NUFIN ALLAH

54

by @anisamuhammadyah897


💕 NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad Yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Page5️⃣4️⃣


Yana jin ya cigaba da amfani da shawarar Ahmad ze kai shi ya baro ne kawai dan yaga alamar so yake shima su raina shi yanda suka raina Ahmad ɗin, ɗan haɗe rai yayi ya koma mata dai Yah Umar din da tasani yace

''Sake ni! ki jira ni inje in dawo ba nisa zan yi ba'' 
Duk da taga ya haɗe rai ba kamar sanda suka shigo ba hakan be sa ta kyale mai rigar sa ba dan wani mugun tsoro ne ya ƙara ka mata '' kar dai ace ma ya kawo ta nan ne ya cilla ta su lions din gurin su cinye naman ta, ko siyar da ita ze yi, in ba haka ba me yasa kawai tana zaman zaman ta zai kira ta daga kira sai zuwa nan bayan ko Momma bata faɗa mawa ba, ba wanda yasan sun fito tare

Tana gama tunanin ta rushe mai da kuka tana kiran '' innalilahi wa inna ilaihir raju'un, wallahi idan na Barka ya Faruq gudu wa zaka yi ka barni anan lions din gurin su cinye ne, wallahi ba inda zan bari kaje ka bar ni'' 

Tana maganar tana ƙara cukwikuye mai riga, tsayawa kallon ikon Allah yayi, jin za ta tara mai jama'a dan wasu har sun fara juyowa suna kallon su ne yasa ya ƙara haɗe rai ya ɗan daka mata tsawa, duk da tsawar ta bata tsoro bata sake shi ba dan tsoron barin ta a gurin yafi na tsawar da yake mata

Shima ganin hakan ba aiki zai yi ba sai ƙara tsorata ta da yayi ne yasa cikin wani irin murya na kwantar da hankali wanda shi kanshi be san ya iya ba yace
'' ki sake mun riga ba inda zan je in bar ki, ba inda Umar zai tafi ya bar Anisa, ke mallaki na ce da bazan taɓa iya nisa na rabu dake ba, taya za'ayi in tafi in bar ki uhmm, ba inda zan je gurin me fruits ɗin can zan je '' ya mata nuni da inda me fruits ɗin yake zaune da cart din shi 

Duk da kalaman nashi sun shige ta amma ta kasa kyale rigar. '' ki kyale ni idan ba haka ba kuma inyi tafiyar tawa in bar ki''. '' to muje tare''. Ita fa ba zata yarda ya bar ta bane duk da ba son zuwa zoo take ba yau ɗazu kafin yace zai tafi ya bar ta se taji ta so safe a tare dashi har tana jin kamar ba abinda zai cutar da ita dan tana side din shi ta riƙe rigar sa, amman ya wani fara kiran ze je ya dawo

'' ya ilahi, nidai yau Ahmad ya gama dani ni ne har da wani kashe mata murya, gashi yau of all people wannan scary cat din na neman caja mai head''
Yayi maganar a ransa yana dana sanin daukar shawarar Ahmad ɗin ai wannan ya gama ja mai raini a wurin ta, shi fa like what's he even thinking ze dauki shawarar wancan mahaukacin

'' mtswww muje amma ki sake mun riga''. A hankali ta saki rigar amman tana an kare idan taga yayi ƙoƙarin gudu wa za ta riƙo shi, a haka suka taka har gaban mai fruits din, idon nan nata har yayi ja dan masifar tsoro irin nata

Ayaba ya siyo bunch ɗaya suka dawo inda su monkeys din suke, guda ɗaya ya miƙa mata ta amsa yace '' ki jefa mai''. Waro ido tayi tace ''ni!!!! A'a nidai bazan iya ba ya haɗa da hannu na, a'a''

Dariya ta bashi wanda seda ya ɗan murmu sa duk da be so hakan ba ya ɗan kauda kai, ɗaya ya ɓalla ya wurga ma birin, shi kuma ya cafe seda ya ci tukuna ya fara musu wasa da tsalle tsalle wanda yake kusa da su ma suka fara kuka, 

