THE RETURN AND A NEW BEGINNING
AMSTERDAM, NETHERLANDS
Washegari da safe, Maryam ta tashi tun kafin alarm ɗin wayarta ya yi ƙara. Ta buɗe idanunta a hankali, ta juya ta kalli Zaid wanda yake maqale da ita.
Ta ɗan yi murmushi ganin yadda yake baccee cikin natsuwa, shidai komai nashi a natse kamar beda matsalar komai, ta tuna da abubuwan da suka faru a kwanakin baya, daga samun labarin cikin da ta yi zuwa saƙonnin ban mamaki da suke karɓa game da FILE 17, duk abubuwan da suke faruwa zayd a natse yake
A hankali ta miƙa hannu ta shafa fuskar Zaid.
“Rouhi…”
Ya motsa kaɗan, sannan ya buɗe idanunsa.
“Hmm? What is it, Haya?”
“Mu tashi mu fara shiryawa, We have a flight to catch.”
Ya kalleta na wasu daƙiƙu, sannan ya miƙe yana murmushi,
“Iyyeh wata na jin daadi zataje gida”
Maryam ta yi murmushi.
“Eh, na matsu inga Mammi”
Zaid ya zauna sosai a kan gadon, ya kamo hannunta.
“in shaa Allah, but first, breakfast.”
Maryam ta turo baki.
“Ba na jin yunwa.”
Ya ɗaga gira.
“Haya”
“Okay, okay. Zan ci wani abu.”
Yayi kissing goshinta kafin ya tashi ya fara shiryawa
Bayan sun gama shirye-shiryensu, Zaid ya tabbatar cewa duk abubuwan da suke buqata na tafiyarsu suna nan, musamman takardar likitar Maryam da ta tabbatar da cewa za ta iya yin tafiyar bisa yanayin lafiyarta na lokacin.
Ba su ɗauki kaya masu yawa ba, amma sun tanadi abubuwan da Maryam za ta buƙata
Kafin su fita, Maryam ta tsaya a gaban madubi tana kallon kanta, taga kamar ta qara qiba, kamar da bump din ya fara fitowa kadan
“Rouhi?”
Ya juyo.
“Yes, Haya?”
Ya ƙaraso ya tsaya a bayanta, yana kallonta ta cikin madubin.
“I can’t wait inga baby bump ya fito miki”
Ya fadi yana zagayo hannayenshi yana hugging dinta ta baya
Ta zumburo baki
“Baby bump ze miki kyau, our baby”
Maryam tayi murmushi
Ya kama hannunta, suka fita daga ɗakin tare, tana yima su Samantha sallama sunata hawaye suna fadin zasuji kewar ta, zayd se Allah Allah yake su tafi kafin itama maryam ta fara mishi hawaye saboda yasan qaramin aikinta kenan
Ba su san irin abubuwan da ke jiran su a Najeriya ba, Amma dukansu sun san cewa dawowarsu za ta buɗe wani sabon babi a rayuwarsu.
ABUJA, NIGERIA
Bayan doguwar tafiya, jirginsu ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Maryam ta ji wani irin motsin zuciya yayin da take kallon garin da suka bari wattannin da suka wuche
Zaid yana tafiya kusa da ita, yana riqe da hannunta yana nanata mata ta taka a hnkali
“You okay, Haya?”
Ta gyada kai.
“I’m fine Mr”
Ya yi murmushi, sannan ya karbi jakar hannunta.
“Welcome home, then.”
Maryam ta kalle shi.
“Thank you, Rouhi.”
Bayan sun kammala abubuwan da suka dace a airport, suka nufi hanyar fita, driver da yazo daukar su yana ganinsu ya sheqo ya karbi kayan da ke hannun zayd, yana gaisawa dasu yayin da suka nufi motar
Yayin da suke tafiya, Maryam tana kallon titunan Abuja ta window, zuciyar ta cike da tunanin me zata tarar, ta tuna yadda aka riƙa kallon babanta a matsayin mutumin da ya yi wa company zagon ƙasa. Ta tuna yadda danginsu suka shiga ruɗani, da kuma yadda Aisha ta ɓace ba tare da wani tabbataccen bayani ba.
Hannunta ya koma kan cikinta.
“Baba, ina fatan zan gano gaskiya,” ta furta a hankali.
Zaid ya juyo gare ta.
“What did you say?”
Ta girgiza kai.
“Nothing, Rouhi. I was just thinking.”
