LOKACI

LOKACI CHAPTER 8

by @fulani32

***


⏳🕛 LOKACI 🕛⏳ 

RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI 

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA 

Under Team Yota's Amazing Pen's.

SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️ 

FULANI ❣️ 
***

        ⏳🕛 LOKACI 🕛⏳


      PAGE 8️⃣

Yana zaune a tsakar gida akan tabarma, da ledoji a gabansa, fuskar shi da bandeji a goshin shi, tsakar gidan a share tas babu alamun datti, babban abin da ya bata mamaki ganin yanda yake ta sakar mata murmushi. "Sannu da dawowa Masoyiya! Nasan daman zaki dawo shiyasa na gyara miki gidan, ga wannan." ya ce yana miƙa mata ledojin gabansa.

Share shi tayi ta nufi ɗakinta, shima dai a gyare yake kamar wajen, zama tayi a gefen gado tayi tagumi, gaba ɗaya bata yarda da shi ba, tasan wanene Auwal fa sai dai ta faɗawa wani, bazai taɓa yuyuwa ba ace wai har ya haƙura da abin da ya faru ba, dole da wani abu a ƙasa. "Tunanin me kike?." Ya tambaye ta yana zama a kusa da ita. Matsawa baya tayi, "Hmm da kin kwantar da hankalinki, duk abin da kike tunani bai zama lallai ya tabbata ba, wataƙila ya tabbata kuma fiye da yanda kike hasashe. Yanzu dai kwantar da min da hankalinki masoyiya."

Duk yanda ya so ta buɗe baki tace da shi wani abu ta ƙiya, tashi yayi ya fita yana murmushin gefen baki.

Bin bayan shi tayi da kallo a bayyane ta ce "Allah ya fika Auwal."


★★★

"Zahra!!!." Kiran baffa ya ratsa kunnuwanta, dum haka zuciyarta ta buga. "Na'am." Ta amsa tana fitowa daga ɗaki.

"Assalamu alaikum, Barka da dare baffa. Sannu da huta wa Mahmah." Harararta Mahmah tayi ta ɗauke kanta. "Barka Zahra zauna magana zamuyi." Ya nuna mata wajen zama yana washe mata baki. A madadin tayi farin ciki yau ɗaya Baffa ya amsa ta har yana murmushi, sai taji gaba ɗaya hankalinta bai kwanta da hakan ba.

Zama tayi ta tanƙwashe ƙafarta, "Zahra yau muna wace rana?" Sai da ta ɗan kalle shi sannan ta ce "Laraba Baffa" yana murmushi ya ce "ƙwarai laraba ta bawa ranar sa'a."

"Yanzu muka rabu da Malam Bala, ya ce ya gama shirya miki ɗakin da zaki zauna baya son a ɗauki lokaci, yafi son ayi auren nan a wuce wajen, tunda ba wata hidima za'ayi ba, ɗaurin aure ne kawai. Ya nemi da ayi ɗaurin auren jibi kenan juma'a, da nace mishi ya ɗan ƙara mana lokaci saboda ko Mahmah zata yi miki shiri irin naku na mata. Mun rabu da shi akan duk yanda akayi zai jini a daren nan zan mishi waya. Toh kuma sai mahaifiyar taki ta ce babu wani shiri juma'ar ma tayi, idan gobe yake so ma a shirye kike."

Batasan ta kafe su da ido ba, sai da taga suma suna kallonta, kamar wacce aka ƙwato kalmar daga bakinta ta ce "meyasa na cancanci haka daga gare ku?". Iska ta busar me zafi daga bakinta, "Allah ya kaimu ya sa hakan shine mafi alkhairi a gare ni". Tashi tayi ta fice tana haɗa hanya dan jiri ne yake neman zubar da ita.

Akan gwiwarta ta zube tana fifita da hannuwanta, dan ji tayi gaba ɗaya ta kasa shaƙar numfashi yanda ya kamata. "Subhanallahi Aunty Zahra meyafaru?" a tsorace Salmah ta dafa ta. "Salmah!!" Luu idonta ya lumshe. "Innallilahi wa'inna ilaihir'raji'un". Da dukkanin Muryar ta furta, hakan ya janyo hankalin Mahmah da Baffa da suke ɗaki, kusan a tare suka shigo ɗakin.

