Sadauki mu je mu karɓi sadaka".
Sadauki ya girgiza kai yace"ba zan sha ba,zan jira ka karɓo ka dawo".
Yana dariya yace"toh".
Ya ruga da gudu ya karasa wurin sauran yaran,Sadauki ya zauna kan wani icce ya na kallon su.
Sani ya dawo riƙe da nonon ɗaure cikin farin leda yana sha kaɗan kaɗan,Sadauki ya miƙe ya ɗauki ƙullin kayan su suka shiga gida.
Inna dake surfe ta bishi da wani wulaƙantaccen kallo tace"ɗan anace,mara zuciya,na rasa wani irin baƙin naci ne haka an raba ka da yaro amma tsabar babu zuciya a ƙirjinka ka kasa fita harkar shi".
Sadauki ya wuce ta ya nufi wurin Umma da ke sauke tukunyar dambu a kan wuta ta ɗora mai.
Yace"Umma sannu da gida".
Ta ɗago tana kallon shi tace"ita innar ka gaishe ta ne?"
Inna tayi saurin cewa"ya riƙe gaisuwar sa ba na buƙata".
Umma ta ɗauke kai ta sauke man da ta ɗora kan wuta, Sadauki ya wuce ta ya cika ruwa a bokiti ya shiga wanka.
Bayan ya fito ya koma ɗakin Umma dake zaune ta na cin dambu,ya zauna kan tabarma ta miƙa mishi kwanon shi dake cike da dambu,ya tashi ya ɗebo ruwa ya koma ya zauna.
Har zai kai lomar farko sai kuma ya dakata ya maida abincin cikin kwanon,Umma dake lura dashi tace"lafiya?"
Yace"zan tafi mu ci tare da Sani".
Umma ta zuba mishi ido,shi duk wulaƙancin da ake mishi ba ya gani,ta girgiza kai tace"sai ka dawo".
Kafin ya miƙe Sani yayi sallama a bakin ƙofar,Umma ta amsa mishi ya shigo yana dariya yace"Umma ina wuni".
Tace"lafiya kalau Sani, wannan dariyar fa?"
Ya yi wani dariyar yace"ai wayo na yiwa Inna ta,ce mata nayi waje zan fita shine na shigo nan".
Umma ta girgiza kai tace"Allah ya shirye ka".
Sadauki ya ɗauki kwanon abincin shi ya miƙe tsaye yace"muje mu ci abinci".
Har su ka fita Umma binsu kawai take da kallo.
Da daddare Sadauki ya kwaso uniform ɗinsu ya naɗe su da kyau ya ajiye ƙarƙashin pillow.
Da safe bayan sun dawo masallaci ya tarar Umma ta ɗora musu ruwan zafi,yana shigowa ya fito daga ɗaki ya ɗuka har ƙasa ya gaishe ta.
Bayan ta amsa tace"ga ruwan zafi nan kai da Sani,ku yi sauri kar ku makara".
Ya amsa da toh ya ɗauko bokiti ya juye ya shiga bayi.
Bayan ya fito ya juye na Sani ya shiga ɗaki ya sanar dashi,ya shirya cikin uniform ɗinsu ruwan ƙasa ya shiga ɗakin Umma.
Ta ajiye mishi kofin kokon da ta dama tun da suka tafi masallaci,yayi godiya ya fara sha a hankali don har lokacin da zafin shi.
Bayan ya gama ya miƙe ya wanko mata kofin ya ajiye.
Ta kwance gefen zaninta ta ciro naira ashirin tace"ga wannan,sai kun dawo Allah ya bada sa'a".
Yayi godiya ya ɗauki jakar makarantar shi da aka ɗinka da buhun siminti ya mata sallama ya fita.
A waje ya tarar da Sani tsaye ya na jiran shi sai tura baki yake don Inna ta hana shi zuwa wurin Sadaukin.
Ƙarfe ɗaya su ka dawo gidan,kallo ɗaya za ka mu su kasan a gajiye su ke.
A gaban murhu su ka tarar da Inna sai haɗa uban zufa take tana rabon faten tsaki.
Lokaci ɗaya mood ɗin Sadauki ya canza,a duniya bayan tuwo babu abinda ya tsana sai faten tsaki.
Ya gaisheta da kyar ta watsa mishi harara.
Ɗakin Umma ya shiga da sallama,ta amsa tana bin shi da kallo.
Yace"Umma sannu da gida".
Umma tace"sannun ku ya makaranta?"
Yace"lafiya Umma".
Ya fita ya ɗauki bokiti ya karasa bakin rijiya ya cika bokitin da ruwa ya shiga wanka.
Bayan ya fito ya koma ɗakin Umma,ta ɗago tace"akwai sauran koko cikin kwanon can ka ɗauka ka sha tunda ka ɗorawa kan ka aiki".
Cike da farin ciki ya zauna ya janyo kwanon ya buɗe yayi bismillah ya fara sha.
Bayan ya gama ya miƙe ya fita.
Bai ƙara dawowa gidan ba sai bayan sun idar da sallah.
Yana shiga da miyar kukan Inna ya fara cin karo,take ya ɓata rai ya shiga ɗakin Umma.
Kallo ɗaya ta mishi ta ɗauke kai,lami ta bankaɗo labulen ɗakin ko sallama babu ta ajiye tuwon ta fita.
Umma ta girgiza kai tace"Allah ya kyauta".
Suna zaune har fin minti goma babu wanda yayi magana a cikin su.
Can ya miƙe tsaye,tace"ina za ka tafi?"
Yace"zan je in kwanta".
Ta mishi kallon sama da ƙasa tace"bani wancar jakan".
Ya karasa ya ɗauko jakar ya miƙa mata,ta zuge zip ɗin ta ciro Naira hamsin tace"ka wuce wurin Salamatu ka siyo dankali ka dawo yanzu".
Cike da murna ya karɓi kudin ya juya ya fita,bai wani daɗe ba ya dawo riƙe da baƙin leda ya miƙa mata.
Tace"ka zauna ka cinye ina kallon ka".
Ya koma ya zauna yayi bismillah ya fara ci ita kuma ta janyo kwanon tuwonta.
Ya ciro guda biyu yace"Umma gashi".
Ta girgiza kai tace"ka cinye duka na ka ne".
Bai ƙara cewa komai ba ya cigaba da cin dankalin,bayan ya gama ya miƙe ya sha ruwa cikin randar dake ɗakin yace"Umma Allah ya amfana".
Ta gyaɗa kai tace"Amin,ka wuce ka kwanta sai da safe".

***
Oum Rijalain
✍️