Rigar sa ta ƙara riƙe wa kam ganin yanda suke faman tsalle tsalle, numfashi ya sauke yana dafe kai shi ya rasa wannan wani kalan tsoro ne da ita ace suna cage taya za'ayi su taɓa ta

'' ki wurga mai ba abinda ze miki ''. A tsorace ta wurga ai kam yayi saurin cafe wa yana bubbuga kirji yana washe hakwaran nan nasa masu kama da ruwan goro, itama murmushi tayi ta juyo ta kalle shi, yanda tayi abun kamar wata ƴar ƙaramar yarinya, hannu ta mika mai alamar ya ƙara mata wani

Biyu ya ƙara mata, cike da farin ciki ta amsa ta wurga, tana ganin ya rike ta ɗan yi baya kaɗan amma ganin ba abinda zai mata kamar yanda ya Faruq ɗin yace yasa ta ƙara sakin jiki suka je cagin na kusa da shi tazo wurga wani security yace musu ba'a basu abinci iya kallo kawai zaka iya yi, cikin yanayin rashin jin daɗi ta kalli securityn tace
'' daga wannan ba zan ƙara ba'' ta nuna mai na hannun ta, yanda ta marairai ce fuska ne kamar wata yar karamar yarinya securityn yace. '' to kyakkyawa wannan ne na ƙarshe''. Wani mugun kallo Faruq ya mai kafin ma ta wurga ya ja hannun ta suka bar wajen cike da ɗacin rai, har ta bude baki zata yi mai magana amma ganin yanda ya wani haɗe rai one time kaman bashi ya gama mata murmushi ba yanzu yasa ta haɗiye abinda zata ce, a zuciyar ta tana tunanin kodai yana da aljanu ne, dama fa ita ta daɗe tana tunanin nan, kamar wani me shafar jinnu, yanzu kaga ya haɗe rai anjima yayi murmushi, can kuma yace baya son kallo bayan yafi kowa iyawa, mostly Kuma baya son raini wani lokacin kuma in ya mata abu sai ta kasa gane kansa, kamar ranar da ya mata shopping ga ranar da ya saka sai ta sha ice cream ga kuma yau ya wani kawo ta nan duk da dai ta fara jin daɗin fitowar 

Tunanin ya katse mata wanda ita bama tasan har sun iso bakin motar ba dan bin shi kawai take ba wai dan tana ganin gaban ta ba. '' tunanin wancan banzan securityn kike yi da ya ke wani yashe miki matattun hakwaran sa, har ba kya jin ina miki magana''. Kallon sa tayi tana mamakin me yasa za tayi tunanin security ita kam,

'' ki ma cire wannan banzan maganar da ya miki ba wani kyau, ko wancan abubuwan albarka, Wani banza dashi a wajen''. Rai ta hade sosai tana jin kwalla na neman Zubo mata amma bata basu dama ba se dai sun cika idanun ta fal, itace me kama da goggon birin ke nan, shima ganin zata mai kuka yaji kamar be kyau ta ba na faɗan da yake mata, tun da ai ba laifin ta bane, ya yi niyyar da farko ya bata hakuri amma jin kan sa ya hana shi maisa ma zai bata hakuri bayan ita ce ta fara wa wannan wawan mutumin magana,

Motar ya shiga ya kyale ta a wajen, har ya tayar bata ƙaraso ba seda ya fara ƙoƙarin kamar dai zebar wajen ya kyale ta sanan ta nufo Motan jiki a sanyaye daman tasan ba sonta yake ba hasashen su Nabila ne kawai amma kalla yanda ya gasa mata magana yanzu har da farko ta fara gasgata zancen su amma itama laifin ta ne ko ta manta waye Ya Umar dama dai wannan haɗin su Mommy ne kawai amma bata jin yana wani sonta kamar yadda suke faɗa 

Yanda bata son shi shima ba sonta yake ba, tunanin hakan ya saka taji wani abu ya to kare mata a zuciya da ta rasa dalilin hakan, gashi yau ko dan bude mata kofar da ya saba ma beyi ba, sai ta ƙara jin ta duk a takure saboda yanda yake haɗe mata rai ya mayi kamar ba ita a cikin motar 


Follow me on arewapen for more 🥹🙏🙏🙏🙏


______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***