Page 8
SAWU BIYU
BY
Khadijah Sulaiman
Young Talented Writers Association (YOTA)
Book 1
Page 8
A galabaice ya koma gefe yana sauke numfashi,lawali da Sani sai sannu suke mishi hankali tashe.
A hankali yace"zan sha ruwa".
Lawali yace"bari in samo".
Ya koma bakin gidan ya buga ƙofar yaron ɗazu ya buɗe,yana ganin shine ya wani haɗe rai yace"me kuma ku ke so?"
A hankali lawali yace"dan Allah ka taimake mu da ruwa".
Yaron yayi tsaki yace"bayan an baku abinci shine harda dawowa neman ruwa?"
Lawali yace"dan Allah ka taimaka mana".
Ya ya tsaki ya buga ƙofar da ƙarfi ya koma ciki ya bar lawali da bin ƙofar da kallo,a sanyaye ya koma wurin Sadauki da ya kife kanshi yana sauke numfashi a hankali.
Sani ya kalle shi yace"ina ruwan?"
A hankali yace"ban samu ba,ku tashi mu bar nan ni yunwa na ke ji".
Sadauki ya miƙe ya kakkabe jikin shi suka karasa ƙarƙashin bishiyar dake can nesa da gidan suka zauna,Sadauki ya matsa can nesa dasu har suka gama cin tuwon.
Yana zaune yana rubutu da wani sanda akan ƙasan wurin cike da tunane tunane.
A haka su ka nufi hanyar komawa makaranta,wani mutum dake tsaye gaban tarin itacen da aka gama faskare masa ya hango su.
Ya ɗago hannu yace"ku zo mana ƴa'ƴan mallam".
Da sauri su ka karasa inda yake tare da gaishe shi cike da ladabi,ya nuna mu su itacen dake gaban shi yace"ku shigar min da wannan ciki".
Jiki na rawa lawali ya ajiye robar sa suka fara shigar da itacen,sun kai kusan minti goma kafin su gama shigar da duka itacen.
Mutumin ya miƙa musu Naira hamsin hamsin,cike da farin ciki suka bar wurin.
A hanya Sadauki ya hango mai awara, ya siya na hamsin shi da Sani,bayan sun cinye suka karasa gaban wani masallaci ya tare hannun shi jikin pampon wurin ya sha ruwa.
Da daddare yana rubutu a ɗaki wani yaro ya shigo,sai da ya gama bin ɗakin da kallo sannan ya tsaida idon shi kan Sadauki yace"Ka je in ji Bala".
Sadauki ya bi bayan shi da kallo har ya fita,Sadiq ya bar abinda yake yace"ka tashi ka tafi,kuma duk abinda ya ce ka yi kar kayi musu".
Sadauki ya ɗago da sauri ya kalle shi jin abinda yace,Sadiq bai ƙara kallon shi ba ya ɗauke kai.
Tsaye ya tarar da su kusa da katanga,Bala ya watsa mishi wani kallon banza ganin yadda ya tsare su da ido ko tsoro babu yace"wai kai mara kunyar ina ne,ba ka san kayi gaisuwa ba,waye sa'an ka a cikin mu?"
Sadauki ya ɗauke kai tamkar bai ji abinda yace ba,da mugun mamaki duk suke kallon shi.
Tanko ya karaso kusa dashi ya ɗauke shi da mari yace"ɗurƙusa kan gwuiwowinka ka bada hakuri".
Sadauki ya tsare shi da ido ranshi in banda ƙuna babu abinda yake.
Garba ya gyaɗa kai yace"kai ɗan iska ko,sai ka gane kiɗa da karatu a gidan nan don ubanka".
Sadauki yace"ba uba na ba".
A fusace Garba yace"sai na uwar ka?"
Bala yace"lallai ka cika tantiri,zanyi maganinka da safe,yanzu ka kwashe kayan nan ka wuce ka wanke su yanzu,ko ɗigon datti kar in gani in ba haka ba jikinka ne zai faɗa maka".
Sadauki ya zubawa kayan ido ganin yawan su,ba su ƙara cewa komai ba su ka bar wurin.
Sadiq ya dafa kafaɗar sa a hankali,ya juyo su ka haɗa ido.
A hankali yace"kayi hakuri Sadauki,watarana sai labari,mu je in taimaka maka tunda lokaci ya ƙure".
