THE WORDS OF A FATHER
*KADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER TWENTY-THREE: 23*
*THE WORDS OF A FATHER*
*JIDDAH BARKUM*
———
Likitan ya ɗan gyara tsayuwarsa, sannan ya kalli iyalan da ke tsaye a gabansa, “Za ku iya shiga yanzu, yana buƙatar ganawa da ku gabadaya,” da jin haka, Inteesar ta miƙe da sauri, ba tare da ɓata lokaci ba ta nufi ƙofar ɗakin, sauran ’yan uwanta suka biyo bayanta, kowannensu da zuciyar da ke cike da fargaba da tunanin abin da Daddy ɗinsu yake son sanar da su, Inteesar ta tura ƙofar a hankali, abin da ta fara hangowa shi ne mahaifinta kwance a kan gadon asibiti, jikinsa a raunane, fuskarsa babu walwala kamar yadda ta saba gani, hannunsa yana kwance a gefen jikinsa, idanunsa kuma suna kallon ƙofar da suka shigo ta cikinta, “Daddy!” Ta kira shi da muryar da ta haɗu da ƙugin kuka, ba ta jira wani ya ce komai ba, ta ƙarasa gaban gadon, ta riƙe hannayensa da duka nata hannuwan, sannan ta fashe da kuka kamar ƙaramin yaro, “Daddy, please…” Ta kasa ƙarasa abin da take son faɗa, kukan ya ƙwace mata magana, numfashinta yana fita da ƙyar saboda yadda zuciyarta ta cika da damuwa, Alhaji Kabeeru ya ɗago hannunsa a hankali, ya ɗora shi a kanta yana shafa gashinta cikin tausayi, “Princess, ki daina kuka, ki nutsu, magana nake son yi da ku gabadaya,” muryarsa ta fito a raunane, tana ɗauke da alamun gajiyar jiki da rashin lafiya, sai dai duk da raunin da yake ciki, ƙaunar da ke cikin kalamansa ba ta ragu ba, Inteesar ta ɗaga fuskarta, tana kallonsa ta cikin idanun da suka cika da hawaye, “Na daina, Daddy,” ta yi ƙoƙarin haɗiye kukan, ta goge hawayenta da bayan hannunta, amma wasu sababbi suka sake zubo mata, ya yi murmushi kaɗan, yana gyada kansa a hankali, “Good girl,” sannan ya ɗaga idanunsa ya kalli sauran ’ya’yansa da suka zagaye gadon, kowannensu yana tsaye cikin damuwa, wasu sun sunkuyar da kawunansu, wasu kuma sun kasa ɓoye yadda zuciyarsu take sukuwa, Alhaji Kabeeru ya yi shiru na ɗan lokaci, kamar yana tattara ƙarfin da zai yi amfani da shi wajen furta abin da ya daɗe a cikin zuciyarsa, ya ja wani nannauyan numfashi, sannan ya mayar da kallonsa kan Inteesar, “Ina son ku san ainihin labarin rayuwar gidan nan… lokaci ya yi da zan buɗe muku littafin baya, the untold history,” kalmominsa suka sa ɗakin ya yi tsit, babu wanda ya yi magana, ko motsin kujera ba a ji ba, kowa yana jiran abin da zai biyo baya, musamman Inteesar wadda har yanzu ba ta fahimci dalilin da ya sa Daddy ya kira su gabadaya ba, Alhaji Kabeeru ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, sannan ya buɗe su a hankali, “Na haɗu da mahaifiyarku, Hajiya Fateema, bayan mijinta na farko ya rasu, a lokacin, ta kasance matar da ta riga ta fuskanci ƙalubalen rayuwa, ta kasance da yara maza guda bakwai, waɗanda ta haifa da mijinta na farko,” ya ɗan dakata, yana kallon fuskokin ’ya’yansa maza, “Sun ɗan girma, suna da fahimtar abubuwa, ba ƙananan yara ba ne da ba za su