Wani irin numfashi take mai firgitar da mai sauraro, hannuwanta dake rawa tasa ka take fifita fuskarta da su, alamun iska tayi mata kaɗan wajen shaƙar numfashi, sosai take kokawa da numfashinta dake barazanar ɗaukewa. "Innallilahi wa'inna ilaihir'raji'un big sister lafiyar ki kiyi min magana dan Allah" cikin wani irin tashin hankali Salmah ke maganar tana jijjiga ta.

Ajiyar zuciya ta fara saukewa a jejjere, ƙoƙarin magana take amman ta kasa.

"Akan zamuyi miki aure shine kike ƙoƙarin haɗiyar zuciya ki mutu? Wallahi Zahra ko zaki mutu babu abinda zai hana auren nan sai anyi" Mahmah tayi maganar duk da yanda zuciyarta tayi mata nauyi. Dan bata taɓa ganin Zahra a irin wannan yanayin data ganta ba. "Mah..mah aure kuma yaushe zaku mata auren." Salmah ta tambaye ta har tana janye jikinta daga na Zahra batare da ta kula ba. "Eh Ranar juma'a insha Allahu". Ta bata amsa alamun babu gudu babu ja da baya.

"Mahmah, me ya sa kike haka ne?" Salmah ta furta cikin muryar kuka. "Wallahi duk abin da ya samu Aunty Zahra, kece sila. Anya ma ke ɗin mahaifiyarta ce? Ta yaya, a matsayin ki na uwa, za ki dinga bada goyon bayan a tozarta miki ƴar ki? "Anya akwai adalci a lamarinki kuwa? Ko da kalamaina sun yi tsauri, ki yi haƙuri, Mahmah… amma addini ma ya ce idan ka ga iyayenka suna kuskure, ka tunasar da su"

"Auren nan fa ba dole ba ne, da za ku dinga ɗaga mata hankali a kansa. Addini ya ce idan har za ka tsare mutuncinka, ba sai ka yi shi ba. Yanzu Mahmah, wane irin aure ne na rashin gata kike shirin yi wa ɗiyarki? Menene laifinta a kan ƙaddararta na jinkirin aure? Haba, Mahmah… don Allah!"

Shiru tayi tana haɗiyar zuciya, kukan da take ta ƙoƙarin danne wa ya ƙwace mata, Hawaye ne suke zubo mata tamkar an buɗe famfo, buɗe baki tayi zatayi magana ta kasa cewa komai saboda shiɗewar da tayi. amma har lokacin tana kallon Mahmah cike da roƙo.

Mahmah ta ɗan yi shiru, tana kallon Salmah da wani irin yanayi na takaici.

“Kin gama?” ta tambaya cikin sanyin murya, amma kalamanta sunfi duka zafi.

Salmah ta sunkuyar da kanta, ta share hawayenta.

Mahmah ta sauke ajiyar zuciya.

"Salmah, kina tunanin ba na son Zahra ne? Kina tunanin ban taɓa jin ciwon halin da take ciki ba? Ita ƴarta ce, kuma duk abin da ya same ta yana shafa ta. Amma ke ba ki san abin da nake gani ba"
Ta ɗan dakata, sannan ta ce "Duk ranar da kika ga yadda mutane suke kallona saboda ɗiyata har yanzu ba ta yi aure ba, sannan ki ka ji irin maganganun da ake yi a bayana, sai kin fahimci dalilin da ya sa nake son ta yi aure"

"Amma Mahmah"

"Ki bar ni in gama!" Mahmah ta katse ta.

"Kin ce aure ba dole ba ne… gaskiya ne. Amma duniya ba ta da tausayi kamar yadda kike tunani. Idan ta ƙi wannan, wane ne zai sake zuwa ya nemi aurenta? Shekaru suna tafiya, Salmah. Ni kuma ina tsoron ranar da zan rufe ido ban san me zai same ta ba"

Salmah ta ɗago kai.

"Amma Mahmah, tsoron makomarta ba yana nufin mu tura ta cikin abin da zai ƙarasa karya ta bane"

Mahmah ta yi shiru. Wannan karon kalaman Salmah sun yi mata nauyi.

"Kin san abin da ya fi mata ciwo? Mahmah?" Salmah ta ci gaba cikin kuka. "Ba wai jinkirin aurenta ne yake kashe Aunty Zahra ba… kalaman mutanen da take tsammanin za su kare ta ne suke kashe mata zuciya"

Mahmah ta runtse idanuwanta. "Ke kina ganin ina cutar da ita ne?" ta tambaya a hankali.

