50
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page5️⃣0️⃣
Da safe bayan sun yi breakfast wuraren 10 Ahmad ya fito a shirye dan shi ze kaisu
'' hope kun gama karku ɓata mun lokaci, bana son tafiyar dare, kuyi sauri, so nake inje in dawo a yau''
''mun ma gama yanzu zamu fito'' Jalila ta faɗi hannunta dauke da handbag da wayanta
Duk fitowa sukayi, ɗakin Ammi suka je suka mata sallama tace
'' Har kun fito kenan yanmatan Ammi, to muje in muku rakiya''
Waje suka yi har Ammi tana ta yaba kwalliyar tasu, Saida suka je part din Mommy suka musu sallama lokacin Aalima na bacci, har bakin mota suka raka su, saida suka tafi tukuna suka koma ciki part ɗin Ammi
Bashi ya tashi ba sai after 10, har yayi wanka ya fito ya shirya bega Ahmad ba, tunani yayi ko ya fita wurin aiki ne, baki ya ɗan taɓe yayi waje,part ɗin Mommy ya fara shiga, Aalima ya gani zaune gaban tv tana kallon disney junior
'' ke matsa daga gaban tv dinnan salon makantar da ido kawai''
Tashi tayi sumsum ta koma kan sofa ta zauna, tana gaishe shi, be amsa ba yace
'' ina Mommy''
'' tana part din Ammi'' juyawa yayi ya tafi be ƙara ce da ita komai ba, itama kallon ta ta cigaba, tana ganin ya tafi ta dawo inda take ɗazu, dan ta saba har Mommy ta gaji da mata magana akan zaman gaban tv
Yana shiga ya same su zaune suna hira, gaida su yayi, yana leƙe, jin gidan yake yi wani irin shiru, Ammi ce tace
''ga food can a dinning kaje kayi serving''
Dinning din ya nufa, zama yayi ya zuba ya fara ci, yanayi yana kallon wayar sa har ya gama, plate ɗin ya ɗauka ya kai kitchen, wayan Ahmad din ya ƙira dan yaji ina ya fita da sassafe shi sai Yanzu ma ya tuna yau Sunday
'' man se yanzu ka tashi kenan''
'' ina ruwan ka, kana ina ne''
'' ganinan hanyar KD zan kai su Jalila gurin Momma''
''me zasu yi a Kaduna kuma''
'' wannan Ammi zaka tambaya''
Wayar ya kashe yana jin mood ɗin shi na canja wa, ko sallama babu ta tafe abinta
Gudu yake ta zubawa dan so yake yaje a yau ya dawo a yau, suna tafe suna hira suna tsokanar Ahmad da Nabila, yau tsabar abu bakin nata ma mutuwa yayi,
Saboda yanda suke ta hiran nasu tafiyar na musu daɗi basu ga daɗewar su ba, wuraren 1 suka isa Kaduna
'' lale da mutan Kano, sannun ku da zuwa, maraba''
'' lafiya klau Momma Ina wuni'' suka faɗa a tare
'' mun same ku lafiya Momma''
'' lapiya klau Baba na ya hanya''
'' duk na gaji''
''ai ba iya kai ba harda yanmatan nawa, ku shiga ku ajje kayan ku ku huta, sannun ku da zuwa''
Kayan suka je suka ijje saida duk sukayi wanka sukayi sallah sannan suka fito parlour gurin Momma
'' sannun ku yaran Ammi, kuje kuci abinci, kuzo ku huta dan nasan kun gaji''
''ni dai ban jin yunwa yanzu ban sani ba ko su'' faɗin Jalila tana zama gefen Momma dan daman itace mutuniyar ta
'' A'a muma sai anjima, mun ci abinci a mota''
Momma bata da yara mata sai maza uku ya Usman ne babba sai me binshi ya Jamil yana Malesiya sai auta Hamza wanda yaɗan girme wa su Jalila da kaɗan
Shiyasa take kaunar su zo mata hutu dan tana son yara mata sosai amma Allah bai azurta ta da su ba sai yara maza Masu albarka
