THE MISSING KEY
BALARABE MANSION
Hasken rana ya ratso ta cikin manyan windows din gidan, yana haskaka tsofaffin takardun da aka shimfiɗa a kan table din da ke tsakiyar parlorn, Mammi tana zaune a kan kujera, A gabanta tsofaffin envelopes ne masu launin ruwan kasa, wasiƙu da suka fara dusashewa, tsofaffin copies na takardun company, da wasu takardu da Hajiya Raliya ta samo daga hannun tsoffin ma’aikatan Northern Crest Holdings da tayi contacting
Duk da kwanakin da suka shafe suna bincike, tambayoyi se ƙara yimusu yawa sukeyi, maimakon su ragu.
Hajiya Raliya ta juya wata takarda da ke hannunta sannan ta tsaya
“Mammi, kin tuna inda kika ajiye keys din ƙofar garden din nan?”
Mammi ta ɗago kai.
“Jiya na fara dubasu ban gani ba, amma ynzu na tuna inda nike ajiye duk wasu makullai da bana amfani dasu, bari inje in duba su a chan”
Ta miƙe ta nufi ƙaramin ɗakin ajiyar kaya da ke kusa da tsohon study office din Alhaji Rahman, dakin cike yake da kwalaye da dama da suka kwashe shekaru ba a taɓa su ba, ta fara bincike a tsakanin tsofaffin tarkace, har ta samu Daga ƙarshe hannunta ya kai ga wani ƙaramin akwati na katako, ta dauko shi Ta buɗe shi.
A ciki akwai tsofaffin makullai dayawa, ta fara duba su a hnkali har ta kai ga Wanda take nema, ta gane su tsab duk da an dauki kusan shekara biyar, tana tuna yadda suke saqale da key holder din mijinta a koda yaushe
Ta yi murmushi a hankali.
“Ga shi nan.”
Ta ɗauko shi, ta fara ƙirga su don ta tabbatar ko sune
“Ɗaya… biyu… uku… huɗu… biyar.”
Sai ta tsaya.
Ta sake ƙirgawa.
“Ɗaya… biyu… uku… huɗu… biyar.”
“Mammi?” muryar Raliya ta shigo daga bakin ƙofar ɗakin. “Kin gan shi?”
Mammi ba ta amsa nan take ba, ta zuba wa maɓallan ido.
“Raliya”
“Naam Me ya faru? Baki gani ba?”
Mammi ta miƙa mata zoben makullan
“Kin tuna wa’innan makullan da margayi ke yawo dasu koina? Zaki iya tuna ko guda nawa ne?”
Raliya ta duba su da kyau.
“Shida ne, idan ban manta ba, me ya sa kika tambaya?”
“Saboda yanzu guda biyar ne kawai.”
Raliya ta karɓe su ta duba dakyau, lallai sune, kuma zata iya tuna guda shida ne
“Kin tabbata shida ne?”
“Na tabbata, Rahman da kansa ya taɓa nuna min su, har yana chewa ze raba su zuwa wurare shidda daban daban
“To, akwai wanda ya ɗauki ɗaya kenan.”
Mammi ta kalle ta.
“Amma wa zai ɗauki mukulli daga cikin kayan Rahman? Kuma don me?”
Babu wanda ya iya amsa wannan tambayar cikinsu
Daga bisani, Raliya ta furta abin da ya sa zuciyar Mammi ta fara bugawa da sauri.
“Kila akwai wani da ke neman abnda muke nema a cikin wannan dakin”
Mammi ta girgiza kai saboda tabbacin ba wanda yasan inda wa’innan makullan suke se dan gida
ƙofar da Rahman bai taɓa wasa da makullanta ba, kenan wani yasan akwai wani abu a dakin?
Ƙofar da ynzu suke zargin tana da alaƙa da wani file da suke nema
“Raliya,” Mammi ta furta cikin rauni, “menene ainihin abnda mijina ya bari a baya? Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un, bnso ache akwai wani hakki akanshi da bamu sauke mishi ba”
Raliya ta sake kallon makullan
“Wannan shi ne abin da ya kamata mu gano.”