Salmah ta girgiza kai, hawaye na sake zubo mata.

"Ba wai na ce kina cutar da ita bane Mahmah. Ina cewa kina son gyara rayuwarta ne ta hanyar da za ta iya ƙara karya ta"

Shiru ya ratsa ɗakin.

Mahmah ta kalli ƙasa, sannan cikin raunin murya, ta furta "To… me kike so in yi Salmah?"

Salmah ta matso kusa da ita, ta kama hannunta.
"Ki tsaya mata, Mahmah. Ko da duniya ta juya mata baya, ki kasance bangon da zata samu ta jingina. Kada ki zama ɗaya daga cikin mutanen da suke sa ta jin cewa ita kaɗai ce ba ta da gata"

Mahmah ta kasa magana. Hawaye suka fara cika idanuwanta. A wannan karon, ba iya Salmah ce kaɗai take kuka ba. Baffa da tun da suka fara maganar baiyi magana ba sai a lokacin ya ce "Ina ganin kawai a haƙura da auren tun da bata so." Sosai mama take girgiza kai kamar ƙadangaruwa "A'a Baffa baza'a fasa ba tayi haƙuri kawai, amman auren nan babu fashi, idan ya tafi wayasan lokacin da wani zai zo?"

Salmah ta buɗe bakinta zatayi magana, Zahra ta riƙe hannunta ta hana ta "Allah ya kai mu Mahmah" ta ce tana miƙewa ta shige cikin ɗaki. Suma duk barin wajen suka yi banda Salmah, data bi bayan Zahra, dan bata jin zata iya barinta ta kwana ita kaɗai. A kwance ta same ta, ta zubawa hannun ta ido. 

"Kina kewar shi big sister?" Salmah ta tambayeta tana zama itama tana kallon hannun nata. "Sosai Autah". Duk shiru sukayi, can Salmah ta katse shirun nasu "kince zaki bani labari wata rana, ki bani yau dan Allah!". Murmushi tayi kawai ba tace komai ba, can ta numfasa ta ce...

★

"Bazan manta ba Salmah a lokacin ina da shekara 14, mu uku ne a wajen Mahmah ni, A'isha, Amina sai kuma cikin zainab da take ɗauke da shi, bansan wani abu wai shi ƙunci ba, rayuwar farin ciki kawai nasani dan shi iyayena suke bani, a gefe ɗaya kuma ga Innar mu kakar mu kenan ta wajen Baffa, wata iriyar soyayya take nuna min da har yau ba ta fasa ba, ni kaina ina mata soyayyar da bansan adadin ta ba, duk da rabi faɗa ne, amman hakan bai hana kowa ya fahimci irin son da take min. Ina j.s.s 1 lokacin Baffa rana ɗaya yace zai canza min makaranta ya mayar dani privet saboda irin ƙoƙarin da nake da shi, nayi farin ciki Salmah duk yanda zan nuna miki bazaki gane ba". Murmushi tayi wanda ya ƙayata kyakykyawar fuskarta. Sannan ta ci gaba.

"Sultan international academy itace makarantar da Baffa ya mayar dani, kai tsaye j.s.s 2 suka kai ni, class ɗin mu maza da mata ne, mutum biyu ne a kowanne bench, namiji ɗaya mace ɗaya, lokacin da uncle ɗin mu ya nuna min wajen zama babu kowa a benchin hakan yayi min daɗi. Dan bana son zama kusa da namiji tsarin baiyi min ba, sosai na gane karatun da akayi a ranar hakan yasa na dawo gida cikin farin ciki. Ban huce gida ba sai na huce gidan Innarmu dan na bata labari, sosai itama ta tayani farin ciki, dan tana son duk abinda nake so, bayan nagama da nan na huce gida wajen Mahmah, itama dai da farin ciki ta tarbe ni, daganan kuma nayi shirin Islamiyya muka huce nida su Amina".

