NUFIN ALLAH

47

by @anisamuhammadyah897


💕 NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Page 4️⃣7️⃣


Amma na komawa gida bayan ta huta ta kira Ammi ta faɗa mata, hankalin ta ne ya tashi sosai dan ita ba ƙaunar fitina take ba

"Yanzu Juwaira ya za'a yi da wannan lamarin''
''ki kwantar da hankalin ki Adda in dai akan lamarin nan ne,Ahmad fah ɗa na ne, Faruq ɗan Adam ne kuma in dai Adam ne kin san halin shi sarai"

''Ai nasan da hakan shiyasa hankalin nawa ya ƙara tashi nasan halin ku sarai, ni ba so nake ayi wani tashin hankali a gaban yaran nan ba wallahi"
''indai haka ne Adda basai a maida su Kaduna ba, suje can wajen Anty Zuhura su zauna, kin ga sai a fara musu gyaran jikin su ma a can, indai abinda kike tsoro kenan"

''to amman dai gaskiya Anty bata kama girman ta ba ya za'ayi ta biyewa Abida bayan tasan ita ba hankali ta cika ba, suje suna zubar da mutuncin kansu a idon surukin su"

''ai Adda ba fa iya Abida bace duk haka suke su biyun dan da itama Anty tana da shi ai ba zata biye mata ba,yauwa Adda danAllah ki kira Munifah ki taushe ta ɗazu naga hankalin ta itama atashe sosai"

"Ba dole ba Juwaira, ƴanuwan ka fah, su ringa wannan abun kunyar gaban mijin ka, ƙari da wai akan ƴar ka wadda suma ƴa ce a gurin su, to Allah dai ya kyauta musu''
''ameen dai''

Tana komawa daƙin su ta shiga ranta a mugun ɓace maganganun Amra sun bala'in ɓata mata rai, shiyasa a ranta taji ko badan komai ba ma sai ta auri Yah Faruq Saidai ta mutu wallahi, saidai gani daga nesa dan ya mata nisa 

Wai an cusa mai ita kalmar nan tafi komi aciki ɓata mata rai, ita bata ce an cusa mata shi ba shine ita waccan ballagazar zata kalla tace wa mara class an cusa mai ita,

Wani irin haushin kanta ma ta fara ji da iya abinda ta faɗa mata kenan bata ƙara mata waɗansu ba, yarinyar da kowani gaja ma saurayin ta ne, aikin banza taja tsaki tana gyara kwanciyar ta, ji take kamar ɗazu ya sake dawowa ta faɗa mata maganganun da suka fi wannan, gani take ai bama ta yaɓa mata ko wani kalar magana ba ta ci bulus

Shigowa suka yi suna cigaba da abinda suka saba, banza ta musu dan bata cikin mood ɗin, dan haka tama kulle idonta gaba ɗaya 

Jalila ce ta lura kamar wani abu yana damun ta ko ya ɓata mata rai, a ranta tace "Allah sa ba ita da wadancan marasa hankalin bane''

Anty ke ta kwala musu kiran su fito suci abinci tunda sun dawo, Nabila da Fareedah da ne suka sauka, Jalila tace tana zuwa su fara gaba, ita kam gwanar ko motsawa ma bata yi ba

Zama tayi kusa da ita tace
"Pixie meya same ki'' 
Buɗe idon ta da yayi ja dan abin ya kona mata rai gashi bata gasa musu magana sosai ba kamar tana jiran dama ta tambaye ta tace

"Pickles wai ni waccan kucakar zata kalla tace wai banda class an cusa wa Ya Faruq ni"
"Wa kenan Amra??"
"Ehmana wai ni aka cusa wa shi kan bala'in can,ai wallahi pickles ko ba dan komai ba sai na aure shi taga cusa mai ni ɗin da kyau wanda ita bata samu darajar hakan ba, gwara ni da cusa mai ni akayi bani ke ƙoƙarin cusa kaina ba kamar ita"

''' kai sister a huce haka to ke wani amsa kika bata"
Faɗa mata yanda suka yi tayi ta ƙara cewa
"Ai naso abinda na faɗa mata yafi haka sai yanzu nake takaicin hakan''
''Ai pixie ko haka kika tsaya wallahi ya isa, iya wannan ma sai ya hanata rintsawa, dan haka ki kwantar da hankalin ki ki tashi muje muyi dinner"

''ohh wai shi yasa kike ta kumbure kumbure'' faɗin Fareedah da Anty da ba wani kuzari ne da ita ba itama sosai tace su dawo su kira su, tace su sakko duka bata son wannan se anjima ɗin nasu 

'' Wallahi sister ki kyale su suyi tayi, Saidai hange daga nesa sedai ko wani nufin Allah da zai sa a fasa amma karyar su wallahi, ai da ina jin tsoron Zulaiha akan ita ke son shi amman banda yanzu wallahi sedai duk ta fanjama fanjam"

Dariya suka kwashe da ita har Anisa jin yanda Nabila ke bala'i kamar ance mata ga Zulaihan aga ban ta 

"To sister duka ku huce haka, ai indai mazajen kune ku barsu baza su samu ba saidai ko ƙaddara ya riga fata su zama cowif.." Jalila bata ƙarasa magana ba Nabila ta bigi bakinta tana faɗin 
"Bala'in can ke kishiya tabb Allah ya kare ni tuf tuf tuf" tana wani tottofe jikinta 

Dariya suka ƙara saka wa Anisa tace
"Allah ya kyauta Miki Wallahi, ke kuma harma sun zama mazajen namu bamu sani ba"
"Ke kishiya fa Allah ya raba yanzu ku so kuke a muku ita?, ko basu zama ba sun kusa!! Na kusa zama cikakkiyar mallakin amadun sweet din shi"

" Daman Wake son ayi mai kishiya, amma kuma idan hakan kaddarar kace, sai ka roki Allah ya zaɓa maka mafi alkhairi kuma ya haɗa ka da ta gari, ba ƴar duniya ba dan ka samu irinsu ka gama yawo sedai idan kaima ɗan duniyar ne" faɗin Fareedah 

" Ke fa Peebles lamarin ki akwai gyara wallahi Allah ya kyauta miki ki ringa mana rashin kunya muraran, Nidai abar zancen kishiyar nan kuzo muje muci abinci,na gaji da zancen'' faɗin Anisa da jikin ta ya yi sanyin zancen kishiyar da suke faɗa, da ko kusa ko nesa bata fatan ta a rayuwarta, saidai idan Allah yayi kaddarar ta ce ta zauna da ita ya zata yi 


Kuyi following ɗina a arewapen 🥺 🥹 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 


______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺 
***