Amma cikin su babu wanda ya san cewa tsawon shekaru biyar, wani daga cikinsu yana ta neman abnda suke nema, sedai kowa da tashi manufar.
Da yamma, Hajiya Raliya na zaune cikin motar ta, a gaban wani office
Ta kwashe kwanaki biyu tana ƙoƙarin ganin wani tsohon ma’aikacin Northern Crest Holdings mai suna Malam Nuhu Garba, shine ya fara aiki a sashen adana takardu a lokacin da Alhaji Rahman Balarabe da Alhaji Bashir Misalati suka fara tafiyar da harkokin kamfanin
Da farko, har Nuhu ya amince zai gan ta, amma da safe ya kira ta yache ya fasa
Abnda kawai yache mata a waya shine
“Don Allah, Hajiya, ki bar wannan magana. Ba zan iya taimaka miki ba.”
Raliya ta fahimci tsoro a cikin muryarsa.
Saboda haka ta yanke shawarar zuwa ta gan shi da kanta.
Bayan kusan mintuna ashirin, sai ta gan shi yana tahowa zuwa ƙofar ginin. Wani mutum ne mai kusan shekara sittin da biyar, gashinsa yayi furfura, fuskarsa kuma tana nuna alamun tsufa. Da ya hango ta, sai ya tsaya cak
“Hajiya Raliya?”
Ta fito daga motar.
“Naam Malam Nuhu, gani nazo da kaina
“Ban fah ce zan taimaka miki ba,” ya amsa a hankali. “Na gaya miki cewa ba zan shiga wannan magana ba.”
Raliya ta nazarce shi dakyau
“To, me yasa ka tsaya ynzu kana magana dani?”
Ya duba gefen titi kafin ya amsa.
“Kawai don in gaya miki ki daina nemana.”
“Ko kuma in daina neman gaskiya kake nufi?”
Ya matse bakin shi da hannun shi
“Hajiya, ba ki fahimci irin abin da kike nema ba inaga”
“To, ka taimaka min in fahimta.”
Ya girgiza kai.
“Wasu abubuwa ya kamata a barsu su wuche kawai”
Raliya ta matso kusa da shi, ta rage sautin muryarta.
“Alhaji Bashir Maisalati ya rasu ana zargin sa da laifin da wataƙila bai aikata ba. Ɗiyarsa ta ɓace a lokacin da take neman gaskiyar abin da ya faru da shi. Yanzu kuma ana aika ma matar margayi Rahman messages na barazana, ta yaya za ka ce a bar maganar?”
Da ta ambaci Aisha, Nuhu ya tsaya cak, gumi ya fara feso mishi
Raliya ta lura.
“Ka sani ai, ko ba haka ba?”
Ya kau da kansa.
“Na san Aishatu sosai” ya fadi a raunane
“Ta taba tuntubar ka?”
Ya yi shiru na wasu daƙiƙu.
Sai ya juya ya nufi cikin ginin office din
“Ba a nan ba, shigo ciki muyi magana”
Suka shiga wani ƙaramin office ba kowa a ciki. Nuhu ya rufe ƙofar, amma ya tsaya a tsaye ya fara magana
“Shekaru biyar da suka wuce,“na yi wani abu da har yanzu nake nadama.”
Raliya ta qara maida hankalinta gareshi
“Lokacin da Alhaji Rahman ya fara rashin lfya har ta kaishi kwanche sosai kafin ya rasu, Northern Crest Holdings an fara fuskantar wasu matsaloli, akwai wasu kuɗaɗen da ba a iya bayyana inda suka tafi ba, akwai lambobin kuɗi da aka canja, da wasu biyan kuɗi da ba su dace da bayanan kamfanin ba, Alhaji Bashir ne ya fara lura da matsalar.”
