SAWU BIYU

Page 6

by @khadijahsulaiman406

SAWU BIYU

BY

Khadijah Sulaiman 

Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1 

Page 6

Ƙarfe tara na safe wata tsohuwar Bus ta faka a ƙofar gidan Mallam Ɗanjuma,bai wani daɗe ba ya fito daga cikin gidan sanye da koɗaɗɗiyar shaddar sa ruwan toka.
Cike da masifa ya kori yaran dake zagaye da Bus ɗin.
"Mutanen nan za su ɓata mana lokaci,an ajiye magana ƙarfe tara za mu bar ƙauyen nan gashi har rana ta fito babu wasu yaran kirki."
Yayi maganar yana saɓa babbar rigar sa.
Baban su Sadauki ya ƙaryo kwana riƙe da kayan Sani da Sadauki,fuskar Sani jage jage da hawaye saɓanin Sadauki da idanuwan nan su ka yi jazur babu alamun hawaye a cikin su.
Mallam Ɗanjuma na hango su yace"yawwa ashe kana tafe,yanzu nake mitar jimawar ku,kasan ba ƙaramin tafiya ke gaban mu ba dole mu hanzarta mu bar ƙauyen nan".
Baba yace"kayi hakuri dan Allah,ka san lamarin mata sai a hankali,sai ka ce idan yaran sun tafi ba zasu dawo ba."
Malam Ɗanjuma yace"ai wannan kusan duk haka suke,babu wani ƙauyen da zamu shiga ɗauko yara iyaye mata ba su ɓata mana lokaci ba,kuma yaran nan karatu za su tafi ba wani abu ba".
Baba yace"to ni ma dai haka na gani,mu ma duk da haka mu kayi karatun".
Malam Ɗanjuma yace"duk wannan abinda suke zasu bari,da sun haɗu da sauran ɗalibai zasu warware".
A haka su ka cigaba da hira har sauran iyayen suka ƙaraso da yaransu,samarin da Baba ya barwa buhuhuwan wake da gero su ka ƙaraso duk aka jera a booth.
Sai da Ɗanjuma ya ƙirga yara talatin cif direba na taya sa sannan ya fara shirya su cikin Bus ɗin kowanne riƙe da jakar kayansa kusa da shi.
Ƙarfe goma na safe motar ta bar ƙauyen Rafin Dawa,Sadauki dake kusa da window ya rufe ido yana tuno yadda Umma ke kuka har ya bar gidan,Sani ya riƙe hannun ɗan'uwan sa da da ƙarfi ya cigaba da kukan da yake ƙasa ƙasa.
Ɗanjuma da driver sai hirar su suke hankali kwance.
Tunda tafiyar tayi nisa motar tayi tsit,kusan gabaɗaya yaran dake cikin motar sunyi bacci,Sani ya kwantar da kanshi kan kafaɗar ɗan uwan shi baccin wahala yayi gaba dashi.
Sadauki dai ko gyangyaɗi bai yi ba sai bin motoci da bishiyoyi kawai yake da kallo.
Ƙarfe huɗu saura suka isa Kanon dabo,Sadauki ya dinga bin ko'ina da kallo ganin cinkoson mutane da ababen hawa.
Malam Ɗanjuma ya gyara zama yace"wai,mun sha tafiya kam, Alhamdulillah tunda mun iso lafiya".
Driver yace"gaskiya".
Yayin da ya shiga wata tsohuwar unguwa dake cike da tsofaffin gidaje,ya taka birki a gaban wani makeken gida dake cike maƙil da yara,wasu zaune ƙarƙashin bishiyar darbejiya riƙe da allunansu,wasu na rubutu a allo.
A can gefe wani tsamurmurin baƙin mutum ke zaune sanye da fararen kaya da rawani yana rubutu.
Mallam Ɗanjuma ya sauko yana saɓa babbar rigar sa ya nufi wurin malamin da sauri.
"Assalamualaikum Mallam".
Malamin ya ɗago da fara'a yace"Waalaikumussalam,Mallam Ɗanjuma kai ne tafe?"
Ɗanjuma yace"wallahi Mallam,isowar mu kenan".
Malam Shehu yace"Masha Allah,sannun ku da zuwa ya hanya?"
Yace"hanya mun gode Allah,ya hidima da yara?"
Yayi murmushi yace"gamu nan mu nayi Malam Ɗanjuma".
Ɗanjuma yace"Masha Allah, ka san ni a kan hanya nake Mallam,muje a fito da yaran".
Mallam ya mike yace"to..to madalllah babu laifi,muje mu gani".
Ko da su ka isa bakin motar kusan duk yaran sun farka su na bin wurin da kallo.
Sani ya riƙo hannun Sadauki yace"ina ne nan Sadauki?"