Ya kamo hannunta ya matse a hankali.
“Whatever happens, I’m here.”
Maryam ta jingina a jikin shi
“In shaa Allah.”
BALARABE MANSION, ABUJA
A lokacin da motar su Zaid tayi parking a gaban part din mammi, Mammi tana zaune a parlorn tare da Hajiya Raliya.
Tun da safe suketa shirin tarbar su zaid
Nan suka ji ƙarar motar a waje.
Wata mai aiki ta shigo tana sanar da su cewa Zaid da Maryam sun iso.
Mammi ta miƙe tsaye, suka fito daga parlorn cikin sauri
Maryam tana tsaye a ƙofar motar lokacin da ta ga Mammi ta fito. Nan take ta nufe ta cikin matsanancin farin ciki
“Mammi!”
“Maryam ɗina!”
Mammi ta rungume ta sosai, tana shafa bayanta cikin farin ciki.
“Sannun ku da sauka, kun sha hanya”
Maryam ta yi murmushi
“Mammi ina wuni? Ya gida?”
Mammi ta ɗan ja da baya ta kalleta sosai, tayi kyau, ta qara haske, kuma ta cicciko
“Da alama dai yana kula min dake yadda ya kamata”
Maryam ta yi murmushi tana jin kunyar kallon da mammi ke yimata
Hajiya Raliya ta ƙaraso, ta rungume Maryam sannan ta ansa gaisuwar da zayd ke mata
“Alhamdulillah, kun iso lafiya.”
“Alhamdulillah Hajiya”
Bayan sun shiga parlor, aka kawo musu abin sha da abinci. Mammi ta ci gaba da tambayar Maryam game da rayuwarta a Amsterdam, amma ta lura cewa Maryam tana dauke da wani abu a zuciyarta.
Bayan ɗan lokaci, Zaid ya kalli Mammi da Hajiya Raliya.
“Akwai abin da ya kamata mu tattauna, amma se zuwa anjima in shaa Allah, zamuje mu dan huta, mammi yarinyar ki da debo gajiya” ya qarasa yana murmushi
Maryam ta turo baki a ranta tana fadin wane anjima kuma ai kawai ayi abnda zaayi
“Allah mammi ban gaji ba, kawai muyi magana”
Mammi taji wani irin tausayin maryam da fargaba sun diro mata a take
Dakyar Mammi ta ajiye cup din dake hannunta
“Zaid muyi maganar kawai hnkalinta zefi kwanciya”
Maryam ta buɗe wayarta ta nuna musu saƙonnin da aka aiko mata da kuma hoton ƙofar garden ɗin.
Raliya ta matsa kusa da ita domin ta karanta saƙonnin sosai.
“FILE 17…” ta furta a hankali “ inaga file din da zamu bincika kenan idan mun shiga dakin”
Mammi ta kalli Zaid.
“Ka san wani abu game da wannan?”
Zaid ya gyada kai.
“Na samu saƙonni makamantan waɗannan. An gaya min cewa wani yana neman shafin da ya ɓace, kuma idan ina son kare Maryam, dole ne in nemo shi kafin Fahad ya same shi, shine lokacin da na kiraki na tambayeki dinnan”
Mammi ta yi shiru.
Maryam ta kalli Zaid a tsorace don batasan zanchen ba, a ranta take chewa Fahad kuma?
Raliya ta yi numfashi mai nauyi.
“Yanzu ai inaga komai ya fara haɗuwa.”
Zaid ya ɗan karkata kansa.
“Kun gano wani abu ne?”
Mammi ta kalli Raliya, kamar tana jiran ta fara bayani.
Raliya ta buɗe jakar takardun da ke kusa da ita, ta fito da wasu takardu.
“Mun yi magana da wani tsohon ma’aikacin Northern Crest Holdings Malam Nuhu Garba, ya gaya mana cewa Bashir ya fara gano wasu kuɗaɗe da suke ɓacewa daga kamfanin kafin rasuwar sa, amma da ya fara bincike shine aka juyar da laifin zuwa gareshi
Maryam ta riƙe hannun zaid sosai.
“Kuɗaɗe suna ɓacewa?” Zaid ya tambaya don shi fah besan takamaiman abnda ya faru a lokacin ba
“Eh,” Raliya ta amsa. “Kuma akwai alamun cewa an canja wasu bayanai domin a nuna kamar Bashir ne yake satar kuɗin.”
Maryam ta rufe idanunta na ɗan lokaci.