“Wa yake da hannu a ciki?” Raliya ta tambaya.
Nuhu ya goge tafin hannuwansa.
“Ba zan iya gaya miki duk abin da nake zargi ba tare da nuna miki sheda ba, amma zan iya gaya miki cewa Alhaji Bashir ba shi ne mutumin da ya sachi kuddin nan ba”
Raliya ta matso kusa da shi.
“To, me ya sa kowa ya gaskata cewa shi ne ya sace kuɗin?”
“Saboda wani yasa an fitar da bayanan company da suka nuna wata magana ta daban wadda ba gaskiya ba”
Ya yi shiru na ɗan lokaci.
“Lokacin da Bashir ya fara binciken sashen kuɗi, sai wasu takardu suka bayyana kwatsam, suna nuna kamar an tura kuɗaɗen kamfanin bisa umarninsa, mutanen da ba su taɓa shakkarsa ba suka fara zarginsa, Wasu ma’aikata suka tsorata saboda sun san tun lokacin da aka assasa wannan company din Bashir ke aiki a nan, duk wani ma’aikaci a nan ya tarar dashi, wasu kuma sun san gaskiya amma suka zaɓi su kare ayyukansu maimakon su faɗi abin da suka sani.”
“Kai fa?” Raliya ta tambaya.
Nuhu ya runtse idanunsa.
“Nima ina cikin wa’inda sukayi shuru saboda su tsira da aikin su”
Fuskar Raliya ta nuna takaici.
“Ka san ba shi da laifi amma kai shuru?”
“Na san akwai abin da ba daidai ba. Amma a lokacin ban da cikakkiyar hujjar da za ta nuna wanda ya aikata hakan. A lokacin da na fara fahimtar girman matsalar, Alhaji Rahman ya riga ya yi nisa da rashin lafiya sosai.”
Muryarsa ta yi rauni.
“Daga baya Alhaji Rahman ya rasu, komai ya canja, dama shine mutumin da muke jira yaji saukee don munsan ze iya kare Bashir
Raliya ta ji wani sanyi ya ratso jikinta.
“Aisha fa? Me ka sani gameda ita?”
Nuhu ya zauna a hankali jiki a sanyaye
“Ta zo wurina lokacin da ta fara aiki tare damu. Ta roqeni akan taji anche ni tsohon ma’aikaci ne, kuma tana binciken takardun kamfanin ne saboda tayi imanin cewa an ƙulla wa mahaifinta makirci, kuma tana son gano ainihin abnda ya faru da har ya rasu duniya tana zargin sa”
“Ka taimaka mata?”
“Da farko, eh.”
Ya kalli Raliya da idanun shi da ke cike da nadama.
“Na gaya mata cewa akwai wata yarjejeniya ta asali tsakanin Alhaji Rahman da Alhaji Bashir amma dai bnsan ko yarjejeniyar micece ba, na gaya mata cewa ba bayanan da aka adana a company dinnan ne kaɗai suka dace a dogara da su ba, saboda a gaskiya duk anyi forging dinsu, Na yi alƙawarin bincika tsofaffin takardu domin in nemo mata abin da zan iya,
“Daga nan se me ya faru?”
Nuhu ya haɗiye yawu.
“Daga nan tache min zata binciko gaskiya, tache min zata fara binciken family din Balarabe don alamu sun nuna mata sharrin da akayima babanta a chan ya fara, shine maganar qarshe da mukayi da ita, daga nan..daga nan..ta ɓace” ya qarashe a raunane
Raliya ta matse hannayenta.
“Me kake nufi da ta ɓace?”
“Ina nufin daga nan bata sake kirana ko tazo wurina ba, kuma na kasa samun ta a waya, kamar ma wayarta ta daina aiki, se naji anche wai ta bache”
“Ka kai report zuwa police ko wani wuri?”
