SAWU BIYU

Page 7

by @khadijahsulaiman406

SAWU BIYU 

BY 

Khadijah Sulaiman 

Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1 

Page 7

Ƙarfe biyar suka koma wurin karatu, sababbin zuwa irin su Sani da Sadauki gaban Mallam suka zauna kowanne riƙe da sabon allo.
Ba su tashi a wurin ba saida aka kira sallar magriba,duk suka shigar da allunan su ciki suka dawo aka yi alwala aka yi Sallah.
Bayan sun idar da sallah wasu suka cigaba da karatu wasu suka shiga ciki.
Sadauki na son yin wanka ya rasa yadda zai yi,ya fito kenan yaji ya buge mutum,kafin ya daidaita tsayuwar shi ya ji an sauke mishi mari.
Ya dafe ƙuncin shi ya kafe sa da ido duk da ba sosai yake ganin sa ba saboda rashin wadataccen haske.
A fusace yace"banza mara hankali,makaho ne kai?"
Sadiq ya karaso da sauri yace"haba Bala,ka san akwai duhu ba lallai ya ganka ba,ka yi hakuri dan Allah".
Da ƙarfi Bala yace"ƙarya ya ke ya ganni sarai,ina lura dashi tun da suka iso sai faman ji da kai yake kamar yafi kowa,idan yafi ƙarfin zuwa nan ya zauna a gidan su mana".
Sadiq yace "kayi hakuri dan Allah yaro ne".
Ya juya ya kalli Sadauki da har lokacin bai daina kallon Bala ba yace"ka bashi hakuri Sadauki".
Ko motsi Sadauki bai yi ba balle ya sa ran zai ce wani abu,ya ɗan taɓa shi yace"ka ji?"
Bala yayi wani shegen dariya yace"ka gani ko?shi ɗan iska,mu zuba ni da kai ne a gidan nan".
Ya juya a fusace ya bar wurin,a hankali Sadiq yace"me yasa ba ka bashi hakuri ba?
Sai lokacin ya sauke hannun shi ya sunkuyar da kai,Sadiq ya girgiza kai don da gani za'a sha daga dashi.
Ganin ya juya zai bar wurin yace"ina kuma za kaje?"
A hankali yace"zan yi wanka".
Sadiq ya waro ido da mamaki yana bin shi da kallo,sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yace"muje in ba ka bokiti".
Bayan sun shiga ciki Sadiq ya miƙa masa bokiti shi kuma ya buɗe cikin kayan shi ya ɗauko sabulun wanka da soso ya fita Sadiq ya bi bayan shi riƙe da torch sanin bai gama sanin kan gidan ba.
Sai da ya cika ƙaramin bokitin da ruwa sannan ya bi bayan Sadiq dake haska mishi hanya har wurin wankar su,wani ɗan gefe aka zagaye da buhu in banda zarni babu abinda yake.
Da kyar Sadauki ya iya sauke numfashi bayan ya shiga,zarnin har tsakar kansa ya ke ji.
A gurguje yayi wankan ya fito suka koma ɗaki.
Suna shiga suka tarar da an kawo tuwo daga cikin gida,a dai dai lokacin nepa suka kawo wuta haske ya gauraye koina.
Kallo ɗaya Sadauki ya yiwa miyan kukan ya ɗauke kai,kore shar dashi ko alamun manja babu.
Wasu daga ciki har sun kusa cinye nasu,Sani dai na riƙe da wani kusa dashi don yasan yayan nasa ba cin tuwo yake ba.
Ya zauna kusa da Sani yace"baka ci tuwon ba?"
A hankali Sani yace"zan ci".
Sadiq dake cin nasa tuwon yace"kai ba zaka ci ba?"
Sani yayi dariya yace"baya cin tuwo ai".
Sadiq ya fashe da dariyar da bai yi niyya ba jin abinda Sani yace.
A hankali yace"tabɗi".
A haka su kusan ashirin su ka kwana a ɗakin kan buhun siminti dake shimfiɗe a ƙasa,sauro kam ba'a magana don sosai ya sha rabon sa.
