LOKACI

LOKACI CHAPTER 12

by @fulani32

***


⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳ 

RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI 

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA 

Under Team Yota's Amazing Pen's.

SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️ 

FULANI 🤍 
***

⏳🕛LOKACI🕛⏳

       PAGE 1️⃣ 2️⃣ 

Maganar ta fito daga bakinta cikin raunin murya, amman haka ta isa kunnuwan Ummu kamar tsawa.

"Khairiyya" 

Ummu ta kira sunanta cikin muryar kuka, ta matsa kusa da gadon.

"Kuyi haƙuri zamu dubata idan mun gama sai ku dawo"

Doctor ya katse Ummu dake shirin magana.

Bayan duk sun fita likitan ya fara dubata, yana mata tambayoyi tana bashi amsa. can ta numfasa ta ce. 

"doctor mai yasa me ni dan Allah"

"Kinyi ɓari ne" ya bata amsa.

Kamar bata fahimci me yake nufi ba ta maimaita kalmar.

"Eh kin samu ɓari na ciki, ɗan kimanin wata ɗaya" ya ƙara bata tabbaci.

Hannunta ta ɗora akan cikinta, wasu zafafan hawaye suka zubo mata, kuka take da dukkanin zuciyarta, abin da take nema ne ido rufe, gashi ta samu amman Auwal yayi mata sanadin sa, ya kashe mata baby.

Har suka fita bata sani ba, yana fita yace iyayenta da mijinta su shiga tana buƙatar su. 
Sai da su Ummu suka shiga, sannan Auwal yabi bayan su kamar munafiki.

Idonta bai faɗa akan kowa ba, sai Auwal dake gefe a tsaye yana kallonta. Kallonsa take tamkar bata taɓa ganinsa ba, ko kuma taga wata sabuwar halittar. Kasa jure irin kallon da take masa yayi ya ɗauke kansa.

"Khairiyya" 

Ummu ta kira sunanta tana riƙe hannunta.

Karɓe hannunta tayi sannan ta ce "Ummu sai da na ce miki a'a ke kuma kika ce eh, nayi miki biyayya na koma, daman na faɗa miki zaki zo ki ɗauki gawata, kinzo duk da gani ban mutu, amman kisani an daɗe da kashe ni, a yau na tabbatar da na ƙarasa mutuwa Ummu"

Tayi shiru, hawaye yana gangarowa da ga kurmin idanuwanta, dan ƙarfin hali take wajen yin maganar.

"Me yasa zaki ce haka Khairiyya?" Ta tambaye ta cikin rawar murya. "Ni ce fa Ummu ɗinki, ta yaya kike tunanin zan zauna a gida ina jiran mutuwar ki? Ta yaya a matsayina na uwa zan so ganin gawar ƴata?"

"Eh Ummu gashi kin zo.." Ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin ta buɗe idonta ta sake kallon mahaifiyarta ta. "Kin zo bayan an riga an gama dani, an gama da rayuwata, bayan an kashe ni kika zo Ummu"

Ummu ta kama bakinta da tafin hannunta, kuka ya ƙara kubce mata, na danasani da kuma tausayin Khairiyyar.

"Waye ya gama da ke?" Ta tambaye ta cikin kuka. Khairiyya bata amsa mata ba. Alhaji da ke tsaye tun ɗazu a gefe, yana sauraron su, ba tare da ya ce komai ba, ya matsa kusa da gadon.

"Khairiyya ki faɗa min abin da ya faru"

Juyar da kanta tayi zuwa inda yake.

"Alhajin mu" muryarta ta fito a hankali dan ta gaji da maganar.

"Ka ɗauke ni daga nan, ka tafi da ni gida dan Allah Alhajin mu"

"Zan tafi da ke Khairiyya" ya amsa mata ba tare da wata_wata ba. "Amma sai kin faɗa min abin da ya faru har kika rasa cikinki"

Runtse idanuwanta tayi, a hankali abin da ya faru a daren jiya suka fara dawo mata, muryar Auwal, fushinsa, tsoronta, da kuma irin azabar da ta sha a hannunsa, jikinta ya fara rawa.

"Alhajin mu.."

"Na'am Khairiyya."

"Kar ka bar ni a nan"

Alhaji ya kalli Auwal da Ummu, sannan ya kuma kallonta.

"Bazan barki ba"

Ta haɗiye miyau da ƙyar. "Ni.. bana son komawa gidan nan" a take Ummu ta ɗago kanta.

"Gidan Auwal?"

