BA NI DA MADOGARA

Chapter 10

by @narrnarhhbukar00

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*











*Bani da Madogara*
  (Sai Allah...)




 



010

Rai bai so ba haka ya miƙe ya ɗauki mukullin mashin ɗinshi ya ƙara gaba ko sauraron maganar da Hannatu take masa bai yi ba. Direct ya nufi ƙauyan kwarin ɗan dodo har inda ta ce su haɗu,ya sameta sanye da hijab da niƙaf tana tsaye a  wajan bishiyar lemu kusa da wani gida tana kallonsa. Koda ya iso wurin sai ya dubeta cike da ɓacin rai ya ce

"Haba Murja ya kike so na yi ne don Allah, Kin ce na baki kuɗi na baki, kusan kodayaushe tambayana kuɗi kike ina baki duk don karki tonamin asiri, Haba don Allah kamar  ba ɗan uwan mijinki ba, mtws!!!"

Cike da ɓacin rai yake maganar don ta kai shi maƙula yau.Mai Murja za ta yi in ba dariya ba, sosai take dariya cikin niƙaf ɗin sai da ta yi dariya ma'ishinta sannan ta dubi Alhaji Zakari ta ce

" Zakari kenan ai a cikin abubuwan da na tanadar don na yi maka ban yi komai ba wallahi, yanzu aka fara wasan,u mm dama wata muhimmiyar magana ce na zo maka da ita, umarni ne kuma zai iya kasancewa na ƙarshe, idan ka yi abinda na ce  baka sake jina a cikin rayuwarka"

Shiru Alhaji Zakari ya yi yana mata kallon uku saura kwata, wai ita ce za ta bashi umarni ya bi ko matarsa Hannatu duk ƙaunar da yake mata ai bata isa ta  umurceshi ya yi abinda bai yi niyya ba balle ita karan kaɗai miya, amma bara yaga gudun ruwanta sannan ya ji wani umarni shegiyar za ta bashi. A daƙile ya ce

"Ina sauraronki"

Gyara tsayuwa Murja ta yi sannan ta fara magana cike da Izza

"Zakari ina so ka auri ƙanwata wacca take zawarci a nan garin!"

Dummmmm!!! Lokaci guda ƙirjin Alhaji Zakari ya bada, ɗan sauran lissafinsa daya rage ya ɓace, har ɗan duhu-duhu yake gani tsabar shiga ruɗun da ya yi, bai san lokacin da ya daka mata wata uwar tsawa yana cewa

" Baki da hankali ne!!! Ni za ki umurta na auri ƙanwarki saboda iskanci da bura-uba, kodan kinga ina bin duk abinda kika bijiromin dashi ba tare da na yi miki musu ba , shi ne yanzu dan rainin hankali kamar wani tsaranki za ki ce na auri ƙanwarki, wallahi ƙaryarki tasha ƙarya! "

Ko gezau Murja bata yi ba sai ma sake gyara tsayuwanta da ta yi, cikin niƙaf ɗinta ta saki munafikin murmushi, Sannan ta ce

" Miye na saurin fusata haka Alhaji Zakari"

Banza ya yi da ita, sai ta ci gaba da cewa

"Karka manta a tsirara nake kallonka, babu abinda ban sani ba a game da kai,idan na ce komai ina nufin komai, kar ka yi jayayya dani idan ba haka ba, Ina gab! Da kwance zaninka a tsakiyar kasuwa, au na manta bara na kira ƙanwar tawa mu gaisa" 

Bata jira mai zai ce ba, ta ciro wayanta ta kira wata numba, ring ɗaya-biyu sai aka ɗau kiran, kai tsaye ta ce 

"Ki fito" 

Sai ta katse kiran. Bata minti huɗu da kashe kiran sai ga ƙanwarta ta fito daga gidan. Alhaji Zakari na haɗa idanunsa da na ƙanwar Murja nan take hankalinsa ya dugunzuma ya yi ƙololuwan tashi, gumi har ya fara jiƙa jikinsa. Bakinsa na rawa ya dubi ƙanwar Murja ya ce

"Kkke Kkke  kke ceee!" 

Murmushi ta sakar masa, Sannan ta ce

"Ƙwarai da gaske ni ce, ka za ci nima karuwar ce hala" 

Abu goma da ashirin daman ba karuwa ba ce a lokacin da ya je gidansu Bintoto, Innalillahi, ya shiga uku ya lalace, kenan ita ce ta naɗi abinda suka aikata shida Bintoto taba Murja, ita kuma take yi mishi barazana, to ya hakan ta faru, ya aka yi basu ankara ba. 

*Waiwaye*

Tun lokacin da Hannatu ta kira Murja akan tana so ayi ma Salim asirin sata tare da sanar mata Alhaji Zakari ya tafi Ƙwarin ɗan dodo akan a rufe ma Musa baki kar ya sake tado da batun auran Hujayrah ta shiga farin ciki domin tasan dole ne ya je wajan karuwarsa Bintoto. Daman ta  daɗe da sanin Alhaji Zakari yana neman matan waje har da na wasu ƙauyakun, kasancewar Ƙanwar mahaifiyar Murja a Ƙwarin ɗan dodo take da zama, sannan tana da yarinya wacca auranta ya mutu a sanadiyyar rasuwan mijinta. Ta wurin ƙanwar ta mai suna Zaliha take sanin idan Alhaji Zakari ya zo wurin karuwarsa a garin, da yake Zalihan akwai wacca ta sani a gidan karuwan . Jin Alhaji Zakari zai je Ƙwarin ɗan dodo wurin malaminsa, to tabbas babu makawa sai ya leƙa wurin Bintoto ya ɗan rage zafi. Bayan su Murja sun gama yanke shawara da Hannatu akan bayan sallar Zuhr za su je ƙauyan Ciri-tawa. Lokacin da Murja ta dawo ɗakin ta sai ta kira Zaliha akan ta yi maza ta je gidan karuwan garin wa'inda suke zama a ƙarshen gari ta naɗo masha'ar da suke tunda tana da wacca ta sani sannan karuwan mafi yawancinsu basa garin sai ta yi kamar ita ma karuwar ce, ta ga abinda suke aikatawa . Da yake akwai yarjejeniyar da suka yi, idan Zaliha ta naɗo abinda su Alhaji Zakari suke yi tunda tana da babbar waye ita kuma Murja za ta yi iya ƙorakinta wurin ganin Alhaji Zakari ya aure Zalihan . 