iya gane abin da ke faruwa a rayuwarsu ba, a lokacin, Khalil shi ne ƙarami a cikinsu, yana da shekaru huɗu kacal a duniya, yayin da babban wansa, Khalid, wanda yake biye masa a wannan jerin shekarun da nake ba ku labari, yana da shekara takwas,” ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ci gaba, “Lokacin da na yanke shawarar aurenta, na yi wani alƙawari mai nauyi a gaban Allah, na yi alƙawarin cewa zan riƙe waɗannan yaran da gaskiya da amana, kamar ni ne na haife su,” muryarsa ta ɗan yi kauri, “Na ɗauki alhakin kula da su, ba don ina son burge mahaifiyarsu ba, ko don in nuna wa duniya cewa ni mutumin kirki ne, na yi hakan ne saboda na san waɗannan yaran amana ne a hannuna, kuma duk wanda ya karɓi amana, zai tsaya ne a gaban Allah a kan yadda ya kula da ita,” ya juya kansa kaɗan, yana kallon kowannensu, “Dukan yaran nan, tun daga Adam, Abubakar, Faisal, Jaafar, Alaamin, Khalil har zuwa Khalid, sun girma da sanin cewa ni ba mahaifinsu na jini ba ne, sun san komai tun suna ƙanana, sun san wanda ya haife su da kuma wanda ya aure mahaifiyarsu,” ya ɗan dakata, “Amma duk da haka, muka zaɓi yin shiru,” Inteesar ta ɗago kanta da sauri, “What?” Maganar ta kuɓuce mata a hankali, idanunta suka zaro cikin tsantsar mamaki, ta yi saurin kallon yayyenta ɗaya bayan ɗaya, tana neman wani abu a fuskokinsu da zai nuna mata cewa wataƙila ba ta ji abin da Daddy ya faɗa daidai ba, amma abin da ta gani ya ƙara girgiza ta, wasu daga cikinsu sun sunkuyar da kawunansu, wasu kuma hawaye suke sharewa a ɓoye, Alhaji Kabeeru ya lura da yanayin fuskarta, ya kalleta cikin tausayi, sannan ya ce, “Inteesar… ke kaɗai ce ba ki san wannan gaskiyar ba a cikin gidan nan,” ta ji kamar wani abu ya tsaya a maƙoshinta, “Ni kaɗai?” Ta maimaita kalaman a cikin raɗaɗi, kamar tana ƙoƙarin fahimtar yadda hakan zai yiwu, Daddy ya gyada kansa a hankali, “Mun ɓoye miki wannan sirrin ne saboda ba mu so ki taɓa jin wani bambanci tsakaninki da yayyenki, ba mu so ki girma kina kallon su a matsayin wasu mutane daban da ke, ko kina jin cewa ba cikinki ɗaya da su ba,” ya ɗan matse hannunta, “Shi ya sa na yarda har sunan mahaifinki ki dinga amfani da nasu, ba na son ki ga sunanki ya bambanta da nasu, ki fara tambayoyi ko ki fahimci wani abu, ina son ki girma kina jin cewa ku iyali ɗaya ne, ba tare da wani abu ya raba ku ba,” Inteesar ta zare hannunta a hankali daga cikin na Daddy, ba don ba ta son ya riƙe ta ba, sai don ta kasa sarrafa yadda zuciyarta take bugawa, ta kalli Yaya Adam, ya sunkuyar da kansa, yana share hawayensa, ta juya zuwa ga Yaya Abubakar, wanda shi ma ya kasa ɗago idanunsa ya kalle ta, ta sake kallon sauran yayyenta, dukansu suna cikin yanayin da ya nuna cewa wannan ba sabon labari ba ne a gare su, sun sani, sun daɗe da sani, ita kaɗai ce aka bar ta cikin duhu, “Why?” ta tambaya cikin raɗaɗi, “Me ya sa ba ku taɓa gaya mini ba?” Babu wanda ya amsa mata, sai muryar Daddy da ta sake katse