“Na yi ƙoƙarin bincike a hankali saboda inajin yarinyar kamar diyata kuma alh Bashir mutumin kirki ne, amma sai aka fara yi mini gargaɗi da barazana a waya. Ana gaya min in daina shiga maganar idan ina son iyalina su zauna lafiya.”
Ya girgiza kai.
“Na ga abin da ya faru da mahaifinta, saboda inada tabbacin hatsarin nan shirya shi akayi, na ga yadda aka maida mutumin kirki wanda ya taimaka wajen gina kamfani zuwa wanda ake zargi da cin amana, sai ga ɗiyarsa ma ta ɓace bayan ta zo wurina.”
Ya ɗaga idanunsa zuwa ga Raliya.
“Ina da yara nima, Hajiya. Ban so in jefa su cikin haɗari”
Raliya ta yi shiru na ɗan lokaci, fushinta ya lafa kaɗan, amma takaicinta bai gushe ba.
“Saboda haka ka bar gaskiya a binne.”
Nuhu ya sunkuyar da kai.
“Hakane”
Wannan amsa guda ɗaya ta ɗauki nauyin shekaru masu yawa na nadama.
Raliya ta buɗe jakarta, ta fito da copy din wata tsohuwar takarda
“Ka taimaka mana yanzu.”
Nuhu ya kalli takardar amma bai karɓa ba.
“Ban san ko zan iya ba.”
“Ba na neman ka faɗi abin da ba ka da hujja a kai, ka karanta wannan ka gaya min abin da ka sani, ka ba mu duk wata shaida in har kanada ita, Idan ka ci gaba da yin shiru, waɗanda suka aikata wannan abu za su ci gaba da ɓoye gaskiya.”
Ya dube ta na dogon lokaci.
A ƙarshe, ya tambaya, “Akwai wasu da suke qoqarin bincike ne a ynzu?
“Eh.”
“Su waye?”
“Maryam Maisalati qanwar Aisha, da mijinta, Zaid Balarabe, sun fara bincike gameda file din da ya ɓace, Ni da Mammi ma mun fara bincike.”
Fuskar Nuhu ta canja a take
“Kenan abin yana sake faruwa.”
“Me kake nufi?”
Ya miƙe, ya nufi window ya bude kamar iska baya isar shi
“Neman ainihin yarjejeniyar.”
Sai ya juyo gare ta.
“Ki saurare ni da kyau, Hajiya. Takardun kamfanin da kuke bincike ba lallai su tabbatar da gaskiya ba, akwai ainihin takardu da aka rubuta aka kuma sa hannu a kansu tun kafin a assasa kamfanin . Idan ɗaya daga cikin waɗannan takardu har yanzu tana nan, to za’a iya gane dalilin duk wannan abun”
Zuciyar Hajiya Raliya ta fara bugawa da sauri.
“Ina ainihin takardun suke?”
“Ban san inda suke yanzu ba. Amma na tuna Bashir ya taba gayamin cewa an yi copies uku. Ɗaya ya kasance a hannun Alhaji Rahman, ɗaya a hannun shi, ɗayan kuma a hannun lawyer dinsu
“Wanene lawyer din?”
“Barrister Mahmud amma ya rasu”
Hajiya Raliya ta gane shi. Lauyan ya rasu shekaru da suka wuce tun kafin rasuwar alh Rahman
“Me ya faru da copy din da hannun lawyer din?” Ta tambaya saboda tasan ga dukkan alama na hannun alh Rahman da alh bashir sun salwanta
“Ban sani ba. Bayan rasuwar shi, an rufe office dinshi, aka rarraba takardun da ke ciki bisaga yadda rubutun sunan kowa yake a jikin takardun su, na ji cewa an mayar da wasu takardu hannun Alhaji Rahman, saboda a office aka kawo aka bashi, amma ba zan iya tabbatar da cewa yarjejeniyar tana cikinsu ba.”
Raliya ta fara tunanin ƙofar nan ta garden, kodai a ciki ya ajiye su?
