62
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad Yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)
Page 6️⃣2️⃣
Tun da aka fara maganar shirye-shiryen bikin, gidan ya fara ɗaukar wani sabon yanayi. Ana ta kai-komo,
Su Jalila kam ba a magana, kafa yaƙi ya zauna waje ɗaya su masu biki besties din amare, ana tattaunawa kan kayan da za a saya da abubuwan da za a tana da kafin ranar da kowa yake jira.
Nabila kuwa ba ta bar su Fareedah da Jalila sun huta ba, domin duk lokacin da suka fara maganar event ko wani abu, sai ta tuna musu da wani abu da ake buƙatar yi.
Fareedah tace '' ke wannan amaryar zumuɗin ki ya fiye yawa''
Ita kam Anisa to dai kadaran kada han, bata baƙin ciki, tana farin ciki amman tana ɗan fargaba, ta rasa maisa take farin ciki, ko da yake ai saboda Ammin tane shiyasa zata yi farin ciki da abinda take so
A gidan Ammi kuwa, ko ina ba masaka tsinke suma shiri suke kain da nain, ba ga Anty ba baga Mommy ba ba ga Amma ba,wasu mutanen ma na Mommy har sun fara zuwa daga Egypt dan bikin yanzu saura kwanaki takwas
Ahmad da Faruq kuwa gidan Amma suka koma da zama dan can ne ba wani hayaniya da yawa, a nan zasu fi samun daman shiri me kyau
Da yamma Ahmad ya shigo gidan bayan ya baro wajen abokan su, dan duk yanda Faruq ke son auren gaba ɗaya zumuɗin sa ya koma ciki, A parlour ya tarar dashi zaune yana duba wasu saƙonni a wayar sa.
“Ango Ango, ya shirye-shiryen bikin?”
Faruq ya ɗago kansa ya kalle shi.
“Alhamdulillah, kaima ai angon ne, kuma tunda kai ke mana shirin kai zan tambaya ya komai ke tafiya.”
Zama yayi kusa da shi, sannan ya leƙa fuskarsa, yace
“To, amma me ya sa kake kama da wanda aka gaya wa za a soke bikin?, baka wani shiga harkar bikin kamar wanda baya so, ko ka daina son nata ne?”
Hararar sa yayi yace.
“Ahmad, don Allah ka bar ni da wannan surutun naka, ni gaba ɗaya ba daɗi garin yake mun kwana biyu”
Dariya Ahmad ya fashe dashi yana wani tafa hannu wa.
“Ni fa tambaya na yi maka. Ko dai har yanzu amaryar ka ba ta nuna maka alamun soyayya ba?”
Ajiye wayar sa yayi, ya sauke ajiyar zuciya.
“Wallahi dude, ban san abin da zan ce maka ba. Wani lokaci idan na yi magana da ita, sai in ji kamar tana fara sabawa da ni, amma daga baya sai ta koma kamar yadda take a da.”
Ahmad ya ɗan yi murmushi, amma ya ɓoye shi da sauri.
“Wata ƙila tana buƙatar lokaci ne.”
“Har yaushe zan ci gaba da jira? Na daɗe ina sonta fa kaima shedar hakan ne, Ahmad. Na yi tunanin cewa idan ta amince da auren, zan fara samun wata dama ta kusantar zuciyar ta, ko ban furta ina son ta ba zata ga alamar haka, amman yanzu har na manta sau ɗari nawa na furta mata ina son ta, amma har yanzu ina jin kamar akwai wani bango tsakani na da ita da yasa taƙi amincewa.”
Kallon sa yayi cike da tausayi yace
“Man, ka tuna cewa ba kowa ne yake iya nuna abin da ke zuciyar sa da wuri ba. Kai kana son ta tun da daɗe wa, amma ita fa tana koyon yadda za ta zauna da kai ne, kuma a kokarin koyar zama da kai zata koyi son ka. Ka ba ta damar fahimtar ka.”
