LOKACI CHAPTER 13
by @fulani32
***
⏳🕛 LOKACI 🕛⏳
RABI'ATU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
Under Team Yota's Amazing Pen's.
SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️
FULANI 🤍
***
⏳🕛 LOKACI 🕛⏳
PAGE1️⃣3️⃣
Koda Zahra ta farka da asubah, sai ta ji wata iriyar nutsuwa ta sauka a zuciyarta. Nauyin da ya mamaye ƙirjinta tun da aka fara maganar auren ya ragu kaɗan, duk da cewa har yanzu akwai abubuwan da take tsoron tuno su, da kuma abin da zai faru anan gaba.
A hankali, abubuwan da suka faru jiya suka fara dawo mata ɗaya bayan ɗaya. zuwan ƴaƴan malam Bala, zuwan Inna, maganar cewa an soke aurenta, da kuma maganar Baffa, wanda shima ya tabbatar mata da cewa an fasa auren. lumshe idonta tayi na wani ɗan lokaci.
Duk da wannan abubuwan da suka faru a wajenta, na farin ciki ne, ya kamata ace sun kawo mata sauƙi, amman ina zuciyarta har yanzu ba ta samu cikakkiyar nutsuwar da take buƙata ba, tashin hankalin da ya mamaye gidan ya bar wani irin tabo a ranta, da ba zai gushe cikin dare ɗaya ba.
Har yanzu tasan babu sassauci a wajen Mahmah, dan tana kallon fasa auren kamar wani babban laifi da Zahra ta aikata mata. sauke ajiyar zuciya tayi, tare da jan dogon numfashi.
"Alhamdullah"
Ta faɗa a hankali, hawaye na gangarowa kan kumatunta, ita kanta bata san meyasa take kuka ba, wataƙila dan gajiya ce, wataƙila kuma dan sauƙin da Allah ya kawo mata ne, bayan kwanakin da tayi su cikin tsoro da fargaba, ko kuma dan ba ta san abin da gobe za ta zo mata da shi ba.
Ta shi ta yi ta shiga toilet, ta ɗan jima sannan ta fito, alamun har wanka ta yi, shirin sallah tayi, bayan ta idar, ta ɗaga hannayenta sama, ta yi addu'a mai tsawo "ya Allah ina roƙonka ka sanya ƙarshen wannan lamari ya zama mafari na alkhairi a rayuwata, ya rabb ka maye duk abun da na rasa da abin da ya fi shi zama alkhairi a gare ni, ya Allah ka tsare ni da ga dukkan abin da ba alkhairi ba ne a rayuwata, ya rahman idan akwai wani abu da nake nema wanda ba alkhairi bane ka cire min shi daga zuciyata cikin salama" bayan ta gama addu'ar, ta share hawayenta, sannan ta fito waje.
Gyaran gida ta fara yi, ta share, ta gyara, ta tattara abubuwan da suka watse, tana ta ƙoƙarin ɗauke hankalinta daga tunanin da yake ta neman dawo mata, bayan ta gama sai ta shiga kitchen ta haɗa musu breakfast mai sauƙi, ta yi komai cikin nutsuwa, kamar babu wani abu da ya faru, amman a cikin zuciyarta, akwai abubuwa da yawa da ba zata iya furta su ba, ta na gama wa ta koma ɗaki, ruwa ta ƙara watsa, sannan ta kwanta, ba dan za ta yi bacci ba, sai don kawai ta samu gangar jikinta ta huta da zuciyarta.
Ba ta daɗe da kwanciya ba aka turo ƙofar.
"Big sister" muryar Salmah ta karaɗe ɗakin.
"Shigo" ta ce ba tare da ta juya ba.