Khairiyya ta lumshe idonta, hawaye suka fara zubo mata, ba tare da ta iya dakatar da su ba. "Ummu kar ki tambaye ni komai yanzu"

"Amman Khairiyya"

"Dan Allah Ummu" ta ɗan ɗaga muryarta, amma raunin da ke jikinta ya hana ta ci gaba, ajiyar zuciya ta sauke, ta fizgo maganar "dan Allah Ummu kar ki tambaye ni"

Shiru ne ya mamaye ɗakin. Alhaji ne ya kalli Ummu, ya fahimci akwai abin da ƴarsa bata shirya faɗa ba, sai ya juya ya kalli Auwal, sosai ya zuba masa ido. Auwal da tun farkon fara maganar su, kansa yake a sunkuye, ya ɗago ya kalli Alhaji dan sosai yake jin kallon har ɓargonsa. Ganin irin kallon da yake masa ya sa zuciyarsa ta buga da ƙarfi.

"Auwal! Me ya faru da ƴarta?"

 Alhaji ya tambaye sa, har lokacin yana karantarsa. dan zai iya ce wa bai taɓa tsayawa yayi masa kallon tsaf irin yau ba, a yau ba Auwal ɗin daya aurawa Khairiyya ya ke gani ba, wani Auwal ɗin daban ya ke gani, wanda duk wani mai hankali kallo ɗaya zai masa ya fahimci shiɗin ɗan shaye_shaye ne, saboda ga bakinsa da idonsa nan sun bayyana wanene shi.

Auwal ya buɗe bakinsa da niyyar magana, amman babu wata kalma da ta iya fitowa.

Ita kam Khairiyya tun tambayar da taji, Alhaji yayi masa ta juyar da kanta gefe, dan bata son ganinsa ko jin muryarsa, wata muguwar ƙiyayyarsa ta ke ji har ƙasan zuciyarta. Shi dai Alhaji duk yana ankare da komai da suke yi.

A karo na biyu ya ƙara tambayarsa "me ya faru da ita"

Auwal ya sunkuyar da kansa.

"Ban sani ba"

Yana rufe bakinsa Khairiyya ta tari numfashin sa, daga sama suka ji muryarta ta ce. 

"Ƙarya kake yi"

Duk juyawa sukayi suna kallonta, bata damu ba idonta cike da hawaye ta kalle shi, kai tsaye ido cikin ido ta ce.

"Ka sani"

Auwal ya tsaya cak, yana kallonta da mamaki, dan bata taɓa kallon idonsa ta faɗa masa magana ba, bama wannan ba, yau ƙiyayyarsa yake gani kwance a cikin idanuwanta, abin da zai iya ce wa, bai taɓa gani ba, sai dai ya ga tsoronsa, da jin haushinsa, amman yau ƙiyayyarsa ce kwance har akan fuskarta.

"Ka san abin da ya faru da ni, tun da kai ne silar faruwar komai" ta katse masa dogon tunanin da ya tafi.

"Khairiyya" ya kira sunanta da wani irin yanayi, yanayin da tun farkon aurensu bata ƙara jinsa, a tare da shi ba, sai yau ɗin bayan komai ya zo musu ƙarshe.

"Kar ka sa ke ka ƙara kiran sunana" sai muryarta ta karye. "Ba a yau ne ya kamata ka kira sunana da wannan muryar ba Auwal, tun lokacin da nake tsananin azaba, da uƙubar aurenka ne ya kamata, ba wai a yau ba da ka kashe min baby, sannan nima ka kashe ni, ka kuma kashe aurenka da ke kaina, a yau ka kawo mana ƙarshen komai Auwal" tayi shiru tana kuka mai cin rai.

Ummu ta kalli Auwal, sannan ta kalli Khairiyya, a karon farko ta fahimci cewa ba wai iya dukan da shaye-shayen da Auwal ya ke bane matsalar, ta fahimci abin da ya faru a jiyan ya fi ƙarfin zaman da suka sa ba yi, idan har hasashenta yana bata dai-dai koma menene yana da alaƙa da zubewar cikin Khairiyya, idan har kuwa haka ne, wannan ɗin al'amari ne mai girma da itama dole zata tsaya mata har auren nan ya zo ƙarshe, kowa ya haƙura idan ba haka ba wata rana ƴarta zai kashe mata.

"Khairiyya" ta kira sunanta tana riƙe hannunta.

"Ki gaya mana abin da ya faru, nayi miki alƙawarin, wannan karan da kai na zan karɓar miki takardar sakinki" Khairiyya ta runtse idanuwanta da ƙarfi, ba'a wannan lokacin ta so jin wannan furucin daga bakin Ummu ba, ta so jin su ne tun kafin akai ga zuwa wannan lokacin, amman sai da komai ya ƙare ta nuna zata tsaya mata.