“Allah Sarki Baba…”
Mammi ta kamo hannunta.
“Maryam yi hakuri zamu gano komai”
Hawaye suka fara zarya a fuskar Maryam
“Na daɗe ina son sanin gaskiya. Ba zan iya ci gaba da rayuwa ina tunanin cewa ana zargin Baba da abin da bai aikata ba ba.”
Zaid ya kalli Raliya.
“Hajiya shikenan abnda Nuhu din ya gaya muku?”
Raliya ta ɗauko wata takarda daga cikin file ɗin.
“Ya ce akwai asalin yarjejeniyoyi uku da suka shafi mallakar Northern Crest Holdings. Ɗaya na Bashir ne, ɗaya na Rahman, ɗayan kuma na lauyansu. Bayan mutuwar lauyan, wasu takardunsa sun koma hannun Rahman.”
Zaid ya sunkuyar da kai yana nazari.
“Which means the lawyer’s copy may be the one hidden in FILE 17.”
Raliya ta gyada kai.
“Shi ne tunaninmu.”
Maryam ta kalli Mammi.
“To, me ya sa bazamu je mu buɗe ƙofar garden ɗin yanzu ba?”
Mammi ta yi shiru na ɗan lokaci.
Dama munche gara mu jira se kunzo
“Toh muje ynzu mu gani”
“Ba za mu yi gaggawa ba, ba mu san wanda yake sa ido a cikin gidan nan ba. Kuma idan Fahad yana neman file ɗin, dole ne mu yi hankali”
Maryam shuru tayi batason tayi gardama
NORTHERN CREST HOLDINGS, ABUJA
Fahad yana zaune a office lokacin da wayar shi tayi ringing
“Sir, Zaid da Maryam sun dawo Abuja.”
Fahad ya ɗaga kai a hankali.
“Yaushe?”
“Yau, sir. Sun iso dazu da safe.”
Ya yi shiru na wasu daƙiƙu.
“Sun tafi gida?
“Eh, sir. Suna Balarabe Mansion yanzu.”
Yayi shuru ya jingina da kujerarsa.
Maryam ta dawo, anya basusan wani abu ba kuwa?
Ya kashe wayar ya aje
Ya miƙe ya zagaya table din da ke gaban shi yana tunanin abin da zai yi.
Shekaru biyar kenan yana neman wannan takarda. Ya shiga ɗakinnan sau da dama, ya binciki duka files da takardun kamfani, amma bai taɓa gano ainihin yarjejeniyar ba.
Yanzu kuma, Maryam da Zaid sun dawo a dd lokacin da ake qoqarin bankado abnda ya dade da rufewa, tabbas wannan ba coincidence bane, tabbas dole yasan abun yi
Ya matse hannunsa.
“Ba zan bari wannan ya faru ba.”
Ya ɗauki wayarsa ya kira
“Ali, Ina son kaje Balarabe Mansion ka tsaya, Kada ka yi wani abu da zai jawo hankali. Ina so kawai ka gaya min duk wanda ya shiga gidan da duk wanda ya fita, every small detail, duk abnda ke faruwa ka gayamin
“Na gane, sir.”
Ya katse wayar.
Fahad ya koma kusa ga windown office.
A waje, yana kallon mutane suna rayuwa kamar yadda suka saba. Amma a zuciyarsa, ya san cewa wani abu yana gab da faruwa dashi, idan Maryam da Zaid suka gano abnda ya aikata, me ze faru? Kai ina baze taba bari ba, ko chinna ma dakin nan wuta zeyi ta yadda komai ze qone, In ba haka ba zasu iya gano cewa duk abin da ya gina a kan ƙarya ne.
Kuma ba zai bari wani ya rusa rayuwar da dade yana ginawa ba
SOKOTO
Hauwa Koulou tana zaune a ɗakinta tana duba littattafanta lokacin da wayarta ta yi ƙara.
Saƙo ne daga Imran.
“Kin gama karatun yau?”
Ta yi murmushi ta rubuta masa.
“Almost. Ina ƙoƙarin gama wani topic kafin in huta.”
Ya amsa da sauri.
“Good. Amma ki tuna cewa hutawa ma yana da muhimmanci. Kada ki wahalar da kanki sosai.”
Hauwa ta girgiza kai tana murmushi.
“Yaya, ka zama kamar lecturer”
Imran ya yi dariya lokacin da ya karanta saƙon.
“At least I’m a caring lecturer.”