Sadiq da kanshi ya ɗebo ruwa a rijiya ya fara wankin Sadauki na ɗauraye mishi,sai kusan ƙarfe goma na dare suka gama,hannun shi har wani zafi yake mishi saboda yawan kayan.
Tunda ya kwanta yake saƙen saƙen abinda zai yiwa Bala da sauran abokan shi ya huce,lokaci ɗaya yayi wani murmushi ya gyara kwanciya.
Washegari bayan an gama karatun safe suka fita bara,gaban wata mata mai tuyan ƙosai suka tsaya kamshi sai dukan hanci su yake.
Lawali ya ƙara bude murya Sani na taya shi.
"Iya dan Allah kiyi taimako,iya ko mai sanyi ne".
Ta buga musu tsawa tace"ku wuce ku bani wuri,wacece iya?iyar ku na can kwance a ɗaki ta turo ku yawon bara saboda son abin duniya".
Wani yayi carab yace"ai inda kika san basu san zafin haihuwa ba,ayi ta haihuwa kaman ƴan tsaki dole a turo su bara,wani da na gani baifi shekaru biyar ba sai kun tausaya masa wallahi,kai tir da wasu iyayen gaskiya".
Wani ya kai ƙosai baki yace"ai duk neman sauƙi suke,ɗan abincin da za'a ba yaro da bai kai ya kawo ba shine za'a turo shi titi yana gantali yana bi kwararo kwararo saboda son zuciya,Allah dai ya raba mu da irin wannan iyayen".
Mai ƙosai tace"Amin dai,ni dan Allah ku tafi ku bamu wuri duk kun cika mana wuri da ɗoyi".
Sadauki ya ja hannun Sani suka bar wurin zuciyar shi na tafarfasa.
A ƙarƙashin wani bishiya suka zauna kowannen su a galabaice,wata mata ta fito yafe da mayafi tana dube dube,tana hango su tace"kai ɗan Mallam".
Lawali da Sani suka miƙe da sauri,har sun yi gaba lawali ya juyo yace"ka taso mu je Sadauki".
Bai ce komai ba ya miƙe tsaye,Lawali ya ruga ya bar wurin Sadauki biye dashi,matar ta watsa musu wani kallon sama da ƙasa cike da izgilanci tace"anya za ku iya ɗiba ruwa?"
Da sauri suka haɗa baki wurin cewa"za mu iya".
Tace"to shikenan ku shigo ku kwaso bokitai,akwai tuƙa tuƙa nan bayan layin,kar ku sa min dattin jikin ku dan Allah,wai ba ku yin wanka ne?"
A sanyaye su ka ce"mu na yi".
Ta watsa musu harara tace "da wannan dattin jikin?to Allah ya kyauta ni dai na roƙe ku da girman Allah kar ku min ƙazanta".
Lawali yace "to Hajiya".
Ta buɗe kofar gidan da kyau tace"ku shigo".
Yaronta dake wasa a tsakar gidan ya yamutsa fuska yace"kar su taɓa mana bokiti suna wari".
Sani da Lawali suka tsaya sororo suna binshi da kallo.
Maman tace"ku dauka ku tafi ,amma dan Allah kar ku min wasa da ruwa tunda baku san amfanin ruwa da sabulu ba,irin wannan warin ai sai ya hallaka mutum".
Jiki a sanyaye suka kwashi robobin suka fita,yana ganin su da rabobi yasa hannu ya karɓa suka tafi.
Mutane sosai suka tarar,sai da layi yazo kansu sannan su ka fara ɗiba.
Drum biyu su ka cikawa matar sannan tace su bar shi haka,ta shiga ɗaki ta ɗauko wani tsohon Naira hamsin ta miƙa musu ta ce su raba.
Tunda su ka fito babu wanda yace komai a cikin su.
A bakin titi suka tarar da mai suyan awara,Lawali ya karasa ya miƙa mata kuɗin tasa hannu ta karɓa bayan ta watsa mishi wani mugun kallo.
Haka suka cinye kamar wasu mayunwata suka sha ruwa.
Da matsanancin ciwon ciki Sadauki ya kwana a wannan daren saboda tsananin yunwa,tun awara kwara biyu da yaci tare da su Sani babu abinda ya sa a cikin shi tsayin ranar.
Yana ji yana gani aka kawo tuwo daga cikin gida amma ba zai iya ci ba,bai taɓa takaicin rashin cin tuwon shi ba sai da ya zo garin Kano.