Sadauki zai bashi amsa aka buɗe kofar, dole yayi shiru ya maida hankalinsa kan Ɗanjuma ganin yadda yake binsu da kallo.
Ya nuna yara biyar dake kusa dasu Sani yace"ku fito".
Da sauri har suna tura juna suka sauko Mallam Shehu ya bisu da kallo.
Ya cigaba da bin yaran da kallo har ya sauke idon shi kan Sani da Sadauki dake riƙe da hannun juna yace"Kai Sadauki ku fito tare da ƙanin ka".
Jikin Sani sai rawa yake ya tashi da sauri zai fita Sadauki ya riƙo hannun shi ganin yadda duk ya bi ya rikice ya durkusa ya ɗauki kayan su dake ƙasa ya fito.
Danjuma ya kalli Ɗahiru dake riƙe da hannun ƙannen sa guda biyu yace"kuma ku fito".
Sai da ya ƙirga yara goma sha biyar sannan ya maida ƙofar ya rufe yana kallon Mallam Shehu yace"waɗannan sune yaran wurin ka Mallam,akwai saƙo daga wurin iyayen yaran a bayan mota bari a miƙa maka". 
Mallam Shehu ya washe baki da sauri yana saɓa babbar rigarsa yace"Masha Allah, Alhamdulillah,a taya mu godiya,na gode sosai".
Driver ya sauka ya buɗe booth ya sauko da kayan ya ajiye a ƙasa,Mallam Ɗanjuma ya miƙawa Malam hannu yace"Nagode Mallam,Allah ya ƙaddara saduwar mu".
Mallam yace"Amin Amin,nagode ƙwarai".
Su Sadauki suka dinga bin motar da kallo har ya bar unguwar.
Ya juya yana kallon yaron yace"ku wuce mu tafi".
Suka bishi a baya har wurin yaran dake karatu, Sani ya maƙale jikin Sadauki kamar kace ar ya ruga.
Mallam yace"a dakata da karatu haka nan lokacin sallah yayi,kai Bala ɗauki yara ku kwaso saƙo gasu can,kai kuma Tanko wuce ka nuna wa yaran nan inda zasu ajiye kaya su fito ayi sallah".
Tanko ya ajiye allon 
sa da sauri yace"to Mallam".
Su Sadauki duk suka bishi a baya kowannen su riƙe da jakar kayansa.
Sai da su ka shiga wani ƙaton soro mai ɗauke da shimfiɗar Mallam da alluna birjik sannan su ka isa wani ɓangare na gidan mai ɗauke da ɗakuna bila adadin,Sadauki ya dinga bin ɗakunan da kallo ganin babu ƙofa sai dai buhu da aka ɗinka a matsayin ƙofa ko labule za'a ce yayi duƙun dukun.
Tanko ya tsaya gaban ɗaki na uku ya ƙirga yara biyar yace su shiga da kayan su ciki,ya ƙirga wasu biyar ciki harda Sadauki ,Sani da Ɗahiru yace su shiga wani daban,sai sauran biyar ɗin yace su shiga ɗakin ƙarshe.
Tun da Sadauki ya shiga ɗakin ya dinga bin koina da kallo ganin yadda ɗakin ke hargitse kaya ne barbaje ko ta ina,wasu an rataye jikin ƙusa wasu a ƙasa wasu cikin buhu,ga kayan duk babu na arziki.
Sani ya riko hannun ɗan uwansa da sauri yana ƙoƙarin fashewa da kuka yace"Ni bana son nan Sadauki,ka kira Baba ya zo ya ɗauke mu".
Sadauki ya haɗiye wani abu mai tauri ya kasa cewa komai.
Ɗahiru ya musu kallo ɗaya ya ɗauke kai ya nufi wani lungu ya ajiye kayar sa ya fita don tun ranar da Sadauki ya mishi wannan dukan ba su ƙara haɗuwa ba sai yau.
Sadauki ya nemi gefe ɗaya ya ajiye kayan,suna kokarin fita wani da zai yi kusan sa'ar Sadauki ya shigo,ya ɗan tsaya yana kallon su,Sadauki ya bashi hanya duk a tunanin shi ko tare masa hanya su kayi.
A hankali yaron yace"idan kun san akwai wani abu cikin kayan ku mai amfani ku maza ku kwashe kafin sauran su shigo."
Sadauki ya zuba mishi ido cikin rashin fahimta, ganin basu fahimci abinda yake nufi ba yasa yace"idan akwai kuɗi ko kayan abinci cikin kayanku ku ɗauke da sauri don za'a iya sacewa".
Yana gama magana ya ajiye allon hannun shi ya juya ya fita.
Sadauki ya zubawa kofar ido jin wani sabon zance, wannan shi ake kira farawa da iyawa.
