KIRAN KADDARA

NO MORE SECRETS

by @nihaalmaalik

Cikin dare maryam ta tashi tana jin qishin ruwa, zata sauka gado zayd ya jawota yana tambayar ta me takeso, tache ruwa, ya dauko ya bata tasha sannan ya hauro gadon ya jawota jikin shi yana shirin komawa baccee yaji ta kira shi

“Rouhi…”

“Hmm, Haya?”

“I’m hungry.”

Zaid, wanda yake shirin komawa bacci bayan ya duba agogon da ke gefen gadon, ya buɗe idanunsa a hankali, ya kalli Maryam, wadda take kwance cikin jikin shi tana kallonsa da wani irin murmushi da ya riga ya fara gane ma’anarsa.

“Haya, qarfe biyu na dare fah ynzu”

“I know.”

“Ynzu kike jin yunwa ?”

Ta gyada kai tana turo baki

“Eh, Allah yunwa nikeji”

Ya sauke ajiyar zuciya, ya ɗago kansa ya kalli fuskarta sosai.

“Me kikeso ki chi?”

Ta ɗan yi tunani.

“French fries.”

“Okay, French fries, se kuma me?”

Ta girgiza kai.

“Just French fries, amma I want them crispy, inason special taste dinnan

Ya lumshe idanunsa.

“Haya, miye kuma wani special taste?”

Tayi dariya, tana ɓoye fuskarta a cikin pillow 

“I don’t know, se idan nachi zan gane”

Ya kalle ta na yan seconds kafin ya sauka daga gadon.

“Fine, Your personal chef is going downstairs.”

Maryam ta ɗaga kanta da sauri.

“Don Allah kasa yaji sosai”

Ya tsaya a bakin ƙofa ya waiwayo.

“Anything else, Your Highness?”

Ta ɗan yi tunani.

“Maybe a little cheese.”

“Maybe?”

“Eh, maybe”

“Anything else?”

Maryam ta yi murmushi.

“Love you.”

Zaid ya girgiza kai yana murmushi.

Ya dawo, yayi kissing goshinta, sannan ya fita daga ɗakin.

Maryam ta bi shi da kallo tana murmushi, kafin ta sake kwanciya.

Tun bayan da suka gano tana da ciki, ya fahimci cewa rayuwarsa za ta sauya ta hanyoyin da bai taɓa zato ba, wa zeyi tunanin CEO na meridians axis yana shiga kitchen 2am don ya soya ma matar shi fries?

Abin mamaki shi ne, bai damu da hakan ba, shi kam duk abnda maryam keso ze yimata 

Bayan kusan minti ashirin, ya dawo ɗakin da plate a hannunsa. Ya ajiye shi a kan ƙaramin table da ke gefen gadon, sannan ya zauna kusa da ita.

“Your order is ready, ma’am.”

“Unmmm” maryam ta amsa cikin muryar baccee 

A ranshi yache kan bala’i wai baccinta ma ta koma kenan, ya dagota ya zaunar da ita yana daura mata plate din kan kafarta a ranshi yana chewa ai se kin tashi kin chi shi

“Thank you” tache tana kallonshi da murmushi 

Ta ɗauki fork din ta debo ta kai baki, sai kuma ta tsaya cak.

Zaid ya kalleta.

“What?”

Maryam ta sake kallon plate din, sannan ta ɗago kai ta kalleshi.

“Rouhi…”

“Yes?”

“Bazan iya chi ba kuma”

Ya tsaya yana kallonta kamar bai ji abin da ta faɗa ba.

“Ba zakichi ba?”

Ta girgiza kai a hankali.

“I’m sorry.”

Ya kalli plate din, sannan ya mayar da kallonsa gare ta.

“Meyasa?.”

“Dama bn tabbatar ko zanso cheese din ba, ynzu da nachi naji banaso”

Kasaqe zaid yayi yanata kallonta ya kasa magana 

Maryam ta kasa riƙe dariyarta seda tayi 

Zaid ya jingina da bayan gadon, yana kallonta da fuskar wanda ya rasa yadda zai yi da lamarin.

“wannan tiny little human da ke cikinki zanyi maganin shi”

Maryam ta fashe da dariya, har sai da ta kwanta a kan gadon

Zaid ya yi saurin matsowa kusa da ita.

“Easy, Haya! Ki dena dariya irin haka.”

“Rouhi, I’m fine!”

Ya kalleta, sannan shi ma ya fara murmushi.

“Fine, ki qare dariyar ki amman gobe inaga restaurant zan samu in saye kuma in dauko miki private chef yadda bazaki sake wahalar dani ba”

Maryam ta share hawayen dariya.

“Gara dai ka rinqa yi da kanka ai kaga zaka qware”

Zaid ya buɗe baki yana kallonta.

“Excuse me? Ynzu kikayi rejecting five star meal din da nayi miki preparing fah”

“Inaga my personal chef din needs more training.”

Ya girgiza kai yana dariya.

“Zo mu koma baccee, in ba haka ba ynzu zanyi charging dinki se kin biyani baccin da kika hana ni“

Ta bude hannunta alamar yayi mata hug

“Come here.”