Hakan ta faru domin suna gama wayar da Murja Zaliha ta ɗauki hijab ta saka sannan ta saka niƙaf kar mutane su ganeta tunda ƴar garin ce, direct gidan karuwan garin ta nufa wanda yake a ƙarshe gari, ta ko ci sa a babu kowa a tsakar gidan sai kawai ta cire hijab da niƙaf ta zauna, koda Bintoto ta fito daga ɗakinta za ta shiga wanka bata wani damu ba ganin Zaliha a zaune a tsakar gidan tunda kowa na kawo baƙonsa a gidan babu mai hana wani a cikinsu , ƙila wata a cikinsu ne ta kawota,  bayan ta shiga bayi ta yi wanka sannan ta koma ɗakinta don shiryawa kafin Alhaji Zakari ya zo. Ba a yi rabin awa ba sai ga tsayuwan mashin ɗin Alhaji Zakari, koda ya shigo gidan da sallama a bakinsa sai ya ci karo da Zaliha a tsakar gidan, shi a tunaninsa wata sabuwar karuwa ce suka samu, a nan dai ya amshi numban wayanta sai ya wuce ɗakin Bintoto.bayan wani lokaci Zaliha ta fara Jin gurnaninsu hakan ya tabbatar mata sun fara masha'arsu, sai kawai ta ciro wayarta a hankali ta je wurin windon ɗakin Bintoto ta naɗi abubuwan da suke aikatawa sannan ta yi saving ta ɗauki hijab da niƙaf ta saka tabar gidan da sauri. (Ikon Jalla  jalalu ƙauye ma sun iya makirci haka🤔🤔🤔) 

Koda Zaliha ta dawo gidansu sai ta kira Murja akan ta naɗi abubuwan da suke yi, sosai Murja ta shiga farin ciki don haƙarta tana gab da cimma ruwa. Kasancewar ƙaramar waya ce a hannunta, sai kawai ta aika a siyar mata da akuyarta wacca take hannun babbar ɗiyarta Hadiza tana mata kiyo,bayan an kawo mata kuɗin ta ba wani ɗan uwanta ya siyo mata ƴar babbar waya wacca za ta iya tura videos ɗin,da za su  tafi ƙauyan Ciri-tawa da Hannatu sai ta bama ɗan uwa nata, ba da wuri suka dawo garin ba, sai kawai washe gari da sassafe ya aikomata da wayan, daman Murja ta taɓa riƙe babbar waya shiyasa bata sha wuyan gane yadda za a yi amfani da wayan ba. Bayan mai afkuwa ta afku akan ɗan Hannatu, Murja ta je ta taya Hannatu alhini sai kawai ta dawo ɗakinta cike da murna, wurin 12:12pm na rana sai ta shirya ta tafi Kwarin ɗan dodo , a nan ta yi sending videos ɗin sannan ta dawo gida wanda wannan shi ne mafarin tashin hankalin Alhaji Zakari ya umurci Hannatu ta kai mata dubu hamsin. Wannan kenan

*Cikin Labari*

Sosai mamakin Murja ya cika Alhaji Zakari, har ya ma rasa abin cewa sai kallo.Zaliha sai wani ragwaɗa da karairaya take tana tauna cewing gum yana bada sautin ƙas! Ƙas! Goge zufar da take saman goshinsa ya yi sannan ya ce

"Ban taɓa ganin mara hankali kuma dabba kamarki ba,in banda rashin lissafi da tunani irin naki taya zan aura ƙanwarki bayan matata aminiyarki ce, ki sani bazan ci amanar matata ba don alƙawari ne bazan taɓa yi mata kishiya ba, sannan daga yau Karki sake kirana batun na auri ƙanwarki don bazan aureta, Kin yi kaɗan ki umurceni da na yi abinda ban yi niyya, wallahi kin yi kaɗan"

Maimakon Murja ta ji haushi ko kuma da tsorata Sai ma ta saki dariya tana tafa hannunta, bayan ta yi dariyar ma'ishinta sai ta ce

"Zakari ni nan da kake kallo ba kanwar lasa bace,sannan da kake cewa Hannatu aminiyata ce a ta yaya ta zamo aminiyata, ni ban taɓa sonta da abota ba hasalima abin hannunta nake kwaɗayi da muradi sai kuma kash! Ta Nuna min *Ramin kura daga ita sai ƴaƴanta* duk wahala da bautar da na nayi mata shekara da shekaru ban taɓa amfanuwa da ita ba,daga ita sai yaranta ta sani shiyasa na neman ma kaina abinda zai fissheni, kasani ni nan Murja *kumurcin kan dutse ne ban fito ba sai da na shirya* idan kai ne to nima ni ce, mu zuba mu gani shege ka fasa ɗan halak sai yanka, dole ka auri Zaliha idan kana son kwanciyar hankali da salama a rayuwarka,na baka daga yau zuwa kwana uku ka yi tunani, idan ka bari kwana huɗu ya wuce to ka tabbata ni Murja matar Zubairu za ta kwance maka zani a kasuwa, sai na tabbatar baka da sauran ɓirɓishin mutunci a idanun mutanan garin nan"

Shiru Alhaji Zakari ya yi bai yi tunani Murja ƴar bala'i bace sai yau duk da yasan ƴan matancinta, munafuka ce sosai amma bai yi zaton har zuwa yanzu halin nan nata na nan ba, ganin har da jikoki gareta amma kamar wacca ake kaɗawa da ruwan hanji haka take, bai san ya zai yi ba wannan shi ake kira da tsaka mai wuyar fita, gaba wuta baya bala'i. Ci gaba da cewa ta yi 

"Ni yanzu kaga tafiyarmu bazan sake kiranka ba, amma kasani idan ka bari  kwana huɗun da na gindaya maka suka wuce Hmmmmm!" 

