KADDARAR ZUCIYA

RACING HOME

by @jiddaahbarkum

*KADDARAR ZUCIYA*

*CHAPTER TWENTY-TWO: 22*

*RACING HOME*

*JIDDAH BARKUM*

———

A daren ranar, abubuwa suka fara sauyawa cikin sauri fiye da yadda kowa yake zato, tun bayan maganar da Mommy Haleema ta yi da Alhaji Kabeeru game da komawa asibiti, yanayinsa ya ƙara sauyawa, gajiyar da yake fama da ita ta ƙaru, numfashinsa ya fara fita da wahala, sannan jikinsa ya yi wani irin rauni da ya sa ko ƙoƙarin tashi daga kan kujerar da yake zaune ya gagare shi, Mommy Haleema ta tsaya tana kallonsa, zuciyarta na bugawa da sauri, “Subhanallah!” Ta furta cikin firgici, tana matsowa kusa da shi, “Alhaji, me yake damunka haka?” Alhaji Kabeeru ya ɗago idanunsa a hankali, ya so ya yi mata murmushi domin ya kwantar mata da hankali, amma har murmushin sai da ya yi ƙoƙari kafin ya bayyana a fuskarsa, “Babu komai, Haleema, wataƙila gajiya ce kawai,” sai dai muryarsa ba ta da ƙarfin da ta saba ji a cikinta, numfashinsa yana fita a hankali, kuma a wannan karon, ko shi kansa ya kasa ɓoye yadda jikinsa ya raunana, Mommy Haleema ta girgiza kai, idanunta suka fara cika da hawaye, “A’a, Alhaji, wallahi wannan ba gajiya ba ce!” Ta ɗauki wayarta da hannu mai rawa, tana ƙoƙarin neman lambar ɗanta, “Zan kira Abubakar, dole ne mu je hospital yanzu,” Alhaji Kabeeru bai sake ƙoƙarin gardama ba, ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, kamar yana tattara ƙarfin da ya rage masa, cikin mintuna kaɗan, Yaya Abubakar ya iso gidan, da ya shiga falon ya hango mahaifinsa a zaune, fuskarsa ta sauya, ya ƙarasa kusa da shi da sauri, “Daddy!” Ya kira shi cikin tashin hankali, yana durƙusawa a gabansa, “Daddy, what happened? Me yake damunka?” Alhaji Kabeeru ya ɗago kai a hankali, “Babu komai, Abubakar,” amma wannan karon, ko ɗan murmushin da ya yi ƙoƙarin yi bai iya ɓoye gaskiyar da ke bayyana a fuskarsa ba, Abubakar ya kalli mahaifiyarsa, ta yi masa alamar cewa sun daɗe suna magana kan yadda jikinsa yake, amma yanayinsa ya ƙara tsananta, ba tare da ɓata lokaci ba, Abubakar ya taimaka wa mahaifinsa ya miƙe, sannan suka nufi motar da za ta kai su asibiti, Mommy Haleema ta bi su, zuciyarta cike da addu’o’i da fargaba, a duk tsawon tafiyar, tana zaune tana kallon mijinta, tana tambayarsa ko yana jin sauƙi, “Alhaji, kana jin sauƙi kuwa?” Ya ɗan girgiza kai, “Ki kwantar da hankalinki, Haleema,” amma wannan karon kalamansa ba su kwantar mata da hankali ba, maimakon haka, sai suka ƙara mata ciwo, domin ta san irin ƙoƙarin da yake yi na nuna kamar komai yana tafiya daidai, alhali jikinsa yana nuna mata wani abu daban, da suka isa asibiti, ma’aikatan lafiya suka karɓe shi cikin gaggawa, bayan dubawa, aka ba da umarnin a kwantar da shi domin a kula da yanayinsa sosai, Alhaji Kabeeru bai fita daga hayyacinsa ba, yana magana, yana gane mutanen da ke tare da shi, amma jikinsa ya yi rauni sosai, ciwon hawan jininsa da diabetes ɗinsa sun tashi fiye da yadda aka zata, nan take aka kai shi ɗakin da za a kula da shi, Mommy Haleema ta tsaya a wajen ƙofar, tana kallon yadda ma’aikatan lafiya suke taimaka masa, hawaye na zuba daga idanunta, a wannan lokacin, ta ji kamar komai ya tsaya, mutumin da ta saba gani cikin ƙarfi da nutsuwa, wanda ya kasance ginshiƙin gidansu tsawon shekaru, yanzu yana kwance a gadon asibiti, yana buƙatar taimakon wasu domin jikinsa ya samu sauƙi, ta dafe ƙirjinta, “Ya Allah, ka ba shi lafiya, ka bar min mijina, Ya Allah,” ta furta a cikin zuciyarta, tana ƙoƙarin danne kukan da ya ƙi barin ta.

