LOKACI CHAPTER 14
by @fulani32
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
Under Team Yota's Amazing Pen's.
SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️
FULANI 🤍
***
PAGE 1️⃣ 4️⃣
"Ba za ki ajiye aikinki ba Mamana, zaki ci gaba da abinki kinji dena wannan kukan" Baffa da shigowar shi kenan ya bata amsa yana share mata hawayen fuskarta.
"A'a Baffa na haƙura, farin cikin Mahmah shine nawa"
Ta bashi amsa cike da karyewar murya da ta zuciya.
Ita dai Mahmah tun maganar Baffa ta ɗauke kanta, dan yanzu ba wani shiri suke ba, tun da aka fasa auren Zahran, da kuma yan da abu kaɗan zai ambaci sunanta, tana ganin kawai ya juya mata baya ne saboda Zahra.
"Wuce ki tafi mamana"
Kasa tafiya tayi sai Mahmah da take kallo tana hawaye. Ita kuma ta ɗauke kanta kamar bata san ma da mutane a wajen ba.
"Maganar iya Mahmah kike ji banda ni ko?"
Kanta ta girgiza masa har lokacin kuka take kamar yarinya.
"Shikenan bara na kira Inna ta zo kawai" yayi maganar yana zaron wayarsa.
Kusan a tare suka kallesa, su duka.
"Malama ki wuce ki tafi ko kinji nace zan hanaki fita? Idan kuma sharri zaki min bismillah"
Juyawa tayi ta fice Baffa ya biyo bayanta, sai da ya saka ta, ta gyara fuskarta, sannan suka fito waje tare, suna tafiya ana nunata, amman ta nuna kamar batasan anayi ba, sai da ya kaita har titi ta hau napep sannan ya dawo gidan.
Tana zuwa ta zubawa wajen ido *Dara restaurant* ta maimaita sunan a zuciyarta, tsayawa tayi a ƙofar na ɗan lokaci, ta kalli wajen kamar wadda ta daɗe ba ta gan shi ba, duk da cewa, kwanaki huɗu ne kawai ta yi, ba tare da ta jeba, sai taji kamar lokaci mai tsawo ta ɗauka ba taje wajen ba.
Gyara rolling ɗin kanta tayi, sannan ta tura ƙofar ta shiga, babu mutane da yawa, reception ta nufa.
"Assalamu alaikum" tayi musu sallama.
"Wa'alaikumus salam" muryar ɗaya daga cikin ma'aikaciyar restaurant ɗin ta amsa, duk juyawa sukayi suna kallonta.
"Zahra!"
Ɗaya daga cikin su ta kira sunanta cikin farin cikin ganinta. Murmushi tayi mata ta amsa, dan yarinyar wani lokacin takanas take zuwa har kitchen wajenta.
"Kin dawo kenan?"
"Eh"
Ta ce "mun yi kewarki wallahi"
Dariya ta yi kaɗan "nima nayi kewarku"
Sai ta nufi kitchen, ta na shiga, ta ɗora apron ɗin akan kayan jikinta, wanke hannunta tayi sannan ta fara duba kayan da za su yi amfani da su na ranar.
Komawar ta bakin aiki ya sa zuciyarta ta samu wata iriyar nutsuwa, anan ne ta fi jin kanta, ba ta buƙatar ta yi maganar aure, ba ta buƙatar ta saurari maganganun Mahmah, sannan babu buƙatar ta yi tunanin abin da mutanen unguwa za su ce, a nan aiki kawai take yi, kuma hakan ya ishe ta.
"Zahra" kiran ya katse mata tunaninta, ta juya.
"Na'am"
Manager ne ya ce "ki taimaka mana da snacks ɗin nan kafin customer's su fara yawa, kwana biyu da bakyanan wajen duk sai a hankali"
"Okay" kawai ta ce, ba tare da ta bashi amsar waccan maganar ta sa ba.