Ta aika masa da emoji na dariya.
Bayan ɗan lokaci, wayarta ta sake yin ƙara.
Imran ne ya kira ta.
“Hello Yaya.”
“Kin ci abinci?”
Ta yi shiru.
“Umm…”
Imran ya yi dariya.
“Hauwa!”
“Zan ci yanzu.”
“Good. Ki ci abinci, ki huta, sannan ki ci gaba da karatun, kada ki faɗi qasa saboda kin manta da kula da kanki”
Hauwa ta yi murmushi.
“Na ji, Yaya.”
Bayan sun yi sallama, ta ajiye wayarta tana tunani.
Ba ta taɓa tunanin cewa zata sake da imran har haka ba, gashi yana kula da ita cikin natsuwa, Imran bai yi mata alkawuran da ba zai iya cikawa ba, maimakon haka, yana nuna mata ta hanyar ayyukansa cewa yana son ta cimma burinta.
Ta yi addu’a a zuciyarta.
Ya Allah, idan wannan al’amari alheri ne a gare ni, Ka sauƙaƙa shi. Idan kuma ba alheri ba ne, Ka shiryar damu zuwa abin da ya fi.
A wannan ranar, Safiyya tana kwance a gadon asibiti labor nata qaruwa
Mijinta Mukhtar Talba yana kusa da ita, yana riƙe da hannunta yayin da nurses suke kula da ita.
Safiyya ta matse hannunsa.
“Please, kada ka sake hannuna.”
“Ba zan sake ba.”
Lokaci na yimata kamar ba ya wucewa. Contractions na zuwa yana tafiya, kuma duk lokacin da ya ƙaru, tana ƙoƙarin bin umarnin ma’aikatan lafiya, taja numfashi ta fitar
A ƙarshe, bayan dogon lokaci, aka ji kukan jariri.
Duniyar Mukhtar ta tsaya cak.
“Is the baby okay?”
Ma’aikaciyar lafiya ta yi murmushi.
“Congratulations. You’ve got a baby boy.”
Idanun Safiyya suka cika da hawaye.
“Alhamdulillah…” Mukhtar ya fadi yana kallon yaron
An kawo mata jaririn bayan an kammala kula da shi da ita. Ta kalle shi, ta shafa ƙaramin kumatunsa a hankali.
“Bismillah,” ta furta cikin hawaye na farin ciki yayin da ta karbe shi daga hannun Mukhtar bayan ya yimishi huduba
A lokacin ne akaba su hajiya Ruqaiya da mamar Mukhtar damar shigowa, suka karbi jariri sunata yimishi addua
Mukhtar ya zauna kusa da maman shi, yana kallon ɗansa da mamaki da farin ciki.
“Allah ya raya mana shi kan addinin musulunci da tafarkin sunnan” ya faɗa.
“Amin,” maman Mukhtar da hajiya ruqaiya suka amsa.
Bayan ta ɗan huta, ta nemi wayarta.
Mukhtar ya kalleta.
“Me za ki yi da ita yanzu? Ki qara hutawa mana.”
Ta yi murmushi.
“Ina son in sanar da su Maryam.”
Ya yi dariya, sannan ya miƙa mata wayar.
“Of course. I should have known.”
Safiyya ta ɗauki hoton jaririn da kyau, sannan ta aika a group dinsu da suke su uku
“Alhamdulillah, ga yaron ku nan yayi landing! ❤️🥹”
Ta ajiye wayar, tana kallon jaririnta hannun hajiya Ruqaiya da fuskar ta dake dauke da wani irin farin ciki
BALARABE MANSION, ABUJA
Maryam tana zaune tare da Mammi da hajiya Raliya da zayd lokacin da wayarta ta yi ƙara.
Ta buɗe saƙon, kuma nan take fuskarta ta canza zuwa murmushi.
“Subhanallah!”
Zaid ya juyo daga inda yake zaune.
“What happened?”
Maryam ta miƙa masa wayar.
“Safiyya ta haihu!”
Mammi ta yi murmushi.
“Alhamdulillah! Ma Shaa Allah, Allah Ya raya muna, dama dazu Ruqaiya ta kirani tache suna asibiti, bari in kirata ynzu” ta dauki wayarta ta fara neman number din hajiya ruqaiya
“Amin,” Maryam ta amsa, tana duba hoton jaririn.