Yaya Abubakar yana tsaye a wajen asibitin, wayarsa a hannunsa, fuskarsa cike take da damuwa, yayin da yake kallon mutanen da ke wucewa ta gabansa ba tare da hankalinsa ya tsaya a kansu ba, a karon farko cikin rayuwarsa, ya ji wani irin tsoro da ya kasa bayyana wa kansa, tsoron rasa mutumin da ya kasance inuwa ga rayuwarsu tun suna yara, mahaifin da ya kasance ginshiƙi, mai ba su kariya, mai jagorantar su, wanda ko da suna cikin damuwa, kasancewarsa kaɗai tana sa su ji cewa komai zai daidaita, amma yanzu fa? Wane ne zai iya tabbatar musu da cewa komai zai daidaita? Ya girgiza kai da sauri, kamar yana ƙoƙarin korar wannan mummunan tunanin daga zuciyarsa, “A’a, Ya Allah,” ya furta a hankali, “Ba haka ba, ka ba shi lafiya,” sannan ya fara kiran ’yan uwansa ɗaya bayan ɗaya, yana sanar da su halin da ake ciki.

A can Abuja kuwa… Yaya Umar ya gama wayarsa da Abubakar, a hankali ya sauke wayar daga kunnensa, amma hannunsa ya ci gaba da riƙe ta yayin da idanunsa suka tsaya a wuri ɗaya, fuskarsa ta canza gaba ɗaya, Nana, wadda take zaune kusa da shi, ta lura da yadda ya yi shiru kwatsam, ta ɗago kai ta kalle shi cikin damuwa, “Lafiya kuwa?” Umar ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, “Daddy ne,” Nana ta miƙe zamanta, “Me ya same shi?” “An kwantar da shi a hospital,” “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un!” Ta furta cikin firgici, tana kai hannu a ƙirjinta, Umar ya dafa kansa, ya yi shiru na wasu daƙiƙu kafin ya ci gaba da magana, “Abubakar ya ce hawan jini da diabetes ɗin sun tashi sosai, jikinsa ma ya yi rauni,” Nana ta zauna a hankali, tana ƙoƙarin karɓar labarin, “Allah Ya ba shi lafiya,” “Amin,” Umar ya amsa, sannan ya ɗan yi shiru, a cikin zuciyarsa, yana ƙoƙarin tsara abin da ya kamata ya yi, a wannan lokacin, babu wani abu da ya fi muhimmanci a gare shi kamar ganin mahaifinsa da kuma tabbatar da cewa yana samun kulawar da yake buƙata, bayan ɗan lokaci, ya ɗago kai ya kalli Nana, “In Sha Allah, gobe da safe zan yi sammako, first flight zan bi,” Nana ta gyada kai, “Ka je, Allah Ya ba shi lafiya, Ya kuma ba ku ikon kula da shi,” “Amin,” ba su san cewa akwai wani a kitchen da yake jin duk abin da suke faɗa ba, Inteesar, tana haɗa tea ne lokacin da maganar ta shiga kunnuwanta, da farko, ba ta fahimci abin da ta ji ba, ta tsaya cak, hannunta riƙe da cup ɗin, idanunta a kan teburin da ke gabanta, Daddy? Hospital? Kamar zuciyarta ta manta yadda ake bugawa na ɗan lokaci, cup ɗin da ke hannunta ya yi kamar zai zame, ta yi saurin riƙe shi da hannu biyu, “Daddy?” Ta furta a hankali, muryarta na rawa, sai wani irin tsoro ya mamaye ta, ta ajiye cup ɗin ba tare da ta kula da inda ta ajiye shi ba, sannan ta fito daga kitchen ɗin da sauri, idanunta sun riga sun cika da hawaye, “Yaya Umar…” Muryarta ta fito a raunane, ta sa Umar da Nana juyowa lokaci guda, “Daddy fa?” Umar ya tsaya yana kallonta, da ganin yadda ta rikice, sai wani irin ciwo ya soki zuciyarsa, ya san irin son da Inteesar take yi wa mahaifinsu, ya san yadda Daddy yake da matsayi na musamman a rayuwarta, kuma tunanin abin da wannan labari zai iya jawo mata ya sa ya kasa samun kalmomin da za su kwantar mata da hankali, “Intee…” Bai ƙarasa ba, domin a lokacin da ta ji sunansa kawai, ta riga ta fahimci cewa lallai akwai wani abu da ya faru, sai ta fashe da kuka, “Me ya same shi?” Ta ɗaga hannunta zuwa bakinta, tana girgiza kai, “Me ya sami Daddy?” Hawaye suka fara zuba mata ba kakkautawa, ta yi ƙoƙarin yin magana, amma muryarta ta ƙi fita yadda take so, Umar ya miƙe ya matso kusa da ita, “Intee, ki kwantar da hankalinki,” ta girgiza kai da sauri, “Yaya, please! Tell me what happened to him!” “Jikinsa ne ya tashi, an kai shi hospital, kuma likitoci suna kula da shi,” ya faɗa a hankali, yana ƙoƙarin zaɓar kalmomin da ba za su ƙara tayar mata da hankali ba, “Everything is going to be fine, In Sha Allah, addu’a yake buƙata yanzu,” amma Inteesar ta kasa samun natsuwa, “A’a…” Ta girgiza kai, tana share hawayenta amma sababbi na zubowa, “Ni ma zan je Katsina,” “Intee…” “A’a, Yaya Umar!” Ta katse shi cikin kuka, “Ba zan iya zama a nan ba, wallahi ba zan iya ba!” Ta matso kusa da shi, kamar tana neman taimakon da zai sa ta samu ƙarfin jurewa, “Please, Yaya, I need to see Daddy, ba zan iya zama a nan ina tunanin halin da yake ciki ba,” Nana ta matso ta rungume ta, tana shafa bayanta a hankali, “Ki kwantar da hankalinki, Intee, za mu je, ki yi haƙuri,” amma Inteesar ta ci gaba da kuka, tana girgiza kai a hankali, “Ba zan iya ba…” Ta furta cikin raunin murya, “Daddy na…” Wannan kalmar ta fito daga bakinta kamar tana ɗauke da dukkan tsoron da ta kasa bayyanawa, Umar ya runtse idanunsa, shi ma yana cikin damuwa, amma a wannan lokacin dole ne ya kasance mai ƙarfi domin ƙanwarsa, ko da kuwa shi kansa yana buƙatar wanda zai kwantar masa da hankali, “Za mu je, Intee, ba zan bar ki a nan ba, za mu je mu ga Daddy,” Inteesar ta ɗago kai ta kalle shi, idanunta cike da hawaye, “Da gaske?” Umar ya gyada kai, “Da gaske,” sai ta sake fashewa da kuka, amma a wannan karon ta yarda da shi, tana ƙoƙarin samun natsuwa daga kalamansa.

