61
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad Yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 6️⃣1️⃣
Gaba ɗaya Ya Faruq ya kasa sanin yanda ze shawo kan Anisa duk ya shiga damuwa, idan ya ƙirata zata dauka zasu gaisa bata kuma bari maganar ya wuce haka gashi Momma tace kar ta sake ganin ƙafarsa a gidan ta sai an fara hidimar biki dan saura baifi 2 weeks ba bikin,
Ahmad ya samu da maganar dan abun na ci mai tuwo a kwarya, labarin kulawar da yake nuna mata ya bashi da yanda take mai responding, amma kuma yana bayyana masa cewa har yanzu Anisa ba ta nuna masa wata alamar soyayya.
Ya Faruq ya ce, “Ahmad, wallahi wani lokacin nakan ji kamar ni kaɗai nake son wannan auren, ba ta wani sona kamar yanda kake faɗi. Ina ƙoƙarin ganin ta saba da ni, ta daina jin tsorona, amma har yanzu ban san abin da ke zuciyarta ba.”
Ahmad ya kalle shi, ya ɗan yi murmushi.
“Amma kai ma Faruq, me kake tsammani? Ka san cewa yarinyar nan ba ta zaɓe ka saboda soyayya ba tun farko. Ka ba ta lokaci.”
girgiza kai Faruq yayi ya sauke ajiyar zuciya.
“Na san haka Man, amma na fara tunanin ko har bayan aure ma ba za ta taɓa sona ba.”
Hannu Ahmad ya ɗora a kafaɗarsa ya ɗan bubuga.
“Idan kana sonta da gaske, ka ci gaba da nuna mata cewa za ta iya samun kwanciyar hankali a tare da kai. Amma kada ka tilasta mata ta nuna maka abin da ba ta shirya furtawa ba yanzu, kayi hakuri ka jure ka bata time.”
Shiru ya ɗan yi na wani lokaci. A zuciyarsa, yana son ya ji kalma ɗaya daga bakin Anisa da za ta tabbatar masa cewa akwai ɗan ƙaramin wuri da yake da shi a zuciyarta.
Kafin yace “ Wani lokaci nakan ji kamar ina ƙoƙarin gina gida ni kaɗai.”
Ahmad ya so ya gaya masa abin da ya fara zargi, amma sai ya yi murmushi ya ce
“Ka yi haƙuri, brother, ba kowane mutum ne yake iya bayyana abin da ke zuciyarsa ba.”
A zuciyarsa kuwa yana cewa, Kai Faruq, da ka san abin da ban sani ba a baya, da ka daina wannan damuwar!
Nabila ce ta faɗa mai irin changes ɗin da suke gani a wajen Anisan idan yazo ta wajen Yah Faruq
Nabila ce ta fara lura da hakan sannan ta sanar da su Jalila, ta lura cewa idan aka ambaci Faruq, yanayin ta gaba ɗaya sai ya canja, ko kuma tana tambayar Ahmad game da Yah Faruq kamar ba komai ba idan sunyi waya da Nabila ta basu su gaisa,
Wata rana, Nabila ta same ta ita kaɗai a garden tana wa Bruno surutai, sai ta ce mata cikin zolaya
“Anisa, wai ke ba kya son Yah Faruq ɗin nan har yanzu ko?”
Anisa ta kalle ta da sauri.
“Me ya sa kika tambaya?”
“Saboda kin ce Ammi kawai kike son faranta mawa shiyasa Koh??.”
Ta yi saurin kau da kai.
“peebles, don Allah ki bar ni, labari Bruno ke bani kar ki dame mu.”
Murmushi Nabila tayi, amma bata ƙara cewa komai ba. A zuciyarta ta fara fahimtar cewa wata ƙila Anisa ta riga ta fara son Faruq, sai dai tana ɓoye hakan.
Amma ba zata gaya masa bane, shine ta faɗa wa Yah Ahmad, amma tace kar ya faɗa mai ya bari ya gano da kansa, ba tare da an tilasta wa Anisa bayyana soyayyarta ba. Itama ta ci lokacin ta ai ba wanda yace ya mata shigar kai tsaye,
Biki nata ƙara towa har yanzu ba ta faɗa masa abinda ke zuciyar ta ba, kullum yana cikin damuwa, amman ya linka kulawar da yake bata fiye da da, duk da ba gari ɗaya suke ba amman yawan cin kullum suna tare a waya duk da ba sake mai take yi ba amma yana jin daɗin hakan ma tunda dai har zata ɗaga wayar ai shikenan,
Anisa ta fara lura da wasu abubuwa a kan Ya Faruq da a da ba ta cika kula da su ba.