“Hajiya, ki fahimci cewa mutumin da kuke nema yana iya kasancewa cikin iyalinki don haka kiyi takatsantsan”
Raliya ta zuba masa ido.
Kafin ta iya tambayar wani abu, ya ƙara da cewa
“Idan dai wannan yarjejeniyar an mayar ma da alh rahman ita, toh ya kamata ku binciko ta kafin ta salwanta.
Lokacin da Hajiya Raliya ta koma gidan, dare ya riga yayi, Mammi na zaune a falo cikin matsananciyar damuwa saboda kiranta da zayd yayi ya gaya mata message din da aka aiko mishi
“Raliya, ina kika je? Inata kiranki baki dauka ba”
“Naje na gana da wani ne.”
Mammi ta lura da yanayin fuskar hajiya raliya
“Raliya, Kin gano wani abu ne?”
“Na hadu da alh nuhu garba, yana cikin ma’aikatan farko da suka fara aiki a record office na northern crest”
“Me ya ce?”
Hajiya Raliya ta gaya mata duk yadda sukayi
Mammi ta saurareta a nutse tana qara shiga damuwa
“Kina nufin Bashir bai sace kuɗin da aketa zargin shi ba? Inna lillahi ya rabbi”
Haj raliya ta katse ta
“akwai yiwuwar cewa wataƙila an ƙulla masa makirci ne”
Ta ga tsoro a idanun Mammi, kuma ta san cewa gaskiyar na iya zama mai zafi a garesu
“Mammi, akwai wani abu kuma.”
“Menene kuma raliya?”
“Alh nuhu ya gaya min cewa Aisha ta zo wurinsa kafin ta ɓace, tana binciken ainihin yarjejeniyar haɗin gwiwar kamfanin don tana tunanin saboda ita ne aka qulla ma mahaifinta sharri”
Mammi ta rufe bakinta da hannunta.
“Aisha?”
“Eh.”
“To, wani ya san tana bincike kenan?”
Raliya ta gyada kai.
Mammi ta fara girgiza kai.
“A’a. Wannan ba zai yiwu ba, kenan akwai yuwuwar saboda Aisha na binciken gaskiya wani ya batar da ita?”
Tashi tayi zata nufi window ta shaqi iska, ba don babu iska a parlorn ba, se don batajin yana isarta dukda ac din da suke kunne, amma tana miqewa ƙafafunta suka yi rauni, Raliya ta yi sauri ta riƙe ta.
Ta dago ta kalli Hajiya Raliya, hawaye sun cika idanunta.
“Raliya, ze iya yuyuwa ache Fahad na aiki a northern crest tun kafin rasuwar babansu amma ache besan da wannan abun ba? Idan kuma har ya sani toh meyasa be gayamin ba? Shin anya kuwa babu hannun Fahad a ciki? Dazu da baki nan zaid ya kirani ya gayamin irin messages din da ake turo musu shi da maryam, kuma yache min wai an aiko mishi wani message akache ya nemo gaskiya kafin Fahad ya nemo ta, gabadaya ban yadda da abnda yache min ba, ganin shima kirana yayi yana neman qarin bayani yasa na tashi inje inji daga bakin Fahad din amma ina kofar shiga part dinshi naji yana waya, kofar bata ida rufewa ba, har zanyi magana se naji yana fadin wani abu da ya dauki hnkalina”
“Me kikaji yana chewa?” Mammi ta tambaya a tsorace
“Ji nayi yana chewa ‘abnda nikeso ka gane shine duk binciken da zanyi a gidan nan nayi amma banga takarda me alamar wannan yarjejeniyar ba, na gaya maka har wannan dakin da ke bayan garden na samo mukullan shi na chire daya daga ciki ina zuwa cikin dare ina bincike a ciki amma bnga wani abu me kama da ita ba, kuma ka sani chewa idan da gaske tana nan toh abnda da ya faru shekaru biyar da suka wuche da kuma shekaru uku da suka wuche duk ana iya tono shi kuma munyi aikin banza kenan’ Ban tsaya na gama ji ba saboda hnkalina ya tashi kawai na juyo na dawo”
Hajiya Raliya tayi shuru tana tunani, ita fah dama tana zargin Fahad saboda dole yasan abnda ke faruwa a northern crest amma yayi shuru, taji mammi ta chigaba
“Shin Raliya akwai wani laifi da na yi wa Fahad da har zaisan da irin wannan ya zabi boye mini?”