Daga baya a wannan daren, Inteesar ta kira Mommy Haleema, tun kafin Mommy ta gama amsa kiran, hawaye sun riga sun cika idanunta, “Mommy…” Muryarta ta karye, “My Princess,” Mommy Haleema ta amsa cikin sanyin murya, duk da cewa ita ma tana fama da damuwa, jin muryar ’yarta ta sa zuciyarta ta ƙara nauyi, “Ki kwantar da hankalinki, Intee,” “Mommy, please…” Inteesar ta kasa ci gaba, ta rufe bakinta da hannunta, tana ƙoƙarin danne kukan da ya ƙi barin ta, “Don Allah ki bar ni na zo,” ta furta a ƙarshe, “Ba zan iya zama a nan ba, I need to see Daddy,” Mommy Haleema ta lumshe idanunta, ta san halin ’yarta, ta san irin soyayyar da ke tsakaninta da mahaifinta, da yadda Inteesar take ɗaukar sa a matsayin ɗaya daga cikin manyan wuraren samun kwanciyar hankalinta, jin kukanta ya sa ta ji kamar tana tare da ita a ɗakin, tana son rungume ta ta ce mata komai zai daidaita, “To, Intee,” ta amsa a hankali, “Ki zo,” Inteesar ta ɗago kai, tana share hawayenta, “Da gaske, Mommy?” “Eh, my Princess, ki zo ki ga Daddy, amma ki yi ƙoƙarin kwantar da hankalinki, kin ji?” Mommy Haleema ta yi ɗan shiru, sannan ta ƙara da cewa, “Daddy yana buƙatar addu’arki, kada tsoro ya sa ki manta da cewa Allah ne Mai ba da lafiya,” Inteesar ta haɗiye wani sabon kuka, “In Sha Allah, Mommy,” “Allah Ya kiyaye hanya, ina jiran ki,” “Amin,” bayan sun gama wayar, Inteesar ta zauna na ɗan lokaci tana kallon wayarta, hawaye na gangarowa a fuskarta, amma wannan karon ta fara ƙoƙarin maida hankalinta kan shirye-shiryen tafiya, ba ta san irin yanayin da za ta tarar a Katsina ba, ba ta san abin da likitoci za su ƙara faɗa ba, amma ta san abu ɗaya, dole ne ta ga Daddy.