Da asuba Sadiq ya bi ya tada gabaɗaya ƴan ɗakin su ka fita,a waje su kayi alwala Mallam ya jasu sallah .
Bayan an idar da sallah aka hau karatu,basu suka tsaya ba sai ƙarfe takwas.
Bayan sun shiga ciki Sadauki ya laluba aljihun wandon shi inda ya zuba kuɗi jiya yaji wayam,da sauri yasa hannu cikin aljihun amma babu kuɗi babu alamun su.
Sani dake kallon shi yace"Sadauki me ka ke nema?"
Sadauki yace"kuɗin mu da na ɓoye jiya,ban gansu ba".
Sani yayi shiru yana kallon shi,Sadiq dake wanki daga can nesa yace"lafiya?"
Sadauki ya mishi kallo ɗaya ya ɗauke kai,Sani ya juyo ya kalle shi ya sanar dashi abinda ke faruwa.
Sadiq ya girgiza kai yace"kayi ganganci,nan gidan ko me ka ke kar ake kallon ka,Allah ya sa rabo ne".
A sanyaye ya nufi ɗaki Sani ya bi bayan shi,gidan yayi shiru kusan duk yaran gidan sun fita sai manyan ciki irin su Sadiq,Bala,Tanko da Garba.
Dab da za su shiga ɗaki su ka ji ance"Ku zo nan".
Suna zaune su uku ƙarƙashin bishiyar darbejiya dake wurin suna cin shinkafa garau garau da mai da yaji.
Sadauki ya tsaya inda yake yana binsu da kallo.
Tanko da Garba suka waro ido cike da mamaki suna kallon shi.
Garba ya tsame hannun shi cikin kwanon shinkafar ya zaro ido yace"kai ! Ka san ina ne nan kuwa,ka san ko su waye mu?"
Bala yayi guntun murmushi, Tanko ya ce"Ku ɗurƙusa a wurin".
Sani ya riƙo hannun Sadauki jiki na rawa yace"ka zo mu tafi Sadauki,ni dai ba ruwana tsoro na ke ji".
Sadauki ya kwace hannun shi ya shige ɗaki.
Gabaɗaya duk suka waro ido su ka bishi da kallo.
Sani dake tsaye a wurin sai zufa yake a tsorace ya ruga ya shiga ɗakin da gudu.
Tanko ya gyaɗa kai yace"yaro yaro ne".
Sadauki na shiga ya tarar da zip ɗin kayan shi a buɗe,ledar garin da ke cikinta an buɗe ta garin ya barbaje a ƙasa.
Cike da mamaki ya kafe kayan da ido,Sani ya shigo ya tsaya kusa dashi yana kallon kayan.
Ya sauke wani ajiyar zuciya ya karasa ya gyara kayan ya zauna a ƙasa.
Sani ya zauna kusa dashi yace"ni bana son nan Sadauki,ka kira Baba ya zo ya ɗauke mu".
A hankali Sadauki yace"nima bana son nan Sani,amma Umma tace mu yi haƙuri mu zauna mu yi karatu".
Sani yace"amma muna karatu a gida, ni dai bana son nan ina son zuwa wurin Inna Yalwati".
Sadauki ya rasa amsar da zai basa,ga tashin hankalin rashin kuɗin su.
Yace"kana jin yunwa ko?"
Sani ya gyada kai,ya miƙe ya dauko kofin jiya ya wanke da ruwa ya zuba garin ya wanke ya zuba musu sugar ya dawo ya zauna.
Suna zaune Dahiru ya shigo ya musu kallo ɗaya ya ɗauke kai ya karasa wurin kayan shi ya ɗauki abinda zai ɗauka ya juya ya fita.
Wuraren azahar wasu daga cikin yaran suka fara dawowa,Sani na kwance kusa dashi bacci ya ɗauke shi ya dinga kallon su.
Mamakin dattin jikin su kawai yake,wai su basa ganin kayan jikin su yayi datti su cire su wanke.
Lawali ya washe baki ya karaso kusa dashi yace"ga shinkafa na samo".
Ya tashi ya zauna da sauri ganin zai kifo mishi abincin a jiki.
Ya ɗan yi murmushi yace"to ka ci".
Lawali yace"kai ba za ka ci ba?"
Sadauki ya girgiza mishi kai.