Ya matso kusa da ita, ya rungume ta yayi kissing goshin ta

“Thank you, my Rouhi.”

Ya kalleta, yana murmushi, sannan ya sake matse ta jikin shi

Daga wannan daren, cin abincin tsakar dare ya zama kamar wani irin wasa tsakaninsu, har yazo ya san abubuwan da take nema da dare, se ya rinqa saka su Samantha suyi su ajiye idan ta nema se yaje yayi warming ya kawo mata, wani lokaci kafin ya kawo ta koma baccee 


zaid ne zaune a office dinshi yana duba takardun wani babban project da suke shirin fara aiwatarwa.

Assistant dinshi ya shigo 

“Sir, these are the revised documents for the Amsterdam project. The team is waiting for your approval.”

Zaid ya miƙa hannu ya karɓa.

“Leave them here. I’ll review them shortly.”

“Yes, sir.”

ya juya zai fita, amma sai ya tsaya lokacin da ya ji Zaid yana magana.

“Wait.”

Ya juyo.

“Sir?”

Zaid ya ɗaga kansa.

“Do i have anything scheduled after lunch?”

“Yes, sir. The meeting with the international partners is at two-thirty.”

“Move it to three.”

“Certainly, sir.”

Da ya fita, Zaid ya jingina da kujerarsa ya kalli agogo.

Be samu baccee sosai ba daren jiya, kuma tunda yazo office yau yake tuna drama dinsu da maryam jiya, wai bazata chi fries dinba tunda dama chewa tayi “maybe with cheese”, kai anya ze iya kuwa? Ya girgiza kai yana murmushi.

“I’m becoming a joke in my own house.”

Ya ɗauki wayarsa ya aika mata message

Zaid: sleepyhead, kin koma baccin ne? How are you feeling?

Bayan mintuna kaɗan, ta amsa.

Maryam: hy Rouhi ❤️ I’m fine.

Zaid: kin chi abnci?

Maryam: Not yet.

Ya daɗe yana kallon saƙon kafin ya rubuta.

Zaid: Haya.

Maryam: What? 😂

Zaid: Go and eat something, please.

Maryam: Okay, Daddy.

Zaid ya tsaya yana kallon kalmar da ta kira shi da ita.

Daddy.

Wata irin nutsuwa ta mamaye zuciyarsa. Bai san dalilin da ya sa kalmar tasa shi jin wani irin farin ciki ba, se ya tuna cewa nan gaba kadan zasu samu tiny human da zai kira shi da wannan suna, sai ya ji kamar zuciyarsa tana cike da wani abu da ba zai iya bayyana wa kowa ba.

Ya rubuta mata.

Zaid: Don’t call me that when I’m at work. I won’t be able to concentrate.

Maryam: Then concentrate, Daddy. 😂❤️

Ya fashe da dariya shi kaɗai.

Lokacin da mataimakinsa ya dawo, sai ya tarar da maigidan nasa yana murmushi yana kallon waya.

Ya tsaya daga ƙofar.

“Sir, is everything okay?”

Zaid ya ɗaga kansa da sauri yana qoqarin mayar da fuskarsa yadda suka saba gani

“Yes. Everything is fine.”

Mataimakin ya gyada kai, amma a zuciyarsa yana mamakin abin da ya sa maigidan nasa yake murmushi shi kaɗai, ya lura kwanan nan haka yake 

Bayan ya fita, Zaid ya mayar da hankalinsa ga papers din, Ya yi ƙoƙarin maida hankali kan calculations din da ze kammala, amma bayan ɗan lokaci sai ya ɗauki wayarsa ya sake rubuta mata.

Zaid: Please eat haya, And don’t forget your supplements.

Maryam: Yes, doctor daddy😂

Ya girgiza kai.

Wannan yarinyar za ta sa ya fita hayyacinsa wata rana, murmushin bai bar fuskarsa ba, haka dai ya daddafa yana qoqarin mayar da hnkalin shi kan aiki don ya samu ya kammala ya koma gidan da wuri

Da yamma, Maryam tana zaune a falo tana kallon pictures a wayar ta, ta shiga messages Tayi scrolling chan sama tana karanta tsofaffin messages dinta

Tun bayan kammala jarabawarta, tana jin daɗin hutun da ta samu, Amma a wasu lokutan, sai ta fara kewar makaranta, abokan karatunta, da yadda suke taruwa suna karatu tare, ta fara missing Susan, se kewar gida ta fara dawo mata, tana tunawa da mama, da su safiyyah 

Zaid ne ya shigo falo ya tarar da ita tana kallon wayarta tayi shiru.

Ya zauna kusa da ita.

“Haya, what’s wrong?”

Ta dago da sauri dan batasan dawowar shi ba, Ta girgiza kai.

“Ba komai, sannu da zuwa.”

Ya kalleta sosai.

“Haya.”

Ta ɗaga kai ta kalleshi.

“I’m okay, kawai ina kewa ne”

Ya fahimci abin da take nufi, ya gyara zamansa, yana sauraron ta.

