LOKACI CHAPTER 3
by @fulani32
***
⏳🕛 LOKACI 🕛⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)
YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA)
Under Team Yota's Amazing Pens
SADAUKARWA GARE KI KARIMAT BASHEER (An Karime, Karime na)
⏳🕛 LOKACI 🕛⏳
PAGE 3️⃣
Cikin barci ta ji ana kiran sunanta. A hankali ta miƙe da addu'a a bakinta. Salma ta gani a kanta tana kiran sunanta. Kallon lafiya ta yi mata.
"Aunty, ki zo inji Baffa."
Duk da gabanta ya faɗi, hakan bai hana ta yin murmushi ba, ganin yadda Salma ta yi wani iri. Tashi tayi ta zura hijabi ta fice. Da sallama ta shiga amma babu wanda ya amsa mata. Bata damu ba, ta gaishe su. Shima ba don ta saka rai za su amsa mata ba. Waje ta samu ta zauna kanta a ƙasa, ba tare da ta kalle su ba. A zuciyarta kuma addu'a take akan Allah yasa su wanye lafiya.
Wani irin kallo mahaifin nata yake mata, wanda duk da ba kallonsa take ba amma tana jin kallon a cikin jikinta. Ƙara haɗe jikinta waje ɗaya tayi, zuciyarta na bugawa a hankali.
"Ɗazu kinyi baƙo?" Ya jefa mata tambayar, har lokacin idonsa a kanta.
Kanta ta gyaɗa masa ba tare da ta ce komai ba.
"Masha Allah, kamar yadda mahaifiyar ki ta bani shawara na kai sanarwa masallaci akan idan akwai wanda yake son ki ya yi magana zamu bashi auren ki sadaka, toh na yi na'am da wannan shawarar tata, dan shawara ce mai kyau. Sai kuma a jiya kafin na ƙarasa masallaci na haɗu da Malam Bala. Bayan mun gaisa ya ke tambayar iyali. Anan nake faɗa masa duk suna gidan su, saura ke. Yanzu haka ma masallaci zan kai sanarwa akan idan da mai sonki zan bashi auren ki sadaka. Sai kuma ya ce shi yana so, shiyasa ya zo wajen ki ɗazu. Kuma ni dai na bashi, dan haka duk wani shiri da zaki yi, ki yi shi. Ba za ki ƙara sati biyu a cikin gidan nan ba, za ki iya tafiya."
"Malam, menene amfanin yi mata bayani? Kawai umarni za a bata. Aure ne babu fashi. Yarinya duk ta tsofe a cikin gida. Dallah, tashi ki bamu waje kafin na make ki."
Kamar wadda take akan ƙaya, haka ta miƙe zumbur ta fice tana haɗe hanya, dan bata ganin gabanta. Jefa ƙafarta kawai take duk inda ta samu. Jin an riƙe ta ne ya sa ta kalli hannun da ke riƙe da ita.
Daga yanayin hannun ta fahimci Salma ce. Duk yadda ta so ta daure kada rauninta ya bayyana, sai da ya nuna, dan sosai jikinta yake rawa. Ta kasa yarda mahaifiyar da ta haife ta ce take bada shawarar a bayar da aurenta sadaka. Auren dole za a mata. Idan ma auren dolen ne da sauƙi a wajenta da irin auren da suke neman su yi mata. Auren rashin gata. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
Sosai jikinta yake rawa, ta kasa yarda da abubuwan da suke faruwa da ita. Ganin tana neman fita hayyacinta ne ya sa Salma ta rungume ta da sauri. Hannayenta ta saka ta zagaye ta da ƙarfi tana sauke ajiyar zuciya. Kuka Salma take na tausayin abin da ƴar uwartata take fuskanta a wajen iyayensu. Wallahi ita kanta, ba don kamannin da ke tsakaninsu da Aunty Zahra ba, sai ta ce ba su suka haife ta ba. Toh amman gaba ɗayanta da Mahmah da Baffa suke kama, dan haka babu wata tantama akan cewa su ne iyayenta.
"Ki yi haƙuri Aunty Zahra, ki yi haƙuri dan Allah ki ci gaba da addu'a Allah ya kawo miki mafita cikin gaggawa. Amman insha Allahu auren nan ba zai taɓa yiwuwa ba, ni ina ji a jiki na mijin ki yana nan ya kusa bayyana. Za ki aure Aunty Zahra, za ki auren da babu wanda ya yi irin shi a cikin ƴaƴan Mahmah. Dan Allah ki kwantar da hankalin ki mu ci gaba da addu'a."
Duk da yadda ta yi maganar da sigar rarrashi, hakan bai sa Zahra ta ji komai ba, sai ma wani nauyi daya ƙara danne ƙirjinta. Bakinta ta buɗe da niyyar ta bata amsa, sai dai kafin ta ce komai muryar Mahmah ta katse ta.
"Sannu munafuka, na ce sannu munafuka! Da kika rungume ta kina kuka da faɗa mata magana hana ta aure za ki yi? Toh wallahi ba ki isa ba. Salma ki fita idona na rufe. Idan ba so ki ke na saka ƙafar wando ɗaya da ke ba." Ci gaba da faɗan ta yi, ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba.