Idan ya kira ta, ko da kuwa ba su da wani dogon zance, sai ta ji daɗin jin muryar sa. Idan ya yi shiru na tsawon lokaci ba tare da ya kira ta ba, sai ta riƙa duban wayar ta tana mamakin dalilin da ya sa bai kira ba, tayi ta jin zuciyar ta babu daɗi har wani lokacin sai taji kamar ta ƙira shi, to amma ta kira shi tace mai me, kar ma ya fara tunanin son shi take.
Amma da zarar ta tuna shawarar Leema, sai ta girgiza kai kamar wadda ta tuna wani abu mai muhimmanci.
Anisa, ki yi hankali. Kada ki bari ya gane abin da ke zuciyar ki da wuri haka, nafi son ki ɗan gasa mana shi tukuna.
Haka ta riƙa faɗa wa kanta, duk da cewa ita kanta ba ta fahimci abin da yake faruwa da ita ba ko kuma ince bata son karɓar gaskiyar hakan.
A wannan ranar da yamma, tana zaune tare da Nabila suna hira, sai wayar ta ta yi ƙara. Ganin sunan Ya Faruq na yawo a fuskar wayar ya sa zuciyarta bugawa da sauri, ita ta cire tsammanin ma zai ƙira ta,
Nabila da take kallon ta ta ɗan murmusa tace,
“Anisa, wayar ki ce fa, ko in amsa miki?”
Da sauri Anisa ta ɗauki wayar tana galla mata harara dan tasan halin ta sarai, se ta amsa ba damuwar ta bace.
“Ke dai Allah ya kyauta miki wallahi Peebles!”
dariya Nabila ta saki tace
“Allah ya kyauta! Ni fa ban ce komai ba, ganin kamar kina son amsawa amma kin ƙi yasa nace zan amsa miki ko nayi laifi ne, tun naga kin yi haka, ai na san wanda ya kira.”
Yi tayi kamar ba ta ji ba, ta ɗaga wayar.
“Assalamu alaikum.” ta faɗa cikin murya mai sanyi da idan tana magana dashi bata san sanda yake zuwa ba
“Wa alaikumus salam, amarya ta.”
Sai da Anisa ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta amsa. Kalmar amarya ta da ta ji ta shiga kunnen ta taɓa fatar kunnen ta har cikin zuciyar ta.
“ kana lafiya?” ta tambaya a hankali.
“Lafiya lau, na kira ne kawai in ji ya kike, na san ba kya son na, gashi jiya ban kira ba yau ma se yanzu da yamma amman baki tuntuɓe ni kinji ko lafiya ban ƙira ba ko mon Cherie, farin cikin ruhin Umar Faruq”
Kasa danne murmushin da ya bayyana a fuskarta tayi jin abinda yace, a hankali dan kar yaji yanayin murmushi a fuskar ta tace
“Ni na ce haka?”
“Na sani baki ce ba amman haka ne, shi ya sa nake son in koya miki.”
“Me za ka koya min kuma?”
“Yadda zaki so mijin ki, da yanda ake hira da miji ba tare da kina amsa masa da kalmomi biyu kawai ba.”
Anisa ta rufe bakinta tana murmushi bata san sanda ta ajje shawara Leema a gefe ba ta biye mai suka cigaba da hirar su
“Ya Faruq, kai dai ka cika magana, dama wai haka ka iya surutu.”
“Ni ne na cika magana? To, ai idan na yi shiru sai ki ce na daina kula da ke.”
“Ni fa ban ce haka ba!”
“Amma za ki iya cewa a nan gaba, ko ba haka ba?”
Ta kasa ba shi amsa.
dariya yayi a hankali yace,
“Shikenan, ba zan ƙara damun ki da kira ba tunda kamar takura miki nake.”
“ni a yaushe nace haka??”