“Tell me more” ya fadi yana zaunawa kusa da ita, ta kalleshi

“Komai nata faruwa da sauri, nayi aure, kafin in sani mun dawo nan and ynzu kuma..I’m..I’m pregnant. I’m happy, Rouhi. I really am. Amma ganin nike everything is happening too fast, rayuwata tanata chanjawa cikin dan lokaci kadan

Zaid ya yi shiru a ranshi yana chewa inna lillahi zata fara

Ya kama hannunta ya riqe su

“Haya, banajin daadin ganinki cikin damuwa”

Ta ɗaga kai ta kalleshi.

Ya gyada kai kafin ya chigaba “idan kinaso ai se ki koma school idan an dawo hutu, tunda zaman gidan ne bakiso ko? Dama I was worried about your health shiyasa nache bazaki koma ba, especially yadda nike ganin kina zama exhausted a kwanakin nan, naso ki huta kawai.”

Ta gyada kai, ya jawota jikinshi 

“ai zamuyi magana da doctor muji what’s safe for you, daga nan zamuyi contacting university din muji  what options you have, Maybe zaki chigaba da lectures online, so that bazaki zama bored ba, kuma shima idan doctor tayi recommending more rest ne, if not se ki chigaba da zuwa school abunki, don’t worry we’ll adjust accordingly.”

Murmushi tayi 

“Thank you”

Ya ɗaga hannunta yayi kissing

“Haya, ki dena yawan rikicin nan da kika fara”

Ta ɗan turo baki

Ya rungume ta yana dariya, yayi kissing goshinta

“I love you haya, And I want you to have the life you dream of, not just the life I can provide for you.”

Maryam ta kwantar da kanta a ƙirjinsa.

“I love you Rouhi”

A wannan lokacin, ta ji kamar an cire mata wani nauyi daga zuciyarta, tana jin daadin yadda mijinta ke tafiyar da al’amuran da suka shafe ta

Zaid ya shafa gashinta a hankali.

“Ynzu dai a biyani ladar aikin lallashin da aka sani ina dawowa gida” ya fadi yana qara matse ta jikin shi

Tayi murmushi “toh nawa za’a baka?”

Ya nuna lips dinta “wannan nikeso”

Ta zumburo bakin tana magama qasa qasa

Bata ankara ba taji ya fara kissing dinta har ya miqe tsaye da ita a jikinshi ya haye upstairs daga nan dai wasan ta chnja salo.

Da dare tana zaune kafin suyi baccee ta kira group video call da safiya da bahijja, tayi dialing Ba da daɗewa ba, fuskar Safiyya ta bayyana 

“Maryam” ta fadi da qarfi seda maryam ta runtse ido

“Kai Safiyya!”

Dukansu suka fara dariya, a dd nan Bahijja Tayi joining 

“Ah-ah! Maryam yanzu sai an gama exams ake tunawa da mu ko? Dama ke da an fara exam shikenan hnkalinki ke fita jikin ki”

Maryam ta yi dariya.

“Wallahi nayi missing ɗinku sosai.”

Safiyya ta gyara zamanta, tana ɗora hannu a cikinta da ya girma sosai haihuwa yau ko gobe

“Muma mun yi missing ɗinki, duba kiga ga yaron ku nan ya maidani qatuwa, wannan babyn naku ya gama gajiyar da ni.”

Maryam ta buɗe baki cikin mamaki.

“Safiyya! Se ynzu naga yadda kika ƙara girma kai kai”

“Toh ba kinyi nisa ba har Amsterdam, kina tsammanin zan tsaya yadda kika banni”

Bahijja tayi dariya.

“Safiyya, Tun da kikaga maryam ta kira mu haka akwai wani abu, ga bakinta nan da alamar magana, fadi muna jin ki”

Maryam ta ɗan yi shiru, ta kalli fuskokinsu a wayar, sannan ta yi murmushi.

Safiyya ta matsa da kunnenta kusa da wayar alamar tana saurare

“Me ya faru? Gaya muna, Nasan dai ba se ynzu aka kashe boss ba, wa’innan zafafan lectures da kike turomin da gani kin riga kin tsufa a haraka”

Maryam ta sunkuyar da kai cikin kunya, se kawai tayi musu nuni da cikinta.

babu wanda ya yi magana na dan lokaci kamar suna processing abun

Sai chan Safiyya ta yi ihu.

“WHAT?! MARYAM!”

Bahijja ma ta buɗe baki amma ta kasa magana

“Wait! You’re serious?”

Maryam ta gyada kai tana dariya.

Safiyya ta fara tafa hannu, idanunta suka cika da hawaye na farin ciki.

“Alhamdulillah! Maryam, Allah ya sauƙaƙa miki, ya ba ki lafiya, Allah yasa kar kiyi wahalar da nayi”

“Ameen, Safiyya”

Bahijja ta girgiza kai tana murmushi.

“Wai ina mijin ki? Ya yayi lokacin da yaji?”

Maryam ta tuna yadda Zaid ya yi shiru a asibiti, da yadda ya kasa samun kalmar da zai furta.

Ta yi murmushi.

“Da farko na dauka ko ya daina jin turanci ne, tun da Dr ta fara bayani har ta qare, kallonta kawai yake”

Safiyya ta fashe da dariya.