Wucewar ta yi ba tare da ta ƙarasa maganar ba, Zaliha ta biyota a baya suka bar Alhaji Zakari tsaye kamar ɗan sanda. Ya daɗe yana tunani daga bisani ya haye mashin ɗinsa ya bar wurin... ✍️

      🌎🌎🌎🌎🌎🌎

A ɓangaren Hannatu bayan tafiyar Alhaji Zakari ta  zauna a kujera tana karanta wasiƙar jaki sai kira ya shigo wayanta, lokaci guda gabanta ya yanke ya faɗi ganin numban mahaifiyarta ɓaro-ɓaro a screen ɗin wayar, tsoro ne ya shigeta har ta kasa ɗaukan kiran, kiran  ya gaji ya tsinke, wani sabon kiran ne ya shigo jiki babu ƙwari hannunta na rawa ta ɗauki kiran. Cikin muryar dake nuni da tsoro ta yi sallama tare da gaishe da mahaifiyarta.A can mahaifiyarta ta amsa tare da ce mata duk abinda take ta bar shi ta zo Giwa yanzu nan, nan da nan jikin Hannatu ya yi sanyi mai afkuwa ta afku kenan,katse kiran ta yi sai ta shiga kogin tunanin 'shikenan  ta yi sanadin ɗanta ya zama ɗan daudu, amma bazata taɓa yafema Murja ba, sai ta ɗauki mummunan mataki akanta, za ta san ko ita wace ce' miƙewa ta yi ta nufa bedroom ɗinsu, daman ta yi wanka sai kawai ta shirya ta fito bayan ta kulle ko ina na sashen nata. Ɗan acaɓa ta samu ya kaita bakin titi sannan ta tsallaka titi biyu ta jira motar da za ta wuce Zaria.

Ta ɗan ɗauki lokaci a wurin tana jiran abin hawa daga baya ta samu wata Golf 3 za ta wuce Zaria sai ta shiga suka wuce Zaria, bayan sun sauka a mota cikin tasha sai ta samu motar da za ta kaita Giwa, sun daɗe suna tafiya sannan suka sauka ta ɗauki mashin har gidansu, bayan ta sauka sai ta sallami mai mashin ta shiga cikin gidan da sallama a bisa labɓanta.Da sauri Hannatu ta ja birki ta tsaya, ƙirjinta na bada sautin Ras! Ras! Waro idanunta ta yi waje bakin na rawa ta ce 

"Yyyyayansuu Harira kai ne hakaa !!!" 

A wurin ta saki Jakarta, sai ta ɗaura hannayanta a kai ta fara  kururuwa tana cewa

"Wayyyo Allah na! Wayyyo ni Hannatu na shiga uku na lalace!!! Ɗana ya zama ɗan daudu!!! Mai degree ya koma ɗan daudu!!! Shikenan tawa ta sameni ni Hannatu" 

Su Innayi ne da ƙaninta namiji suka fito daga ɗaki jin kururuwanta. Ƙaninta ne ya ce

"Haba Yaya naga zuwanki za ki fara kururuwa ki tara mana mutane alhalin babu wanda yasan komai, salati da istigfari ya dace ki yi ba ihu ba" 

Bata saurari mai ƙanin nata yake cewa ba sai ma ƙara ɗaga muryarta take, notikan kanta basu gama kwacewa ba sai da ta ji ɗanta na mata magana irin ta rikƙun ƴan daudu yana faɗin

"Mom ke ce a garin, saukar yaushe ya ƙannena suke fatan kuna lafiya, fatan kin zo min da kayan make up" 

Yana magana yana yarfa hannu irin na ƴan mata, sanye yake da doguwar rigar Innayi wanda aka ɗinka mata irin ɗinkin tsofaffi,rigar bata kai masa har ƙasa ba saboda yafi Innayi tsawo, rigar nono na jikar Innayi wacca take riƙo ya ɗauko har da kayan kwalliyanta, ƴan tsummokarai ne ya samu ya yi ciko a rigar nonan sai suka taso kamar na asalin, ya ɗaura ɗan kwali kamar mace, ya sha hoda da barbaɗe kumatu, duk wanda yaga Jamilu a lokacin dole ya ci dariya ya kuma tausaya misa, don bashi da wata maraba da mace har ma yaso finsu zaƙewa a wurin iyayi. Jamilu namiji ne iya namiji mai cikar zati shiyasa da ya yi shigar mata sai ya yi wani kala dashi. 

 Innayi ce ta ja hannunta zuwa cikin ɗakin sannan ta aiki jikarta da take riƙo akan ta yi maza ta kira mahaifiyarta da ƙanwar mahaifiyarta su zo Hannatu ta zo. Hijab jikar ta saka sannan ta tafi aikan. Shiru ɗakin ya yi baka jin motsin komai sai shassheƙan kukan Hannatu da jan majinanta,Innayi bata ce mata komai sai ido da ta zuba mata, sun kai tsawan lokaci a haka daga bisani ƙannanta suka zo har da namijin da ya fara  mata lokacin da take kururuwa. Bayan sun zauna sai Innayi ta ce

"Hanne!" 

