Chapter 5:
by @nasreelml
🌸🌹🌺FUREN ZUCIYA.
Flower of the heart.
By Nasreel R.L.
🤍A hausa love story…….
Chapter 5;
Sosai Hanat ke kallon Miral ganin yanda tsantsan kyanta ya fito. Wani bakinciki taji ya daki zuciyarta da saida idanunta suka rikida suka koma ja, gashi yanda Miral take cikin towel santala santalan sexy legs dinta duk a waje so nicely shaped ga manya manyan light brown eyes data waro mata tana kallonta tayi looking so bewitching.
Ajiyar zuciya Hanat tasaki tana jin yanda zuciyarta ke tafarfasa gashi Ummi tayi mata warning me tsanani akan dukan Miral, bakuma tasan meyasa Ummi zatayi mata hakan ba, dan a tunaninta kodan za’a mayar da ita gida Ghair Muaddal ne saidai kuma Layla ta fada mata babu wanda zai anshe ta koda an kawo ta. Sosai abun yaba Hanat mamaki gashi Ummi takasa gaya mata dalilin kawai dai tafada mata saboda ita takeyi sannan idan lokacin yazo zata gode mata dakanta.
Tuna hakan ne yasa ta kwantar da wutar bakin cikin dake ruruwa a cikin zuciyarta ta zayyanar ma Miral sakon da Ummi ta aikota dashi tana danasanin shigowa dama yar Aiki ta fadamawa. “Kallon uban me kikemun haka ne barauniya?”. Saurin sauke ido Miral tayi tana addua Allah ya rabata da Hanat lafiya batason a taba mata lafiyar jikinta yanzu.
“Ki hada e naki e naki gobe zamu wuce Ghair Muaddal, kiyi shigan arziki dama kan ace muna musguna miki, mai kama da maza kawai”. Ta fada tana kallon kirjin miral da yanzu yadan ciko bakamar da ba sannan ta juya ta fita tareda buga kofar shut a bayanta.
Miral dake kallon kasa jin ta fice yasa ta dago tanajin wani iri a zuciyarta takasa gane mema takeji. Wai gobe zasu koma Ghair Muaddal. Shin dadi takeji ne kokuwa tsoro ne, tanaso taji dadi da tasan yanzu komai ya nuna kanshi cewa dawoda ita gida za’ayi toh kenan sunaso tadawo tunda har Hanat tace tayi shiga mai kyau kada a gane ana musguna mata. Wani feeling ne ya mamaye zuciyanta mai kama da happiness da excitement, kenan sun yafe mata? Kodai sun gano gaskiya ne? Dama shiyasa Ummi tadawo da ita nan kenan ake bata ci da sha harda su supplements dan tayi kamar ana kula da ita?
Kara kallon kanta tayi a mirror a take kuma taji tanason tayi looking best dinta inzata koma. Kallon kurilla tayima jikinta saidai duk towel din yarufe komai babu abunda take gani sai chinyoyinta dayake mirror din ba har kasa bane. Zare towel din tayi a hankali tana kallon kofa kada a shigo daga ita sai wata half vest data gani a cikin suitcase din sai pants jikinta yaciko shima sosai ko ina yayi bul bul sosai shape dinta yakara fita waist dinta still so small and flat hips dinta da su sukafi cika a cikin jikinta da butt dinta so round and shapely shape yafito asalin pear dinshi dukda bawani kiba ne tayi ba.
Chest dinta ta kalla da shima yadan ciko amma ba sosai ba, ta tuna maganar Hanat wai mai kama da maza tasan da kirjinta takeyi, wani iri taji tuna yanda kirjin yanmata yake ita nata har yanzu kamar bazasuyi girma yanda ya kamata ba. Tunani takeyi kodai tasha supplements dinne tunda zai iya yuwuwa ne kiba ne dan boobs dinta su kara saidai kuma tasan batasan na menene ba bazatayi gangancin shaba.
Sakin towel din tayi gabadaya kawai ta wuce ta bude suitcase tafara daddaga abayoyin ciki. Luxury abayas ne irin wayanda Hanat kesawa, sababbi ne duka tabisu tana kallo daya bayan daya sosai sukayi mata kyau da batasan sanda wani smile ya bayyana a face dinta ba. Colors uku ne, wajen guda 8 black ne saidai kowanne design dinshi daban, guda 2 kuma pink sai 2 white.
Daya daga cikin black din ta dauko da aciki tafiyi mata kyau da haduwa sosai tasha beads akan embroidery design na jiki baiyi too much ba baikuma yi kadan ba. Camisole dake hade da kowanne abaya ta dauko na black din ta zura sannan ta zura abayan gudu-gudu tayi gun mirror tana kallon kata ba karamin kyau tayi ba sosai black din yayi complementing skin dinta.
