NUFIN ALLAH

52

by @anisamuhammadyah897

💕 NUFIN ALLAH 💕 
   By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Under team yota's amazing pen

Page5️⃣2️⃣


Wani murmushin baki isa ba Amma da tun da aka fara magana bata ce uppan ba tayi jin furucin Mamee, ɗauke kai tayi dan tasan wannan zancen ma ba me yiwa bane 

''Wai ban ce bana buƙatar jin bakin kiba Abida ko ni bansan me nake ba'' Abba Munir ya faɗa cikin zafin rai dan tun ɗazu take ƙoƙarin hasala shi, Baba ne ya ciro wayar sa ya fara kiran Ahmad, yana part din su ya gama wanka yana saka kaya zai fita yaga kiran Baba, tunanin ko lapiya yayi dan yasan dai duk suna cikin gidan 

Yana ɗaukar wayar be jira amsa sallamar sa ba yace '' kazo part din Daddyn ku yanzu'' ya kashe wayar dan shima ranshi a ɓace yake da abinda Mameen keyi, ita da yake Mama makira ce sedai ta zuga Mameen ita tayi ta tsiyar ita kuma tana daga gefe 

Kofar ya turo ya shigo cikin parlourn da sallama, duk jigum jigum ya gansu kamar waɗanda aka yiwa mutuwa duk sun zubo mai ido, gaban shi ne ya ɗan faɗi yana tunanin shi kuma wani laifin yayi, me yayi haka

''Ƙara so daga nan'' Abba Munir ya faɗa, a ƙasa wurin kafar Ammi ya zauna da gaba ɗaya hankalin ta a tashe yake ita da Anty dan duk ba son fitina suke ba gashi fitinar ma akan yaransu take, ji take da da dama sai tayi wani abu akan lamarin amma bata san abin yi ba dan bata son ace wai za'a fasa auren dan harga Allah har cikin zuciyar ta haɗin nan take jin sa

'' Ahmadu tambayar ka nake son yi''. '' Allah yasa nasani Abba''. Jinjina kai Abba Munir yayi yace 
'' shin kana son Nabila ko baka son ta''. Tambayar ta zo mai wani bambarakwai wai shi ake tambaya yana son Nabila ai shi ji yake kamar numfashi ɗaya suke shaƙa karewar yana sonta

''eh Abba ina son ta''. '' alhamdulillah to kana son Zulaiha''. 

'' Zulaiha!!'' ya kira sunan a ɗan razane shifa be gane me yasa ake mai wannan tambayoyin ba, be fa gane ba, ba rami me ya kawo maganar rami, shi me zeyi da wata Zulaiha ana zaune kalau. 
''na tambaye ka kayi shiru ka amsa mun ina ji''

'' A'a Abba gaskiya Nabila kawai nake so'' kai Abba Munir ya ƙara jinjina wa yace. '' ina shi Faruqun yake''
'' ya je Kaduna yin wani aiki''
'' to shikenan kira mun shi a waya yanzu'' wayar ya dauko ya fara kiran sa, be daɗe yana ringing ba ya ɗaga 

'' hello man ya akayi''.
 '' Abba munir ke son magana da kai'' kafin ya ƙara cewa komai yaji Muryar Abban
'' Assalamualaikum faruqu''. '
' Abba an yini lapiya''. 
'' lapiya kalau tambayar ka nake son yi''.
 '' Allah ya sa na Sani Abba''.
 '' kama sani, shin kana son yar uwar ka Anisa ko baka son ta?''

Kan shi ya ɗago suka haɗa ido da ita dan har yanzu suna kan dining ɗin, kai ta kawar tana cuno baki gaba tana mai ƙunƙuni, wani murmushi ya saki da har seda hakwaran sa suka fito ya ƙara riƙe wayar da kyau kamar ana tambayar sa rayuwarsa ne

''hello hello, Umaru kana ji na'' Abba Munir ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi, tashi yayi ya bar wajen dan ba zai iya bada amsar nan a gurin ba. '' eh Abba ina ji''. '' to ka amsa mun tambaya ta mana'' 