shirun, “Kafin na auri mahaifiyarku, na yi aure-aure da dama a rayuwata, amma duk da haka, ban taɓa samun haihuwa ba ko ɗaya,” ya yi ajiyar zuciya, idanunsa suna kallon wani wuri da ya wuce su, kamar yana ganin hotunan shekarun da suka shuɗe, “Da lokaci ya ja, har na fidda rai gaba ɗaya da samun ɗan kaina a duniya, na rungumi ƙaddarata, na karɓi abin da Allah Ya ƙaddara mini, na ci gaba da rayuwa, ina ƙoƙarin ganin cewa na yi abin da ya dace a matsayina na miji da kuma uba ga yaran da na ɗauki nauyin rainonsu,” ya ɗan yi murmushi mai rauni, “Ban taɓa sanin cewa wata rana Allah zai ba ni wannan ni’imar da na daina tsammani ba,” ya lumshe idanunsa, muryarsa tana rawa, “Har a shekara ta huɗu da aurena da Fateema, Allah cikin ikonsa Ya ba ta cikin Inteesar,” da jin sunanta, Inteesar ta ɗago kanta, Daddy ya kalleta, kuma a wannan karon idanunsa sun cika da hawaye, “Princess ɗina… ba za ki taɓa fahimtar irin farin cikin da na ji ranar da na samu labarin cewa mahaifiyarki tana ɗauke da cikinki ba,” ya yi shiru na ɗan lokaci, yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa, “Na yi farin ciki da ba zan iya kwatanta miki shi ba, na ji kamar an ba ni damar sake fara rayuwa, bayan shekaru da dama da na yi ina tunanin cewa ba zan taɓa samun ɗan kaina ba, sai ga shi Allah Ya amsa mini addu’ar da na daina tsammani,” ya yi murmushi, amma murmushin ya dusashe nan take, “Sai dai a lokaci guda, na ji wani irin tsoro a raina,” Inteesar ta matso kusa da shi, “Tsoro, Daddy?” Ya gyada kansa, “Eh, Princess, a lokacin ina da shekara hamsin da biyar a duniya, na zauna ina tunani, ina tambayar kaina ko zan rayu tsawon lokacin da zan ga girman abin da za a haifa mini,” muryarsa ta yi rauni sosai, “Na tambayi kaina ko zan kasance a raye don in ba ki kariya, in riƙe hannunki idan kika fara tafiya, in ji muryarki kina kirana da Daddy, in ga kina girma har ki zama mace mai hankali da tarbiyya,” ya haɗiye yawu, idanunsa suka koma kan Inteesar, “Na ji tsoron kada na rasa damar kasancewa tare da ke, na ji tsoron kada Allah Ya ba ni ni’imar samunki, amma rayuwa ta hana ni ganin yadda za ki girma,” hawayen Inteesar suka sake zubo mata, “Daddy, please…” Ta sake riƙe hannunsa da ƙarfi, kamar tana tsoron kada ya ɓace mata idan ta sake shi, Alhaji Kabeeru ya shafa hannunta da babban yatsansa, “Ki saurare ni, Princess, labarin bai ƙare ba,” ya gyara kwanciyarsa a kan gadon asibitin, yana ƙoƙarin samun sauƙin numfashi, sai ya sake matse hannunta kafin ya ci gaba, “Bayan Allah Ya ba mahaifiyarki cikin nan, mun kula da ita sosai, ni da Hajiya Fateema mun ɗauki lamarin cikin nan da muhimmanci fiye da yadda za a iya bayyanawa, mun yi komai cikin taka tsantsan, saboda mun san irin darajar wannan ni’ima a gare mu,” ya juya kansa ya kalli Mommy Haleema, wadda ke zaune a gefe tana goge hawayenta da gefen mayafinta, “A lokacin, Haleema ita ce amintacciyar hadimar mahaifiyarki, her most trusted confidante, mace