Smile ne akan face dinta ear to ear data kasa boyeshi tayi sarin komawa ta dauki mayafin abayar ta daura a kanta tayafa shi. Sai kallon kanta takeyi ita kanta tasan tayi kyau tawani juya idanu tareda fashewa da dariya kawai hango kanta takeyi a Ghair Muaddal tareda familyn ta itama tazama kamar yanda su Hanat dasu solail suke. Tunani take inama da kayan makeup, da ko kwalli ne tasa.
Komawa tayi kan suitcase din pocket dabata ma lura dashi ba sai yanzu ta bude yan kayayyaki ne a ciki daga lip gloss sai kwalli sai scrunchies guda 3 na daure gashi basuda kauri sosai sai kuma set biyu na jewelry kana gani kaga pure gold ne guda daya dayen kuma silver chain ne mai wani diamond shape crystal da tana gani tasan diamond din gaske ne.
Ganin harda jewelries yakara tabbatar mata da lallai gida zata koma dakuma dukka alamu zasu karbeta. Face na layla ne ya fado mata arai kwatsam. Tunani takeyi shin zataga Layla a gidan? Sunanan har yanzu? Umm Layla ma nanan? Ko asirinsu ya tonu shiyasa akace a dawo da ita? Shin layla sunyi regretting abinda suka mata itada umm Layla? Ko za’a sata school itama su shiga tareda solail da Hanat University of Ghair Muaddal?
Ganin tunane tunanen Layla na neman fidda ita daga cikin farin cikin datake ciki yasa kawai ta cire abayar ta saka doguwan riga a jikinta ta koma gado tana sauke nunfashi duk wannan excitement din na fita daga jikinta dan duk yanda taso tacire tunanin Layla da Umm Layla takasa. Tana cikin haka bacci ya kwashe ta.
A bangaren Ummi kuwa sosai suke ta shire shirye itada Hanat datake jin kanta kamar zaiyi hayaki komai ya kwabe mata. Yau mijin ta MR. Omar Zolkrov watanta uku bataji daga gareshi ba, yadena daukar wayanta, data fara kiranshi da wayar Hanat ma saiya dena dauka saidai ya kira yarshi kawai da kanshi cikin dare ko idan tana school danma kada taganshi tayi mishi magana. Sosai abun ke damunta bawai yau suka fara fada a tsakaninsu yatafi yayi watanni baiyi mata magana ba baikuma dauki wayarta ko yabari ansan inda yake ba.
Saidai tana ji a jikinta wannan din na daban ne dan tasamu labarin a yanzu hakan yana Ghair Muaddal, sannan kuma an ganshi da wata yarinya wanda shine yafi daga mata hankali dan a duniya zata iya jure komai musammam ma akan mijinta Omar dan kodan yanda mutane a friend circle dinta suke zama jealous and pink with envy yanda tasamu miji mai kudi kamar Omar. Bawai su mazagen nasu basuda shi bane shi Omar yakai wani matsayi a duniya da kudi kadai bazai siya ba, dan haka dole duk yanda zatayi tazama ita kadai, sannan sucigaba da zama sai yanda takeso zatayi shi.
Babban tashin hankalin nata shine maganar tafito fili kafin mutanen dasuka yi mata alkawari guda Biyu kachal da bata bukatan wani abu bayansu na cewa mijinta zai zama nata ita kadai sai yanda tayi dashi ko yanaso ko bayaso kuma babu asiri ko laya dazasuyi anfani dashi a cewarsu sunfi karfin wannan.
Sannan kuma zasu mallaka ma Hanat Imad wanda bayan Crown Prince na Ghair Muaddal shine second in line to the throne.
Abu daya dayasa zuciyar ta ta kasa kwanciya dukda tasan lallai dole zasuyi mata hakan dan idan abunda ya wuce wannan ma zasu iya ba kananan mutane bane kungiya ce suke da ita babu Wanda yasan mesukeyi saidai ta gagari duniya da koda ansan abunda sukeyi duk wata kasa ko kungiyan security duk girmanta da shahara a duniya saisun shafe ta dan haka babu wanda yake shiga sabgar su.
Matsalar kawai shine sunkasa su fada mata yaushe ne takamai-mai zasu biya mata bukatunta. A cikin contract din sun bayyana cewa harsai sun dauki Miral zasu cika mata alkawarin dasuka dauka. Amma kenan yaushe ne zasu dauketa? Sunki fada. Gashi batada yanda zatayi tayi contacting dinsu.