Lokaci ɗaya ya rame ya lalace ya saje da sauran almajiran gidan,ido yayi zuru zuru saboda rashin wadataccen abinci.
Idan kayan shi sunyi datti sai dai ya zuba a ruwa ya wanke tunda sabulunsa sun ƙare,suman kanshi ya taru yayi datti babu ƙudin aski.
A gefe guda ga Bala da abokan shi da suka sa shi gaba,ya rasa mai ya tare mu su,ko sau ɗari suka ganshi sai sun sa shi aiki,abinda ke bashi mamaki bai wuce yadda su ke shiri da Ɗahiru ba,ya zama ɗan gidansu,har abinci su kan aiko mishi dashi don su ba su da damuwar abinci.
Kusan kowanne lokaci za ka gansu tare.
Bayan sallar magriba Mallam ya shigo sassan abinda bai cika yi ba,gabaɗaya almajiran aka fito bayan an sanar da isowar sa,fuska ɗaure ya dinga kallon su ɗaya bayan ɗaya yace"an kawo min kuɗin sadaka dubu goma ɗazu kafin sallar magriba kuma kusan kowa na wurin,yanzu na duba ban gansu ba,a cikin ku dole akwai wanda ya ɗauki wannan kuɗin,idan ka san kai ka ɗauka kayi maza ka fito dasu".
Wurin yayi tsit sai kallon juna kawai ake,wasu daga cikin su jikinsu har ya fara rawa,ganin babu wanda yayi motsi a cikin su yasa shi cewa"Bala !kai da Garba ku shiga ku caje min gabaɗaya kayan dake ciki,idan aka samu kuɗin nan cikin kayanka sai ka gane Borno gabas take".
Da sauri Bala da Garba suka shige ɗakunan,sai da suka caje sauran ɗakunan tsaf sannan suka shiga ɗakin su Sadauki,ba su wani daɗe ba su ka fito riƙe da kuɗin da jakan kayan gabaɗaya.
Bala ya ajiye jakan kusa da Mallam yace"Mallam an gansu".
Mallam ya ƙanƙace ido yace"jakar waye wannan?"
Bala ya nuna Sadauki yace"gashi can".
Mallam ya bi Sadauki da kallo,da mugun mamaki yace"kai ne ƙasurgumin barawon kenan,ashe duk wannan shirun naka babu alkhairi a ciki,Bala ! wuce ka ɗaure min shi,gobe idan ya ga abinda ba nashi ba zai ɗauke kai".
Sadauki da tun lokacin da Bala ya fito riƙe da kuɗin da jakar kayan shi ya kafe shi ido wani irin tsanar shi na sake mamaye zuciyar shi,me ya mishi,me ya tare mishi da ya ɗauki karan tsana ya ɗora mishi?
Duk abubuwan da yake nuna mishi bai taɓa damuwa ba amma na yau ba ya jin har ya mutu zai iya manta abinda ya faru.
Jiki na rawa Bala ya riƙo hannun Sadauki ya jashi ya bar wurin,Mallam ya baza babbar rigar sa ya juya ya tafi.
Sani dake can baya ya fashe da kuka,ko dukka jikin shi kunnuwa ne ba zai yarda Sadauki ya ɗauki kuɗin ba,Sadiq na tsaye ya harɗe hannun shi a ƙirji ya bi su da kallo.
Bai wani daɗe da sanin Sadauki ba amma ko rantsuwa yayi ba zai yi kaffara ba ya san Sadauki bai ɗauki kuɗin nan ba,amma yana da yadda zai fitar dashi ne?
Can wani ƙaramin ɗaki dake ƙarshen gidan Bala ya tura Sadauki,ko hasken kirki babu a ɗakin balle abin shimfiɗa.
Ya tura shi tamkar kayan wanki ya tsugunna Garba ya haska mishi tocila ya ɗaure mishi ƙafafuwa jikin wani garƙamemen katcha ya maida kofar ya rufe yasa mukullin a aljihu suka bar wurin.
Ya kwantar da kanshi jikin bango ya lumshe ido,a ranar ko bacci ɓarawo bai samu nasarar sace shi ba,gashi ko ɗigon hawaye babu a idon.