Ɗan ɗago da kanta Hannatu ta yi ba tare da ta amsa ba sai Innayi ta ci gaba da magana

"Ina so ki faɗa mana meke faruwa dake ne don haka nan Jamilu bazai yi sata babu dalili ba, tun yana yaronsa bai taɓa ɗaukar tsinke da sunanta sata ba sai yanzu daya mallaki hankalinsa yasan ciwon kansa, ace an sameshi da irin wannan hali, bayan haka abinda ya sake ɗaure min kai shi ne na yau lokaci guda ace ya koma ɗan daudu, taya hakan ta faru, idan kinsan wani abu a kai ki yi magana don nasan halinki, wannan mummunar ɗabi'ar dana hanaki Allah yasa ba ita kika yi ba har ta taɓa ɗanki"

Shiru Hannatu ta yi tana shessheƙar kuka kamar wata yarinya, tasan mahaifiyarta sarai ta tsani zuwa wurin bokaye, sai dai idan abu ya yi tsamari  ta ce a tayata da addu'a, takasa gane a wannan zamanin sai da zuwa wurin bokaye mace take iya cira tuta, ta zama tauraruwa wurin mijinta koda kuwa bata da hali mai kyau. Katse mata tunani Innayi ta yi da cewa

"Dake fa nake Hanne kin yi mana shiru" 

Ɗan gyara zama ta yi rai bai so ba haka ta basu labarin tun daga asirin da taso ayi ma Salim har aka samu ya dawo kan Jamilu da sake zuwanta wurin bokan ya karya asirin sai ya yi mata sharaɗi akan dole ɗanta ya koma ɗan daudu sannan asirin zai karye. Bata ɓoye musu komai ba tana kuka tana sanar musu har ta ɗige aya. Mai su Innayi zasu yi inba salati da sallallami, ita Innayi har ta tafi da hannu tana salati, sosai hankalinta ya tashi ashe mugun halin yarinyarta yana nan bata daina ba. Cike da faɗa Innayi ta fara magana

"Kayya! Kayya! Albasa bata yo halin ruwa ba, da kuwa ta yi Hanne da baza ki taɓa zuwa wurin wani neman taimako ba balle zuwa wurin boka, sai wurin Allah mahaliccinki wanda shi kaɗai keda Ikon yin komai a lokacin da ya so, Kin bani kunya Hanne kamarki da ƴaƴa har kin fara tara jikoki amma kike aikata irin wannan mummunar ɗabi'a ga yaran wasu, Allah kenan ba a masa shisshigi a al'amuransa,kin so ɗan wani ya shiga mugun hali ya koma yana ɗauke-ɗauke sai kuma ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya, ya dawo kan ɗanki, haba Hanne"

Kuka sosai Hannatu take yi kamar wata yarinya ƙarama tana jan majina. Innayi bata jira cewar Hannatu sai ta ci gaba da cewa

"Daman ance Idan za ka gina ramin mugunta ka gina shi  gajere domin wata idan baka yi wasa ba kai za ka faɗa cikinsa, Kin so ɗan wani ya shiga  cikin mawuyacin halin gashi yanzu  ɗanki ne yake a ciki, me yasa Hanne? wani irin abu mahaifiyarsa ta yi miki da za ki cutar da ɗanta, bakya tunanin kina da yara da jikoki wata rana hakan za ta iya faruwa dasu,waya faɗa miki aikin boka yana yi, na ɗan wani lokaci ne fa, aikin daga baya zai karye, shi fa sharri da kike ganinsa ɗan aike ne, duk daran daɗewa zai dawowa mai shi"

Cikin rawar murya Hannatu ta ce

"Innayi duk laifin Innar Balki ce ita ta wargaza komai" 

"Ai na ji daɗin da ta wargaza asirin har Allah ya ƙaddara ya dawo kan ɗanki, ishara ce Allah ya nuna miki amma idan kin hankalta,saboda gobe ki kula amma fa idan kin ji don tun ba yau ba nake miki wa'azi akan zuwa wurin malaman tsubbu amma kin ƙi saurarena, ai ga irinta nan Allah ya ɗorama ɗanki wahala, bawan Allah babu ruwansa da hayaniya a sanadiyar muguntarki ya shiga cikin tsaka mai wuya, ki farka ki gane Allah ɗaya ne hakan zai sa ki samu sauƙi da salama a cikin zuciyarki"

Sosai wa'azin Innayi ke ratsa jini da ɓargon Hannatu, lokaci ɗaya tsoran Allah ya ɗarsu a cikin zuciyarta, makaman yaƙin data ɗauka na ganin bayan Zaytuna da ahalinta ta ajiye gefe, yanzu bata su take ba sannan za ta gyara halinta kodan ɗanta ya dawo daidai, sababbain makaman yaƙi da Murja ta ɗauka domin yanzu ta gane babu maƙiya kamarta, ita ce sanadin shiga halin da ɗanta yake cijj. Bayan Innayi ta yi mata nasiha da faɗa sosai kasancewar Innayi dattijuwar ƙwarai ce mai tsoran Allah da bin ƙa'idojin musulunci babu ruwanta da zuwa wurin malamin tsubbu balle boka, da Allah ta dogara domin babu wata madogara sai tashi, hakan yasa take ganin daidai tun daga yarintarta har zuwa tsufanta a duk yaranta babu mai mugun hali sai Hannatu duk da ita ce ƴarta ta biyu amma halinta ya banbanta dana sauran ƴan uwanta, ita kaɗai ce ta fita zakka a cikinsu har mazan. 