"Sannu da hutawa, big sister"
"Yawwa Autah"
Salmah ta kalleta na ɗan lokaci, sannan tayi murmushi. "Kiyi haƙuri da duk abun da ya faru, in sha Allah, lokaci zai zo da za ki yi farin ciki"
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "ina fatan hakan Salmah idan har ina da rabo"
Hannunta Salmah ta riƙe "za ki yi, ki dai yi haƙuri, ki bar komai a hannun Allah, shi ne ya fi mu sanin abin da ya dace da rayuwarmu"
Shiru ta yi tana jin kalaman Salmahn har cikin zuciyarta, ƙoƙarin murmushi ta yi, hancin Salmah ta ja. "Allah ya sa ka da alkhairi, Autah ta"
Ita ma tana murmushi ta ce "Amin ya rabb big sister" ƙara rarrashinta tayi da wasu kalaman kwantar da hankali, har sai da taga Zahran na murmushi daga ƙasan zuciyarta ba na yaƙe ba. Hira suka ci gaba da yi kamar sako da sako, ba zaka taɓa cewa akwai ratan shekaru me tarin yawa a tsakanin su ba.
★★
Kwanan Zahra huɗu ba taje aiki ba, tana ihutu, Alhamdullah, abubuwa sun fara yi mata sauƙi kaɗan, Mahmah dai har yanzu tana yawan jifanta da maganganu masu zafi, amman Baffa ya sauya sosai, yanzu lallaɓa ta, ya ke sosai kuma take jin daɗin hakan, dan abu ne da ta rasa tsawon lokaci, lokaci bayan lokaci zai kirata ya tambaye ta, ko akwai abin da take buƙata.
"Bana buƙatar komai Baffa" wannan shine amsar ta, a duk san da ya tambaye ta. shi kuma zai ce mata "ki kwantar da hankalinki ina tare da Mamana, babu abin da zan bari ya ƙara faruwa da ke in sha Allah" duk sanda ya faɗa mata haka sai taji wata iriyar nutsuwa ta lulluɓeta. Koba komai yanzu ta samu mutum biyu da suke tare da ita a cikin gidan.
A yanzu dai babu wanda yake matsa mata da maganar aure, kuma wannan kaɗai ya bata wata iriyar nutsuwa, da ta daɗe ba ta ji ta ba, duk da yanda ƙananun maganganu suke ta shi a wajen mutanen unguwarsu, ana ta magana a kan, yadda ƴaƴan malam Bala, suka zo har gida, suka ci mata mutunci, har aka kai ga soke aurenta.
Wasu suna tausayinta, wasu kuma suna ganin kamar ita ce sanadin da yasa aka fasa auren, dama wazai aureta duk ya gama yawo ta da sunan aiki, tsoho ma ya fasa bare kuma yaro, amman sosai ta yi ƙoƙarin toshe kunnenta daga duk waɗannan maganganun, bama fita take ba bare su ganta, Salmah ce dai muddin ta ji zata tsaya ayi rigima da ita, duk da tana ta ƙoƙarin hana ta, amman a banza.
Wani irin nishaɗi take ciki na komawar ta aiki gobe monday in sha Allah.....
★★★
*ZAYD'S SIGNATURE RESTAURANT*
Babban restaurant ne mai hawa biyu, wanda aka gina shi cikin wani irin tsari na zamani. ginin yana da faɗi da fili sosai, tun daga wajen sa mutum zai fahimci cewa ba ƙaramin restaurant ba ne.
Launin ginin waje ya kasance cream mai ɗan duhun beige, tare da haɗin dark brown da golden touches, wanda ya ba wurin wani irin kyan gani na musamman.
A gaban restaurant ɗin akwai babbar ƙofar gilashi mai buɗewa ta atomatik. Saman ƙofar kuma da akwai babban allon dake ɗauke da sunan restaurant ɗin me haske da aka rubuta.
*ZAYD’S SIGNATURE RESTAURANT*
Da zarar an shiga, akwai reception desk mai kyau, sannan a bayansa akwai babban logo ɗin ZAYD’S da aka yi cikin salo na zamani.
Bangon cikin restaurant ɗin an yi shi da warm cream, yayin da wasu sassan bangon aka yi musu wooden paneling mai launin walnut. Floor ɗin kuma shiny tiles ne masu launin cream da ɗan ƙirar marble, wanda yake ƙara wa wajen haske.
A saman restaurant ɗin akwai fitilun warm white, tare da chandeliers masu sauƙi da kuma pendant lights da aka rataya a saman wasu tebura. tebura da kujerun an tsara su cikin wani irin salo, teburan wooden ne masu kyau, yayin da kujerun suke da laushi da upholstery mai launin beige da brown. A wasu sassan kuma akwai manyan sofa seats.