Bayan sun gama wayar da Mommy Haleema, wayar Inteesar ta sake yin ringing, Aliyu ne, da ta ga lambarsa a screen, sai ta ɗan yi shiru kafin ta ɗaga kiran, a ɗaya gefen wayar, Aliyu yana kwance yana duba wayarsa, fuskarsa cike da murmushi, “Intee!” Ya kira ta da muryar raha, “Inata kira, kina ta busy, ko dai da saurayinki kike magana ne?” Ya yi dariya da kansa, yana jiran ta yi wata magana ta shagwaɓa kamar yadda ta saba, amma ba ta amsa ba, shiru kawai ya ji, murmushin da ke fuskarsa ya fara gushewa, “Intee?” Ya sake kira, wannan karon cikin mamaki, sai ya ji muryarta, muryar kuka, nan take ya miƙe zaune, jikinsa ya yi sanyi, “Subhanallah!” Ya furta cikin tashin hankali, “Intee? What happened?” Ya matso da wayar kusa da kunnensa, kamar hakan zai taimaka masa ya fahimci abin da ke faruwa, “Please, talk to me, me ya faru?” Inteesar ta yi ƙoƙarin amsawa, amma kukan da ke cin ƙarfinta ya hana ta magana sosai, Aliyu ya yi shiru, yana sauraron ta, a wannan lokacin, bai sake yin barkwanci ba, bai yi ƙoƙarin tilasta mata ta yi magana da sauri ba, bai katse ta da tambayoyi marasa iyaka ba, ya bari ta yi kuka, ya ba ta lokacin da take buƙata, bayan ta ɗan samu nutsuwa, sai ta fara gaya masa halin da ake ciki, tana tsayawa lokaci zuwa lokaci saboda hawaye, da ta gama, Aliyu ya yi shiru na ɗan lokaci, zuciyarsa ta cika da tausayinta, da ace yana kusa da ita, da ya so ya zauna a gefenta kawai, ya ba ta damar yin kuka har sai ta samu sauƙi, amma a wannan lokacin, abin da yake da shi shi ne muryarsa da kuma kalaman da zai iya yi mata, “Intee…” Ya kira ta a hankali, “Hmmm…” Ta amsa cikin rauni, “Cuta ba mutuwa ba ce,” ya faɗa cikin nutsuwa, “Ki yi wa Daddy addu’a, Allah Ya ba shi lafiya, Ya tashi kafadun shi,” “Amin…” Ta amsa a hankali, “Ki zama mai haƙuri da dauriya, Intee, na san kina tsoro, kuma ba zan ce miki kada ki ji tsoro ba, saboda na san irin son da kike yi wa Daddy,” ta lumshe idanunta, tana sauraron sa, “Amma ki tuna, yanzu Daddy yana buƙatar addu’arki da ƙarfin zuciyarki, kada ki bar tsoro ya sa ki yanke ƙauna,” Inteesar ta share hawayenta, “Na ji tsoro, Aliyu,” kalaman sun fito daga zuciyarta, ba tare da wani ƙoƙarin ɓoye rauninta ba, “Na sani Intee,” muryarsa ta ƙara laushi, “Da ace ina kusa da ke, da na zauna a gefenki har sai kin samu sauƙi, amma don Allah, ki yi ƙoƙarin numfasawa a hankali, ki yi addu’a, ki tuna cewa Allah Ya fi mu sanin abin da ya fi alheri a gare mu,” ta rufe idanunta, tana ƙoƙarin bin abin da yake faɗa, “Everything will be okay, In Sha Allah,” kalaman nasa ba su kawar da tsoron da ke zuciyarta gaba ɗaya ba, ba su sa ta manta da cewa mahaifinta yana asibiti ba, amma sun ba ta wani abu da ta rasa tun lokacin da ta ji labarin, natsuwa kaɗan, wani ɗan haske a cikin duhun da ya mamaye tunaninta, wata tunatarwa cewa har yanzu akwai fata, kuma akwai Allah, “Na gode, Aliyu,” ta furta cikin sanyin murya, Aliyu ya yi murmushi, ko da yake ba ta gan shi ba, “You don’t have to thank me, Intee, I’m here for you, okay?” Inteesar ta yi shiru na ɗan lokaci, a wannan lokacin, ta fahimci cewa wani lokacin kulawa ba ta buƙatar kalmomi masu yawa, ba lallai ne mutum ya yi mata alƙawarin zai gyara komai ba, wani lokaci, jin muryar wanda yake shirye ya saurare ta kawai yana iya taimaka mata ta sake samun ƙarfin da take nema, “Okay,” ta amsa a hankali, “Ki huta kaɗan idan kin samu damar yin hakan, kuma ki sanar da ni idan kun tashi tafiya,” “In Sha Allah,” bayan sun yi sallama, Inteesar ta ajiye wayar a hankali, ta share hawayenta da bayan hannunta, sannan ta kalli sama, “Ya Allah, ka ba Daddy lafiya,” ta sake maimaitawa a cikin zuciyarta, domin a wannan daren, babu wani abu da take nema fiye da ganin mahaifinta cikin sauƙi.

Washegari da sassafe… tun kafin fitowar rana sosai, an riga an kammala shirye-shiryen tafiya, Umar, Nana da Inteesar suka kama hanyar zuwa Katsina cikin gaggawa, kowannensu yana ɗauke da nasa tashin hankalin, Nana tana ƙoƙarin kwantar da hankalin Inteesar, yayin da Umar ya fi mayar da hankalinsa kan yadda za su isa asibitin da wuri, Inteesar kuwa ta zauna tana kallon ta taga, idanunta cike da tunani, duk da cewa Aliyu ya taimaka mata ta samu ɗan natsuwa a daren jiya, zuciyarta ba ta daina fargaba ba, a duk lokacin da ta tuna da Daddy yana kwance a asibiti, sai ta ji wani irin nauyi ya sauka a ƙirjinta, ta ɗaga hannayenta a hankali, ta fara addu’a, “Ya Allah, ka ba Daddy lafiya, Ya Allah, ka sauƙaƙa masa, Ya Allah, kada ka rabani da shi,” hawaye suka gangaro daga idanunta, ta yi saurin share su kafin Nana ta lura, amma Nana ta riga ta gani, ba tare da ta ce komai ba, ta miƙa hannu ta riƙe nata, Inteesar ta juyo ta kalle ta, sannan ta matse hannunta sosai, babu wanda yake da kuzarin yin hira, sai addu’a, da kuma fargaba.