Sani ya girgiza shi da sauri yace"muyi sauri mu cire kafin su shigo,akwai kuɗi da Inna ta bani bari in ɗauko".
Da sauri ya karasa gaban Ghana most go ɗin shi ya zube zip ɗin ya sa hannu can ƙasa inda Inna ta sa mishi kuɗin cikin ɓakin leda ya ciro ya dawo wurin Sadauki dake tsaye har lokacin.
Yana kallon shi yace"gashi Sadauki ka ɓoye min".
Sadauki ya sauke wani ajiyar zuciya yasa hannu ya karɓi ledan ya koma wurin nashi kayan ya bude ya ɗauko kuɗin wurin Umma ya hada da na wurin Sani ya cusa cikin aljihun shi.
Kayan abincin ne dai babbar damuwar sa,to ina zai ɓoye kayan abinci yanzu?
Hayaniyar da ya ji ya sa shi kallon ƙofar da sauri,Sani ya riƙo hannun shi yace"ya za muyi Sadauki?"
Yace"ka zo mu tafi kawai,babu abinda zai faru".
Ba don hankalin Sani ya kwanta ba ya bi bayan shi su ka fita.
A bakin ƙofar suka tarar yara kusan goma suna wawason abinci cikin wani roba,Sadauki ya matsa da sauri kar su ɓata mishi jiki,duk da haka sai da aka shafa mishi miya,ya tsaya yana bin rigar da kallo cike da takaici da tsananin ƙyama.
Wani daga cikin su yayi dariya ganin yadda Sadauki ke bin rigar shi da kallo ya kai hannu ya sake shafa mishi hannun shi.
A fusace ya ɗago ya zuba mishi ido,sauran dake wurin suka fashe da dariya.
Wanda ya shafa miyan yace"sai in kwara maka miyar da ya rage in ga ta tsiya".
Sadauki ya ɗaga hannu zai kai mishi duka ya ji an riƙe hannun,rai ɓace ya ɗago idon shi ya sauke kan wani dan saurayi don zai girme shi sosai yace"lafiya?"
Wani irin huci kawai Sadauki yake,tunda yake a rayuwar shi ba'a taɓa ɓata mishi rai irin yau ba.
Saurayin ya watsa wa yaron harara yace"na ga abinda ka yi,maza ba shi haƙuri".
Yaron ya buɗe baki da ƙyar yace"kayi hakuri".
Ya juya wurin Sadauki yace"gashi yace kayi hakuri,ya sunan ka?"
Sani dake maƙale jikin Sadauki dake huci har lokacin yayi saurin cewa"Sadauki".
Saurayin yace"Masha Allah,kai kuma fa?"
Yace"Sani".
Saurayin yace"sannun ku da zuwa,ni suna na Sadiq,ku wuce ku yi Sallah Mallam na jiran ku a waje".
Sani ya ja hannun Sadauki dake bin yaron da kallo da ƙyar su ka fita,a saman tabarma su ka tarar da su Ɗahiru.
Can inda ya hango butoci ya ja Sadauki su ka tafi ya zuba mishi ruwa a buta ya miƙa mishi,ya ɗago idanuwan shi da su ka ƙada ya zuba mishi.
A hankali Sani yace"kayi hakuri Allah zai saka maka".
Dama shi abinda yake faɗa kenan idan an mishi abu in har Sadauki ba ya kusa,muddin kuwa ya sani ko ba'a ranar ba sai ya rama masa,Unlike Sadauki da duk abinda aka masa sai ya rama.
Ya sauke ido ya karɓi butan ya zauna kan wani ƙaramin dutse da ke wurin Sani ya ɗurƙusa kusa dashi suka yi alwala.
Wani almajiri dake gefe ya nuna musu inda zasu tsaya suyi sallah.
Bayan sun idar ya riƙe hannun Sani har wurin malamin dake zaune yana karatu sai su Ɗahiru da ke zaune a gefe duk sun yi laushi,ya ɗan dakata yace"me kuke a ciki tun ɗazu?"
Sani yace"mun tsaya ajiye kaya ne".
Kamar zai yi magana sai kuma yace"ya sunan ku?"
Sani yace "Sunana Sani,shi kuma Sadauki".
Malam Shehu yace"shi bai da baki ne?"
Sadauki ya sunkuyar da kai a hankali yace"ina yi".
Malam Shehu ya zuba mishi ido na ɗan lokaci,sai kuma ya ɗauke kai ya cigaba da karatun da yake.
Sai da suka kwashe kusan mintuna goma a zaune sannan ya rufe Qur'anin dake gaban shi ya yi gyaran murya yace"Barkan ku da zuwa tsangayar Malam Shehu,da farko dai nan wurin neman ilimi ne da tarbiyya,duk wani banzan hali ko rashin tarbiyya yaro ya ajiye a gidan su kada ya kawo mana nan,abincin dare kawai za'a baku daga cikin gida,sauran lokutan kuma idan kana da abinda za ka ci to falillahilhamdu,idan babu kuma sai dai ka fita ka nemo,ina fatan kun fahimce ni?"