"Na yi tunanin idan na yi haƙuri, komai zai gyaru, na yi tunanin idan na ci gaba da zama matar kirki, idan na ci gaba da yi masa biyayya, duk kuwa baƙar wahalar da nake sha a hannunsa, wata rana zai daina cutar da ni"

Ummu ta fara girgiza kanta, tana jin itama tana da laifi a duk abin da Auwal ɗin ya ke aikata mata, da ace tun farko ta nuna masa, ita ɗin tana da daraja da ba'a zo yanzu ba, da ace ta bari mahaifinta ya shiga lamarin da tuni anyi wa tufkar hanci, amman yanzu komai ya lalace.

"Amman jiya na fahimci abu ɗaya, ba kowace mace ba ce haƙurinta, yake cetonta ba, wani lokacin haƙurin da kake ya na sa ka ne kawai ka ƙarasa rasa kanka" ta buɗe idonta, dan tun da ta fara maganar ta runtse su, komai yana dawo mata a cikin kanta, bazata ce haƙuri ba shi da amfani ba, tabbas yana da shi amman ba'a wajen maza irin su Auwal ba. Wani irin hawaye take, bawai na abin da Auwal yake mata ba a'a, na asarar cikin da ta fitar da ran zata samu, sai gashi Allah ya ji ƙanta ya bata amman, Auwal ya zubar mata da shi.

Alhaji juyar da kansa gefe yayi, yana jin wani irin zafi ya cika masa zuciya, ba iya zafin Auwal ya ke ji ba, har da zafin Ummu ya ke ji da ta ɓoye masa, abu mai girma irin wannan, da farko da Maryam tana faɗa masa bai yarda ba, shiyasa ya haɗa meeting ya ce ta maimaita a gaban kowa, yanda idan har ƙarya take bazata iya ba, sai gashi a gaban Ummun ta faɗa kuma bata mu sa ba, wai ƴar sa ce, miji ya mayar kamar jaka, ya daketa, ya sakata wanki da aikin wahala, tsawon shekara biyu, tana a cikin wahala amman bai sani ba, ya na tsayawa ƴaƴan wasu ma bare na shi, amman babu komai ya karɓi ƙaddara, sai dai abu ɗaya ya sani wallahi Khairiyya ta gama zaman aure da mutumin nan, idan ma baiyi shari'a da shi ba.

Auwal kuwa kamar an kafe shi a wurin, ya kasa kataɓus.

Kallonsa na ƴan daƙiƙu ta yi ta ce.

"Ka san wani abu Auwal?" Muryarta tayi wani irin sanyi.

"Abin da ya fi min ciwo ba wai yan da kazo min bane ai ba shi ne na farko ba, amman sai da na ce maka bazan iya ba, ka sani banda lafiya, amman baka tausaya min ba duk da daman ba tausaya min kake ba, babban abin da yafi min baƙin ciki da aurenka, na taɓa kallonka a matsayin mutumin da zai kare ni, ya bani farin ciki, amman daga ƙarshe kaine mutumin da nafi jin tsoron kasancewa a tare da shi, duk kuwa yan da na so kasance a tare da kai a can baya, kai ne mutumin da ko farin ciki nake naji muryarka sai na neme sa na rasa, firgici ya maye gurbinsa"

"Na tsane ka Auwal!! Bazan taɓa yafe maka kashe min baby da kayi ba, kuma wallahi saika sake ni..."

Juya kanta gefe tayi, numfashinta na seezing saboda yanda take kuka tana magana.

Babu wanda ya iya ce mata komai sai hannunta da Ummu ta ƙara riƙewa cikin nata, shi kuma Alhaji ya fara shafa mata kanta da hular ta cire, idonsa jajir.

Juyawa yayi ya kalli Auwal.

"Kaje ka kawo min takardar sakin yarinyata, cikin ruwan sanyi idan ba haka ba, wallahi sai na ɗaureka, kar takardarta ta wuce yau a hannuna, fita ka bani waje"

Kasa ɗaga ƙafarsa yayi a wajen, dan zai iya cewa bai taɓa jin soyayyar Khairiyya irin wannan ranar ba. Kamar mara laka haka ya juya yabar ɗakin.

Baccin wahala ne ya ɗauketa, sai da Alhaji ya tabbatar baccin nata yayi nisa ya fita ba tare da ya ce da Ummu komai ba da take kuka sosai. Kai tsaye wajen likita yaje akan yana son a bashi transfer zai canza mata asibiti, sai dai likitan yace masa, idan jinin ya ƙare zuwa dare ma zai iya sallamarta, dole ya haƙura ba dan ya so ba.