Da suka isa Katsina, kai tsaye hospital suka nufa, motar ba ta tsaya gaba ɗaya ba, Inteesar ta riga ta buɗe ƙofa da sauri, ta fito, ta fara tafiya da hanzari zuwa cikin asibitin, zuciyarta na bugawa da ƙarfi, “Daddy…” Ta furta a hankali yayin da take shiga, ta yi saurin zagayawa cikin harabar asibitin, tana ƙoƙarin gano inda iyalinsu suke, da ta isa wajen da aka kwantar da Alhaji Kabeeru, sai ta hango su, dukkan yayyenta suna nan, Abubakar yana tsaye kusa da ƙofar ɗakin, Adam yana zaune a kan kujera, yayin da Faisal da Salim suke can gefe, Khaleel ma yana nan, amma babu irin walwalar da ya saba nunawa, kowa fuskarsa cike take da damuwa, da ganin Inteesar, Adam ya miƙe tsaye, “Intee,” bai ƙarasa ba, domin Inteesar ta riga ta ƙarasa gare shi, ta rungume shi tana fashewa da kuka, “Yaya Adam…” Muryarta ta karye a kirjinsa, “Daddy fa?” Adam ya rungume ta sosai, yana shafa bayanta a hankali, “In Sha Allah, Daddy zai samu lafiya, ki yi haƙuri,” amma Inteesar ta girgiza kai, tana ƙoƙarin ɗago fuskarta, “Yaya, ina Daddy?” Ta kalli ƙofar ɗakin, sannan ta sake kallon ɗan’uwanta, “Ina son ganinsa,” Abubakar ya matso kusa da ita, “Princess,” ya kira ta da sunan da mahaifinsu ya saba kiranta da shi, jin sunan ya sa ta ƙara jin zafi a zuciyarta, domin a wannan lokacin, ta fi komai buƙatar jin muryar Daddy yana kiranta da wannan sunan, “Ki kwantar da hankalinki, Princess,” Abubakar ya ci gaba da magana a hankali, “Likitoci suna tare da shi yanzu, za mu jira su ba mu damar shiga,” Inteesar ta share hawayenta, sannan ta kalli fuskokin yayyenta ɗaya bayan ɗaya, sai a lokacin ta lura da yadda dukansu suka rame saboda damuwa, Yaya Faisal, wanda ya saba yin dariya a kowane lokaci, yanzu fuskarsa babu walwala, Salim ya yi shiru, idanunsa a ƙasa, har Khaleel, wanda kullum yake barkwanci da ƙoƙarin sa kowa dariya, yana zaune kansa a sunkuye, hannayensa haɗe a gabansa, babu wanda yake magana da yawa, babu wanda yake dariya, babu wanda yake ƙoƙarin yin kamar komai yana tafiya daidai, a karon farko a rayuwarta, Inteesar ta ga tsoro a fuskokin yayyenta, tsoron da suka kasa ɓoyewa, kuma ganin hakan ya ƙara tayar mata da hankali, domin idan har waɗannan mutanen da take ganin suna da ƙarfin jure komai sun shiga wannan yanayin, to yaya za ta iya samun ƙarfin da za ta jure nata tsoron? Ta runtse idanunta, tana ƙoƙarin daidaita numfashinta, Ya Allah, ka taimake mu, ta roƙa a cikin zuciyarta.