ce da Fateema ta amince da ita, wadda take kula da ita da gaskiya da riƙon amana,” Mommy Haleema ta sunkuyar da kanta, hawayenta suka sake zubo mata, Inteesar ta kalleta cikin mamaki, tana ƙoƙarin haɗa abubuwan da take ji da duk abin da ta sani game da iyalinta, Alhaji Kabeeru ya mayar da kallonsa gare ta, “Har Allah Ya sanya cikin ya yi girma sosai, dukan yayyinki maza sun yi ta farin cikin cewa za su sami ƙanwarsu, kowa addu’a yake yi a haifi ɗiya mace, saboda ba su da ’yar uwa mace a gidan nan,” ya ɗan yi murmushi, kamar yana tuna farin cikin yaran a wancan lokacin, “Dukansu suna ɗoki, kowa yana jiran zuwanki, everyone had so much love and expectations for the little princess who was about to join the family,” Inteesar ta kasa cewa komai, ta ji labarin haihuwarta yana fara buɗe mata wani sabon babi na rayuwarta, wanda ba ta taɓa sanin yana nan ba, Daddy ya sake ja wani nannauyan numfashi, “Wata rana, muna zaune da mahaifiyarki a falo, tana cin ɗanwake cikin jin daɗi, ni kuma ina gefenta ina ta tsokanarta saboda yadda cikinta ya yi girma sosai, har ya fito fili,” sai ya ɗan yi murmushi, “Abubakar yana durƙushe a ƙasa a gefenta, yana matsa mata ƙafafuwanta waɗanda suka ɗan kumbura saboda nauyin cikin, a lokacin, kowa yana ƙoƙarin ganin cewa Fateema tana jin daɗi, saboda ga matsu ya ga ta haihu lafiya,” murmushin ya ɓace daga fuskarsa, “Amma ba zato ba tsammani, sai Khalil ya shigo falon da gudu, yana kuka mai sauti,” ya dakata, kamar har yanzu yana jin sautin kukan a kunnuwansa, “Ƙanwata, Hajiya Maimuna, ce ta biyo bayansa tana ta faman faɗa da surutu, Maimuna mace ce mai tsananin masifa, ba ta da kirki ko kaɗan, kuma ita da Fateema ba su taɓa shiri da juna ba,” ya kalli yaran da ke tsaye a gabansa, “Tana baƙin cikin irin riƙon amana da soyayya da nake nuna wa yaran Fateema, a ganinta, bai kamata in riƙe yaran wani mutum kamar yadda zan riƙe nawa ba, ta kasa fahimtar cewa a gare ni, su ma ’ya’yana ne,” dukan ’ya’yan maza da ke cikin ɗakin suka sunkuyar da kawunansu, musamman Khalil, wanda sunansa aka ambata, ya kasa ɗago kansa, fuskar tasa ta nuna irin nauyin tunanin da ya dawo masa da wannan tsohon lamari, Alhaji Kabeeru ya ci gaba da labarin, “Maimuna ta tsaya a tsakiyar falon, ta fara jifan yaran da kalaman ɓatanci, ba ta damu da cewa yaran suna gabanta ba, ko da kuwa za su ji zafin kalamanta,” ya ɗan yi shiru, sannan ya maimaita kalamanta kamar yadda ya tuna da su, “‘Yara duk kun cika gida! Ku ba gidan ubanku ba! Ina aka taɓa ganin mace ta kwaso yara har guda bakwai, agololi, ta taho da su gidan mijinta? Mu dai gaskiya ba mu san irin wannan haukan ba sai da aka aure ki!’” Ɗakin ya sake yin tsit, Inteesar ta kalli yayyenta cikin tsantsar tausayi da firgici, ta kasa yarda cewa waɗannan mutanen da ta taso tana kallonsu a matsayin manyan ginshiƙan rayuwarta, sun taɓa zama yara da aka wulaƙanta saboda ba su da uba a gidan, ta ji wani irin zafi ya ratsata a zuciya, ta