“CEO Zaid Rahman? Wanda ake cewa idan ya shiga meeting sai kowa ya yi shiru?”

“Shi ɗin fah,” Maryam ta amsa tana dariya, Tana kallon side din yake zaune, taga ya ajiye laptop din da yake aiki da ita gefe yanata kallonta

Bahijja ta ɗago yatsa “hey look at us me kike kallo a chan gefe”

Maryam tayi Murmushi kawai

Safiyya ta gyara zamanta tulelen cikinta se binta yake duk direction din da tayi

“Yanzu ki saurare ni zan baki shawara from someone with experience😂 ki ci abinci, ki huta, ki bi duk abnda dr ze che miki, kuma wallahi kada ki bari mijinki ya dame ki ta yadda har zaki kasa natsuwa, wallahi idan suka san daadin ciki sun ringa maqale ma mutum kenan

Maryam ta yi dariya sosai tana kallon zaid da yayi shuru shima yana kallonta 

“Ke ai ba ki san ma yadda yake ba ma, a rana yana tambaya ta nachi abnci yakai so ashirin”

Bahijja ta yi ihu, “Ke shegiya bashi aka nufi ba wai miyasa kike bari kanki yana marfi”

Maryam da taji zasu ballo mata ruwa ta miqe tana qoqarin shigewa bathroom ya kamota ya zaunar da ita jikinshi a karkace ta yadda bazasu hango shi ba, 

Safiyya ta karbi zanchen bahijja

“Ki batta kawai tasani sarai abnda nike nufi, ai idan ya tambayeta tachi abnci so ashirin shima zesa ta bashi nashi abncin so ashirin”

Dukansu suka fashe da dariya bnda maryam da tayi wuqi wuqi da ido kamar an jijjiga bera a buta

Safiyya ta juya camera din wayarta tana nuna musu wasu kayan jariri da ta fara shiryawa a akwati

“Duba, na fara shirya kayan baby na asibiti, EDD ya matso sosai ina so komai ya kasance a shirye.”

Maryam ta kalla cikin sha’awa.

“Safiyya, they’re..so..cute!” Ta fadi a dan rarrabe saboda yadda take jin hannun zaid cikin jikinta yana shafa cikinta a hnkali 

“Ki fara shirya naki ma.”

Maryam ta buɗe baki.

“Ke Safiyya, ina zuwa appointments ne kawai ban ma fara antenatal ba”

Bahijja ta ɗan karkata kanta tana lura da yadda maryam ke magana 

“Maryam, bari in tambaye ki.”

“Inaji”

“Tun da dai ynzu mijinki ya kusa ya zama daddy yana barin ki kina tafiya da ƙafarki, ko ɗaukar ki yake? Ynzu ma dai na kasa gane inda kike”

Maryam ta fashe da dariya tana qoqarin kashe wayar zaid ya riqe hannunta

“Bahijja!”

Safiyya ta yi dariya har ta rufe fuskarta.

“Kai jamaa ku dena tsokanar yayana fah”

Maryam ta girgiza kai, “kai ku dena samuna ido”

Bahijja ta dafe ƙirjinta, “kin dai ji shawara kyauta safiya ta Baki”

“Wallahi kuwa, don ni nasan abnda na gani!” Safiyya ta amsa, tana dariya.

Ai daga nan ta kife wayar da sauri gudun kar su fadi wani abu don tasan halin mutanen nata

Zaid yayi dariya yana chigaba da shafa cikinta a hnkali “wai me suke nufi ne, yimin bayani ban gane ba”

Maryam tana yunqurin tashi ya matse ta gam, “ai nima ina buqatar a bani abnci” ya rada mata a kunne

Jin yadda yake mata cikin kunne yasa ta matse rigar shi gam a hannunta, ai tuni ta bada kai bori ya hau saboda itama ynzu ta gane wannan cikin ne kesa tanason jinta tareda mijinta koda yaushe


SOKOTO

 Imran na zaune cikin motarsa bayan ya kawo Hauwa Koulou gida, shima sun tashi daga gidan da suke gadi sun koma gidan da ke kallon na su mama wanda ya saye ya gyara, gidan yanada dan girma ba lefi kuma 4 bedroom ne da da parlour biyu

Inna tanada nata daki haka shima baba, se imran ynzu shima dakin shi daban na auta daban, amma auta dakin inna yake baccee kayan shi kawai ke dakin shi, dakin baba hade yake da babban parlour wanda ke nuni da shine master bedroom daga farkon shigowa gidan

zaune suke a mota don yache ma hauwa zeyi magana da ita, tun kusan mako uku da suka wuche, yana ta tunanin yadda zai bayyana ma hauwa abin da yake ji, ya san ba ya son ya yi gaggawa ko kuma ya sata cikin yanayin da za ta ji dole ta amince da shi.

Amma kuma ya san cewa idan ya ci gaba da ɓoye abin da ke zuciyarsa, ba zai taɓa sanin ko suna da makoma tare ba

Hauwa ta cire seat belt ɗin motar da ke jikinta, ta juya ta kalleshi.