A gefe guda kuma, Mommy Haleema tana zaune kusa da ɗakin da aka kwantar da Alhaji Kabeeru, idanuwanta sun kumbura saboda kuka, fuskarta kuma ta nuna gajiyar rashin barci, tun da safe ba ta ci komai ba, ko yunwa da ƙishirwa ba su da wani matsayi a zuciyarta a wannan lokacin, addu’a kawai take yi, lokaci zuwa lokaci, sai ta miƙe ta leƙa cikin ɗakin, tana son ganin mijinta da idonta, ta tabbatar yana nan, yana numfashi, yana karɓar kulawar da yake buƙata, domin duk da shekarun aurensu, har yanzu zuciyarta ba ta iya jure ganin mijinta cikin ciwo, shekaru da dama sun haɗa su, sun yi dariya tare, sun fuskanci ƙalubale tare, sun gina gida da iyali tare, kuma a duk tsawon wannan lokacin, kasancewar Alhaji Kabeeru a gefenta ya zama wani abu da ta saba da shi har ba ta taɓa tunanin yadda rayuwarta za ta kasance ba tare da shi ba, yanzu kuwa, ganin sa a gadon asibiti ya sa ta fara fahimtar yadda tsoron rasa mutum yake da nauyi, ta ɗaga hannayenta ta sake yin addu’a, “Ya Allah, ka ba shi lafiya, ka mayar mana da shi cikin ƙoshin lafiya, Ya Allah, ka tausaya mana,” muryarta ta yi rauni, ta kasa ci gaba da addu’ar da ƙarfi, sai ta sunkuyar da kanta, tana share hawayenta.

Bayan kusan awa guda, babban likitan da ke kula da Alhaji Kabeeru ya fito daga ɗakin, nan take kowa ya miƙe tsaye, Abubakar ya ƙarasa kusa da shi, damuwa a fuskarsa, “Doctor, how is he?” Ya tambaya cikin rashin haƙuri, yana ƙoƙarin karanta amsar a fuskar likitan kafin ya yi magana, likitan ya gyara tabaransa, sannan ya kalli kowa cikin natsuwa, “Alhamdulillah, Alhaji Kabeeru yana amsar magani,” numfashin da suka riƙe ya ɗan sauka, Mommy Haleema ta ɗaga kanta da sauri, “Da gaske, Doctor?” “Eh, Hajiya, amma akwai abubuwan da muke buƙatar ku fahimta,” kafin farin cikin ya zauna sosai a zukatansu, likitan ya ci gaba da magana, “Yanayin hawan jininsa da diabetes ɗinsa ya tashi sosai, jikinsa kuma ya yi rauni matuƙa,” fuskokin kowa suka sake sauyawa, “Dole ne ya kasance ƙarƙashin kulawa ta musamman, za mu ci gaba da lura da yanayinsa, mu tabbatar da cewa yana samun magungunan da suka dace,” ya ɗan dakata, sannan ya ƙara da cewa, “Bayan ya samu sauƙi, zai buƙaci ya kula sosai da lafiyarsa, ya kamata ya guji gajiya mai yawa, ya riƙa shan magungunansa yadda aka tsara, kuma ya guji abubuwan da za su iya ƙara masa damuwa,” ya kalli ’ya’yansa, “Ku ma, ku taimaka wajen tabbatar da cewa yana samun isasshen hutu da kulawar da yake buƙata,” shiru ya mamaye wajen, Mommy Haleema ta dafe bakinta, tana ƙoƙarin hana sabon kuka fitowa, Abubakar ya