Restaurant ɗin yana da babban kitchen mai matuƙar tsafta da tsari. An ware wani babban sashe na musamman domin snacks da pastries, saboda snacks na ɗaya daga cikin abubuwan da restaurant ɗin ya fi shahara da su.
A kusa da wajen shiga akwai babban glass display da ake jera snacks cikin tsari mai ƙayatarwa. A ciki akwai meat pie, samosa, spring rolls, doughnuts, buns, cakes da sauran pastries iri-iri.
Akwai kuma drinks section da refrigerator mai cike da abubuwan sha, tare da ƙaramin coffee da tea corner.
Hawan bene na biyu kuma yana da VIP/private dining section, inda akwai wasu tebura da aka ware domin iyalai, baƙi na musamman da kuma mutanen da suke son samun waje mai nutsuwa mara hayaniya.
An ƙawata cikin restaurant ɗin da manyan indoor plants, framed artworks, mirrors masu kyau da ƙananan flower arrangements a kan wasu tebura. Ba'a cika wurin da decorations ba, saboda me restaurant ɗin yana son komai ya kasance cikin tsari mai sauƙi.
Ana kunna soft music a hankali a cikin restaurant ɗin, wanda yake sa wurin ya kasance mai daɗin zama ba tare da wata hayaniya ba.
A wajen restaurant ɗin kuma akwai ƙaramin sitting area mai kyau, wanda aka ƙawata da kujeru da plants. Da dare, fitilun wajen suna haskawa cikin nutsuwa, suna ƙara wa restaurant ɗin kyau, bayan sitting area akwai gardine na restaurant ɗin, an jera kujeru da tebura a ƙarƙashin manyan umbrellas, sannan ƙananun fitilu sun kewaye wurin. Sai kuma ƙaton parking space.
Babban abin burgewa a cikin restaurant ɗin, shine tsaftarsa, da tsarinsa, da kuma yanda suke kulawa da komai, kallo ɗaya zaka wa wajen kasan dukkan abinda aka zuba a cikinsa mai quality ne, babu wani abu da aka barsa haka kawai, komai yana da wajen da aka ware masa.
Kai tsaye idan mutum ya nutsu zai fahimci, mamallakin restaurant ɗin ya kasance mutum mai son, tsari, tsafta, quality da kuma paerfection.
★
Zaune yake cikin office ɗinsa, baka jin komai sai ƙarar ac da ƙamshin turaren air freshner, wanda ya haɗu da ƙamshin turaren jikinsa, suka bayar da wani irin ƙamshi mai sanya nutsuwa a zuciyar duk wanda ya shaƙe shi.
Sanye yake cikin suit blue-black, sosai kalar ta fito da hasken fatarsa, a hannunsa na hagu a akwai agogo da azurfa guda biyu, wanda suka ƙara ƙawata hannayensa da suke cike da ɓakar gargasa.
Hankalinsa gaba ɗaya yana kan computer ɗin da ke gabansa, dannawa yake cikin nutsuwa, ya jima yana dannawa kafin daga bisani ya dakata, ɗan jingina yayi da kujerarsa, sannan ya matsa yatsun hannunsa a hankali, ƙarar da sukayi da ya matsa sai suka katse shirun da ke cikin office ɗin.
Cikin nutsuwa ya miƙa hannunsa ya ɗauki wayar da ke office ɗin.
"Ka same ni a office yanzu"
Ya faɗi haka cikin husky voice ɗin, cike da ba da umarni, sannan ya katse wayar. bayan lokaci kaɗan aka yi knocking ɗin ƙofar.
"Shigo"
Ƙofar aka buɗe wani mutum ya shigo wanda zai iya girmansa da kaɗan, gaishesa yayi ya amsa, sannan ya nuna masa kujerar da ke gabansa.
"Zauna" ya ce har lokacin idonsa akan computer duk da ba dannawa yake ba.
Zama yayi, shi kuma ya ɗago idanunsa daga kan computer ya kallesa.
"Manager me ya ke faruwa a restaurant ɗin nan"
Shiru wanda aka kira da managern yayi dan bai san akan me yake magana ba, gashi kuma yasan ogan nasa baya son yayi magana ayi masa shiru.