Ya ƙara cewa"me yasa ba ku je bara ba?"
Sadauki ya kafe shi da ido ya kasa bashi amsa.
Ya zauna kusa dashi ya tankwashe ƙafa ya fara kai lomar shinkafar shi hannu baka hannu ƙwarya yace"ai idan an gama karatun safe bara ake zuwa sai lokacin salla ake dawowa,da rana ma idan ba ka fita ba sai yunwa ta kusa hallaka ka,da daddare ake ba da tuwo daga gidan Mallam".
Ya suɗe robar tas ya haɗa da yatsun hannun shi yayi wata gyatsa da ta kusa firgita Sadauki ya rage murya can ƙasa yace"idan ka dawo da abincin da ya burge su Garba ka shiga uku a hannun su don kullum sai sun kwace su barka da hamma,amma ka ga Sadiq shi ba ruwan sa ba mugu ba ne".
Sadauki dai har ji yayi kanshi na kokarin ciwo tsabar takura masa da yayi,ya koma ya kwanta a hankali yana tunanin Umma.
Ko me take yanzu,ƙila ta dama koko da safe da rana kuma ƙila ta ci shinkafa ko ɗan wake ko dambu.
Yana wannan saƙe saƙen bacci ya ɗauke shi.
Cikin bacci ya ji an sheƙa masa ruwa,ya tashi da sauri don abu ne da bai zata ba.
Sauran yaran suka fashe da dariya banda lawali da Sani,Dahiru har da kwanciya tsabar mugunta.
Bala ya gyara bulalar hannun sa da kyau yana kallon Sadauki yace"kai ɗan marasa kunya ko?zan yi maganin ka gobe idan ka ga manya da suka girme ka dole ka yi biyayya kamar yadda kowa ke yi,hatta shi Sadiq da naga sai ƙoƙarin shige maka yake a ƙarƙashin mu yake".
Yana kai ƙarshe ya zabga masa ɗaya, Sadauki ya sunkuyar da kai yana jin yadda bulalan ke shigar sa.
Bala ya gyaɗa kai yace"irin ka nake so masu taurin kai".
Ya ƙara ɗaga bulalan ya zage duk ƙarfin da Allah ya basa ya ƙara watsa masa,Sadauki ya rintse ido da ƙarfin gaske amma ko ɗigon hawaye babu,idon nan ya kaɗa yayi jawur kamar garwashi.
Hakan ba ƙaramin ɓata masa rai yayi ba,ya dinga zabga masa bulalan kamar ya samu bawa.
Sani na gefe yana kuka,hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba ganin abinda bai taɓa gani ba.
Ya ɗago zai ƙara zabga mishi Sadiq ya riƙe bulalan.
Rai ɓace yace"haba Bala,menene haka dan Allah,wani irin duka kake mishi kamar bawan gidan ku,me yasa baka tsoron Allah ne wai?"
Bala ya watsa mishi harara ya fizge hannun shi yace"ka fita ido na in rufe Sadiq,bana son shisshigi ka daina shiga abinda bai shafe ka ba,ka san abinda ya yi?"
Sadiq yace"babu abinda ya maka Bala,baƙin muguntar ka ce kawai ta motsa in ba haka ba me wannan yaron da ko magana wuya take masa zai maka daga isowar sa jiya".
Ya watsa masa wani kallo ya juya ya kalli Sadauki dake durƙushe har lokacin babu ɗigon hawaye yayi ƙwafa ya juya ya fita sauran suka mara mishi baya.
Sadiq ya bi ɗakin da kallo ya daka musu tsawa yace"duk ku fita".
Da sauri har su na ture juna suka bar ɗakin,ya karasa ya zauna kusa da Sadauki ya ɗaga rigar jikin sa,hankali tashe yace"innalillahi wainna ilahiri raju'un,anya Bala na da hankali kuwa?"
Sani ya sake fashewa da kuka ganin yadda shatin bulala ya fito raɗau a bayan ɗan uwan sa.