runtse idanunsa, Adam ya sauke kansa ƙasa, yayin da Faisal ya jingina da bango, yana ƙoƙarin sarrafa tunaninsa, Umar kuwa ya lumshe idanunsa a hankali, “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un,” ya furta cikin raunin murya, sai Inteesar, da take tsaye tana kallon likitan kamar ba ta fahimci abin da ya faɗa ba, ta matso gaba kaɗan, “Doctor…” Muryarta ta fito a raunane, likitan ya juya ya kalle ta, “Eh, my dear?” Ta haɗiye yawu, idanunta suka cika da hawaye, “Ba zai mutu ba, ko?” Nan take wajen ya yi tsit, kamar kowa ya manta yadda ake numfashi na wasu daƙiƙu, Mommy Haleema ta rufe bakinta, sabon kuka ya ƙwace mata, Adam ya juya kansa gefe, yana ƙoƙarin ɓoye yadda tambayar ƙanwarsa ta karya masa zuciya, Abubakar ya runtse idanunsa, ya kasa kallon fuskarta, domin wannan tambayar ba ta fito daga son sanin makomar ciwon mahaifinsu kawai ba, ta fito ne daga tsoro, tsoron da ya mamaye zuciyar wata ’ya da ba ta shirya ko tunanin rayuwa ba tare da mahaifinta ba, likitan ya kalle ta cikin tausayi, “Ki kwantar da hankalinki, a yanzu yana amsar magani, kuma muna ci gaba da kula da shi sosai, amma yana buƙatar kulawa da hutu, za mu yi duk abin da ya dace domin taimaka masa, In Sha Allah,” ya ƙara da cewa cikin natsuwa, “Ku ci gaba da yi masa addu’a,” Inteesar ta girgiza kai a hankali, hawaye na gangarowa daga idanunta, “Okay…” Ta furta, amma muryarta ta nuna cewa zuciyarta ba ta samu cikakkiyar nutsuwa ba, kafin likitan ya juya ya tafi, ta riga ta durƙushe a hankali, jikinta ya kasa ɗaukar nauyin tsoron da ke cikinta, “Daddy…” Ta furta da raunin murya, “Daddy na…” Umar ya yi saurin kama ta daga gefe guda, yayin da Adam da Salim suka matso kusa da ita, Mommy Haleema ma ta ƙaraso ta rungume ’yarta, tana shafa kanta kamar yadda take yi mata tun tana ƙarama, “Ki yi haƙuri, my Princess,” ta rada mata a hankali, duk da cewa nata hawayen ba su daina zubowa ba, “Ki yi haƙuri, Allah yana tare da mu,” Inteesar ta rungume ta sosai, tana kuka a kirjinta, “Mommy, I can’t lose him,” kalaman suka fito a hankali, amma nauyinsu ya sa Mommy Haleema ta ƙara matse ta a jikinta, “A’a, Intee, ki yi addu’a, kada ki bari tsoro ya rinjaye ki,” ta shafa bayanta, “Daddy yana nan, za mu yi duk abin da za mu iya domin ya samu lafiya, kin ji?” Inteesar ta gyada kai a hankali, amma hawaye suka ci gaba da zuba mata, a wannan lokacin, babu wanda ya damu da yadda suke tsaye a tsakiyar harabar asibiti, babu wanda ya damu da mutanen da ke kallonsu, abin da suka sani kawai shi ne, a yanzu dukansu suna buƙatar juna.