“Yaya, are you okay? Tun da ka daukoni yau bakada walwala”

Ya ɗan yi murmushi.

“Lfya qalau, dama maganar da nache zamuyi”

Ta dan kalleshi 

“Toh yaya Inaji”

Imran ya ɗauki numfashi a hankali.

“Hauwa, tambayar ki zanyi, ba dole se kin bani ansa ynzu ba, kije kiyi tunani, ki gayamin tsakani da Allah, duk hukuncin da zaki yanke ki tabbatar abnda kikeso kenan, kada kiji kunya ko nauyin gayamin duk abnda kika yanke, in shaa Allah zan fahimta”

Hauwa ta yi shiru tana sauraro.

“Tun lokacin da muka fara sabawa, ina dan fahimtar abubuwa game da ke, yadda kike tunani, yadda kike mu’amala da mutane, da kuma yadda kike ɗaukar rayuwar ki da muhimmanci.”

Ta ɗan sunkuyar da kai, tana jin kunya.

Imran ya ci gaba.

“Nayita qoqarin gayama kaina chewa ke qanwata che kawai, amma maganar gaskiya abnda nakeji ynzu ina tunanin yafi gaban abnda nike tursasa ma kaina dauka”

Ya tsaya na ɗan lokaci, sannan ya kalleta.

“Ina sonki, Hauwa. Kuma ina son mu qulla alaqa da niyyar gina dangantaka mai ma’ana da gaskiya, wadda zata kaimu ga aure, idan kina da ra’ayi, ba na son in matsa miki kan maganr aure ko in yi miki alkawuran da ban kai matsayin da zan iya cikawa ba tukuna. Abin da nake so kawai shi ne mu fara da gaskiya da kyakkyawar niyya, mu ba juna dama mu ƙara sanin juna, se muga inda Allah zai kai mu”

Hauwa ta yi shiru.

Imran ya lura da yadda ta sauke idanunta, sai ya fara tunanin ko ya yi kuskuren faɗar abin da yake ji ne

Ya yi ƙoƙarin ƙara bayani.

“Ba ynzu zaki amsa min ba, kije kiyi tuna..”

“Yaya”

Ta ɗaga kanta ta kalleshi, zanyi tunani in shaa Allah” 

Yadda yaga yanayin fuskarta kamar da damuwa yasa beche mata komi ba ya gyada kai kawai ta bude motar ta fita

Tunda ta shiga gida taje ta gaida mama ta wuce dakin maryam da yake matsayin nasu a ynzu, mama ta lura da yanayinta amma bata tambayeta ba, bata fito daki ba se da akayi kiran sallar magrib ta fito tayi arwallah ta koma, shuru shuru har karfe goma mama bata jita ba, tache maryam qarama taje ta kira mata ita

Da sallama ta shigo parlor inda mama take zaune, mama ta kalleta na dan lokaci 

“Hauwa me ke faruwa? Naga kamar kina cikin damuwa”

Har zatache ba komai se taga ai bari kawai ta gaya ma mama ko zata bata mafita, a take ta zayyano ma mama duk yadda sukayi da imran, a mamakinta se taga mama na murmushi

“Toh Hauwa miye abun damuwa daga maganar alheri kuma?”

Tayi shuru ta kasa magana

“Ko baki son shi ne?”

Ta kasa amsawa, tsakani da Allah idan tache batason imran tayi qarya, saboda ya dade yana burge ta, amma ya zaayi tayi soyayya da wanda anty maryam tayi soyayya dashi har suka kusa aure? Anya zata iya?

A natse tayima mama bayanin dalilinta

Mama tayi murmushi 

“Toh hauwa koulu in banda abun ki ina maryam din take? Inache tana chan wata qasa da mijinta? Shikenan shi kuma kada ya chigaba da rayuwar shi ya tsaya yayita zama tunda maryam tayi aure?”

“Aa mama ba hakanan nike nufi ba, kawai inajin kunya ache zan auri wanda anty maryam tayi niyyar aure a da”

“Hauwa babu wannan maganar, wannan tsohuwar magana che da ta riga ta wuche, ai shi imran yanada hnkali, cikin hnkalin shi ya ganki yaji yanason ki, ko akwai haramci ciki?”

Ta girgiza kai

“Yawwa, indai kina son shi toh kada kiyi sanya wurin ansawa, imrana yaron kirki ne kamar ni na haifeshi haka nikeji, kuma zanso wannan abun ya tabbata, sedai idan baki son shi toh bazan taba matsa miki ba, ga maryama qarama nan se in bashi ita, don gaskiya inason imran ya zama cikin ahali na”

Ai se hauwa taji kamar mama ta kwada mata mari jin zanchenta na qarshe, haka dai ta daure har mama ta gama yimata nasiha sannan ta sallameta.