Washegari da safe Bala ya ɓude kofar ya ajiye mishi ruwa a kofi ya maida kofar ya rufe, zuwa azahar aka ƙara kawo mishi wani ruwan.
Alwala kawai yake da ruwan da ake turo mishi ya fuskanci gabas yayi sallah.
Babu wanda ya ƙara bi ta kan shi sai da daddare aka turo mishi kwanon tuwo da miyar kuka,ya maida kwanon gefe ya lumshe ido.
Sai da yayi kwana biyu sannan Malam ya aika a buɗe shi,yasa aka kwantar masa dashi kan tabarma ya gyara dorinar shi mai baki biyu ya zuba mishi guda goma lafiyayyu gaban sauran ɗaliban.
Ko ɗigon hawaye babu a idon Sadauki har aka gama,hakan ba ƙaramin mamaki ya bai wa manyan dake wurin ba,su kansu shaida ne da irin zafin bulalar.
Da mugun tausayi Sadiq ya bishi a baya har su ka shiga cikin gidan,wani irin jiri ya kwashe shi yayi saurin taro shi ya faɗa jikin shi.
Wani irin zazzabi mai zafi ya rufe shi,Sadiq ya rasa yadda zai yi dashi gashi shima ba kuɗi bane dashi balle ya siya mishi magani.
Haka ya fita ya dawo riƙe da paracetamol da ruwa sai awarar hamsin,duk yadda yaso ya ci awarar bai ci ba sai maganin kawai ya bashi ya sha.
Sani ya ci kuka kamar ba gobe,yana zaune kusa da shi har bacci yayi nasarar ɗaukar shi.
Sai da yayi sati ɗaya a kwance babu isasshen magani da kulawa,in banda Sadiq dake iya ƙoƙarin shi na bashi abinda zai ci,Sani da Lawali dake fita bara ba wani abin arziki suke samo wa ba.
Sai da yayi sati biyu a gida sannan Sadiq ya yarda ya fara fita.
Sauran ɗalibai suka dinga binshi da kallo kamar sunga sabuwar halitta,shi kam babu wanda ya ɗaga ido ya kalla a cikin su har su ka bar gidan.
Sun sha yawo har kusan sha ɗaya saura babu abinda suka samu,a galabaice su ka karasa gaban wani masallaci su ka kwanta.
Wani mutum da ya fito daga cikin masallacin zai shiga motar shi dake wurin ya sa hannu a aljihu ya zaro sabuwar ɗari biyu ya miƙa musu.
Sani yasa hannu ya karɓa jiki na rawa,gabaɗaya suka haɗa baki wurin cewa"mun gode Allah ya bada lada".
Mutumin ya gyada kai ya shiga mota ya bar wurin.
Da wannan ɗari biyun suka siyo shinkafa da mai da yaji suka ci sannan suka koma makaranta.
A haka rayuwar su ta cigaba da gudana,a kullum su uku suke fita bara,idan an basu tuwo sai dai suci su kaɗai don yunwa bai sa ya haƙura ya fara cin tuwo ba.
Ranar asabar da safe bayan ya gama wankin kayan shi da na Sani,yana shirin barin wurin yaji ance"kai ɗan ƙauye".
Duk da bai juyo ba amma sarai ya gane mai magana.
"Mara kunya,ba ka ji ana kiran ka ba ne,waye ɗan ƙauye idan ba kai ba?"
Garba yace yana watsa mishi wani mugun kallo.
Sadauki ya juyo yana bin fuskokinsu da kallo fuska ɗaure,Dahiru na tsaye kusa da Bala riƙe da wani ƙaton kwano cike da shinkafa.
Bala ya tsartar da yawu yace"ɗan koma baya duk ka cika koina da warin jikinka".
Sadauki ya maida idon shi kan Bala idon shi jajir,bai taɓa jin ya tsani mutum kamar yadda ya tsane shi ba.
Bala yayi wani murmushi yace"da za ka sauke kai kamar wannan da ka ke gani".
Yayi maganar yana nuna Ɗahiru, sannan ya cigaba da cewa"da ba za ka cigaba da rayuwa cikin yunwar da ka ke ba,Sadiq da kake maƙalewa babu abinda yake dashi shima maula yake kamar dai kai kafin ya sami na kaiwa bakin salati".
Garba da Tanko suka fashe da dariya,Sadauki da zuciyar shi ke cike da mugun tsanar su duka yace"bana so".
Oum Rijalain
***