Ƙanin Hannatu ne ya ɗora daga inda Innayi ta tsaya kasancewarsa ustaz ne mai riƙo da addini sosai, shima wa'azi ya shiga yi mata yana jayo mata ayoyi da hadisai yana fassarasu  tare da tsoratar da ita akan masu hali irin nata basa gamawa da duniya lafiya sannan idan sun je lahira wutan Jahannama za su shiga. A nan jikin Hannatu ya ƙara yin sanyi don sosai ƙaninta yake mata wa'azi wanda yake ratsa jiki da ɓargonta, har zuciyarta ta karye tare da komawa yin nadama da dana sani akan abubuwan data aika munana a baya. Sun daɗe suna mata wa'azi daga bisani cikin sanyin murya mai nuni da tsantsan nadama Hannatu ta ce

    "Innayi daga yau in shaa Allahu na daina zuwa wurin ko wani irin malami ne,na tuba Allah ka yafemin don ishara ce babba Allah ya saukar min akan ɗana wanda na ƙwallafawa rai kuma yafi soyuwa a gareni, in shaa Allah bani ba zuwa wurin wani malamin tsubbu ko boka, to yanzu Muntari shikenan ɗana ya koma ɗan daudu kenan"

Ƙaninta Muntari ya saki murmushi sannan ya ce

"Akwai abinda ya gagari Allah ne Yaya? babu shi kuma ba a yi shi ba sannan ba za a taɓa yinsa ba, Allah mabuwayi kuma gagara misali shi kaɗai keda Iko akan komai kuma shi ke sama da komai, in shaa Allah Jamilu zai koma yadda yake, akwai malamina wanda nake ɗaukar karatu wurinsa, yana da sani sosai akan ɓangaren daya shafi sihiri da aljanu, zuwa anjima dana fita, gidansa zan nufa  na yi masa bayani akan matsalar da ta samu Jamilu nasan in shaa Allah za a dace, ke dai kawai ki riƙe Allah za ki ga canji sosai a rayuwarki da yardar mai sama"

"In shaa Allahu na zan canja daga yau babu ni babu zalintar wasu sannan abubuwan dana aikata a baya Allah ya yafe min su" cewar Hannatu tana matsar ƙwalla, don yanzu da gaske take ta shiryu. 

Ƙannanta mata ma sun yi mata wa'azi iya saninsu sannan suka canja akalar hirar zuwa hirar yaushe gamo saboda Hannatu ta daɗe rabonta da Giwa sai dai su gaisa a waya. Wannan kenan... ✍️

       🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Gida Dubu,Gubi Housing Estate,Bauchi State. Nijeriya*

A ɓangaren Hujayrah bayan Razina ta fito daga wanka sai ta ce Hujayrah ta shiga ta yi wanka, miƙewa ta yi ta shiga bayin duk da ta yi wanka a sashen ma'aikata hakan bai hanata yin wankan ba saboda ganin ƙwaƙwaf, bayan ta shiga bayin sai ta tuɓe kayan ta, ta rasa ina za ta kunna ruwan ya zo, sai kalle-kalle take tana taɓe-taɓe a garin taɓe-taɓan ta je ta danno ɓangaren da yake bada ruwa mai sanyin  ai nan da nan ta ƙwalla ƙara tana kulle fanfon. Jin ƙaran Hujayrah Razina ta matso kusa da bayin ta ce

"Sister meya sameki na ji kina ihu" 

"Wani wurin na danna sai ruwa mai shegen sanyi ya zubomin a jiki" tana maganar ƙara rungume jikinta ta da kyau saboda azababban sanyin da take ji

"maida kayan ki na shigo sai na koya miki yadda ake kunnawa" 

Da sauri da maida kayan sai ta ce ma Razina ta maida kayan. Handle ɗin Razina ta murɗa ta shigo bayin zuwa inda water bath ɗin yake, Sai Hujayrah ta je wurin ita ma, nuna mata yadda ake kunna ruwan sanyi tana zafi da kuma yadda ake controlling kowanne, sai ta nuna mata yadda ake flushing da dai wasu abubuwan da ya kamata ta sani sannan ta baro bayin. Kamar yadda Razina ta koya mata haka ta kunna ta yi wankata tare da ɗaura ɗaya daga cikin towel ɗin Razina ta fito. (Su Hujayrah manja, wato an samu wuri har da ɗaura towel ɗin Auta Razina🤭😂) 

Razina ta nuna mata wani stool kusa da mirror, babu musu ta zauna, kayan shafa Razina ta matso mata dasu tare da nuna mata yadda ake amfani da kowanne, ɗaya bayan ɗaya Hujayrah take amfani dasu har ta kammala.wata haɗadɗiyar Jallabiya sabuwa Razina ta ɗaukoma Hujayrah da yake kusan tsawansu ɗaya da Hujayrah sai ɗan jiki da cikar halitta da Hujayrah tafi Razina amma tsawansu ɗaya ne, miƙa mata ta yi sannan ta fito daga ɗakin. Saka Jallabiyar Hujayrah ta yi, sosai ta yi mata cif! A jiki kamar don ita aka yi Jallabiyar,mai ruwan madara ce tasha adon stones gaba da baya.Ta ɗan kama Hujayrah kaɗan don Hujayrah ba dai hips ba boobs ba. Bayan ta kammala shiryawa sai ta fito daga ɗakin hannunta riƙe gyalen Jallabiyar kanta ɗaure da ribbon ƙarami, gashin baƙi siɗik! Ya saukar mata har baya, a ɓangaren gashi mamminta ta ɗauko har ma ta so finta tsawon gashi da cika. 

Food warmers ne da jug a gaban Razina da plate tana jiran Hujayrah ta fito.Da Razina ta yi arba da Hujayrah bata san lokacin da ta furta 

"Woooow Hujayrah Kinga yadda abayar nan ta yi miki kyau kuwa, kamar wata African queen" 

Murmushi Hujayrah ta yi sannan ta samu wuri ta zauna. 