A karon farko cikin shekaru masu yawa, iyalan Alhaji Kabeeru sun taru a wuri guda ba saboda bikin aure ba, ba saboda wata babbar nasara ba, ba saboda murna da walwala ba, sun taru ne saboda tsoron rasa ginshiƙin da ya haɗa su gaba ɗaya, mutumin da kasancewarsa ta zama wata al’ada a rayuwarsu, mutumin da suke komawa gare shi idan sun shiga damuwa, mutumin da ya koya musu cewa iyali ba wai jini kaɗai ke haɗa su ba, har da kulawa, sadaukarwa da kasancewa tare a lokutan da rayuwa ta yi musu tsauri, yanzu kuwa, su ne suke tsaye a gefensa, su ne za su kula da shi, su ne za su yi masa addu’a, kuma su ne za su yi ƙoƙarin zama masu ƙarfi, ko da kuwa zukatansu suna cike da tsoro, amma a ƙarƙashin wannan damuwa, akwai wata tambaya da babu wanda ya iya amsawa, me zai faru idan yanayin Daddy ya ƙara tsananta? Shin za su iya jurewa? Shin komai zai koma yadda yake a da? Ko kuwa wannan rashin lafiyar za ta zama farkon wani sabon babi a rayuwarsu? A wannan lokacin, babu wanda ya san amsar, abin da suka sani kawai shi ne, dole ne su kasance tare, domin a yanzu, fiye da kowane lokaci, suna buƙatar juna, kuma babu wanda ya san cewa wannan rashin lafiyar da ta taso za ta sauya abubuwa da dama a rayuwar kowa, ba a cikin gidan Alhaji Kabeeru kaɗai ba, har ma a zuciyar Inteesar.