Raliya ta tsaya cak.
Muryar Mammi ta qara karyewa
“Na taɓa nuna masa bambanci da Zaid? Na taɓa nuna mishi cewa ba ɗana na cikina ba ne? Na taɓa sa shi jin cewa shi ba cikakken ɗan wannan gida ba ne?”
Ta ɗora hannunta a ƙirjinta.
“Mun ɗauki yaron nan tun besan abnda yake ba muka kawo shi gidanmu, mun ciyar da shi, mun tufatar da shi, mun ba shi ilimi, mun ƙaunace shi. Lokacin da duk yake rashin lafiya, nakan kwana ina kula da shi. Lokacin da yake cikin damuwa, nakan saurare shi, ban taɓa yin wani abu da zesa ya ji cewa shi ba dan gidan nan bane, se lokacin da Rahman beda lfya yache ze gaya mishi, nache ya bari se idan suna su biyu kadai saboda bazan iya kallon yadda zuciyar shi zatayi rauni ba”
Hawayenta suka zubo.
“To, me ya sa shi da yake dan wannan gida ze boye wannan maganr da zata iya hana margayi kwanciyar kabari?, shin Raliya anya kuwa beda sa hannu a ciki?”
Raliya ta riƙe hannunta.
“Mammi, kada ki ɗora wa kanki laifin zaɓin da ya yi.”
“Amma idan na gaza masa a wani fannin da ya zamana shine dalilin da yasa yayi wannan zabin fah?”
“Kin ƙaunace shi mammi, wannan ya isheshi komai, kin fi nuna mishi soyayya fiye da zayd da kika haifa, duk zabin da yabi wannan son zuciyar shi ne kawai”
Mammi ta kalle ta.
“To, me ya sa, Raliya? Me ya sa?”
Raliya ba ta da amsa, a halin yanxu tsoro take kar wani ciwon ya kama mammi don dama mammi tanada hawan jini
A cikin shirun da ya biyo baya, Mammi ta fara tunanin ranar da Fahad ya fara shigowa rayuwarsu.
Wani dan ƙaramin yaro mai idanun da suke cike da rauni da tsoro da rashin lfya
Yaron da wata rana ya riƙe hannunta ya kira ta Umma, ta kuma tuna murmushin mijinta a wannan rana, wani abin farinciki ne da ta riƙe a zuciyarta tsawon shekaru.
Amma yanzu, ta fara tambayar kanta ko ta taɓa gazawa a kan tarbiyyar yaron da suka kawo gidansu tun yana dan qarami, saboda ganin take duk abnda Fahad zeyi toh da tarbiyyar ta zeyi amfani
SOKOTO
Yayin da tsoffin sirrika suka fara bayyana a Abuja, rayuwa a Sokoto ta ci gaba da tafiya.
Imran ne yayi parking motarsa a gaban lecture hall din su maryam, ya duba lokaci a wayar shi yayi murmushi shi kaɗai.
Tun lokacin da suka amince su ba wa alaƙarsu dama ta gaskiya, Imran ke ƙoƙarin daidaita kanshi ya nuna mata ƙauna da kuma mutunta karatun ta, Ba ya son ya zama dalilin da zai hana ta ci gaba, Yana son ya zama mutumin da za ta iya dogaro da shi.
Bayan wasu mintuna, Hauwa ta bayyana daga kofar lecture hall din, tana ɗauke da jakarta da tarin littattafai, ta nufo motar
“Assalamu alaikum,” ta gaishe shi tana buɗe ƙofar motar.