Aikin ta fara cike da ƙwarewa, cikin sauri take haɗa abubuwan da take buƙata cikin tsari, ba ta kula da yadda wata ma'aikaciya ke ta faman kallonta tana murmushi ba.
"Wallahi Zahra, duk wanda ya ga yadda kike aiki zai san ke ƴar baiwa ce"
Murmushi ta yi mata tace ta gode.
"Da ace kina da naki restaurant ɗin da kin yi suna sosai"
Sosai maganar ta bawa Zahra dariya. "Nawa restaurant ɗin kuma?" ta tambayeta har lokacin da dariya a muryarta, abu ne da take ganin ba zai taɓa yuyuba.
"Ehmana"
Kanta ta girgiza ta tsagaita dariyar "Ni kam aikin nan kaɗai ya ishe ni" daga haka ta maida hankali akan aikinta.
Bata ɗauki wani tsawon lokaci ba ta gama. Ranar yini tayi tana aiki, 4pm na yi tayi musu sallama ta wuce, dan ba ta kai dare a wajen, saboda Mahmah ba zata amince ba, duk da farko basu yarda ba, amman da suka ga zata ajiye aikin dole suka barta.
Bayan ta koma ta samu Salmah ta dawo, wanka tayi da sallah sannan taci abinci.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, ba zata ce tana zuwa aiki Cikin nutsuwa ba, dan duk sanda zata tafi da maganar da Mahmah zata faɗa mata, sai dai ta miƙa wa Allah lamurran ta kullum cikin roƙonsa take, akan kar ya bari kalaman Mahmah su kamata ko suyi tasiri akanta.
Wannan kenan..
★★★★
ZAY'D..
Lokacin tafiyarsa gida ba tayi ba ya tafi, dan baya jin yana da nutsuwar zaman restaurant ɗin.
Kai tsaye rijiyar zaki ya nufa cikin g.r.a, a gaban wani ƙaton gida ya tsaya, horn yayi babu ɓata lokaci aka buɗe masa, danna hancin motar yayi ciki, ya jima a ciki kafin ya fito ɗauke da jakar laptop, sai wayoyin sa guda biyu a hannu, kai tsaye main gidan ya shiga, tun kafin ya ƙarasa ya ke jin hayaniya, gajeran tsaki ya ja, dan tun da ya ji haka ya tabbatar da yaran gidan suna parlown.
Ciki ciki yayi sallama, kamar yanda yayi tunani, suna zaune a gaban plazma suna buga p.s game, ko kula da shi ba suyi ba, waje ya samu ya zauna yana muzurai shi kaɗai.
Ƙarar takun takalmin da suka jine, yasa su dakatawa daga abin da suke, duk a tare suka juya, suka kalli benen da murmushi a fuskarsu.
"Oyoyo ammie na" suka haɗa baki wajen faɗa, da murmushi ta ƙarasa sakkowa saidai idonta ba'a kansu yake ba wani wajen daban take kallo.
"Zay'd" ta kira sunansa tana karantar yanayinsa.
Suma sai a lokacin hankalinsu ya kai kansa, yana zaune ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana danna waya.
Ɗagowa yayi ya kalleta ya kwaɓe fuska kamar ƙaramin yaro.
"Ammieey" yaja sunan nata.
Zama tayi kusa da shi ta shafa sumar kansa.
"Me ya faru? Wanene ya taɓa min babban mutum"
Baice mata komai ba sai lumshe idonsa da yayi.
"Barka da dawowa yaya zay'd"
"Sannu da zuwa brooo"
Suka furta a tare, buɗe idonsa yayi ya harare su ba tare daya amsa gaisuwar ba.
"Teemah kawo masa ruwa ya sha" ta ce ganin yanda tayi tsururu.
"Kai kuma khaleel bansan yaushe zaka dena biyewa Teemah kuna abu kamar yara ba, idan ita yarinya ce sai a kace kayi ta biye mata haba"
Kan sa ya shafa ya ce "toh ammie idan banyi wasa da ita ba, da wa zanyi, she's our little princess fa"
Kanta kawai ta girgiza, daman tasan sai ya nemi abin da zaice.