Kafin ma yayi magana Mamee ta ce. '' to ai bazai iya ba tunda ba son ta yake ba cusa mai ita akayi dan anfi ƙarfin sa''. ''a'a Abba wallahi ba wanda ya cusa mun ita, ina sonta da dukkanin zuciyata, ina mata son da ban taɓa yiwa wata ƴa mace ba a duniyar nan bayan iyaye na'' 

 wani zabura Mamee da Mama sukayi a lokaci ɗaya dan amsar Ahmad bata basu mamaki ba dan tun can sun san labarin soyayyar shi da Nabila har sanda 
Zulaiha ta taɓa kafa mata warning ma, amma basu taba tunanin Umar na son Anisa ba a dai yanda halin sa yake basu taba tunanin ze so wai ƙanwar sa ba gudun raini ko wani abu 

'' to kana son yar uwar ka Amra''.
 '' Ni!!! me zanyi da amra ana zaune kalau Abba, yarinyar nan da ko isasshen kamun kai bata dashi uwa uba tsafta''. 
 '' tambayar ka akayi tsaftar ta da rashin kamun kanta ko in kana son ta da zaka ringa aiba ta mun ƴa''. 

Mama ta faɗa cikin ɗacin rai dan a tunanin da take koda ace Mamee ta gama musu kumfar bakin da tasan idan ma haɗawar ne sedai Amra da Umar tunda shine aka cusa wa ƴa amma tasan da kyar daman Zulaiha Ammah ta amince, yanzu kuma wai ze zo mata da wannan banzan maganar wai yana son ta

'' to shikenan Faruq se ka dawo ayi aiki lafiya''.
 ''ameen Abba Nagode''.
 Yana katse wayar ya kalli Mama da Mamee yace
'' kun dai ji da kunnen ku ba wanda ya tursasa su, zaka iya tafiya Ahmad Allah yayi albarka''. Tashi yayi ya amsa wayar sa ya fice daga parlourn 

''Mufita anan shine ku haƙura Allah zai kawo wa naku yaran mazaje na gari bawai ku ringa ƙoƙarin cusa su inda ba son su ake ba, daga baya kuma idan abu yaƙi yiwu wa a ɓata zumunci madadin gyara wa''

'' yanzu Abba wannan shine mufitar? ai Adda na faɗa miki ba son mu suke ba a family dinnan saboda mune mara sa wadata bamu da arziki, shi yasa baza ayi da namu ba ni gani nake ma duk wannan haɗin baki ne'' 

'' to idan haɗin bakin ne anyi din, auren yaran kunne dai Umar ko Ahmad ba wanda zeyi acikin su, aje a mun cusa musu yaran namu, kuzo ku cusa nakun mana, aikin banza'' Amma da suka fara kai ta bango ta faɗa, Ammi ce ta rike hannun ta tana girgiza mata kai amma tayi biris tace.  
'' adda ki bar ni wallahi sun fara kaini bango, nan aka kira yaran da suke iƙrarin cusa musu auren aka yi suka faɗa da bakin su amma kuma tana son ta ƙara tado wani fitinar''

'' ya isa haka Juwairiya ban son jin bakin ki kiyi shiru a gurin nan, tunda su basa jin nasu bakin'' shiru tayi bawai dan ta gaji da magana ba se dan ba son musu take da Abba Munir din ba

Anty da Mommy Kam ba wanda yace komai, ita Anty tsoron rigima yasa ta yin shiru da kuma bata da abin cewa, itakam Mommy tsabar takaici ne da kuma tasan ta buɗe baki abun ba zai yi musu kyau ba ita da Mamee shiyasa, Abba Munir ne yace. '' Hafizu yi mana addu'a dan ina ganin ba sauran abinda ya rage kowa yaje yayi abinda ke gaban sa''

Gyara zama Abba yayi, yana mamakin rashin hankali irin na Mamee kuma sai a yau ta ƙara tabbatar mai bata dashi, suka yi addu'a kowa ya kama gaban sa da wanda jikin su ya mutu da wanda zuciyar su take ta fasa da wanda hakan ya musu daɗi duk suka tafi, su Mommy part din Ammi suka yi su kuma su Daddy suka fita dan yin issha da aka ƙira,

Hange hange take dan ganin inda yake, tun ta fito gaban ta ke faɗuwa dan ba wanda ma ya ankara da fitowar ta, ta ku taji ta bayan ta a hankali ta juya dan ta tsorata, tana juyowa sukayi ido huɗu


Arewapen please 🥹 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 follow and like my account 
____________________
By 
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***