“Wa alaikumus salam,” Imran ya amsa. “Sannu yan jamia”
Ta yi dariya tana shigowa motar
“Lecturer dinmu ne ya tsawaita lecture din fiye da time dinshi”
“To, ina fatan lecture din ta cancanci wannan wahalar.”
“Ta cancanta, ya nuna muna hanyoyin bunƙasa al’umma da yadda za a samar da damar ilimi ga kowa.”
Imran ya gyada kai yayin da ta ɗaura seat belt ɗinshi
“Na san za ki ji daɗin wannan lecture, da alama kinason taimako sosai”
“Ina son taimaka wa mutane a aikace, Ba wai in riƙa magana game da taimakonsu kawai ba, Allah ya bani iko”
Ya kalle ta a gefe.
“In shaa Allah”
Ta yi murmushi.
“Amma ya akayi ka sani?”
“Saboda duk lokacin da kike magana game da rayuwarki, kina fara ambaton abin da kike son yi wa wasu kafin abin da kike son yi wa kanki.”
Hauwa ta yi shiru na ɗan lokaci.
“Da gaske?”
“Yayi murmushi”
Ta juya tana kallon titi, tana ɓoye murmushinta.
Haka suka chigaba da tafiya, sunata tattaunawa game da karatunta, aikinsa, da makomar da kowannensu yake ƙoƙarin ginawa.
Suna ta fira a hankali kuma a natse har suka shigo kwanar gida, Imran ya juya kan motar ta yadda ze tsaya bakin gate din mama, yana kallon gefen fuskar hauwa, tunaninsa ya ɗan koma ga Maryam, A da, be taɓa tunanin wata makoma daban ba tare da ita ba
Amma ynzu wannan babin na rayuwarsa ya ƙare, kuma ya amince da hakan. Maryam ta riga ta gina nata rayuwar, kuma da gaske yana mata fatan alheri.
Yanzu, Imran ya fahimci cewa nasa makomar ma tana fara ɗaukar sabon salo.
A daidai nan suka iso gaban gidan, Imran ya jira ta tattara littattafanta.
“Ki yimin message idan kin gama karatu da dare, bnso in dameki lokacin da kike karatu”
“In shaa Allah”
Ta rufe ƙofar motar, ta nufi ƙofar gidansu tana murmushi.
Imran ya jira har ta shige cikin gida kafin ya juya kan Motar don ya shiga nasu gidan .
Amsterdam
A wannan daren, Maryam tana zaune kusa da window, tare da Zaid, hannunshi ɗaya a hankali yanata shafa cikinta.
Cikinta bai yi girma ba tukuna, kuma duk da cewa ta fara sabawa da sauye sauyen da jikinta yake ciki, wani lokaci tana kasa yarda da yadda rayuwarta ta canja cikin ɗan gajeren lokaci.
Watanni kaɗan da suka wuce, tana damuwa da jarabawar da zatayi, tana tunanin yadda makomarta za ta kasance, yanzu kuma tana ɗauke da ciki, kuma tana da tambayoyi game da mutuwar mahaifinta da batan yar uwar ta da ba za ta iya ƙara kau da kai daga gare su ba a karo na biyu.
Zaid ya lura da yadda tayi zurfi cikin tunani, ya dauko wani glass cup da ya ajiye a gefen table Wanda ke dauke da wani vitamin da ya jiqa mata, ya kai mata bakinta
“Haaa”
Maryam ta yi murmushi, tana dan juya fuska
Ya miqe ya tsaya a gabanta.
“Kin san zan iya dura miki shi ko”
Tayi murmushi ta bude baki ya bata
Ya girgiza kai, yana ƙoƙarin ɓoye murmushin shi, haka yayita bata seda ta shanye sannan ya zauna kusa da ita
“Me kike tunani?”
“Gida” ta fadi a shagwabe kamar zatayi kuka
Zaid ya riƙe hannunta.