Tana shiga dakin su ta dauki waya tayi mishi text

Hauwa: Allah ubangiji ya zabar muna and a yafi zama alheri yaya, Allah yasa haduwar mu ta zama alheri garemu da yan uwa gabadaya”

Imran na zaune shuru yana tunanin yanayin da ya gani a fuskar hauwa dazu da yayi mata magana,

Se yaji qarar shigowar message ya dauka ya duba yaga abnda ta aiko mishi

Imran: “Alhamdulillah, Allah ya shige muna gaba yasa mu dache da alheri” shine reply din da ya aika mata 

Ta mayar mishi da 

Hauwa: Allahumma ameen”

ya jin wani irin sanyi a ran shi 

Wani irin farin ciki ya bayyana a fuskar Imran, ba kamar lokacinda ya shigo gida dazu ba, amma yanata ƙoƙarin danne shi

Yayi tunani na ɗan lokaci sannan ya sake aika mata da wani message 

Imran: akwai abun da nake so mu fahimta kuma mu amince da shi tare.

Hauwa: okay 

Imran: kar muyi rushing komai, kinga kinada karatu ahead, mu tafiyar da komai a hnkli ba tareda gaugawa ba, ko forcing wani abu. 

Hauwa: in shaa Allah 

Ajiye wayar yayi ya fito parlor ya tarar da inna da auta suna kallon sunna tv

Wani irin yanayi yake ji, ba wai na jin daadin fara soyayya a karo na biyu ba, aa, yanajin cewa ya fara gina wani abu da zai iya kasancewa mai muhimmanci a rayuwarsa

Zaunawa yayi kusa da inna, ta ɗaga kai ta kalleshi.

“Ya akayi imrana? Meyasa kake ta murmushi haka?”

Imran yana qoqarin daidaita fuskar shi

“Babu komai, Inna.”

Inna ta yi murmushi kawai

“In tayi tsami maji”

Se kawai yaji maganar ta fito bakin shi kamar an tunkudo ta

“Na yi magana da Hauwa yau.”

Inna ta karkato hnkalinta zuwa wurin shi

“Hauwa Koulou?”

Imran ya gyada kai.

A dd nan baba ya shigo, suka miqe suna yimishi barka da zuwa

Baba ya kallesu “Meeting kukeyi na ganku haka?”

“Eh kaima zauna ayi da kai” inna ta amsa mishi

“Toh, me kuka tattaunawa?”

Inna ta gaya mishi abnda imran ke gaya mata

“Toh ya kukayi?”

“Na..umm..na..tambaye ta ko za ta ba ni damar mu fara sanin juna da niyyar gina dangantaka mai kyau.”

Inna tayi murmushi sosae

“Allah ya zabar muku abunda yafi zama alheri”

Baba ya yi murmushi, amma ya yi ƙoƙarin ɓoye farin cikinsa.

“Kuma me ta ce?”

“Ta amince mu fara sanin juna sosai, ba tare da gaggawa ba.”

Inna ta amsa mishi 

“Allah ya sa alheri, imrana”

Baba ya yi murmushi “Allah ubangiji yayi muku albarka”

“Ameen ya Allah Baba.”

A wannan daren, Imran ya kwanta da zuciya mai natsuwa. Bai yi gaggawar tunanin aure ko tsara dukkan rayuwarsu ba. Abin da ya sani shi ne, ya hau sabon mataki a karo na biyu, kuma yana son ya gina shi da gaskiya.

A ɗayan ɓangaren, Hauwa ma tana kwance tana tunanin maganar da suka yi, Allah ka shige min gaba, ta fadi tana runtse ido.


ABUJA

A Balarabe Mansion, Mammi tana zaune a ɗakinta tare da Hajiya Raliya.

A gabansu akwai tsoffin wasiƙu, kwangiloli da wasu takardu da aka tattara tun bayan rasuwar Rahman Balarabe, wa’inda hajiya Raliya tayi contacting tsofaffin abokan aikinta na northern crest ta wurin su ta samo su, tun lokacin da suka fara binciken tsohuwar haɗin gwiwar Rahman da Bashir Misalati, Mammi ta fara fahimtar cewa wasu abubuwan da ta ɗauka a matsayin tsohon tarihin iyalin ta sunada alaƙa da matsalolin da suka taso bayan rasuwar Alh Rahman da aka fara binciken Alh Bashir.

Hajiya Raliya ta ɗauki wata wasiƙa ta karanta ta a hankali.

“Wannan takardar tana magana ne game da rabon kadarorin da aka amince da shi tun lokacin da Rahman da Bashir suka fara aiki tare.”

Mammi ta gyara zamanta.

“To, idan an rubuta hakan a takarda, me ya sa aka bar al’amarin ya rikice har tsawon waɗannan shekarun?”

Raliya ta sauke ajiyar zuciya.

“Saboda wani ke amfana da rikicin. Amma ba za mu zargi kowa ba sai mun sami hujja.”

Mammi ta kalli takardun da ke gabanta.

“Fahad ɗana ne, kuma shi ne yake kula da yawancin harkokin company, me ya sa kikache kar in gaya mishi?” 

Raliya ta ɗaga kai da sauri.

“Mammi, kada ki bari dangantakarki da shi ta hana ki neman gaskiya, ki bar binciken nan tsakanin mu a ynzu dai”

Mammi ta girgiza kai.

“Ban fahimta ba, amma dai zanyi yadda kikache”

Hajiya Raliya ta ɗauki wata takarda mai ɗauke da wasu bayanai ta ajiye gefe.