Sunfi shiri da Jalila sosai dan ita baki uwar magana ce ba kamar Nabila da Anisa ba, dan duk surutun Nabila Jalila ta fita, ita ki barta da tsiwa da tsokana anan tafi auki, itakam Anisa ga tsoro ga ban tsoro kamar farar kura saboda shegen tsoron ta ga tsiwa, idan kuma ƴan abun nata sun motsa sai ta share su dan ta iya miskilanci in taso, Fareedah ma sai hutu hutu tukuna suke zuwa tare, ita dama bawai ta cika surutu bane sai tana tare dasu ne suke saka ta magana
Tare suka shigo parlourn Ya Ahmad Hamza da ya Usman, Hamza ne Yace
'' kai wai dama kune baƙin da Momma ke magana akai zamu yi''
'' ehmana baka ji daɗin ganin mu ba kenan''
'' haba dai Reedah ni a suwa zance haka, ni wannan dabadan nama sanku ba inna ganku a hanya ai se ince ba ku bane''
'' saboda mun koma dodanni ko''
'' A'a yanzu ke Anisa idan wani ya ganni ya ganki sai ace kin girme ni mana, wai duk tarin ƙannai nane a zaune'' dariya ya fashe dashi yana tafa hannuwa
'' kai bana son shirme'' Usman ya faɗa dan be cika son hayaniya ba, shi kuma Hamza akwai surutu shiyasa kullum suke faɗa
Gaishe shi suka yi yana musu ya gajiyan hanya, a haka suka cigaba da hirar su, shidai banda short abu idan an saka dashi ba abinda yake sai satar kallon Jalila dake kwance kan ƙafar Momma tana danna wayar ta
So yake yasan sanda zasu dawo, dan shifa harga Allah baya son tana nisa da shi, in be ganta na kwana ɗaya ba sai yaji kamar yayi shekara be ganta ba, ko lokacin da yayi 2 years kafin ya zo hutu kullum zuciyarsa na hasaso ko ta ƙara girma ko ta canja ko ta ƙara tsawo ta dena wannan tsoron da saurin kuka, duk pics dinta da yake dasu duk bata da wani girma shiyasa ya ringa Allah Allah ya zo Kano hutu, kuma koda sukayi hutu kam wannan karan ko Egypt beje ba yana baro portharcourt yayo Kaduna shima dan kawai ya saba ta nan yake fara biyawa ne,
A ranar da ya ganta kam, bama a magana shiyasa yama gidan Abba tsinke dan a ransa yana fatan kar wani yazo ya mai shigar sauri, abinda yasa ya ringa ma Abba sintiri kenan
Gaba ɗaya gidan ji yayi baya mai daɗi ga Ahmad ma baya nan, amma yasan shi bazai wuce zuwa gobe ko jibi ba
Wayar sa ya dauko ya kunna data, Instagram ya hau sannan ya koma Whatsapp, status yaga ta saka, veiwing yayi yana jin kamar in ya shiga part ɗin Ammi zai ganta a can
Ganin bama ta wani daɗe da sakawa ba yaji kamar ya mata magana amma ya fasa ya kashe datan ya kwanta a kan cushin ɗin da yake kai ya kifa wayar a ƙirji
'' Momma bara inzo in koma dare na yi''
'' kaje ina kenan Baba na ba nan zaka kwana ba daman''
'' A'a Momma Kano zan koma Saboda gobe zan je aiki, akwai wasu muhimman abubuwan da zanyi goben shiyasa bazan iya kwana ba''
'' eyya banso ba, yanzu ka koma gajiyar sai yayi maka yawa ga na zuwa ga na komawa ga gobe kuma kafita, dabadan kace kana da muhimmin aiki ba ai ba inda zaka je''
Murmushi yayi yace. '' ai nima Momma da badan aikin ba sai nayi sati irin haka kafin in koma''
'' wata rana sai kazo kayi wata ma, duk da dai yanzu ka daina zumuncin, sai dai in ta motsa kayi a waya''
'' Nima nasan na rage Momma shiyasa nace ni zan kawo su dan inga Momma ta''
'' ai ko a haka nagode na ganin ka danayi tunda ka kwana biyu baka zo ba''
agogon hannunsa ya duba yaga to 6 yace
'' Bara in bari ayi magriba tunda an kusa sai in tafi, kar dare ya gama yi''
'' ai tafiyar dare dole, dan ka kai daren saidai Allah ya kiyaye''
Follow me on arewapen for more updates 🥹 🙏 🙏 🙏
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***