NUFIN ALLAH

49

by @anisamuhammadyah897



💕 NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Page4️⃣9️⃣


Ɗan ɗago kai tayi ta ganshi, ji tayi ina ma ƙasa ta tsage ta shige dan tsabar kunya, ƙara sunkuyar da kanta tayi tana riƙe hannun Reedah kamar ace takk ta zura a guje 

Mommy ya kalla ya ɗan haɗe rai, shifa duk wannan kayan rainin baso yake ba, daga shigowar sa sun kama wani dariya, clown suka gani ne da zasu riƙa mai dariya 

Ganin yayi kicinkicin da Fuska, Mommy tace
'' ni bana suruka dake, ƴa nake dake, shine surukin mu, koba haka ba'' 
Fareedah ƴar zakiya ce tace
''Aikam dai Mommy, bama suruka dake sister'' ta ɗan yi dariya tana mintsinin Anisa 

Duk da taji zafi amma taƙi cewa komai amma taci alwashin suka fita duk mintsinin da ta mata sai ta rama daman tun ɗazu take tsugular tata 

Aalima ce ta fito tana murza ido alamar daga bacci ta taso, hayaniyar su ne ya tashe ta dan ita ba mai son hayaniya bace gata da ƙulafucin Mamanta, shiyasa koda yaushe tana kusa da ita ko wajen yara ƴanuwanta bata fiye shiga ba, dan kusan halin su ɗaya da Faruq, 9 years take, tana ganin Anisa ta saki murmushi dan Allah ya haɗa jininsu 

Indai suka zo Kano idan bata wajen Mommy to tana daƙin Anisa, yanzu ma ganin su dukansu ne ya saka bata Wani zuwa gashi suka ma tattara suka tafi gidan Anty 

Har kuka tama Mommy wai akai ta wajen ta, tace
'' a can zaki zauna idan kika je har sai sanda zasu dawo kin yarda''
'' A'a saidai muje mu dawo an jima''
Dariya suka yi har Ammi jin me tace

'' Adda Anisa!!''.Tayi inda Anisa take da sauri ta faɗa jikin ta

Riƙe ta tayi tana murmushi tace ''leema tah ya kike, kin tashi kenan''
'' eh na tashi, shine ranar nan kike tafi ba kice mun goodbye ba ko''
''gashi na dawo to yanzu ai''
'' to zaki saka mun Korean film ɗinnan naki''
Kai ta jinjina mata tana murmushi 
'' to yaushe, zaki saka mun anjima?''
'' taso muje yanzu in saka miki'' ta faɗa daman neman hanyar barin parlourn take dan shigowar sa ta ƙara ta kura mata

Gashi tun ya zauna sai kace besan da ita a wajen ba, amma Ita tana iya jin idanun sa akanta idan ta motsa, da ta saci kallon sa ma taga kamar dai ba kallon nata yake ba hirar su kawai suke da Ahmad, a ranta tace to wai nice na tsargu kome ?

A nashi side ɗin kam duk wani motsi nata a idon shi, gani yayi yau ɗin ta ƙara mai wani kyau ji yake da da dama sai ya ce tayi mai kyau but gani yake idan yayi hakan banda raina shi ba abinda zata yi kawai ya kama cewa tayi kyau

Sallama suka yi wa Mommy suka fito gaba ɗayan su, suna fitowa ta sa ɗayan hannun nata da bata rike Aalima dashi ba ta mintsini Fareedah tace

'' ai daman nace sai na rama''
Wani ihu farida ta saki tace
'' bala'in can wallahi wannan mugunta ne ai ni ba shammatar ki nayi ba''
''oho dai ke kika sani saura hudu''
'' A'a ɗari ba huɗu ba, kin ji hannun ki kamar na cinnakar gaske, muguwa kawai''
'' an girma ba'a san an girma ba'' fadin nabila tana tafa hannuwa kamar wata mai yin waƙa
''ai duk halin ku ɗaya kuyi ta abu kamar yara'' faɗin Jalila tana wani maze wa
'' to Anty Babba ai kinfi kowa abun yara'' cewar Anisa 
'' Tabb abun yara ta kai ki, ke ai gaɓa ɗaya ma yarinya ce underage da anyi abu se ki sawa mutane kuka, ohhh nikam Ya Faruq zega abu'' cewar Nabila 

'' oh shigar wa in-law ɗin ki kikayi, idan underage ce ai baza mu aurar da ita ba,ai. Lokacin kam idan ba tayi wannan shagwabar ba ba sunan ta Anisa ba,to nima na shigar wa in-law ta'' faɗin Fareedah tana hararar nabila

Dariya Anisa da Jalila suka kwashe da ita tare suka ce
'' su in law manya''
'' idan ma in law dina na shigar wa se me''
'' se ba komai mutuniyar'' Jalila ta faɗi suna kashe hannu

Ɗaki suka shiga suna ta wa juna tsiya, zama tayi akan gado ta daura leema kan cinyarta tace
''na saka miki cartoon?'' ''eh'' zootopia 2 ta saka musu daman itama tun tayi downloading ne bata kalla ba

Ammi ce ta shigo ɗakin, su Nabila na ƙasa suna hira Fareedah na kallo itama a wayar ta su kuma su Anisa na kwance kan gado suna kallon su, 

Duk juyowa sukai suna kallon ta Jalila ce tace
'' Ammi ina wuni'' 
Shigowa tayi sosai tana murmushi ganin su duk guri ɗaya

'' yan matan Ammin su, kuna nan kuna hutawa abunku, to kun haɗa kayan ku dai ko? Ko Antn ku bata faɗa muku ba''
''eh Ammi mu hada ta faɗi mana tun kafin mu zo'''
'' madallah, gobe da safe zaku tafi dan bana son tafiyar yamma''
'' Ammi Adda zata ƙara tafiya ta barni''
Aalima tayi maganar tana kwaɓe fuska zatayi kuka tana riƙe rigar Anisa kamar ance yanzu zasu tafi 

'' A'a ba inda zamu je leemancy tah kinji, kar kiyi kuka kiyi kallon cartoon ɗin ki''
''tom''

'' ikon Allah ke Aalima da nice zan tafi baza kice zakiyi kuka ba dan munafun fun'' faɗin Reedah tana kama haɓa

'' to jelly jelly kike yi dani kenen'' 
'' oho kudai kuka sani''
''ke kun cika mun kunne wallahi kunƙi ku bari in gane me nake kallo'' faɗin nabila tana ɓata rai

'' to sannu mu da bakin mu zaki hana mu magana'' Jalila ta faɗi 

Ammi dai fita tayi abin ta, bazata iya da surutan su ba dan ta biye musu ciwon kai zasu saka ta dan ta lura basa gajiya da surutu kamar radio bakin su yake idan ta zo ta surutu 


Follow me on arewapen please 🥹 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 


_____________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