Se da ta furta ta san me tace, wani kunya ne ya rufe ta duk da ba a gaban shi take ba
Shima cike da farin ciki yace
'' To ga alama nan jiya ban kira ba yau ma sai yanzu amman ba ki damu da hakan ba''
Kasa amsawa tayi a zuciyar ta tace '' hmmm baka san yanda hankalina ya tashi ba, har wani zazzaɓi na ke ji dan baka kira ba, baka san yanda garin ya mun duhu ba ne kake faɗin haka''
A zahiri kuwa ''hmmm'' kawai tace, yace
'' zan yi wani abu yanzu, sai anjima ki kula min da kanki kinji, Mon Cherie, ruhin Faruq''
'' kaima haka''
Tayi saurin kashe wayar zuciyar ta cike da farin ciki, ta daɗe tana kallon wayar tana murmushi.
“Anisa!”
Ta firgita da jin muryar Nabila, gaba ɗaya ta manta ma tana zaune a wajen
“Lafiya?” ta faɗi tana haɗe rai kar ta mata zancen dan wani kunya kunyar Nabilan take ji
matso wa tayi kusa da ita ta dafa ta tana ɗan murmushi tace,
“Wai me ya Faruq ɗin ya ce miki har kika kasa daina wannan murmushin? Tun da kika kashe wayar kike kallon ta kamar kin ga wata taska! Har kin manta dani a nan”
“Ke dai kin cika surutu! Da neman jin kwaf, wallahi ni ki barni”
Nabila ta ɗaga hannuwan ta sama tana murmushi tace,
“To, na ji, amma ki sani, wannan abu kamar a gaban su pookie.”
Pillow ta jefa mata tana hararar ta, murmushin fuskar ta ya gaza ɓacewa, suka fashe da dariya.
Amma a cikin zuciyar ta, ta san cewa murmushin da ta yi ba don zolayar Nabila ba ne. Muryar Ya Faruq ce ke ta sa ta farin ciki.
---
A can Kano kuwa, Ahmad yana zaune a parlour yana chat da Nabila se murmushi yake zubawa, Umar ya shigo, kallon sa Ahmad yayi fuskar sa ɗauke da murmushi.
“Ango, ina ganin ka fara samun sauƙi.”
Zama kusa da shi Umar yayi yace,
“Wane irin sauƙi kuma?”
“Damuwa da amaryar ka, ko dai ta fara nuna maka alamun tana son ka ne?”
Fuskar ta canja yace,
“A'a, Man, har yanzu dai ban ga wani abu makaman cin haka ba, ko jiya dana gwada ƙin kiran ta in gani ko zata kira ko ta tambaye ni lapiya bata kira ba saida na gaji na kira ɗazu shima ko a murya ta ban ji alamar damuwa ba”
Ahmad ya yi shiru yana kallon sa. Ya san Anisa ba ta bayyana soyayyar ta a fili ba, amma ya fara zargin cewa akwai wani abu da take ɓoye wa.
“Faruq, ka yi hakuri, ba za ka iya tilasta zuciyar ta ta yi saurin bin naka ba.”
Ajiyar zuciya ya sauke yana jin zuciyarsa a cunkushe yace.
“Na san da haka, amma ina tsoron kada wata rana ta zauna a gidana tana na damar auren nan.”
Ahmad ya ɗan yi shiru kafin ya ce, “Ka ci gaba da zama mutumin da zai ba ta kwanciyar hankali Man, Kada ka sa ta ji dole ne ta nuna maka soyayya saboda kai kana son ta.”
Gyada kai Umar yayi zuciyar sa na mai ba daɗi.
Amma Ahmad bai gaya masa abin da ya fara zargi ba. Zai jira ya ga yadda abubuwa za su ci gaba, domin yana son abokinsa ya samu soyayyar da yake fata tun da daɗewa.
Sai dai abinda Yah Faruq be sani ba shine,
Anisa ta fara ba Faruq wani gurbi a cikin zuciyar ta ba tare da tasan tana hakan ba, dan ita tunanin ta kawai tana tausayin ganin shi yana faɗi tashi akan ta so shi ne, ba tare da tasan itama ta fara zurfi a kogin son shi ba.
Follow me on arewapen for more updates 🥹 🥰 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏
______________________
By
Anisa Muhammad Yahaya 🌺
***