Su uku ne yaranta Zay'd ne babba, sai Ibrahim Khaleel, tsakanin Zay'd da Khaleel tazarar shekara shida ne, Zay'd yana da 35years, Khaleel kuma 29years, Sai Auta Fatimah, ita kuma yanzu ne take da 18years, har ta cire rai da haihuwa Allah ya kawo cikinta. A shekarar nan za tayi candy.
Khaleel yana aiki a Companyn babansu, saɓanin Zay'd da yake da Companyn kansa, da kuma restaurant, wanda a dalilin restaurant ɗin, ya samu matsala da mahaifinsa, dan yana ganin akan me zaice zai gina restaurant, bayan duk abin da ya mallaka, da kuma wanda su kansu iyayen su suka mallaka, sosai aka kai ruwa rana akan restaurant ɗin, dan kafin yayi Company restaurant ɗin ya so farayi, amman mahaifinsa ya hana sa, hakan yasa shi tsayawa tuƙuru har saida ya tsaya da ƙafarsa, ya gina nasa Companyn, sannan kuma ya cika burinsa, wajen gina restaurant ɗin, tana tuna rigimar da akayi akan sunan restaurant ɗin, wanda daga ƙarshe da ƙyar ta samu ya yarda ya haƙura da wancan sunan ya saka, sunansa a restaurant ɗin.
Sosai yaranta suke da haɗin kai, gaba ɗayansu ji suke da Teemah, mussamman Zay'd da shi ne ya raɗa mata suna, yanda yake ƙaunarta ma ɓata baki ne, babu abin da take nema ta rasa, dan ji suke kamar zasu mayar da ita ciki, Zay'd shine ya saka mata princess, har sunan yazo ya bita, shi ɗin ba mazauni bane, yafi zaman Abuja fiye da Kano, saboda harkokinsa sunfi yawa acan, amman duk abin da ya taso a restaurant ɗin sa baya wasa da shi, zai iya haƙura da komai akan restaurant ɗin nasa, wanda har yau basu san dalilin da yasa yake matuƙar ƙaunarsa fiye da duk wani abu daya mallaka ba.
Ajiye masa ruwan tayi sai ta zauna a wajen ƙafarsa, kanta da yake babu ɗan kwali yaja. "Ouch" ta ce cike da muryar shagwaɓa. Da ido yayi mata nuni akan ta je ta saka ɗan kwali.
"Yahh Zay'd!" Ta kira sunansa cike da marairaice fuska.
Bai amsa ba sai kallonta da yake.
"Wayana ne ta fashe" sai hawaye sharr ya biyo kan kumatunta.
Wayarsa ya ɗauka yayi danne danne. "Bro naga kasa min kuɗi" khaleel yayi maganar yana kallonsa.
"Ka ɗauketa kuje ka siya mata waya, kai ma idan kana buƙata ka canza, idan kuɗin bai isa ba ka kirani" wani irin ihu suka fasa a tare, da sauri ta faɗa kansa tana jera masa addu'a. Murmushi yayi ya janyeta daga jikinsa, Ammie ma albarka ta saka mishi.
Ya buɗe baki yana shirin magana aka turo ƙofar aka shigo, da sallama, dattijo ne da babu wani abu da ya raba sa da Zay'd sai furfura da kuma jikin manyantaka, gaishesa sukayi banda Zay'd da ya miƙe yana tattare abubuwansa zai bar parlown, sai da yazo giftasa sannan ya ce.
"Barka da zuwa" daga haka ya fice da sauri.
Duk binsa da kallo sukayi, banda shi, da ko amsa shi baiyi ba, sannu suka yi masa, sannan ko wannensu ya nufi ɗakinsa.
