58
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad Yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page5️⃣8️⃣
'' Amarya Amarya, se yau kika tuna da ni tun kuka tafi ko har hey ɗinnan babu''
'' kiyi hakuri Leema wallahi abubuwa ne da yawa suka ɗauke mun kai amma ba gashi yanzu na miki magana ba''
'' ai kin kyauta, ya KD ya su Nabs da Jalys''
'' duk suna lapiya Leema, I want to talk to you, magana ne me muhimmanci, bana son yin maganar da Jalila ko Nabila kuma bazan iya yin ta da Fareedah ba''
'' lapiya?? Allah dai ya sa lapiya ''
'' to za'a iya cewa lapiya, Leema akan ya Faruq ne''
'' me ya miki, innalilahi wainnailaihir raju'un meya faru?''
'' ke Matsala dake over worrying ba abinda ya faru but yana son faruwa''
Labarin changes din da ta samu a wajen shi har abinda yace mata ɗazu da kuma yanda take jin zuciyar ta ta faɗa mata
'' Anisa''. '' na'am ''. '' irin shawara na kike so in baki ko irin shawarar da zuciyar ki ke so in baki''
Dariya tayi a fili ta ja ɗan guntun tsaki, duk ido suka zobo mata, ta kawar da kanta gefe, '' wanne ne kuma shawarar da zuciyar tawa take so, da tana da shawarar da take so ai bazan neme ki ba''
'' haka dai kika ce amman tana da shi, kawai dai kin ki kuyi accepting abun da take so ne, ko ki so ko kar ki so kina son ya Faruq kema, which is a good thing, amman shawarar da zan baki duk da dai ya sakko ya ajiye wannan baya son raini attitude din nashi, kee riƙe kunnen ki da hannu ɗaya ma ki saurare ni da kyau''
'' inji wa yace Miki ina son shi?, ni ba wani son shi da nake yi, to Anty Leema na riƙe ina sauraron ki''
'' kedai kika sani, tunda dai ni nasan kina son shi kiyi ta denying, yauwa abinda zance miki shine duk da ya fara sake miki fuska kar kiyi saurin bada kai bori ya hau in ba haka ba ze ga ya same ki a ɓagas ne, saboda ya nemi auren ki kwatsam ba da yardar ki ba, kuma kin amince, yanzu kuma yana son shawo kanki ne ki amince da shi ba tare da ya furta yana son ki ba, to shawara ta anan shine kisa shi se ya furta da bakin sa kafin ayi auren nan, ki nuna mai duk jiji da kan namiji a tafin hannun mace yake, ina son ki sauke mai wannan jin kan nashi ke ko baki sa shi kuka ba kisa ya durƙusa miki, kin gane Kohh''
Ganin abinda Leema tace seda ta waro ido Ya Umar fa, shine ze durƙusa mata bare ma ya mata kuka,
'' Ya Faruq din? gaskiya baki san waye ya Faruq ba shi yasa, yanzu ma ina mamakin da akacye wai ni kanwarsa yake so balle akai ga ya durƙusa mun har ya kai ga mun kuka''
'' ke namiji ne fa, ke kuma mace, a yanda na fahimta wallahi yana mugun sonki, irin sosai ɗin nan da zeyi fiye da hakan dan ki amshe shi, gashi har ya iya sauke girman kan shi saboda yasan ba kya sakewa idan yana cin miki magani yana haɗe miki rai, to wallahi idan kika yi sake sai ke ya raina kin, kin dai ji na faɗa miki, kuma kika bari ke ya raina ki ya raina irin capacityn ki da ƙimar ki a wajen shi to kina cikin yanayi, kin jini ko baki jini ba''
'' naji ki Malama Halima''. '' faɗi ki ƙara lectures zaki fara ɗauka yarinya daga yau indai zaki yi abinda nace, in Kuma baza kiyi ba to kanki, wannan shawara ce ta ragewa mai shiga rijiya''
Dariya sosai take yi Nabila ce da ta gaji tace
'' Malama wai ke lapiya kuwa, ko kin fara taɓuwa ne''
Kasa bata amsa tayi se Jalila ce tace
'' wallahi dai Anisa kin samu matsala ko duk auren ne''
Dariya ta ƙara bata, itakam Fareedah kai ta girgiza tace
'' Allah ya kyauta miki''
'' wai kunje kun duba umma tunda kuka zo kuwa?''
'' eh Momma ko ɗazu da safe mun shiga mun gaida ta''
''Allah sarki yar tsohuwar mu da ido kawai take bin mutane ba bakin magana''
'' ai dole ta daina ma yunƙurin maganar tunda ko ta ma yi ba ganewa ake ba'' Nabila ta faɗa jin abinda Fareedah da Anisa suka faɗi
'' Allah dai ya yaye mata wannan ciwon daya ƙi ci ya ƙi cinyewa, wannan har gwara ta mutu tasan ta huta, idan na ganta tausayi take ba ni shiyasa bana mason zuwa ɗakin ta'' Jalila ta faɗa
'' to ce miki suka yi suna son ta mutu ai zata warke In Sha Allah ''
'' Allah yasa Anisa, amman ai addu'a me kyau tayi indai shine hutu a gare ta, idan kuma Allah ya tayar mana da ita ma muna so da fatan haka''
Momma ta faɗa kwalla na ciko wa kurmin idanun ta dan halin da mahaifiyar tata ke ciki na damunta, barin ma yanda tana wannan ciwon amman Abida da Shaheeda suka juyawa uwar da ta haife su baya
A baya da Umma ke tunanin gata take musu bata kwaɓar su idan sunyi ba daidai ba, duk abinda suke so shi za suyi ashe ba gata take musu ba, tafi fifita su a kaf yaranta amman sune waɗanda suka juya mata baya yanzu suna kyankyamin ta
Sanda papi ya rasu Umma ta shiga cikin depression sosai sosai ga Abida tun bayan da ta gama iddah da kyar da kyar ta fara yawo, ita ce can itace nan, ga ba kowa a gidan daga ita sai Abidan dan Muneef gidan ya bari ya koma Kano wajen Abba Munir da zama ya fara koyan kasuwanci dan daman ba wani aiki ne na Company ya samu ba shiyasa da yaga takaici ze kwasa ya bar musu gidan
Kwata kwata Abida bata jin maganar ta a cewar ta harda ita aka haɗa baki aka raba ta da mijinta me kaunar ta dan haka dukan su munafukai ne, a garin yawon ta zubar ɗinta ta jajibo ciki, nan ma hankalin Ummah ya ƙara tashi ta rasa inda zata saka kanta, itama Abidan hankalin ta tashi yayi, taso zubarwa amma yaƙi ya zube se da kyar
Follow me on arewapen for more 🥹🥰🙏 🙏 🙏 🙏🙏
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***