Ta ji wani irin farin ciki ya cika zuciyarta. Ƙawarta ta zama uwa, kuma ita ma tana ɗauke da wani sabon rai a cikinta, ko ya zataji idan ta haihu?
Ta aika wa Safiyya voice message
“Safiyyaaa! Alhamdulillah! Allah ya raya mana shi, ya sanya shi cikin salihai. Wallahi na yi farin ciki sosai! Da na ga hoton nan, sai na ji ina son na zo in rungume ki yanzu yanzu in che miki welldone. Amma ba damuwa Dr Mukhtar na nan, Ki huta sosai, ki kula da kanki, kuma ki turo min hotuna da yawa pleaseeee, kin ganshi dani yake kama, lol, I can’t wait to meet my little prince!”
Zaid ya kalleta yana murmushi.
“Someone is already acting like an auntie.” Ya fadi qasa qasa
Maryam ta juya ta kalle shi.
“Of course! That’s my best friend’s baby.”
Ya yi dariya.
“Allah Ya raya shi.”
“Amin.”
Maryam ta sake kallon hoton jaririn, sannan ta ɗora hannunta a kan cikinta.
“Rouhi, ka ga yadda yake ƙarami?”
Zaid ya matso kusa da ita ya kalli hoton.
“Very tiny.”
Maryam ta yi murmushi.
“In shaa Allah, one day we’ll be holding ours too.”
Zaid ya sumbaci goshinta.
“In shaa Allah, Haya”
Ai koda maryam ta ankara ta juya mammi da hajiya sun bar parlorn
Taji wata irin kunya kamar zata nutse amma Zayd kam ko a jikinshi
A wannan lokacin, duk da asirai da suke ƙoƙarin warwarewa, Maryam taji wani irin kwanciyar hankali. Haihuwar Safiyya ta tuna mata cewa rayuwa ba ta tsayawa ga abin da ya faru a baya
Akwai sabbin abubuwan da suke farawa, akwai so, akwai bege, akwai farin ciki in shaa Allah
Kuma akwai ƙananan rayuka da suke zuwa duniya domin su kawo farin ciki garesu
“Rouhi, Gobe, ya kamata mu fara binciken FILE 17 da gaske.”
“Za mu fara. Amma za mu yi komai cikin hankali.”
Zaid ya kama hannun Maryam.
“Together.”
Maryam ta kalle shi, sannan ta gyada kai.
“Together.
WANI WURI A ABUJA
A cikin wani ɗaki da babu wanda ya sani, wata mata tana zaune kusa da ƙaramin table
Wayarta tana hannunta, kuma a kan table, akwai wasu tsofaffin takardu da hotuna.
Ta buɗe wani hoto da aka ɗauka shekaru da suka wuce.
Hoton Bashir Misalati.
Ta daɗe tana kallon hoton kafin ta rufe idanunta.
“Baba…”
Muryarta ta fito a hankali, cike da raɗaɗi.
Shekaru sun wuce, amma ba ta manta da abin da ya faru ba. Ba ta manta da tsoron da ta ji lokacin da ta fara gano gaskiya ba. Kuma ba ta manta da abnda da ya sa ta ɓuya ba.
Ta ɗauki wayarta, ta buɗe wani message da aka aiko mata
“Maryam da Zaid sun dawo Abuja”
Wannan yana nufin cewa abubuwa za su fara canzawa.
Ta kalli takardun da ke gabanta.
“Ku yi hankali,” ta furta. “Kuna kusa da gaskiya fiye da yadda kuke zato.”
Ta sake ajiye hoton Bashir a kan table din
A wannan karon, ba za ta bari tsoro ya hana ta taimaka musu ba.
Amma har yanzu ba za ta iya bayyana kanta ba, sai lokacin da ta tabbatar cewa tana da isasshen kariya
Domin idan Fahad ya gano cewa tana raye, abubuwan da suka faru a baya za su iya maimaituwa.
Ta kashe hasken ɗakin don tayi baccee
Kuma a cikin duhun, sirrin da aka ɓoye tsawon shekaru ya ci gaba da jiran lokacin da zai fito fili.
Aisha tana raye.
Amma har yanzu, Maryam da Zaid ba su san inda take ba.
Kuma ba su san cewa tana ƙoƙarin kai su ga gaskiya ba.
Wasu sirrika suna ɓoyewa tsawon shekaru, Wasu gaskiyar kuma suna jiran wanda zai iya fuskantarsu, Amma ƙaddara tana da nata lokacin bayyana komai.
Join our WhatsApp group
***