NUFIN ALLAH

51

by @anisamuhammadyah897


💕 NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA


Page 5️⃣1️⃣


Kusan kwanan su biyar da zuwa Kaduna kenan, Momma ta dauko wata me gyaran jiki tun daga Maiduguri washe garin ranar da suka zo, 

Jiya aka fara musu amma sun murje sunyi kyau tun ba'a yi nisa ba, suma Fareedah da Jalila sun kafe sai anyi da su tunda ai sune manyan ƙawayen amare, Momma kuwa tace a haɗa dasu 

Tun ganin an fara wannan gyaran jikin tasan dai auren nan da gaske ake za'ayi, gaba ɗaya tun aka fara ta zama wani so silent duk wannan rahar da tsiwar ta ɗauke kamar ba ita ba, saidai idan sunyi abu ta bisu da kallo ko ta sakar musu murmushin da gwara kuka ta saki

Gani take gaba ɗaya kamar a mafarki wai yau ita zata auri Ya Faruq, tana jin fargaba kaɗan kaɗan ba kamar da ba dan kwana biyun nan ta dage da addu'a sosai har tsakar dare take tashi sallah 

Bata san yanda za'ayi wannan zama ba tsakanin su, ita bata ga wani alamar yana sonta bafa har yanzu, kuma itama bata ji tana wani son shi ba, sedai tsoron da take mai kusan 55 percent ya ragu

Turus tayi taɗan yi baya ganin wanda bata zata ba a parlour zaune shi da ya Usman suna hira, a ranta take tunanin yaushe yazo Kaduna, baya tayi a hankali ta shige ɗakin, daman ta fito taje kitchen daukan ruwa ne ta gansu danma Allah yayi basu lura da ita ba, anya zaton ta na aljani ne Ya Faruq ba gaske bane kuwa?? yanzu ta gama tunanin sa sai gashi a gaban ta

A kan idon shi ta fito har ta koma, dan murmushin gefen baki yayi dan tun ɗazu yake kallon hanyar ɗakin tunda yasan in sun zo nan suke sauka, gani yayi ta ƙara yi mai kyau a idon shi sosai kodan ya dade be ganta ba

Kaji fah sai kace wanda yayi wata da watanni ko shekara be ganta ba

Be daɗe sosai da shigowa ba, ana shiga masallaci ma lokacin sallar issha ake, ya fito ya fara zuwa masallacin, acan suka haɗu da Usman da Hamza, suka shigo cikin gidan Hamza yayi part din su sukuma suka shigo ciki

Momma suka samu itama na sallah shine suka zauna yana jiran ta idar,amma duka hankalin sa na kan yaga koda giftawar ta ne
'' baban yaya shigowar yaushe'' 
'' ban daɗe sosai ba Momma, na same ku lafiya''
'' lapiya klau alhamdulillah, koda yaushe in tayi maka faɗa akan tafiyar dare amma kaƙi ka daina Kohh??''

'' ba haka bane Momma ya bi jikina ne,se a hankali tukuna, kuma tafiyar dare yafi daɗi da nutsuwa''
'' to Allah dai ya kyauta maka'' 

Bayan sunyi sallar suka fito dan yin dinner, duk suna zaune kan dining table din har sun ma fara cin nasu, zama suka yi suma, duk tana jin ta duk wani iri tun sanda tagan shi, gashi yanzu tana jin wannan Mayun idanun nasa da a kullum suke hana ta sukuni na yawo a kan ta
Suma su Nabila sunyi mamakin ganin shi amma basu nuna ba suka gaida shi suka nemi wajen zama 

Reedah ce ta ja hannun ta ta zaunar da ita kusa da ita wanda kujerar dake facing nashi kenan, wayar ta ta ɗauka duk dan rage jinta da tayi a takure 

Message ne ya shigo mata, dan daman tana cikin Whatsapp ne, ko Instagram bata fiye hawa ba sosai saidai Snapchat da shima streaks kawai ke kai ta
'' kin iya tafiya ba sallama kohh?, kin kyauta''. Ɗagowa tayi ta kalli inda yake, abincin shi yake ci cikin kwanciyar hankali kamar besan tana kallon nashi ba, yana yi yana danna wayar sa

Wani message ɗin ne ya shigo mata, tana dubawa taga '' kin wani kafe mutum da ido salon in shaƙe''
Ƙasa tayi da kanta, tana ƙunƙuni ƙasa ƙasa 
'' se kace bashi ke kafe mutum da idanu ba kabi ka kasa sukuni, ko gajiya ma baya yi'' 

Ko rabin abincin ba tayi ba taji ta ƙoshe dan ta takura da yawa ga suma su Jalila sai kallon su suke sai kuma su ɗanyi kuskus din su, tashi tayi niyyar yi ta koma ɗaki wani message ɗin ya shigo mata 

''karki kuskura kice tashi za kiyi'' fuska ta ɗan yamutsa se yanzu ta maida mai reply 
'' Yah na ƙoshi''
'' seat down karki ma soma, ko kin koshin se kin tura shi''
Ya faɗa yana haɗe rai dan shikam be gaji da ganin ta ba

''kai Hafeez dan ba yaran ka bane yasa kake so su a bar su, dan son zuciya kasa a ka haɗa da ɗiyar ka, yanzu kuma kace hakan baze yu ba??'' mamee ke fadin haka ta daura kafa ɗaya kan ɗaya tana wani jijjigawa 

Duk iyayen suna part din Daddy saboda maganar auren dan mamee Abba munir dake nan Kano taje har gidan shi wai ta kai mai ƙara, ai yaransu ya kamata ayi dasu amma dan son zuciya dakuma su amma basu daukesu a ƴanuwa ba basu ɗauke su da muhimmanci ba yasa suka haɗa da nasu yaran suka maida nasu bare

'' yara dai namu ne koh to koda ace basu suka kawo zaɓi ba, wanda muka ga dama zamu basu, ba wanda za'a tilasta acikin su ya aura wacce baya so su suka kawo zaɓin su dan haka duk wannan shashancin da ke damun kanki gwara ki ajje shi a gefe''

'' kai Adam nice shashashar, tsabagen sun zuciya ai nasan ba yadda za'ayi Umar yaso Anisa in ba dai cusa masa ita kuka yi ba, daman shi Ahmad baƙin halin uwarsa bazai bari tasa ya aura Zulaiha ba dan tsabar kun tsane mu da zuciya dubu kuke zaune da mu ai da kun haɗa dasu Zulaihan, in ba munafurci da son zuciya ya ba, yanda zaka san daman alamarin an riga da an shirya saida aka gama komai sannan aka faɗa mana dan ba'a ɗauke mu da muhimmanci ba''

Daddy zai kara magana Abba munir ya ɗaga mai hannu, numfashi ya sauke yace 
'' naji duk abinda kikace Abida, kuma na ji na side din Hafeez, dan haka ina son a kira mun Ahmad da shi Umar din nan gurin yanzu inji suma ta bakin su yanda zan san mufitar da za'a nema''

''ai Abba mufita kawai shine idan har su Nabilan baza su hakura ba sedai su haɗa su duka su aura kowa yayi bibbiyu acikin su''




Kuyi following ɗina a arewapen for more updates 🥹 🙏 🙏 🙏 


______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺 
***