“Gobe zan kira wani tsohon ma’aikaci da ya yi aiki tare da Rahman da Bashir. Wataƙila yana da bayanin abin da ya faru da tsoffin takardun kamfanin.”

Mammi ta kalleta.

“Kina ganin zai iya taimaka mana?”

“Ba zan iya tabbatarwa ba. Amma idan akwai wanda ya san yadda aka sauya bayanan haɗin gwiwar, dole ne mu fara da waɗanda suka kasance a cikin company din tun a lokacin.”

Mammi ta yi shiru, sannan ta ɗauki envelope ɗin da aka rubuta sunan Bashir Misalati a kai.

“Har yanzu ina mamakin yadda wannan takarda ta kasance a cikin abubuwan da Rahman ya bari. Idan da gaske Bashir yana da haƙƙi a cikin kadarorin nan, to iyalinsa sun daɗe suna rayuwa ba tare da sun san abin da ya kamata su sani ba, mu kuma muna zaune akan hakkin su”

Hajiya Raliya ta kalli envelope ɗin.

“Shi ya sa dole ne mu gano gaskiya, ki tuna, ba mu san duk abin da ya faru ba saboda haka bamuda laifi, kuma akwai mutanen da ba za su so a sake buɗe wannan al’amari ba wanda tun farko su suka rufe shi”

Mammi ta ɗaga kai.

“Kina tunanin akwai wanda zai iya cutuwa saboda waɗannan takardun?”

Hajiya Raliya ta yi shiru na ɗan lokaci.

“Ina tunanin akwai wanda zai iya jin tsoro idan aka fara bincike. Shi ya sa ba za mu sanar da kowa ba har sai mun san abin da muke riƙe da shi.”

Mammi ta gyada kai, sannan ta mayar da takardun cikin envelope, lokacin da suke tattara sauran takardun, wayar Mammi ta yi ƙara.

Ta ɗauka ta duba wayar. Saƙo ne daga unknown number 

Unknown Number: Ku daina tono abin da ya kamata ya kasance a binne. Ba kowane sirri ne aka halicce shi domin a tona ba.

Mammi ta ji wani irin sanyi ya ratsata. 

Ta miƙa wayar ga Hajiya Raliya ba tare da ta ce komai ba.

Raliya ta karanta saƙon sau biyu. Fuskarta ta canza, amma ta yi ƙoƙarin ɓoye damuwarta, ta ɗauki wayarta ta ɗauki hoton saƙon.

“Ki bar saƙon a wayarki. Kada ki amsa. Za mu adana shi a matsayin hujja.”

Mammi ta kalleta cikin damuwa.

“Raliya, wannan yana nufin wani ya san abin da muke yi.”

“Eh,” Raliya ta amsa a hankali. “Kuma wannan ya nuna mana cewa dole ne mu ƙara yin hankali.”

Ta tattara takardun cikin envelope ta rufe shi 

“Daga yanzu, kada ki tattauna wannan al’amari a waya, kuma kada ki bar takardun a inda kowa zai iya gani, sannan ki nemo mukullin qofar nan ta bayan garden a duk inda kike tunanin kin ajiye shi, saboda akwai file da nike tunanin yana cikin dakin nan, kuma cikin shi zamu iya samun cikakken bayanin komai”

Mammi ta gyada kai, amma zuciyarta cike take da tambayoyi.

Wa ya aiko mata wannan saƙon

Meyasa yake son a bar tarihin Bashir a binne?

Kuma idan babu abin da za a ɓoye, me ya sa wani yake tsoron a gano gaskiya?


Amsterdam

A daren wannan ranar, Maryam tana zaune a kan gadonta tana jiran Zaid ya gama wani business call da yakeyi.

Ta ɗauki wayarta tana duba messages din Safiyya da hotunan kayan jaririn da ta turo mata.

Ta yi murmushi lokacin da ta ga new message

Safiyya: I can’t wait for you to come back. I’ll keep sending you pictures as the day gets closer. ❤️

Maryam tayi mata reply tana murmushi sannan ta ajiye wayar a gefenta.

A lokacin ne wayar ta sake yin ƙara.

Ta ɗauka tana tunanin ko Safiyya din che, ce ta sake aiko mata wani message

Amma tana buɗe message din, murmushin da ke fuskarta ya ɓace.

UNKNOWN NUMBER DIN DAI

Saƙon kuwa ya kasance gajere.

Unknown Number: FILE 17 maryam

Ta tsaya cak.

Ta sake karanta saƙon.

Kafin ta samu lokacin tunani, wani saƙo ya sake shigowa.

Unknown Number: Abin da aka ɓoye a bayan ƙofar garden din  Balarabe Mansion ya fi abin da kike tsammani muhimmanci akan batan yayarki da rasuwar mahaifin ku, kada ki yarda da duk wanda zece yanason ya taimake ki, kada ki yadda da kowa

Maryam ta ji zuciyarta tana bugawa da sauri.

Ƙofar nan ta garden kenan a ciki zata samu File 17?

Waɗannan kalmomin sun tuna mata da hoton ƙofar da aka taɓa turo mata, tare da gargaɗin kada ta koma Abuja ita kaɗai.