"A lokacin da na ɗauka ban zo ba, na lura abubuwa sun fara yin ƙasa, musamman cinikin snacks da pastry, me ya faru?"
Sauke numfashi managern yayi.
"Oga Zay'd ba mu kaɗai bane muke fuskantar wannan matsalar ba, kusan duk restaurant ɗin da ke kusa da mu suma suna fama da ita"
Ya ɗan dakata ganin kamar ba saurarensa yake ba, saboda idonsa a lumshe a yake. Ware masa manyan idanuwansa yayi, hakan ya sa shi sauke kansa ƙasa sannan ya ci gaba.
"Amma akwai guda ɗaya da a yanzu shine ya fi kowanne tashe, kuma shine ya ƙwace mana customer's masu yawa"
Zay'd ya ɗaga girarsa sama da suke a cike har sun haɗe da juna, sannan ya ce.
"Wanne?"
"Dara restaurant"
Ya basa amsa.
Shiru yayi baice komai ba, sanin halin me gidan nasa sai ya ci gaba da masa bayani.
"Sun samu wata ƙwararriyar ma'aikaciya ne, tun bayan zuwanta, cinikin snacks da pastry ɗinmu yayi ƙasa, mutanen da suke yawan saka mana order sun koma can"
Zay'd ya kalli manager ɗin da wani irin yanayi da ba za'a iya karantar shi ba cikin sauƙi.
"Ma'aikaciya ɗaya?"
"Eh sir"
Ƙara jingina yayi da kujerarsa.
"Me take yi?"
Manager ɗin ya amsa masa "abin da na ji shi ne, snacks da pastry ɗin da take ta ƙware akan su, ta yanda zai yi wahala a samu ƙwararriyar da ta iya kamarta, dan gaskiya bansan adadin customer's ɗin mu da suka koma can saboda ita ba.
Zay'd baice komai ba, sai dai wannan karon gaba ɗaya hankalinsa ya bar kan computer da yake kallo.
A gajarce ya ce "sunanta?"
"Bansaniba sir"
"Zaka iya tafiya"
Yana fita ya mayar da idonsa ya lumshe.....
★★★
Washe gari da wuri Zahra ta gama duk abin da za tayi, tayi shirin tafiya wajen aikinta, tun da safe sukayi sallama da Salmah data tafi makaranta dan har yanzu batayi candy ba, yanzu ne take a ss3, fitowa ta yi ta nufi ɗakin Mahmah gabanta yana faɗuwa, da sallama ta shiga.
"Barka da safiya Mahmah, kin tashi lafiya? Daman zan tafi wajen aiki ne?" Tayi mata maganar a jere muryarta na rawa.
"Daman abin da kike so kenan ki ka ƙi aure, safiya ta yi kishirya ki ce kin tafi aiki, bayan nasan babu wani aiki da kike zuwa, sai dai yawon ki na ta zubar"
"Mahmah" ta kira sunanta a hankali muryarta na rawa.
"Wallahi wallahi Mahmah ban taɓa aikata abin da kike zargina da shi ba, Mahmah wallahi ban taɓa tsayawa da wani namijin ba bare har na aikata abin da kike tunani, wallahi Mahmah aikina kawai nake so, Mahmah a lokuta da dama ina jin kamar na ajiye aikin kodan hankalin ki ya kwanta kidena zargina, sai dai Mahmah ina son aikina saboda shine kawai abin da nake na samu nutsuwa a cikin zuciyata, wallahi Mahmah babu wani abu da yake bani farin ciki bayan aikina"
Shiru tayi tana datse bakinta dan kuka ne yake ƙoƙarin ƙwace mata mai ƙarfi.
"Zan haƙura da aikin Mahmah, zan zauna a gida idan har hakan zai saka ki farin ciki, amman dan Allah Mahmah kiyi min izini naje na ajiye aikin na dawo, nayi miki alƙawarin ko ƙofar gida bazan ƙara takawa ba, Mahmah na haƙura da abin da nake so fiye da komai idan har hakan shine burin ki, Mahmah wallahi na haƙura"
Wani irin kuka take har tana neman shiɗewa...
FULANI
***