Da sauri Zahrah ta raba jikinta da na Salmah ta nufi ƙofar ɗakinta, dan ba za ta iya ci gaba da sauraron kalaman Mahmah ba.
"Amman Mahmah, dan Allah ba kya jin tsoron mugayen kalaman da kike wa Aunty Zahra su kama ta?" Cike da takaici Salma ta jefa mata tambayar da take yawan yawo a cikin zuciyarta.
"Salmah!!!" Ta kira sunanta cike da tsawa. Bata iya tsayawa jin me za ta ce mata ba, ta shige ɗaki a guje tana gunguni.
Zaman dirshan tayi a ƙasan carpet, ta yi tagumi da hannu biyu, dan a halin da zuciyarta take ciki kukan ma ya ɗauke mata. Sosai take son ta gano menene laifinta akan rashin aure. Shin ita ce ta hana kanta auren ko kuma ita ce ta nemi zaman gida? Ita ma tana buri da fatan ace yau ta yi aure, gata a cikin gidanta na aure da ƴaƴanta. Toh menene laifinta? Mai yasa ba za a taya ta da addu'a ba sai a dinga jifan ta da mugayen kalamai? Meyasa ba za su gane aure LOKACI ne da shi ba? Jin kanta ya kulle ne ya sa gaba ɗaya ta rasa wane irin tunani za ta yi.
Gajiya ta yi da zaman, ta tashi ta shiga toilet ta yi alwala. Inda darduma take ta je ta tayar da sallah. Ta jima tana sallar, a sujjadar ƙarshe ta daɗe tana kaiwa Allah kukanta cikin hawaye. Bayan ta idar ta ɗakko Qur'ani ta fara karantawa. Tana zaune a wajen har aka yi sallar asuba. Tashi ta yi ta sake alwala, sallah ta yi raka'a biyu sannan ta ɗora da sallar asuba. Tana cikin azkar barci ya ɗauke ta a wajen. Ƙarfe 7 daidai alarm ya buga a wayarta, hakan ya sa ta tashi duk da irin barcin da ke cikin idanuwanta.
Ɗakinta ta fara gyarawa, sannan ta fito waje, kamar yadda aikin gidan ya dawo kanta gaba ɗaya. Cikin rashin kuzari take aikin, duk da daman ita ba zafin nama gare ta. Tana gamawa ta shiga kitchen ta haɗa musu breakfast. Zuwa 9:30 ta gama komai, ɗaki ta koma ta shiga wanka. Bayan ta fito ta zauna ta shirya cikin doguwar riga maroon, sosai rigar ta haska ta. Tana cikin rolling Salma ta shigo da sallama a bakinta.
"Wow big aunty, kin ga yadda kika yi kyau!" Ta faɗa tana washe baki, dan dagaske ita kanta ta san yayarta me kyau ce.
Murmushi ta yi mata tare da miƙa mata hannu suka gaisa, ba tare da ta amsa waccan maganarta ba. "Allah ya sa yau idan kin je wajen aiki ki dawo min da yaya." Take kuwa murmushin fuskarta ya ɗauke, hannunta ta zare ta ci gaba da abinda take yi. Ganin haka ne ya sa jikinta ya yi. "Ki yi haƙuri Aunty Zahra dan Allah." Wani murmushin ta ƙaƙalo ta yi mata tare da ce wa "Salma baby, Salma autar Mahmah ce ta." Jin abinda ta ce ne ya saka Salma dariya.
Agogon wayarta ta duba, ganin tana neman ta makara ne ya sa ta ƙarasa shirinta ta rataya jaka. Tare suka fito da Salma za ta mata rakiya. Suna fitowa Mahmah na fitowa daga ɗaki ita ma. Har ƙasa ta tsugunna ta gaishe ta. A madadin ta amsa mata sai tambayar da ta jefa mata, "Ina za ki je?" Ta tambaye ta tana jifanta da wani irin kallo.
"Wajen aiki ko kuma wajen yawo?" Shiru ta yi ba ta ce komai ba, kanta a ƙasa. "Ki koma babu inda za ki je, gidan Sadiya za ki, ki yi mata girki da gyaran gida, mijinta ya yi tafiya zai dawo."
"Mahmah aiki za ni amman..." Bata barta ta ƙarasa ba ta katse ta.
"Ina magana kina faɗa min aiki za ki je? Yaushe na fara haka da ke? Toh na ce ba za ki je aiki ba, za ki je ki yi mata. Idan da kin yi aure zan aika ki gidan ƙanwar ki ki yi mata aikin ne? Kar ki sa na rantse, wallahi daga nan har zuwa auren ki da Malam Bala kullum sai kin je kin musu aikin gida. Idan kina musu kuma bismillah, ki ki ƙara magana na ji."
Duk da yanda zuciyar ta take bugawa, hakan bai hana ta roƙon alfarma a wajen ta ba. "Mahmah zani, amman dan Allah girman Allah kiyi min Alfarmar na fara zuwa aikin. Idan ya so duk inda 1 take zan tafi gidan nata nayi mata aikin dan Allah Mahmah...."
Fulani
***