Ta ɗauki numfashi a hankali, tana ƙoƙarin kwantar da hankalinta.

A lokacin ne Zaid ya juyo ya kalleta

“Haya, what’s wrong?”

Maryam ta ɗaga kai da sauri.

“Nothing, Rouhi.”

Ya tsaya yana kallonta.

“Maryam.”

Ta san wannan yanayin nasa, ya riga ya gane akwai abnda ya tada mata hankali, me zatache mishi? Anche kada ta yadda da kowa, amma tanada tabbacin zayd baze cutar da ita ba, ta gaya mishi kawai? Kai ina bazata iya ba, wane bayani zata mishi ynzu da ze yadda da ita bayan duk abubuwan da ta boye a baya?

Ya matso kusa da ita ya zauna a gefen gadon.

“Show me.” Kawai yache yana kallon wayarta, saboda yanada tabbacin ko minene ya daga mata hnkali daga wayar ne, don daga inda yake zaune yana waya yana kallonta sanda take chatting tana murmushi tundazu amma ynzu kawai yanayinta ya chnja

Ta kalli wayar da ke hannunta na ɗan lokaci, ta yi tunanin ta nuna masa kawai, Amma sai ta tuna cewa shima yana da abubuwan da bai bayyana mata ba, ai an taba aiko mata da saqo chewa yana kusa da Gaskiya fiye da ita,

Ta ja numfashi.

“It’s just a message.”

“Me akache? Wa ya aiko?”

“Ban sani ba. An unknown number.”

Zaid ya miƙa hannu.

“In gani”

Maryam ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta miƙa masa wayar.

Ya karanta saƙonnin, kuma nan take fuskarsa ta sauya.

“The garden door?”

Maryam ta kalleshi.

“Haka akache, nima bn sani ba Rouhi.”

Ya sake karanta saƙon, sannan ya ɗaga kai ya kalleta.

“Dama ana aiko miki messages irin wannan ko yau ne kawai?”

Maryam ta ji zuciyarta ta yi nauyi.

A wannan lokacin, ta fahimci cewa ba za ta iya ci gaba da ɓoye duk abin da ta sani ba har abada, kuma ta yadda da zaid, gara kawai ta gaya mishi tunda ya riga yaga wannan

“Rouhi, akwai wani abu da ya kamata in gaya maka”

Zaid ya kalleta sosai.

“Then tell me Haya, ina jinki”

Ta riƙe wayar a hannunta, tana ƙoƙarin tsara kalmomin da za ta fara da su.

Amma kafin ta fara magana, wayar Zaid da ke kan tebur ta yi ƙara.

Ya tashi ya dauka ya bude

Ya kalleta.

Saƙo ne daga unknown number.

Ya buɗe shi.

Unknown Number: FILE 17 ba sirri ba ne kuma a ynzu, wani ya fara neman shafin da ya ɓace. Idan kana son kare Maryam, ka nemo shi kafin Fahad ya same shi.

Zaid ya daina motsi.

Maryam ta lura da yadda fuskarsa ta sauya.

“Rouhi? Minene?”

Ya ɗaga kansa ya kalleta.

A karon farko cikin kwanaki da dama, dukkansu suna kallon juna da sanin cewa abin da suke ɓoyewa abu guda ne

File 17.

Zaid ya kama hannunta.

“Haya, daga yau, za mu fuskanci wannan abun tare, ba sauran ɓoye ɓoye, ynzu ki gayamin komai”

Maryam ta gyada kai a hankali, a natse ta fara jero mishi duk abnda ta sani daga farko har qarshe

Seda zayd yaja numfashi ya sauke sannan ya kama hannunta ya riqe 

“Haya, ya kamata muje musan me ke cikin wannan file 17 din, inada tabbacin keys din qofar suna wurin mammi, zan tambayeta”

Ya kalli saƙon a wayarsa, sannan ya mayar da kallonsa gare ta amma hnkalin shi ya riga yayi nisa, kalmomin ƙarshe na saƙon suka ci gaba da maimaituwa cikin kan shi..

I should Find it before Fahad does.

Me Fahad ya sani? Miye ma’anar wannan saqon?


A wannan daren, Maryam ta fahimci cewa abin da ya fara a matsayin messages na ban mamaki gareta, a ynzu ya zama wani al’amari da zai iya sauya rayuwar iyalinsu gaba ɗaya.

Kuma a Abuja, a cikin wani ɗaki da aka daɗe ba a buɗe ba, tsohuwar ƙofar nan da take kulle.

Akwai sirrin da ke bayanta wanda yake ƙara matsowa kusa da haske.

Domin wani lokaci, Kiran Ƙaddara ba ya zuwa domin ya gaya maka abin da zai faru. Yana zuwa ne domin ya kai ka inda ƙaddararka take jiran ka.

Kuma ga Maryam da Zaid, ƙaddarar su ta fara kira da ƙarfi fiye da da. ❤️‍🔥


Join our WhatsApp group


Follow this link to join my WhatsApp group:

***

174C2D6E-930B-4863-A1FC-C0CF0D7A568B.png