48
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 4️⃣8️⃣
Ammah, Anty ta ƙira ta sanar da ita yanda suka yi da Ammi, daman Ammi ta kira ta ɗazu tana kwantar mata da hankali
Itama Ammahn kwantar mata da hankali tayi ta ce
"Maybe zuwa gobe sai Ahmad ko Umar ya kai su Kadunan, nawa Anty Zuhura magana ma"
"To Adda Allah dai ya kyauta lamarin"
''ameen dai''
Wayar shi yake juyawa yana tunanin ya ƙira ta, ganin ya kasa deciding ya saka ya shiga Whatsapp, bata daɗe da ɗaura status ba
Veiwing yayi yana cewa a ranshi ''ashe dai tayi saving numbern na,to ko dame tama yi saving numbern??'' ɗan murmushin gefen baki yayi ya juya kwanciyar shi akan kujerar yana scrolling status ɗin nata amman yaƙi ƙarewa, reply ya mata a wani status ɗin ya cigaba da kallon status din nata kafin ya koma Instagram
Zaro ido tayi ganin ya mata magana, veiwing tayi taga yace
'' wai ke ba kya gajiya da saka status, wannan uban status kamar wadda zata tashi sama idan kazo ƙarshen shi''
Har zata yi reply sai kuma ta rasa abin da zama ta ce mai gashi tayi veiwing da ba haka ba ba zata yi reply din ba, kar yaga tayi veiwing bata mai reply ba nan ma ya zama laifi, kawai ta ce
'' Yah Faruq ina wuni ''
Ba wani jimawa yayi mata reply
'' lapiya''
'' madallah'' tayi saurin typing ta kashe datan dan ba so take maganar yafi haka tsawo ba
'' ba kuyi bacci ba har yanzu??'' faɗin Anty da ta shigo ɗakin yanzu
'' eh yanzu zamu kwanta''
Jalila dake kaƙƙabe gadon ta faɗa
'' ita kaɗai ke muku aiki kuna zaune yayar ku nayi, instead ku amsar mata ko''
Tashi suka yi suka fara taya ta, bayan sun gama ne tace
'' yauwa ku zauna magana za muyi daku''
Zama suka yi suka bata full attention suna sauraron ta, dan da alama maganar is very important
''An saka ranar auren ku Nabila da Anisa, nan da 1 month, so zaku koma gidan Anty Zuhura a Kaduna ku zauna har zuwa sanda za'a fara biki, gobe sai ku koma gidan Ammin ku Ahmad ko Umar zasu kai ku jibi''
Tun da ta kira 1 month taji duniyar ta ɗauke mata, ya tsaya cak, yayi kusa da yawa, ita da tayi tunanin irin sai nan da kusan shekara haka, za'a ce 1 month,
zuciyar tace tayi wani irin bugawa, anya zata iya, banda ''innalilahi wa inna ilaihir raju'un''
Ba abinda take faɗi a ranta, harta fara samun ɗan nutsuwa aranta, amincewa kawai tayi bawai dan tana da niyyar auren nan kusa ba, ba wai dan ta shirya wa hakan ba
Nabila kam farin ciki ne ya kusa kashe ta a zaunen da take, kanta ta sunkuyar ƙasa dan karma su haɗa ido da Anty har sai bayan da ta fita, ta saka musu ihun murna
''A gaishe ki Nabila, wannan uban ihun haka''
'' hmm barta pickles ai duk murnar an saka mata rana ne mai makon ta yi hamdala sai shashan ci, Allah ya sa Anty ta jiyo ki''
'' ba Ameen ba!!'' ta faɗa tana juyi
Ita dai Anisa jikin ta duk ya mutu, Jalila ce ta lura da hakan ta kama hannun ta ta ɗan mata murmushi, itama zuciyar ta ta danne ta kirkiro murmushin wanda da shi gwara ma kukan ta ta saki
Da safe bayan suna gama ma Anty duk ayyukan gidan, suka yi breakfast suka shirya baba habu driver yazo ya ɗauke su ya dawo da su gidan Ammi
Suna fitowa dashi ta fara arba, Nabila ce ta ɗan buga kafaɗar ta daidai yanda ita kaɗai zata ji tace
'' uhmm ga sanyin idaniyar ki ya fito kamar ya san kin ƙaraso''
'' to ya son ranki '' ta faɗa tayi gaba abin ta,
''Su Anisa an fara head da da ne sedai ki ringa wani ke ba kya so ko ki saka mun kuka yanzu har magana ake mayar ma mutane da shi''
'' da yake kuma nafi kowa iya hawaye akan wannan maganar zan fara miki kuka kamar mara aikin yi''
Gaishe shi sukayi suka shiga cikin gidan, Ahmad na zaune a parlour yana kallon football
''yaran Ammi kun dawo kenan''
Gaishe shi suka yi shima
Basu ga Ammi a parlourn ba, suka yi ɗaki, suna shiga suka ijje kayan su suka fita zuwa gaida Ammi
A kan dadduma suka same ta, bata dade da idar da Sallah ba ta zauna addu'a suka shigo, gaida ta suka yi ta amsa musu,tana tambayar su ya Antyn tasu take
Jalila ce tace
'' tana lapiya tace tana gaida ki ma''
''madallah ina amsawa''
''Ammi bara muje mu part ɗin mommy mu gaida ta'' faɗin Nabila
Part ɗin mommy suka je, suna shiga suka same ta a parlour, gashe ta suka yi, Anisa nata boɓɓoye wa bayan Fareedah, dan ita bata san me yasa ka kwanakin nan take jin nauyin da kunyar Mommy ba
Sun ɗan jima a part ɗin dan Mommy na da sakewa sosai, suka yi ta hira, ita dai duk a takure take jin ta, ko tambayar ta tayi sai ta sunkuyar da Kai
Sai da Mommy ta gaji da yanda take ƙunbiya ƙunbiyan tace
'' wai Anisa kunyar wa kike ji anan''
Reedah ce tace
'' probably ke mana Mommy, kin manta ko yanzu ke kin koma suruka''
Dariya suka kwashe da ita gaba ɗayan su, Mommy tace
'' auu wai yanzu ni kike jin kunya, to aini ke ƴata ce, shi ne suruki na'' tayi maganar tana nuna Umar daya shigo part ɗin Ahmad biye dashi a baya
Follow me on arewapen please 🥺 🥹 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***