Fita yayi daga part ɗin gaba ɗaya ya nufi part ɗinsa dake cikin gida, ƙaton parlow ne, sai kuma 2 bedroom's da kitchen sai dianing area duka a parlown, ɗaya daga cikin bedroom ɗin ya shiga, kayan jikinsa ya rage, sannan ya shiga toilet, ya jima a ciki sannan ya fito yana ƙamshin shower gel, shiryawa yayi cikin kaya masu sauƙin nauyi, ya nemi waje ya zauna.
Gaba ɗaya ya rasa nutsuwarsa, akan maganar da yayi da manager ɗinsa, game da dara restaurant, sosai maganar take yawo a cikin kansa. Ba zai iya zuba musu ido su ci gaba da kwashe masa customer's ba, yana da abinyi da yawa a gabansa, amman bazai iya yinsu a yanzu ba, dole ya gama da matsalar restaurant ɗinsa, saboda baya wasa da duk wani abu da ya shafi wajen.
Zama yayi a gefen gadonsa, ya ɗora hannunsa akan goshinsa, yana nazarin matakin da ya kamata ya ɗauka, yana shirin yanke hukunci kenan, ƙarar wayarsa ta katse masa tunani, ɗaukar wayar yayi dan ganin mai kiran, baya wasa da wayar bussiness ɗinsa ko kaɗan.
*Manager Zay'd holding's Abuja*
Sunan ya bayyana a jikin screen ɗin, ɗaga wayar yayi.
"Hello" shiru yayi sannan ya amsa gaisuwar da akayi mishi, daga nan kuma ya tsuke bakinsa.
"Sir, akwai meeting na gaggawa a company, ana buƙatar kasancewarka a wajen"
Shiru yayi na ƴan daƙiƙu, duka kwanansa ɗaya da dawowa Kano.
"Yaushe" ya tambaya kamar baya so.
"Gobe idan Allah ya kaimu, mun riga da mun sanar da sauran shugabannin sassa, akwai wasu muhimman abubuwa da suke buƙatar amincewar ku"
Ajiyar zuciya ya sauke.
"Alright, prepare everything, zan zo" ya katse wayar.
Kallon agogon hannunsa ya yi, abu na farko ya na shirin mayar da hankali kan Dara restaurant, amman yanzu dole ya ajiye komai a gefe, Abuja ta kira shi, kuma dole ya amsa.
★★★
Da sassafe, Zay'd ya isa filin jirgi, baƙar suit ce a jikinsa, fuskarsa cike da kamala, hannunsa na hagu sanye da agogo, sai azurfa guda biyu da baya taɓa rabuwa da su, bayan ya shiga cikin jirgi ya zauna cikin nutsuwa, laptop ɗinsa ya ɗakko ya ajiye a gabansa.
Aike ya ke, duba wasu takardu yake da suka shafi, Zay'd Holding's, sababbin yarjejeniyar kasuwanci, rahotannin kuɗi, da wasu ayyukan da companyn nasa ke shirin ƙaddamawar wa, aikin yake cike da nutsuwa da ƙwarewa.
Ƙarfe 10 a cikin Zay'd Holding's tayi masa, babban gini ne, mai hawa uku, yana shiga ya samu ma'aikata da masu mu'amala da company na ta kai kawo, motarsa na tsayawa, ya fito cikin nutsuwa, kai tsaye cikin Companyn ya shiga cikin tafiyarsa, da kai tsaye zaka kirata da ta ƙasaita, sai dai ba haka bane, nutsuwar da take a tare da shi ne ake masa kallon haka.
Duk inda ya gifta miƙa masa gaisuwa ake, cikin girmamawa, bai wuce office ɗinsa ba, kai tsaye babban ɗakin da suke meeting ya nufa, da sallama ya shiga, duk miƙewa tsaye sukayi suna gaishesa, cikin girmamawa, da mutane a ciki, hakan yasa ya fahimci shi kaɗai ake jira, masu manyan hannun jari ne a cikin office ɗin.