"Ga abinci mu ci sai mu tafi part ɗin Ammie ta kira driver ya kaimu saloon da shopping" 

Tana maganar tana buɗe food warmers ɗin, jollof ɗin taliya da kifi ne wanda tasha kayan lambu ƙamshi sai tashi yake, a plate ɗaya Razina da saka musu abinci. A ƙoshe Hujayrah take amma sai da ta  lodama cikinta  abincin. A natse suke cin abincin har suka gama, ganin yadda Razina take jin abinci a natse shi yasa Hujayrah natsuwa suka ci abincin. Wata mai aiki ce ta yi sallama cikin ɗakin,sai Razina ta ce ta kwashe kayan zuwa kitchen, with full respect matar ta kwashe kayan ta fita dasu. A tare suka miƙe zuwa part ɗin Ammie, da sallama suka shiga ɗakin tana waya yasa bata amsa musu ba. Da murmushi a fuskar Hajiya momma take amsa wayan da alamu tana jin daɗin wayan da take. Da sauri Razina ta je kusa da Hajiya momma tana faɗin

"Ammie Ya Arqam ne?" 

Gyaɗa mata kai Hajiya momma ta yi, sai Razina ta saki murmushi tana cewa

"Ammie nima zan gaisa dashi har da Hujayrah ma" 

"Ga  uwar rigima da Hujayrah za ku gaisa" tana maganar tana miƙama Razina wayar, cike da zumuɗi Razina ta amsa wayan ta kara a kunnanta da faɗin

"Ya Arqam ina wuni" 

A can Arqam ya amsa mata cikin deep cool voice ɗinsa Wanda Kamar anyi masa dole ya ce

"Little sis how are you, kina nan da rashin jin naki ko kin daina, ummm" 

"A'a Ya Arqam ai na tuba yanzu, kuma ina faɗama Ya Arqam na yi New sister mai suna Hujayrah, she is damm beautiful ga ta da green eye masu kyau wallahi" 

Jin sunan nata yasa gabanshi faɗuwa ya rasa dalili, ko ɗazu da Ammie ta yi masa maganar yarinya gabansa sai da ya faɗi, wace ce ita? Mai hakan yake nufi da just her Name ke sakashi faɗuwar gaba? Mai yasa idan an ambata masa sunanta zuciyarsa ke bugawa? Why!??? . Cikin muryar nan tasa kamar wanda aka  yi masa dole ya ce 

"To talkative na tambayeki ne, uwar zance ko ba yanzu kika ce kin tuba bane Eh" 

Kamar yana kallonta ta yi saurin girgiza masa kai tana cewa

"I'm sorry Ya Arqam, ga Hujayrah itama ta ce za ku gaisa" 

"Ok" 

A natse Hujayrah ta amsa wayan ta kara a kunnenta, cikin zazzaƙar muryar ta ce 

"Assalamu Alaikum Ya Raqam" 

Dariya Hajiya momma da Razina suka yi saboda yadda ta kira sunan wai *Ya Raqam* , gyara mata sunan Razina ta yi da cewa

"Hujayrah ba Ya Raqam ake cewa ba Ya Arqam ake cewa" 

"Au yi haƙuri, sunan ne akwai wuyar faɗi" 

Arqam bai ma ankara da canja mishi sunan da ta yi ba, don muryarta ta daɗe da tafiya da ruhinsa, salon da ta yi amfani dashi wurin yi masa sallama ya saukar masa da kasala har ma ya kasa amsa mata sallamar. Jin shirun ya yi yawa sai kawai ta miƙama Razina wayan tana faɗin 

"Kamar ya katse kiran fa Razina" 

"Bara na duba" 

Amsar wayan Razina ta yi kafin ta duba sai ya katse kiran, daman yana jin abinda take faɗa kawai bakinsa ya yi masa nauyi ne yasa ya kasa amsa mata. Bayan Razina ta duba wayan sai ta ce

"Laah ai ya katse kiran ƙila ma bai ji na ce za ku gaisa ba, amma Ammie yaushe zai dawo ne ya fa daɗe rabonsa da Nijeriya" 

"Nan da kwana biyar in shaa Allah" 

"Allah ya kaimu rai da lafiya" cewar Razina tana gyara rolling gyalen abayarta

"Ameen ya Rahman kun shirya kenan" 

"Eh Ammie" 

Miƙa ma Razina Atm card da wata jaka Hajiya momma ta yi tare da cewa

"Ga Atm card Sai ku fara zuwa saloon ayi mata gyaran Gashi da jiki daga can ku wuce boutique ki zaɓo mata kayan sawa sannan wannan jakar ki biya ki ba Hajiyan Sama" 

Amsar Atm card ɗin Razina tayi, sai Hujayrah ta shiga yi mata godiya har suka bar ɗakin. Razina sai da ta koma ɗaki ta dauko handbag ɗinta ta ɓakin glass wanda  ta ba Hujayrah tasa sannan suka fito zuwa harabar gidan, kowannensu Sanye yake da Jallabiya, sun yi rolling ɗan gyalensu, flat shoe ne a ƙafarsu suna tafiya suna dariya, su Hujayrah ansha baƙin glass mai kyau sai ya ƙara fito da kyawunta sosai, ma'aikatan gidan sai kallonsu suke suna gulmarsu. Part ɗin Hajiyan Sama suka nufa da sallama a bisa labɓantu suka shiga ciki. Babu kowa a falon sai Razina ta ce su wuce sama tasan Hajiya Sama tafi zama a can. A natse suka tattaka matattakalan benan zuwa falon Hajiyan Sama idan  Hujayrah da Baba Uwani suka zo ɗazun. Sallama suka yi sai suka jira aka amsa musu tare da bada izinin shigowa, Razina ce a gaba Hujayrah na biye ta ita. Hujayrah data haɗa ido da Hajiyan Sama da matar da suke tare sai ƙirjin ya buga da matuƙar ƙarfi har sai da ta faɗe ƙirjinta, lokaci guɗa ta ji bata son matar daman tun lokacin da suka zo wurin Hajiyan Sama taji bata son Hajiyan Sama,ga wannan matar ita ma zuciyarta ta tsaneta to mai hakan yake nufi. Cike da girmamawa Razina ta gaishesu ita ma Hujayrah ta gaishesu da girmamawa amma maimakon su amsa mata, buɗar bakin Hajiyan Sama ta ce

"Wa nake gani haka Razina a bayanki, wannan matsiyaciyar yarinyar dana kora daga wurina shi ne kuka ɗauka har da bata kayanki ta saka?!" 