Tunani takeyi shin mezasuyi ma Miral din? Saidai tasan batada ansar wannan kuma koda ta tambaya ba ansa mata zasuyi ba. Abu daya datasani wanda yaje baya dawowa duk rintsi ko tsiya shiyasa babu wanda zaizo yace ga abunda sukeyi, dan ba’ayi wanda ya shiga ya fito ba bare yafada abunda ke wakana a cikin kungiyar. Sannan bazaka taba cewa ga inda suke ba, basuda inda zaka duba kace anan suke. Shiyasa kamasu ma ba abunda zai yuwu bane.
Hanat dake dakinta bayan ta fita tabar Ummi tagama mata complain akan daddynta da ita ko a jikinta a cewarta matsalarsu ce ba nata ba sunsaba. gabadaya hankalinta nakan zuwa Ghair Muaddal gobe. Abubuwan dazatayi sai replaying dinsu takeyi akai kamar film hardaddiyar fuskar nan nata yau banda dariya babu abunda ke kanta.
Hango kanta takeyi gata ga Solail da Layla sun fara zuwa University of Ghair Muaddal. Ga classy rich girls like her da wanda suka fita suzama kawaye. Friends life, night parties, rich handsome boyfriends, girls night da duk batayi anan ba dayasa takejin nan din is boring dan duk ta raina yaran dasukeyin high school dasu shiyasa koda tayi graduating last year taki fara school ta dage saida Daddynta ya yarda taje Ghair Muaddal.
Bata kwasa komai ba dan tun achan tasa anyi mata shopping anyi stocking kayanta a gidan su Solail dan achan zata zauna Ummi dawowa zatayi. Tunanin Miral tafarayi, tunda itama gidansu zata koma kenan zai zama a gidansu Miral zata zauna kamar yanda itama Miral take a gidansu yanzu?. Wani iri taji a zuciyanta dan kwata kwata ganin Miral takeyi a matsayin kaskantacciyar baiwa da babu wanda keso dan haka kwata kwata bataji tanason zama a gidansu ba. Wata zuciyar ne tace mata ai koda a gidan su Miral din ta zauna tafi Miral matsayi dan Solail tafada mata bazasu karbeta ba.
Dan dariya tayi tuna yanda taga Miral dazu cikin farinciki. Tasan bazai wuce tana tunanin zata koma gidansu bane itama tazama classy gorgeous rich babe kamar ita da solail. Wani kwashewa da wata azzalumar dariya tayi tana hango fuskar Miral idan sukaje taga ba yanda tayi tunani bane.
Kan bed dinta ta fada tareda daukar latest iPhone dinta ta shiga Instagram ta dauki hoton freshly done nails dinta dasukayi tsawo da tsini kamar zatay dambe tayi caption ‘ Bye to my old life✌️’.
Ko 5min ba’ayi ba saiga likes da comments rututu kowa nason yaji metake nufi. Tanada wajen 10m followers a instagram kawai. Tana posting pics dinta sosai da lifestyle dinta datasan kowa na envying. Abunda yafi zama viral shine car collection dinta a cikin underground garage datake sa followers dinta su zabar mata motar dazata hau for the day.
Sosai takeson attention din da take samu a social media dan tana ganin yanda mutane keta tambaya tayi wani murmushin gefen baki aranta tana ayyana bazatayi posting wani abuba sai bayan two days dan tasamu comments dayawa na masu guessing mezai faru.
Call din daddynta ne yashigo wayarta, da mamaki take kallon call din na ringing dan sunyi waya jiya bawani waya sosai sukeyi ba. Gyaran murya tayi sannan ta tashi zaune ta dauki call din. Voice call ne a nutse tayi mishi sallama kamar ba Hanat ba.
Bai ansa gaisuwar ba ya tambayeta ina Ummi. Gaya mishi tana daki tayi voice dinshi sak na Hanat saidai kanaji kasan na miji ne. Ok ya ansa shiru baice komaiba harta zata ya kashe zata cire wayar a kunninta yace “Ki gaisa da new mom dinki”. Wani durum kirjinta yayi saida ta hadiya iska tama kasa ansawa.
Muryar dataji tashigo daga wayar yasa kanta bugawa. Aunty dinta, no. Cousin din mamanta dasuka dauka kamar Uwa. Magana takeyi amma kwata kwata Hanat takasa ma gane metake fadi. Muryar daddynta dataji yasata dan dawowa daidai yana tambayanta meya faru. Ba komai tace mishi tabashi hakuri kawai ta kashe wayar ta mike da gudu ta fita daga dakin sai dakin Ummi.
[tohfah guys. Mekuke tunanin zai faru? Wannan wani irin set up ne mijin Ummi zai auri cousin dinta? Shin Ummi zata bar hakan ta faru kuwa?].
For more information, contact me via WhatsApp on ***.