“Za mu koma bada dadewa ba in shaa Allah”
Ta jingina kanta a kafaɗarsa.
“Ina kewar Mama. Ina kewar ƙawayena. Kuma yanzu, da duk abubuwan da suke faruwa, ina jin kamar ina nesa da mutanen da wataƙila sun san abin da ya faru da Baba da Aisha”
“Na fahimta.”
Ta ɗaga kai.
“Kana tunanin wasu daga cikin ma’aikatan northern crest ko makusantan mu sunada alaqa da wannan abun?”
Seda gaban shi ya fadi da ya tuna last message din da aka aiko mishi akan Fahad
“hakan yana iya yiwuwa, amma ba na son mu yanke hukunci kafin mu samu hujja.”
Maryam ta gyada kai.
Suka yi shiru na ɗan lokaci.
Sai wayarta ta yi ƙara daga kan kan table
Saƙo daga unknown number
Zaid ya lura nan take.
Ta ɗauki wayar.
Saƙon ya ƙunshi wasu kalmomi kaɗan.
Unknown number: FILE 17, Ba a taɓa lalata ainihin yarjejeniyar da ke ciki ba, Idan kina son sanin abin da ya faru da mahaifinki, ki daina neman wasu abu daban, amsar tana Abuja.
Maryam ta ji wani iri
Ta sake karanta saƙon, sannan ta miƙa wa Zaid wayar.
Ya karanta saƙon a hankali.
“Duk wanda ya aiko da wannan saƙon ya san da ainihin yarjejeniyar,”
“Kenan da gaske mahaifina yana da hannu a ciki?”
“Yana iya yiwuwa”
Maryam ta kalle shi.
“Rouhi, idan wannan mutumin yana ƙoƙarin taimaka mana ne fa? Tunda ya gaya muna inda zamu samu abnda muke nema”
“To, dole ne mu gano ko waye ai”
“Haya, na yi miki alƙawarin cewa ba za mu ƙara ɓoye wa juna abubuwa ba. Ba zan barki ki fuskanci wannan matsalar ke kaɗai ba, in shaa Allah zamu warware komai”
Idanun Maryam suka yi laushi.
“To, me za mu yi?”
“Inaga mu shirya mu koma Nigeria, zan tambayi dr idan zaki iya flying, daga nan se mu tsara komai yadda ya kamata, sannan mu koma Abuja, idan tafiyar ba za ta jefa ki cikin haɗari ba. Za mu bincika dakin, mu gano abin da FILE 17 ya ƙunsa.”
Maryam ta dan kalleshi
“Are you sure about this?”
“Na tabbata cewa muna buƙatar mu san gaskiya. Kuma na tabbata cewa duk abin da za mu gano, za mu fuskance shi tare.”
Maryam ta matso kusa da shi, ta ɗora kanta a kirjin shi
A waje, fitilun birnin Amsterdam sun haskaka sararin dare.
A wani wuri a Abuja, makullin da ya ɓace yana hannun wanda da ya kwashe shekaru biyar yana neman takardar da bai iya ganowa ba.
A cikin wannan gida kuma, Mammi da Hajiya Raliya sun fara fahimtar cewa iyalin da suka sani sun gina wani ɓangare na rayuwarsu a kan sirrin da ba su taɓa zato ba.
Maryam ta sake kallon wayarta.
FILE 17.
Ba ta san wanda ya aiko da saƙon ba.
Ba ta san abin da ainihin yarjejeniyar ta ƙunsa ba.
Kuma ba ta san ko Aisha tana raye ba.
Amma ta san abu guda.
Ba za ta iya ci gaba da kau da kai daga tambayoyin da suka shafi mutuwar mahaifinta ba.
Zaid ya matse hannunta cikin nashi
Da alama lokacin zuwan su Nigeria ya gabato
Za su koma su nemo gaskiya.
Join our WhatsApp group
Follow this link to join my WhatsApp group:
***