so ta tambaye su yadda suka ji a lokacin, ta so ta san ko sau nawa suka fuskanci irin wannan wulaƙancin, da kuma yadda suka iya ci gaba da rayuwa ba tare da barin kalaman mutane sun karya su ba, amma kafin ta samu damar cewa komai, Daddy ya ci gaba, “Mahaifiyarki, Hajiya Fateema, ta sunkuyar da kanta tana kuka, ta saba da irin waɗannan maganganun na wulakanci daga wasu cikin dangina, ta yi ƙoƙarin jurewa ne saboda ba ta son ta haifar da matsala a tsakanina da ’yan uwana,” ya yi ajiyar zuciya mai nauyi, “Amma a ranar, raina ya ɓaci fiye da yadda zan iya bayyanawa, I completely lost my temper,” ya ɗan motsa kansa a kan matashin gadon, “Na tashi tsaye da sauri, na nuna Maimuna da yatsa, na ce mata, ‘Maimuna, ki shiga taitayinki! Ban ja miki kunne a kan waɗannan banzayen maganganun naki ba? Sau nawa zan gaya miki cewa ba zan yarda ki wulaƙanta matata ko yaranta a gidana ba?’” Muryarsa ta ƙara kauri yayin da yake tunawa, “Na fara yi mata faɗa, inda nake shiga ba nan nake fita ba, na gaya mata cewa idan har ba ta da mutuncin da za ta girmama Fateema, to aƙalla ta girmama gidana da mutuncin da na ɗauka a kaina,” ya yi shiru na ɗan lokaci, “Amma duk da haka, Fateema tana zaune a wurin tana zubar da hawaye,” Alhaji Kabeeru ya kalli Inteesar, idanunsa cike da wani irin baƙin ciki da ya daɗe yana ɓoyewa, “Princess ɗina, akwai abubuwa da dama a rayuwa da ba ki sani ba, wasu daga cikinsu na iya sa ki yi mamaki, wasu kuma za su sa ki fahimci dalilin da ya sa iyalinki suke yadda suke a yau,” ya ɗan matse hannunta, “Amma ina son ki fahimci abu guda ɗaya: ba duk wanda ya haife ka ne yake nuna maka soyayyar uba ba, kuma ba duk wanda ba shi ne ya haife ka ba ne ba zai iya zama uba na gaskiya a gare ka ba,” ya juya kansa ya kalli ’ya’yansa maza, “Waɗannan yaran sun shigo rayuwata ne a matsayin yaran matata, amma a hankali, suka zama wani ɓangare na zuciyata, na raina su da gaskiya, kuma na so su gwargwadon abin da na iya,” sai ya dawo da kallonsa ga Inteesar, “Kuma ke, Princess, kin zo a matsayin amsar addu’ar da na daina tsammani, amma ba ki taɓa zama ke kaɗai ’yata ba a cikin wannan gida, tun kafin a haife ki, waɗannan yaran sun riga sun zama ’yan uwanki,” hawayen Inteesar suka zubo mata ba tare da ta iya hana su ba, a wannan lokacin, ta fahimci cewa abin da Daddy yake son gaya musu bai tsaya ga sirrin asalin yayyenta ba, akwai wani abu mai zurfi a cikin wannan labari—wani abu da ya shafi soyayya, amana, sadaukarwa da kuma irin ƙaddarar da Allah Ya rubuta wa kowannensu, ta sake riƙe hannun mahaifinta, ta sunkuyar da kanta a kansa, “Daddy…” Ta kira shi kawai, muryarta cike da ƙauna da raɗaɗi, shi kuma ya shafa kanta a hankali, “Ina sauraronki, Princess,” amma Inteesar ta kasa magana, domin a wannan lokacin, kalmomi ba za su iya bayyana yadda zuciyarta take ji ba, ta dai san cewa wannan labari zai sauya yadda take kallon abubuwa da dama a rayuwarta, kuma Daddy bai gama ba tukuna.