55
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad Yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page5️⃣5️⃣
Ganin tafiyar tasu taƙi ci taƙi cinye wa yasa ta kalle shi amman ta kasa cewa komai saboda yanda ya haɗe rai
Ba shida niyyar koma wa yanzu da badan ma wannan banzan ya bata mai rai ba so yake se kamar an kusa magriba haka sannan bayan sunyi sallah a wajen se su baro gamjin dan da daddare yafi daɗin zuwa, amman yanzu gaba ɗaya be fi ma 5 wani abu ba, dan seda suka yi laasar kafin suka fito
Garin suka ringa zagaye wa seda ya gaji sannan ya dau hanyar gida, a wani suya spot ya tsaya ya siya sannan ya dawo suka cigaba da tafiya, tun ya shigo yake satar kallon ta, ganin yanda ta wani marairai ce fuska kamar zata yi kuka yasa yace
'' me yafaru''. Juyowa tayi ta kalle shi ta wani haɗe rai itama tana cuno baki, bayan ya gama ci cimma ta magani har yana haɗa ta da wannan birin shine yake tambayar ta me yafaru, banza ta mai taƙi ta tanka shi kamar bata ji ba ta juyar da kanta tana ƙunƙuni tana cuno baki gaba
Yanda tayi gaba ɗaya se ta bashi dariya haka nan yake jin zuciyarsa na washe wa, kai ya girgiza kawai yace. '' ba magana nake miki ba''.
'' To Yah ni me zance na fito ban faɗa wa Momma ba, nasan na koma waɗancan masu bakin akun ba bari na za suyi na huta da tsokanar su ba, sannan yah ka kawo ni gamji duk da ina jin tsoro da tunin za ka gudu ka bar ni kuma ka ce wai ina kama da goggon birin nan ''. Tayi maganar kwalla na zubo mata dan taji zafin na goggon birin nan
Burki yaci ba shiri, motar dake bayan sa ce ta fara mai horn Allah ma yaso ba wasu motoci a titin ma, ya shawo kwanar titin unguwar dosa unguwar su Momma kenan
'' Ni a yaushe nace kina kama da goggon biri??'' ya faɗa jin zata mai sharri dan har ga Allah shi be san sanda suka yi haka da ita ba, kallon shi tayi cike da haushi, daman haushin shi take ji kuma yanzu se ta amayar mai da abinda ke ranta
Kasa amsa mai tayi se hararar da ta mai da bata ma san tayi ba tana kara cuno baki ga kwalla da ya cika idon ta, da kallo kawai yake bin ta, yana ganin ikon Allah yau bayan ɗazu taga mai tsoro da yarin ta yanzu kuma tsiwa take ji da shi
'' ki faɗa mun yaushe mu kayi haka da ke''.
'' ba ɗazu bane kace ina kama da goggon biri da zamu fito''. Kallon ta yayi yana son tuna exact statement da yayi dan yasan ko giyar wake yasha ba zai taɓa iya faɗin haka ba
'' kuma abinda na faɗa kenan??''. '' ba exact abinda ka faɗa ba kenan buh ai haka kake nufi''. Ajiyar zuciya ya sauke ya kure ta da ido, yanda ta dage wai ita lallai haɗe rai take ne ya bashi dariya, kai ya kawar gefe ya ɗan murmu sa aiko akan idon ta, kwallar da take riƙewa ne ya sakko, wato ya ma maida ita mahaukaciya shiyasa yake mata dariya
'' me yasa su Jalilan zasu tsokane ki??'' ya mata tambayar yana kafe ta da idanu, baki ta cuno ta kauda kanta bata ce komai ba
'' yau na ga alamar dai na sake miki da yawa har kike son se kin raina ni koh??"
baki ta ƙara turo wa tace. '' Nima ban san musu ba''. ''Hmmm'' kawai yace ya tada motar suka cigaba da tafiya, shi statement din da yayi ma da yayi akan securityn wajen ne amman ita ta juya mai zance
Har suka iso bakin kofar ba wanda ya ƙara cewa komai se kallon ta da yake a kai akai, ita ko ta haɗe rai dan ita har ga Allah wannan kallon nashi na mugun takura ta, kai ta ƙara kauda wa tana ƙunƙuni ƙasa ƙasa, banda ɗazu gaba ɗaya yau ta faranta mishi rai
Suna yin parking yayi saurin sa lock kafin ta fita kallon ta yake yi cike da shauki da tsantsar so, itama kallon shi tayi duk tayi narai narai da fuska tunanin me zata ma ce wa Momma take yi ba ta tambaye ta ba ta fita daga gidan duk da dai ba ita taso fitar ba
'' ki sa a ranki Umar Faruq ba in da zai taɓa tafiya ya bar Anisa, zan zama wani bangon jingina a rayuwar ki a koda yaushe In Sha Allah, bazan kara zama wani dodo a idon ki ba daga yau se na cire wannan kallon da kike mun a matsayin wani mugun yaya ko wani dodo a bun gudu, Faruq a kullum me son Anisa ne, zan nuna miki soyayyar da baki taɓa tunanin zan iya miki ba''
Kwakwalwar ta ce ta tsaya na ɗan wani lokaci, anya daga bakin ya Faruq ta ji wannan zance, gaskiya bata tunanin shine wani abun ne daban ya shige shi ba shi ke mata wannan zancen ba, daman tasan yana da aljanu, to tana tunanin ɗaya daga cikin sune ya bayyana yanzu
Ƙarar kofar da ya buɗe ne ya dawo da ita hayyacin ta ta ɗago ta kalle shi tsaye a bakin kofar ta, gira ɗaya ya ɗaga mata alamar meye, saurin kauda kanta tayi zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri ta rasa dalilin da yasa take jin hakan, tun ya fara magana take jin zuciyar ta na bugawa da sauri,
Ba wai waɗansu kalamai yayi mata masu yawa ba amma aciki ta gane saƙon da yake son isar mata, ita tasan bata son ya Umar amman ta rasa dalilin da yasa zuciyar ta a kullum in ta gan shi ko taji muryar sa take doka wa, ta rasa me yasa wannan kalaman da ya mata yanzu suka saka ta ji ta kamar wata sarauniya a duniyar ta, ta rasa me yasa take jin ta so safe in tana tare da shi duk da idan ya kafe ta da wannan idanun nasa se ta ji ta a takure, ta rasa me yasa a kwanakin tun ya dawo take jin tana ɗan iya sakewa da shi ba kamar da ba, ta rasa ta rasa, ta rasa abubuwa da yawa mai yasa suke faruwa, tasan dai wani dalilin ne can daban amma bata son shi, ita ba wanda take so, dan Ammi kawai zata yarda ayi wannan auren
''ba kya son fitowar ne??'' ya watsa mata tambayar ganin kamar ma bata da niyyar fitowa, numfashi ta sauke ta fito jiki a sanyaye dan tambayoyi ne da yawa da ta rasa me amsa mata suke yawo a kanta
Suna zuwa bakin kofar parlourn ta ci burki ta kasa buɗe kofar bare su shiga, ganin ta tsaya ne yasa shi tura kofar ya shiga, ya juyo ya na mata nuni da ta shigo, kamar munafuka haka ta shigo, cikin rashin Sa'a kam duk suna parlourn ana shan hira, duk ido suka zubo musu, ganin haka tayi ƙasa da kanta, zuciyar ta na bugawa dan tsabar rashin sanin abinda zata ce
Follow me on arewapen for more updates 🥹 🙏 🙏 🙏 🙏🙏 🙏 🙏
___________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***