44
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 4️⃣4️⃣
Abba ne ya shigo parlourn, dawowarsa kenan ba wani jimawa ya ma tsaya yin magana da wasu ne kafin ya shigo
Gaida shi suka yi, tayi saurin tashi ta koma sama,dan murmushi Abba yayi irin nasu na dattawa
Anty ma ba jimawa ta sauko taga Abba
"Ah ah Abba yaushe kadawo"
"Yanzun nan shigowa ta kenan"
"Sannu da dawowa"
Ta faɗa tana amsar jakar hannun shi
Shima ya Faruq din gaishe ta yayi, ta amsa tana tambayar sa yasu Ammi
"Ashe ma tare kuke kai ka kawo ta"
"Eh daman nace ne bara inzo in gaida ku"
"Aikam ka kyauta"
"Ke ina abun da kika ce kin manta"fadin Jalila
"Ke dalla gashinan ta ɗauko a binda ta manta ɗin"
"A ina ɗin"
"Ke daɗi na dake wata rana ba'a zuwa dake, gashi can a parlour, ko ke kinga alamar ta dawo da wani abu bayan shi"
Faɗin Nabila, ta ƙara cewa
"Ai shekaran jiya kawai hankali ta raina mana tana cewa bata son shi dan munafurci"
Tana maganar tana hararar ta tana ɗan dariya
Ido ta zaro jin sharrin da Nabila ke yi mata, magana tayi niyar yi sai kawai tamata shiru dan ba mata da abinda zata ce mata, dan tasan tsokana take nimanta dashi
"To ya san ranki,idan ma shine dai ina ruwanki, gulma ko me"
Ta faɗa tana barin ɗakin dan tasan tsiyar Nabila
"Ehhhhhh sister, seda keee!!!!!"faɗin Jalila tana jinjina wa Anisa hannu tana dariya jin abinda tace da Nabila
Itama Fareedah ɗan murmushi tayi ta na janyo wayar ta dan ba so take ta huce ba yanzu sai taji sanda akace mata Anisa ta amince da auren yayanta
So so ne amman san kai yafi, Dan Allah yasan taji daɗin wannan haɗin, amma Anisa nason mata fuckup, tasan duk da ya Umar baya da sakin fuska but he's a very nice guy zata ji daɗin zama dashi, amman shegen tsoro da taurin kai irin nata ya hana ta ganewa
Hanyar stairs ɗin ya ƙara kalla ba ita ba alamun me kama da ita, aran shi yana tunanin sai yaushe kuma zai sake ganin ta oho, sallama yama su Abba ya tashi ya tafi, da murmushi Anty tabi bayan shi dashi tana kallon hanyar stairs ɗin itama, ta jinjina kai
Ɗakin su Majeed ta shiga abin ta suka yi ta hira daga karshe ma sukace zasu koya mata video games dinsu na sojoji, sai after magriba ta fito shima jin ana kiran sallah ne, saida ta saka su suka yi alwala a gabanta suka tada sallah sannan ta bar ɗakin ta koma nasu
"Kin dawo kenan" fadin Jalila da fitowar ta kenan daga toilet
"Ai da kin kwana dasu Majeed ɗin kawai"
Faɗin Nabila tana shiga toilet
"Kudai Allah ya yaye muku da neman tsokana ta wallahi, barin ma ke Nabila, sisterr wai ni me na miki haka ne tun nazo ko kula ni bakiyi ba"
Tayi maganar tana zuwa inda Fareedah take kan kujerar ɗakin ta zauna kusa da ita ta rungume ta
"Ni nace kin mun wani abune??"tayi tambayar tana ƙoƙarin ture ta
"Baki faɗa da baki ba amman kin nuna min a aikace, sorry kinji sister ta, kiyafe wa wannan ƴaruwar taki"
Ta faɗa tana kara rike ta
"Dalla ni ki sakeni sai wani matse ni kike"
"Sone ya janyo haka"
"To naji ƙyale ni"
"Sai kin dena jin haushi na"
"To ki maida ni ciki kawai"
"Ai idan akwai abinda yafi wannan ma zanyi indai zamu shirya"
"Ya ilahi sakeni wai, pickles ki rabani da wannan ƴar"
"A'a nima ina bayan ta kiyi mata abinda take so"
"To shikenan Anisa ki kasheni da wannan maƙurenin da kikayi"
"Haba dai yaya zan kashe ƴaruwa abar so na"
Ashraf ne ya shigo ɗakin yana kiran
"Adda Anisa Abba yace wai ki zo ki same shi a parlourn shi"
Ya juya da gudu ya koma dan cigaba da wasan shi
Wani irin bugu zuciyar ta tayi da bata san sanda hannayen ta suka saki reedah ba, zufa taji yana yanko mata tun kafin ma taje dan tasan bazai wuce amsar shi yake son ji ba
Jiki ba kwari ta tashi ta nufi parlourn tana adduo'i a ranta dan ji tayi ma tun kafin ta ƙarasa wani kuka na taho mata, ji take yanzu kuma kamar tace bata amince ba
Wani numfashi ta sauke ta murɗa handle ɗin ta shiga,
Zaune yake kan kujera sanye da medicated glass yana ɗan duban laptop dinshi
Ɗagowa yayi ya kalle ta harta zauna ƙasa nesa da ƙafafuwansa kaɗan tace
"Abba barka da yini"
"Yauwa ƴa ta yakuke"
Da lafiya ta amsa jikinta na ɗan rawa amma da ta tuna dan Ammin ta zata yi sai taji fargabar da take ya ragu sosai
"Amsar tambayar da na miki nake son ki bani tunda lokacin da muka yi da ke ya cika"
Numfashi ta sauke tana ƙara sunkuyar da Kai bata ce komai ba, Abba yace
"Baki amince bane"
Kai ta girgiza masa da sauri alamar a'a
"To kin amince kenan"
Da kyar kamar an shaƙeta ɓera a kwana tace "eh"
"To Allah yayi albarka, daman ba zamu yanke hukunci ba har sai munji daga bakin kowanne a cikin ku to alhamdulillah, Allah ya muku albarka gaba ɗayan ku"
"Ameen" ta faɗi a hankali
"Tashi kije kinji ƴaralbarka"
Tashi tayi ta fito jiki a sanyaye kamar an watsa mata ruwan ƙanƙara, wani zuciyar ne ya ke cemata ta juya ta koma ta ce ma Abba bata amince ba, ta fasa,
Follow and like my account on arewapen danAllah ba dan halina ba se dan kawo muku sabbin Updates🥰🙏🙏
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***