LOKACIFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

LOKACI

  • 1views
  • 14chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · LOKACI CHAPTER 1

*** LOKACI 🕛⌛BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA)*Under Team Yota's Amazing Pen's*NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN KACOKAN ƊIN SHI GARE KI KARYMAT BASHEER (AN KARIME KARIME NA) ALKHAIRAN ALLAH YA KAI MIKI HAR GADON BACCIN KI.Wannan littafin ƙirƙirarren labari ne. Duk wasu abubuwa da za ku ci karo da su a cikin labarin, ƙirƙirarre ne kawai domin isar da saƙo. Ban rubuta shi da niyyar cin mutuncin kowa ko tozarta wani ba. Ina fatan zaku bani haɗin kai, tare da biyo ni sannu a hankali domin ku ji irin salon da nazo muku da shi a wannan karon.Gaisuwar ban girma da jinjina a gare ki amintacciya ta *AMINA MUHAMMAD HARUNA* tare da ke ta hannun damana *FATY SABO* Da kuma abokiyar shawara ta *AYEESHAT KISSAR* ubangiji Allah ya yi mu ku abinda zato bai taɓa bai taɓa zato ba. Allah ya ba ku Aljannah. Ina godiya da irin gudunmawar da kuke bani. FULANI proud of you my people.Ina miƙo gaisuwa ta musamman ga jama'ar Yota da shuwagabannin mu masu capacity, Alkhairin Allah ya ci gaba da riskar ku.Ina alfahari da ku Team Yota's Amazing Pen's, ƴan team ɗina, Allah ya ci gaba da dafa mana ya yi mana jagora baki ɗaya.Bissmillahirrahmairrahim    FULANI*** ⌛🕛 LOKACI🕛⌛      PAGE 1️⃣ A zahiran ce tafiya take cikin nutsuwa, amma a cikin zuciyar ta sauri take harda sassarfa, tunda taga yamma tayi hankalin ta yayi mugun tashi, kuma tunanin ta yayi hijira ya koma gidan su, a halin yanzu bata da wani buri daya wuce ta buɗe ido ta ganta a cikin gidan su, saidai me titin kamar anyi shara babu ababen hawa, hakan ne yasa ta yanke hukuncin ta taka a ƙafar ta ko Allah zaisa ta dace.Saida tasha wahala kafin ta samu napep ɗin daya ɗauke ta ya shigar da ita cikin unguwar su, dake nan kuntau old airport, tana zuwa ƙofar gidan su ta sauke ajiyar zuciya, dan sosai ta samu relief ganin ba'ayi sallar magriba ba ta dawo gidan, kuɗin shi ta ciro ta bashi a cikin jaka, sannan ta nufi gidan da zan iya cewa yafi kowanne gida girma a layin, tana da key a hannun ta hakan yasa bata tsaya knocking ba, kawai ta saka ta buɗe ta shiga da sallama.   "Barka da yamma mahmah" ganin ko kallon ta batayi bane yasa cikin sanyin jiki ta matsa kusa da ita "sannu da gida mahmah"Wani shegen kallo ta ɗago ta watsa mata wanda yasa jikin ta ya fara rawa a hankali, ƙasa tayi da kanta batare data bar wajen ba, duk kuwa da yanda zuciyar ta take bugawa da tsananin ƙarfi.   "Sau nawa zan faɗa miki babu ruwan ki dani a cikin gidan nan idan har bani ce na neme ki ba? Kinje gantalin ki kin dawo shine zaki zo kina wani sunne min da kai kamar ta Allah? Tunda har kika fara kai gab da magriba a waje nan gaba kaɗan nasan kwana zaki farayi a can wajen yawon ki" yanda take mata faɗ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters14
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play