Duk suka gyaɗa kai da sauri duk da ba kowannen su ya fahimci abinda yake faɗa ba.
"To shikenan za ku iya komawa ciki".
Gabaɗaya duk aka miƙe su ka shiga ciki,cikin su babu wanda baya jin yunwa,musamman Sadauki da koko Umman shi ta dama mishi sanin baya cin tuwo ta aika aka siyo mishi alala ya haɗa dashi saboda ya riƙe mishi ciki.
Gabaɗaya sauran yaran da ke tsakar wurin su ka zubo musu ido,Sadauki yaja hannun Sani suka shiga inda ya ajiye kayan su.
Yara ne kusan guda biyar a ɗakin sai wannan da ya kira kanshi da Sadiq dake zaune can ƙuryar ɗakin yana rubutu a allo.
Sadauki ya buɗe jakar kaya ya ɗauki kofi da cokalin da Ummah ta sa mishi cikin kaya,ganin yana ƙoƙarin fita Sadiq yace"ga ruwa a wannan butan idan ruwa ka ke nema".
Ya ɗan kalle shi ya karasa ya ɗauki butan yana bin ruwan da kallo.
Sadiq ya cigaba da rubutun da yake yace"yana da da kyau,idan kuma wannan bai maka ba sai a ɗebo maka a cikin gida".
A hankali Sadauki yace"a ina zan ɗebo?"
Sadiq ya kalli yaran dake binsu da kallo kamar sun samu television yace"lawali raka shi cikin gida ya samo ruwa".
Lawali ya miƙe da sauri don dama cikin shi in banda kiran ciroma babu abinda yake ya nufi waje Sadauki ya bi bayan shi.
Ƙaton tsakar gidan suka shiga mai ɗauke da ɗakuna birjik,tsakar gidan nan kaca kaca da datti,yara fin goma sha ke wasa,Sadauki ya dinga bin koina da kallo da mamaki ganin tarin ƙazantar dake wurin,ya san dai duk da daga ƙauye suke amma bai taɓa ganin gidan su haka ba.
Matan gidan su huɗu dake zaune ƙarƙashin bishiyar mangwaro suka bisu da kallo,mace ɗaya ke sanye da hijabi,sauran t shirt da riga ne kawai a jikin su.
Jummai tace"lawali baƙo ku ka yi".
Lawali yace"eh,yau su ka taho,su na nan da yawa".
Sadauki ya gaishe su suka amsa suna binshi da kallo.
Ɗayar da ke zaune kusa da ita tace"tabdi,ashe yau kuna da aiki a gidan nan".
Lawali ya ƙarasa gaban wani drum dake buɗe ƙudaje sai shawagi suke a ciki ga ƙananun datti kana gani ƙiri ƙiri yace"ga ruwan".
Sadauki ya leka ciki ya ɗago da sauri yana kallon shi,a hankali yace"wannan ne ruwan?"
Lawali ya gyaɗa kai cike da rashin fahimta yace"eh".
Ji yayi hankalin shi yayi mugun tashi,ina zai iya shan wannan ruwan?
Lawali ya ƙura mishi ido ganin yadda ya rikice,a sanyaye yace"idan ba ka son wannan ga rijiya can,sai dai akwai zurfi".
Da sauri Sadauki yace"eh mu je".
Lawali ya koma inda rijiyar yake ya ɗauki gugan dake gefe ya zura cikin rijiyar ya ɗebo ruwan.
Sadauki ya miƙa mishi cup ɗin hannun shi ya zuba suka bar wurin.
Sani na zaune har lokacin yana jiran shi,ya ɗauraye ɗaya cup ɗin da spoon ya haɗa musu garri ya zuba sugar ya miƙa masa ya zauna kusa dashi,ganin yadda sauran suka zubo musu ido yasa ya ɗan kalli lawali yace"ka kawo abu in zuba maka".
Lawali ya miƙe jiki na rawa ya ɗauko wani ƙaton roba duk datti ya kawo,Sadauki ya bi roban da kallo yace"akwai datti ka je ka wanke".
Sadiq dake zaune har lokacin yana rubutu yayi guntun murmushi.
Lawali ya ruga da gudu ya fita ya wanko roban sama sama ya dawo, Sadauki dai babu yadda ya iya da dattin ya zuba mishi a haka ya dinga godiya ya koma ya zauna, sauran almajiran sai kallon lawali su ke amma ko kallo basu ishe sa ba.





Oum Rijalain 
***