"Sister ɗina ce ai Dad ya yarda ta zama ƴar gida, Sannan a ɗakina ma zata dinga kwana, Hajiyan Sama Hujayrah na da kirki sosai wallahi ga na..." 

Bata ƙarasa abinda ta yi niyyar faɗa ba Hajiyan sama ta daka mata wata uwar tsawa tana cewa

"Sister ɗin Ubanki! Wannan ƴar matsiyaciyar ce ƴar uwarki, naga Zahriyya ta kuke sa'anin juna bakya sake mata fuska, ko maganar kirki bakwa yi da ita balle Fauziyya data girmeki, dede da rana ɗaya ban taɓa jin kince Zahriyya ta zo ku kwana ɗakinki ba sai wannan mai idon mujiyar ɓaƙa siɗiƙ kamar amalan ƴarbawa kike sonta har da iya cewa ta ɗinta kwana ɗakinki, ehhh! "

Razina da ta tsani faɗa  balle tsawa da hargagi sai kawai ta ajiye jakan ta jawo Hujayrah suka fito daga ɗakin don idan ta ci gaba da sauraron Hajiyan Sama matsala za a samu domin gasa mata magana za ta yi sai dai idan Ya Arqam ya dawo da mata duka amma sai ta mata rashin kunya, ita yaran da take riƙon iyayin tsiya sai cinyewa Abbanta kuɗin suke wai suna karatu. Zuciyar Razina na tafarfasa suka bar part ɗin, ita Hujayrah bata ce komai ba sai ma kafesu da kaifafan idanunta da ta yi tana ƙara yin nazari akan su, dole tasa ido sosai akansu don da alama mugayan mutane ne masu cutar da al'umma. Har suka zo harabar gidan inda ake ajiye motoci zuciyoyinsu babu daɗi, driver daman tuni Hajiya momma ta yi kirasa tare da sanar masa da fitansu Razina, shiyasa ya fito ta duba motar da za su fita da ita, ya tsaya a gefe yana jiran isowansu.Suna isowa suka Shiga motar sai ya tada motar suka bar wajan. 

Razina basu suka dawo gidan ba sai kusan ana gab kiran sallar magrib, driver ne ya tayasu ɗauko kayan zuwa part ɗinsu. Idan kuka ga Hujayrah Hmmmm za su ce anya ita ce domin fatar jikinta babu abinda take illa glowing, sosai aka gyara mata jiki,gashinta ma yasha gyara sai tashin ƙamshin mayukan yake. Ta fito kamar wata mai fita gasar kyau,Razina bata yi ƙarya da ta faɗi African Queen ba domin kana kallonta za ka ce African queen ce ko kuma queen of beauty, Don Hujayrah na tattare da sihirtaccan kyau wanda sai kana tare da ita za ka gasgata hakan.Suna shiga part ɗinsu basu tsaya ko'ina ba sai a ɓangaren Hajiya momma har falonta na sama suka haura,basu sameta a falon ba sai suka ajiye kayan sannan suka nufi ɗakinsu su yi sallah, bayan kowannensu ya yi sallah sai suka kuma falonta, a lokacin tana zaune tana latsa waya. Gaishe suka yi sannan suka nuna mata siyayyar da suka yi sannan Razina bata faɗa ma Ammie abinda Hajiyan Sama ta yi musu ba. Sosai ta yaba da kayan da Razina ta zaɓoma Hujayrah. Sai suka wuce ɗakinsu da kayan.

A can part ɗin Hajiyan sama Koda su Hujayrah suka bar falon sai baƙuwa  ta dubi Hajiyan Sama ta ce

"Wai Hajiya Izzatu har yanzu lokaci bai yi  da za ki cimma ƙudirinki akan kishiyar nan taki da yaranta bane? Kin ga fa ƙara tsufa muke  ke kuma ba haihuwa kika yi ba balle kiyi tunanin samun gado" 

Wani ƙasaitaccan murmushi Hajiyan Sama ta saki tana ƙara gyara zama ta ce

"Hajiya Zinatu kenan daɗina dake gaggawa, bari ki ji lokacin cin moriyar ganga ya yi ya zo ai, lokacin da zan yi wandaƙa da dukiya ya yi,ba wai nabar Mubina  bane ta haihu  sai don inci dukiyarta wanda mahaifinta yabar mata gado, idan da naso wallahi wallahi wallahi da bata isa ta haihu da Mijina Imrana ba, amma kwaɗayin dukiyarta nake shiyasa nabarta ta haihu da Imrana"

Ajiye waya Hajiya Zinatu ta yi tare da gyara zamanta tana duban Hajiyan Sama sannan ta ce

"Ta ya za ki ci   ɗumbin dukiyar Hajiya Mubina wanda mahaifinta ya bar mata?" 

Wani ƙasaitaccan murmushi Hajiyan Sama ta saki har ana ganin haƙoran makkanta guda biyu   ta ce

" Karki manta da Izzatu ce mai suffar muminai, jira nake ɗanta Arqam ya dawo ƙasar nan na fara shiri na akansa"

Cike da zaƙuwa Hajiya Zinatu ta ce 

"Akan ɗanta kenan za ki fara shiri kenan" 

"Eh ai dalilin riƙon Fauziyya da nake ai saboda ɗanta ne Arqam, Ina jira da ya dawo ƙasar nan sai na ɓullo da maganar haɗin gida, Ina so Arqam ya auri Fauziyya sai Khalil ya auri ƙanwarsa Nazima wacca kishiyarki  Hajiya Nafisa take riƙon, kinga anyi tuwona mai na, da an yi auran saina ta fi zuwa ga plan ɗina na biyu, Kinsan duka dukiyar Hajiya Mubina tana hannun Arqam har ta wasu kamfanonin Alhaji duk Aqram ke juyasu, Allah ya bashi baiwa da fasahar iya sarrafa naira ɗaya ta koma biyar"