Gida suka koma duka mazan, aka bar Ummu da aunty Maryam a wajenta, tunda suka tafi Maryam ta ƙara nunawa Ummu koma menene ya sami Khairiyya tana da hannu a ciki koda kuwa yau ace mutuwa tayi, wanda hakan shine babban abin da ya ke ƙara ɗaga mata hankali, ga fushin da Alhaji yake da ita, a rana ɗaya sai gashi ita ma duk ta faɗa, tayi zururu kamar mara lafiya.

Tun da Khairiyya ta farka bata ƙara cewa kowa komai ba, sai dai ido kawai, da zarar ta tuna ciki ta samu ya zube, sai taji komai ya fitar mata a rai, tsanar Auwal ta ninku a ranta.

Alhaji bayan sun koma gida bai ɓoyewa yayyanta komai ba, yayi musu bayani, sosai suka ɗauki zafi akan sai sun ɗaure shi, amman ya ce a'a, raba su kawai shine abin da yake buƙata ba tashin hankali ba, yaje sun bar shi da Allah dole suka haƙura badan ran su ya so ba.

A ranar aka sallamota suka dawo gida, inda suke nuna mata wata iriyar soyayya da kulawa, dan kaf ɗin su babu wadda ta taɓa fuskantar abinda Khairiyya take fuskanta a rayuwa, duk da dai ba za'a rasa ɗan adam da ƙalubalen rayuwa ba.

★★
Auwal tun da ya dawo gida bashi da aiki sai shaye_shaye dan yana ganin shine kawai abin da zai cire sa daga damuwa, mahaifiyarsa ta gaji da jinsa shiru hakan ya sa ta biyo sahunsa, sosai hankalinta ya tashi dan ta na matuƙar ƙaunar ɗanta.

"Me ya faru haka Auwal kake neman hallaka kanka" ta tambaye sa cike da tashin hankali.

"Matata suka ƙwace min wai sai na rabu da ita" ya bata amsa cikin muryar maye.

"Mekayi mata da har iyayenta zasu ce haka Auwal" 

Yana shirin bata amsa suka ji ana bugun gidan, ita ce ta tashi ta duba ko waye.

Ahmad ne da ƴan sanda guda uku.

"Malam lafiya" ta tambaye shi, tsoro rubuce akan fuskarta.

Har ƙasa Ahmad ya tsugunna ya gaisheta, sannan ya faɗa mata wajen Auwal yazo idan yananan, shi yayan matarsa ne.

"Toh muje ciki amman su dai su jira anan, sai muyi magana"

Baiyi musu ba yabi bayanta suka shige.

"Ina jinka me ya faru na ganka har da ƴan sanda" ta tambayesa.

"Mahmah daman akan takardar sakin Ummul khairi ne, mun jira tsayin sati bai kawo ba, kuma bai aiko ba, shine muka ce gwara a saka hukuma a ciki kawai zaifi"

"Basai anyi haka ba, Auwal sakar musu ƴar su" ta ce bayan ta ɗagosa daga kwancen da yake. Ture ta yayi ya ce "babu ɗan shegiyar da zai raba ni da matata"

Tashi yai yana tangaɗi ya riƙe rigar Ahmad yana zaginsa, bai biye masa ba sai waya daya kira yace su shigo. Babu ɓata lokaci suka shigo, duk iskancin ɗan wiwi yana tsoron police, hakan yasa ya fara ƙoƙarin sakin Ahmad, ita kuma mamarsa tana ta bashi haƙuri.

Ƙarshe da yaga dagaske tafiya za'a yi da shi ya ce, ya sake ta saki ɗaya.

"Yayi kaɗan" inji Ahmad.

"Na sake ta saki biyu" 

Haka ya ce saki uku zai yi mata, Amman maman tace a'a, biyun ma ya isa.

Tafiya suka yi, suka bar shi, duk da police ɗin sun so tafiya da shi amman ya hana..

Bayan ya koma gida ya kunna musu, videon da ya ɗauka na sakin, ya ce abin da ya sa ya ɗauki video, saboda bai bashi a rubuce ba, kuma zai iya dawowa ya ce bai yi ba, amman tun da da video bai isa ba.

Khairiyya hawayen farin ciki ne ya zubo mata, tana jin zuciyarta fes da farin ciki, nauyin da ƙirjinta yayi mata a take ta neme sa ta rasa, duk da tabon rashin gudan jininta ya nan a ranta.

"Alhamdullah" ta furta a bayyane.

FULANI
***