"Sosai na matsu safiya tayi na huce na tafi makaranta, dan sosai makarantar ta shiga raina, ina zuwa na nufi sit ɗin da na zauna jiya, ban ƙarasa ba na tsaya ina kallon wanda yake zaune a wajen, dan jiya ban ganshi a class ɗin ba. Malami ne ya shigo hakan ya sani wuce wa na zauna a kusa da shi a takure, baiyi min magana ba nima banyi mishi ba, a haka muke zaune har satin ya ƙare. Tunda naje ban taɓa magana da kowa ba, banyi ƙawa ba kuma banyi aboki ba, ina ganin yanda kowa yake da partner ɗin shi amman banda ni, akwai wata a gaban sit mu tana yawan kallona, sai da ga baya na fahimci bani take kallo ba wanda yake kusa dani take kallo".

"Lokaci nata garawa mukayi first term exam, ranar hutu aka ba mu result, sunana aka kira da shi Muhammad Sani Muhammad, sai Ummulkhairi Umar Muhammad. Haka aka ce mu fito gaban allo. Bayan mun fito aka bamu result ɗin mu a hannu, nice na ɗauki first position, shi kuma second sai Ummulkhairi third. Text book aka bamu kyauta, sannan aka tafa mana, muka koma muka zauna, tunda muka zauna na fahimci yana yawan kallona, saɓanin da, dako inda nake baya kallo".

"Daga baya na fahimci kallon da yake min na haushi ne, ashe shine yake ɗaukar first position, daga zuwa na kuma na ɗauka, hakan yasa masa jin zafi na, bayan mun koma hutu bansan ya akai ba, muka fara magana sama_sama da shi duk da gaisuwa ce, sai kuma Khairiyya data shigo cikin mu, wadda zan iya cewa ma itace take yawan saka mu magana ta dole, a hankali sabo ya shiga tsakanin mu sosai da sosai, komai tare da muke a makarantar, zuwa lokacin da muka shiga j.s 3 munyi shaƙuwar da baki bazai iya faɗar ta ba, Khairiyya tana ce mishi kakana ni kuma ina ce mishi my friend, shi kuma yace min best friend. Khairiyya kuma ya kira ta jikata, tun ranar da mukayi jiniour candy har inda yau take ban ƙara saka Muhammad a cikin idanuwana ba, mun neme shi nida Khairiyya har mun gaji, wannan azurfar da take hannuna ta sa ce, bazan manta ba a ranar jiniour candy mu ya bani ita, shima yana da ita a hannun sa, amman tashi ta maza ce, a lokacin tayi min yawa sosai hakan yasa na ajiye ta, amman yanzu kinga yanda tayi min ai". Ta ƙarasa idonta cike da hawaye amman murmushi ne a kan fuskarta.

"Aunty soyayya kuke kenan?" Salmah ta tambayeta ita ma da murmushi a fuskarta.

Sosai ta waro idanuwanta waje "Soyayya fa auta classmate ɗina ne, bayan haka ma age mate muke da shi fa, Allah ya kiyaye. Kawai dai aboki nane".

Itadai Salmah shiru tayi kawai.

"Bayan haka muka ci gaba da rayuwa, kinsan Khairiyya ai, ita kaɗai ce ƙawata har yanzu, tayi aure sau biyu amman Allah bai taɓa bata haihuwa ba, tayi na uku ina fatan a shi zamu samu ƙaruwa insha Allah.
Bayan nayi candy na zauna a gida ban ci gaba da karatu ba, saboda Baffa baya so yafi son ya aurar damu, Allah ya azurta Mahmah da ƴaƴa mata gamunan guda bakwai, wani ikon Allah gaba ɗayan mu, duk wanda yayi candy a cikin ku sai kiga Allah ya fito mishi da mijin aure. Hakan ya sakawa Mahmah farin ciki da alfahari ta yanda duk inda ta zauna ko ana sabga ko wani abu zaki ji tana faɗa cike da jin daɗi cewa ita ƴayan ta da zarar sunyi candy take kai su ɗakin aure, kuma haka ne dan duka mutum biyar da ta kai suna candy aka aurar da su, nice kawai Allah bai yankewa, sai kuma kema da nasan baki rasa mane ba, ina da tabbacin kuma insha Allah kina candy zaki tafi ɗakin ki Autah".

"Bazan taɓa aure baki yi ba Big aunty. Shima wannan auren da suke cewa zasuyi miki bazai taɓa yiyuwa ba, zaki ce kuma na faɗa miki".

Ƴar dariya tayi kawai wadda zan iya cewa batakai zuci ba. "Bakin alƙalami ya riga da ya bushe Salmah...."
Daga haka ta juya ta kwanta ta bata baya.....



FULANI
***