Jingina Kai Hajiya Zinatu ta yi sannan ta ce

"Dole na jinjina miki uwar ɗakina, keta dabance wallahi, a gaskiya kin iya hangen nesa w, ki ce kin ɗaɗe da wannan shirin" 

Dariya Hajiyan Sama ta yi sannan ta ce

"Sosai ma Kuwa, ina bin komai a sannu ne, Ina rataya rigar da ba nawa ba, na ɗaɗe da lulluɓe kai na da fatar akuya , a zahiri kallon mutuniyar arziƙi mai son jama'a sukemin a baɗini hhhhhh! Kura ce ni mai lulluɓe da fatan akuya,Kin san duka yaran da na riƙe tun daga kan Khalil, Fauziyya da Zahriyya na horar dasu  ne akan tsarina, bana shakku ko kwanto akansu, duk abinda na sakasu shi za su min ba tare da jayayya ba, kinga kuwa plans ɗina zasu tafi yadda ya kamata"

Ci gaba da hirarsu suka yi wanda kusan akan yadda Hajiya momma ne, sun ɗaɗe suna hira sai kusan yamma Hajiya Zinatu tabar gidan. 

A washe gari Lesson teacher wanda yake koyama Razina karatu ya fara koya ma Hujayrah karatu tun daga farko, babu laifi Hujayrah nada saurin ɗaukar karatu.Ita kuma Razina ta wuce makaranta idan ta dawo za su je gidan Hajiya Nafisat ƙanwar Abbansu wacca take riƙon yayar Razina mai suna Nazima. Wannan kenan... ✍️

        🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*New G.R.A. Bauchi state Nijeriya*

Wani tanƙameman falo ne mai kyau da tsari,kujerun alfarma a zagaye  a tsakiyar falo masu kalar royal blue da ratsin gold, a tsakiyan falo center table ne an ɗora box na flowers masu kyau da ƙamshi, sai tanƙameman plasma TV a Kunne. Wata hamshaƙiyar mata ce a zaune a saman three sitter Sai wata kyakkyawar budurwa fara tar! Ta yi pillow da cinyar matar, kallo ɗaya za ka yi mata ka tabbatar da ƴar hutu ce, jiki duk madara in ji celebrities kuma ajin farko. Matar sanye take da atamfa super Holland Mai tsaba, an zuba mata ɗinki ga stones sai walwali suke, kunnanta, wuyanta da zubbanta duk zinari ne, tasha ɗauri irin na ministan man fetur Ngozi Okonjiwela, irin manyan matan nan ne da suka amsa sunansu masu ji da kuɗin da Izzar mulki. Budurwar yarinyar sanye take da riga pink da jeans trouser three-quarter a iya gwiwa ya tsaya mata,kayan sun kamata sosai ga kitson attach akanta anyi shi ƙananu ta ɗaure da pink ribbon. Cike da shagwaɓa ta ce 

"Mom  Ya Arqam is about coming back  finally to Nigeria Kuma kin san daya dawo za a fara mishi maganar aure,tun kan su aura mishi wata gwara ki yi wani abu mamarsa ta yadda ya aureni" 

Murmushi mahaifiyar ta yi tana shafa gashin dokin da ta ɗaure ta ce

"Why are so in vein Tahseen, Ai babu wacca ta isa ta auri Arqam bayan ke, domin Arqam naki ne ke kaɗai" 

"Mom baya sona fa, mamarsa itama she hates me, Uncle Imran ka ɗai ne ya yarda da auran" 

"Hmmmm bar shegiya ba ita tana ji da ubanta ya bar mata dukiya ba shiyasa take mana iskanci ,idan kuɗin ne take tunƙaho  naga ubanki Senata ne sannan muna saka ran wata shekaran zai fito takarar gwamna kuma ya ci kinga kuwa babu abinda za ta nuna mana indai maganar Naira ce, mu ma a cikinta muka taso kuma a cikinta muke luntsum! , Hmmmm! idan tasan wata ai bata san wata ba, ai tunda ɗan uwana ya amince da maganar auran ai bata isa ta hana ba, bara Arqam ɗin ya dawo sai ayi wacca za a yi" 

Tashi daga kwancen Tahseen ta yi tana duban Mominta, ta yi wani kicin-kicin ta fuska kamar mai shirin kuka ta ce

"Mom na rantse da Allah idan ban auri Ya Arqam ba mutuwa zan yi, wallahi shi nake so, shi ne rayuwata, kullum da kaunarsa nake kwana kuma da ita nake tashi amma shi baya sona kullum cikin kiran wayarsa nake  baya picking sai wulaƙantani yake,kiga  ko a club yadda maza suke rushing ɗina suna sona amma naƙi kulasu saboda ba basu da suffar kalan namijin da nakeso,Ya Arqam kaɗai ne keda irin suffar, please Mom do something"

Sosai Tahseen taba mahaifiyarta tausayi don tasan tun tasowan Tahseen take mutuwar son Arqam yaron ya'yan ta Alhaji Imran, amma shi ɗan shegiya yana bin zugar mahaifiyarsa Hajiya momma shi yasa baya sonta, bazata bari tilon ƴarta ta halaka ba saboda soyayya, dole ta yi wani wannan dole ne. Kwanto ta Tahseen mom tayi a jikin tare da shafa mata baya cikin sigar lallashi ta fara magana

"It's ok Tahseen kisa a ranki Arqam naki ne ke kaɗai, zan yi maganin Hajiya momma da kanta za ta tirsasa shi ya aure ki ko baya so, cikin ruwan sanyi zan yi maganin ta bara na kira Hajiya Lubna... ✍️







*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***