Sadiq yace"kayi hakuri Sadauki,amma abu ɗaya zan faɗa maka,kaga mutane ukun nan?ka fita hanyar su,babu ruwan ka da su,idan ka gansu a hanya ka gaishe su,idan sun sa ka aiki kayi,ba su da mutunci ko kaɗan,idan kayi haka za ku zauna lafiya,amma idan kace wannan taurin kan za ka dinga nuna musu tabbas za ka sha wahala".
Sani ya zauna kusa da shi ya riƙo hannun shi ya dinga bashi hakuri,a hankali yace"Allah zai saka maka".
Ya buɗe ido ya sauke kan Sani,Sadiq kanshi sai da ya tsorata da yadda idon ya kaɗa.
Ya miƙe a hankali ya fita ya nemo buta ya zuba ruwa yayi alwala ya koma ɗaki.
Har la'asar yana ɗaki tare da Sani,jin an kira sallah ya sa shi mikewa suka fita waje.
Tare da Mallam aka yi Sallah,bayan an idar kowa ya dauko allo aka hau karatu.
Cike da ƙarfin hali Sadauki ke zaune,jikin shi wani irin zafi ya ɗauka ga raɗaɗin da bayan ke masa.
Kiran sallar magrib yasa aka dakata da karatun.
Bayan an idar da sallah wasu suka shige ciki,wasu suka cigaba da harkokin gaban su har aka kira sallar Isha.
Bayan sun koma ciki aka kawo tuwo daga cikin gida kamar dai jiya.
Sadauki ya ɗauki bokitin Sadiq ya ɗebo ruwa a rijiya ya shiga wanka.
Bayan ya fito ya tarar da Sadiq riƙe da wani roba,yana ganin shi yace"ga shinkafa na kawo maka".
Kamar zai ce a'a sai ya tuna rabon shi da cin wani abincin kirki tun a gida,tunda ya zo garin garri kawai yake sha.
Ya karasa ya sa hannu ya karɓa yace"Nagode".
Sadiq yace"tunda ba ka cin tuwo ka dinga fita bara in ba haka ba za ka wahala".
Ya zauna kusa da Sani dake cin tuwo,a hankali yace"ka zo muci".
Sani ya girgiza kai yace"a'a gani ina cin tuwo".
Babu yadda Sadauki bai yi da Sani ba amma yace ba zai ci ba, sai da ya ga ranshi ya ɓaci sannan ya ci loma biyu yace ya ƙoshi.
A haka suka cigaba da rayuwa,idan an kawo tuwon dare kowa zai ci banda Sadauki,da safe ya haɗa garri ya sha,da rana ma haka.
Sauran yaran da aka kawo su tare duk sun saki jiki har Sani dake kukan zai koma wurin Inna Yalwati yana shiga cikin sauran yaran banda Sadauki,shi dama tun asali bai da shiga mutane kamar Sani.
Ranar yana ɗago ledar garrin ya ga babu komai sai leda,ya ƙara buɗewa da kyau ya ga da gaske dai ya kare babu komai a ciki.
Sani ya matso kusa dashi yace"Sadauki garin mu ya kare,ka zo mu tafi bara tare dasu lawali".
Sadauki ya zuba mishi ido,idan bai yarda yaje bara ba yana da inda zai sami abinci ne?
Haka ya shirya ya bi bayan su lawali su ka fita,tunda su ka fita suke yawo gida gida,Sadauki dai na biye dasu.
Sai sun gama bara za'a ce su yi hakuri,har sha biyun rana suna yawo ko ƙanzo basu samu ba.
Zuwa sannan babu wanda bai galaɓaita ba a cikin su,da kyar bayan sunyi bara a wani gida yaro ya leƙo yace su kawo kwanon su,da sauri lawali ya miƙa masa yana washe baki.
Suna nan tsaye yaron ya dawo da roban cike fal da sauran tuwo,an zuba miyan kuɓewa a kai sai tashin tsami yake.
Lawali ya sa hannu ya karɓa yayi godiya yaron ya koma ciki.
Sadauki ya ruga bakin kwararon dake gefe ya hau kakarin amai.
Da sauri suka karasa kusa dashi ganin yadda ya galabaita kasancewar babu komai a cikin sai ruwa.




Oum Rijalain 
***