NUFIN ALLAH

53

by @anisamuhammadyah897


💕 NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Page 5️⃣3️⃣

A ɗan tsorace ta juyo dan ganin waye a wajen ta hange shi jin gine da bangon dake gurin ya ƙure ta da ido, fuska ta kwabe tace

'' Allah naji tsoro yah'', bece da ita komai ba ya ƙaraso inda take, baya ta ɗan yi, ita fa bata san dalilin da zai wani ce ta same shi a waje ba harda wani wai ta saka hijab, da badan sanda ya mata wannan text din yana gurin ba kuma ga alamar ta gani ba abinda zai sa ta fito ko ta nuna taga saƙon nashi 

'' let's go '' ya faɗa yana gaba, baya ta ɗan ƙara ja kamar ace takk ta zura tace
'' ina zamu je'' be amsa ba sai tsare ta da yayi da waɗannan idanun nasa, '' ban faɗa ma Momma na fito ba bara..'' shiru tayi ta kasa cigaba da musun, shima jin ta ƙatse kanta da kanta yasa shi juyawa ya cigaba da tafiyar sa hankali kwance 

Juyowa yayi yaga har lokacin bata fara tahowa ba ya kara kafe ta da idanu, sai lokacin ta fara tafiya kamar an fasa mata kwai a ciki, tana raya ina zasu je a ranta 

Motar ya buɗe mata be ce komai ba itama ta shiga ba tare da ta ƙara mai magana ba, shima shiga yayi yaja suka bar gidan 

'' ke wai ina pixie ne, Ban ganta ba tun ɗazu'' 
Nabila dake chatting ta ɗago ta kalli Jalila da tayi maganar tace
'' wannan yarinyar kuma ita tasan inda ta shiga, maybe ma tana garden ɗin Momma tunda kin san halin ta da parrots''
Ta cigaba da abinda take yi,zama Jalila tayi kusa da ita tace
''aikam dai se ma wannan shegen akun nata wai tsire, ko wani shegen suna ne tsire oho''
Dariya Nabila tayi bata mata reply ba, se murmushi da take ta faman zabgawa 

''wai me kike yi haka ne'' ta kwace wayar 
'' pickles bana son iskanci wallahi zo ki bani waya ta''. '' Bazan bayar ba ai kema kika amsa wayar mutane bincike kike musu dan haka saina ga me kike yi''
'' wai ku za'a iya samun ranar da zata zo ta wuce ba kuyi tsokana ba ko guje guje kamar yara'' Fareedah dake Bacci hayaniyar su ta tashe ta ta faɗa da Muryar bacci tana ɓata rai 
'' to sannu babba'' suka faɗa tare 
'' ai da yake ba ita ake yi ne zata wani ce haka''
'' idan kin yi hakuri kwana nawa ne za muyi aure mu bar ki a daina wannan ɗan enjoyment ɗin, sai kin ƙara ganin mu ai kuma lokacin kowa ba zeyi ba''
'' to mara kunyar amarya, ke gaba ɗaya kin dawo mara kunya tun ba'a yi auren ba ma''
'' eh ya son ranki Hajiya''

Gamji suka je, da mamaki take kallon shi, me za suyi a park kuma?, yana jin yanda idonta ke kallon shi ci keda tsoro da mamaki, amma be ce da ita komai ba sai tuƙin shi daya cigaba har suka je bakin gate yayi paying aka basu ticket din shiga 

'' bafa na son kallo, menene??"
'' yah me kuma za muyi a gamji,ban faɗa ma Momma bafa na fito zasu neme ni, mu koma Please!!!''
'' kin cika mun kunne fah'' ya faɗa yana juyowa ya kalle ta, idon ta fall kwalla ƙiris take jira su zubo, tayi tunanin fa ita wani ma maganar ze mata yasa ta fito ko su jalila basu sani ba dan ma kar su mata tsiya 

A ranshi yace '' ya ilahi, shi ya rasa me yake tunani da zai ringa amfani da shawarar Ahmad gashi nan zata mai kuka ba gaira ba dalili kamar wacce ya sato 

'' kin san Allah kika kuskura kika bari hawayen nan suka zubo am going to deal with you'' ya faɗa da ɗan faɗa faɗa, duk tana neman jagula mai lissafi, ganin tana goge hawayen tayi shiru, sai kuma yaji be kyauta ba faɗan da ya mata dan tana da gaskiya 

Ya kuma tuna Ahmad yace mai ''faɗa da haɗe rai Man bashi zai sa ta saki jiki ta so ka ba fa, ko ba zaka sake wa kowa fuska ba atleast dai banda ita, taya zata yarda ta raɓe ka kana mata waɗansu muzuran da wani ciccin magani, idan zaka saki fuska malan ka saki fuska kamar yanda idan muna tare kake yi ko fiye da haka ma'' 

Boyayyen numfashi ya ɗan sauke se ya kalle ta yace ''mu shiga'' fuska ta marairaice ta kalle shi amma bata ce komai ba tayi kokarin bude handle ɗin amma ya sa lock, kallon shi tayi sai kuma ta saki handle ɗin, cire lock ɗin yayi ya fito sannan ya buɗe mata itama ta fito

A hankali take bin bayan shi kamar wata wadda za'a sace dan ita ba kaunar fitowar nan tayi ba ga fargaban idan sun koma me zata faɗawa Momma dasu wadancan iyayen gulman, tunda itama b sanin fitowa daga gidan za suyi ba da ta faɗawa Momma 

Mini zoo din gurin suka fara nufa, dabbobin gurin gwanin sha'awa amma tsoron su take ji, ko a Kano idan akace suje zoo kin yarda take sedai su ya Ahmad suje su kaɗai ta gwammaci zaman ta gurin Ammi ko Amma Wani lokacin ma taje gidan Anty suyi ta game dasu Ashraf, a cewar ta wai dabbobin idan suka zama loose waye ze temake ta ita ba iya gudu tayi ba sedai su cinye naman ta a banza

Yah Ahmad ne yace '' to ke banda ma shiritita da shirme a ina kika ga ana sakin su harda za su fito su cinye mutum'' 
'' barta fa yaya iskanci ne irin nata da shegen tsoron tsiya'' 
'' wai ku kuke ma wahalar da bakin ku tunda bata so ku barta now tayi ta zama a gida'' Nabila ta faɗa cike da takaicin se lallaɓata suke taki yarda suna ƙara ɓata musu lokaci tunda tasan halin Anisan idan ta kafe kamar wata tsohuwar babur, suma nacin tsiya yasa sai kokarin sata suke bayan sun san ba zata je ba

'' wallahi idan kuka biye mata dare ne ze muku kuma idan dare yayi ba inda zaku gwara ku tafi tunda ita bata son zuwa''
'' yauwa Anty nerh kidai faɗa musu ko ana dole ne''

Tsabar tsoro bata san sanda ta riƙe rigar shi ta baya ba sanda suka tsaya gaban cage din wani goggon biri 

Juyowa yayi ya kalle ta yaga yanda ta cukwikuye mai riga har ya fara squizing har ya buɗe baki zai yi mata magana sai kuma ya kyale, wani me fruits ya hanga yace '' ina zuwa''. '' zuwa ina??'' ta tambaya ko gama maida yawu be yi ba, kana ganinta kasan gaba ɗaya a tsorace take, dariya ta nemi bashi yanda duk ta firgice kamar wadda aka ce gata ga zaki a gabanta



Follow me on arewapen danAllah 🥹🙏🙏🙏🙏🙏🙏


______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***