"Good morning sir"
"Morning, Please have your seats" ya ce yana zama a kujerarsa. Manager sa ne ya matso ya kunna laptop ɗin da ke gabansa.
"Sir, mun kira wannan meeting ɗin ne, saboda akwai abubuwa uku da suka taso, wanda dole muna buƙatar amincewarka"
A hankali ya ɗaga kansa daga danna computer ya ce "go ahead"
Screen ɗin da ke gabansa ya danna.
"Na farko sabon project ɗinmu na real estate development, an kammala binciken wajen, kuma da buƙatar approval naka, kafin a fara construction"
Ɗaukar takardun dake gabansa yayi ya duba, ya ɗan ɗauki tsawon lokaci kafin ya ce "budget ɗin?"
"An shirya shi a nan sir" ya bashi amsa yana miƙa wasa wani file.
Duddubawa yayi na ƴan daƙiƙu, sannan ya ɗago ya ce "reduce unnecessary expenses. ina son quality a komai, amman ba na son a kashe kuɗi a inda ba dole ba ne"
"Yes sir ya amsa masa"
Ci gaba suka yi da tattaunawa, har suka kawo kan ƙarshen meeting ɗin, duk inda ya kamata ya saka hannu ya saka, bayan sun gama kowa ya fice, ya jima a ciki suna tattaunawa da manager shi, kafin ya tashi ya nufi office ɗinsa.
A ranar ya so komawa kano, amman haka bai samu ba dole ya zauna yana kula da abubuwan da suka shafi nan, aiki ya sha masa kai hakan yasa ya manta da komai aikinsa kawai yake.
Ranar da ya cika kwana 10, suka zauna da manager ɗinsa, dan jin abubuwan da suke tafiya, dan shi yana akan komai da ya shafi company da kuma restaurant, bayan sun gama tattaunawa, ya kula da magana a bakinsa.
"Uhm ina jinka?"
"Sir daman akan wannan document ɗin ne, da ya shafi Zay'd restaurant"
Daga jin sunan da ya ambata, ya dakata daga duk abin da ya ke ya mayar da hankalinsa kansa
"Me ya faru?"
Jin yanda yayi tambayar sai da ya ɗan dube sa, dan shi kaɗai ya san matsayin da restaurant ɗin ya ke da shi a wajensa, saboda ba iya manager ɗinsa bane, abokinsa ne koma ya ce amininsa.
"Ba wata babbar matsala ba ce Zay'd, ka kwantar da hankalinka, sales report na restaurant ɗin ne naga yayi ƙasa, kuɗin da yake shiga ya ragu sosai sai fita da ya ke, shiyasa nayi maka magana naji ko da akwai matsala ne"
Shiru yayi, sai kuma ya ce.
"Dara restaurant"
Da mamaki Sameer ya kallesa.
"Sunan restaurant zaka canza, ko kuma sabo zaka buɗe?"
"Bansaniba"
Murmushi yayi "nasan yanda kake son wajen nan kamar rayuwarka, dan haka faɗa min me yake faruwa da wajen namu"
Kamar bazai magana ba, sai da ya gama jan ajinsa ya ce.
"Tun da naje zuwan nan na ga akwai matsala, na bincika an kuma min bayani, na manta ne, amman kuma yanzu ka tuna min dole zan tafi kano a yauɗin nan"
Shi kaɗai ne yake fahimtar ɓacin ransa akan abu, koda fuskarsa bata nuna ba, bare kuma magana ake akan restaurant ɗinsa.
"Har yanzu baka faɗa min abin da ya ke faruwa ba"
"Imagine dude wai yarinya guda ɗaya ce, take neman ruguza min restaurant, taya za'ace, tafi kowa iya snacks da har manyan customer's ɗina zasu koma restaurant ɗin da take aiki, dole zan tafi, zan je naga wace ita, ya zama dole na ɗauki mummunan mataki akan ta, ba zan zuba mata ido ba, zan je wajenta a yau ba sai gobe ba......
FULANI
***