Shiru yayi na ɗan lokaci sannan yace
“Abin da ya fi damu na shi ne, bana son ta zauna da ni saboda kawai tana son faran ta wa Ammi rai, dan nasan ba zai wuce dan Ammi zata amince ba.”
Dafa kafaɗar sa yayi yace.
“Allah ya sa abin da kake so ya zama alheri a gare ka.”
Sai ya ɗan yi murmushi ya ƙara da cewa,
“Amma idan ka ci gaba da wannan damuwar, kafin ranar aure sai ka zama kamar wanda aka kwashe masa jini! Ka zama kamar wani zombie”
Duka ya kai mai suna dariya dukan su Umar yace
“Ahmad!!!”
Saurin dojewa Ahmad yayi yace
“Na ji, na ji! Ango ya fusata saboda an faɗi gaskiya!”
Duk da damuwar dake zuciyar sa, ya kasa hana kansa murmushi, shiyasa a ko yaushe yake son ɗanuwan nasa kuma aminin sa
---
A can gidan Momma kuwa, duk suna zaune a ɗaki suna duba wasu yadi da aka kawo musu na girls night. Anisa na riƙe da wani yadi tana kallon sa, amma hankalin ta yana wani wuri.
Jalila ce ta lura da hakan cike da zolaya tace
“Anisa, tun da na fara magana kina kallon wannan yadin kamar kina neman wani abu a cikinsa, Lafiya kuwa?”
Firgigit ta juyo tana kallon su, duk sun tsaya kallon ta Nabila na ƙunshe dariyar ta dan tasan ko ba'a faɗa ba ba zai wuce tunanin Ya Umar take yi ba
“Lafiya lau, me kuma zai faru?”
Nabila ta yi murmushi, tace
“To, shikenan, amma ina ganin akwai wani abu da ya fi wannan yadin ɗaukar hankalin ki.”
Kai ta juya ta kalli Nabila tace
“Me kike nufi?”
“Ba komai, ni dai ina ganin tun da aka fara maganar bikin, kina yawan yin shiru.”
Idon ta ta mayar kan yadin hannun ta tace
“babu komai kawai tunanin na kusa taka wani babban matsayi na rayuwa ta nake”
Gyada kai Fareedah da bata ce komai ba tun ɗazu tayi a hankali tace,
“Wannan gaskiya ne aure babban al'amari ne, amma Anisa, kada ki manta cewa ba sai kin iya faɗin komai a rana ɗaya ba. Ki ba kanki lokaci ki fahimci abin da kike ji.”
Anisa ta ɗago kai ta kalle ta, maganar Fareedah ta taɓa wani wuri a zuciyar ta.
“Ke ma kina ganin kamar akwai wani abu da ke faruwa da ni ne?”
murmushi Fareedah tayi me sauti, ta kalli su Jalila suma suka murmusa, tace
“Ni ba zan iya gaya miki abin da ke zuciyar ki ba. Ke ce kaɗai za ki iya sanin hakan, amma ai ba iya ni ba kowa ya gan ki yasan kina ɓoye wani abu, sedai idan ba'a zauna dake ba.”
Shiru ta ɗan yi, tayi tunanin duk kokarin ɓoye wa da take yi ba wanda ze gane halin da take ciki, to sun gane ta fara son Yah Faruq kenan ko me,
Wayar ta ce tayi ringing, tan dubawa taga massage daga Ya Faruq.
“Mon Cherie, ina fatan kina lafiya. Na san ana shirye-shirye da yawa yanzu, don haka kada ki wahalar mun da kanki. Idan akwai abin da kike buƙata, ki sanar da ni, idan baza ki iya faɗa min ba ki faɗawa ko su Nabila ko Ahmad su faɗa mun, amman zan so ki faɗa mun da kank kin ji ruhin Faruq.”
Ta karanta saƙon kusan sau uku, wani irin daɗi ya mamaye zuciyar ta.
Sai ta fara rubuta amsa, sai ta goge. Ta sake rubuta wa, ta sake goge wa.
Daga ƙarshe dai ta tura,
“Alhamdulillah, ina lafiya. Nagode sosai.”
Ta ajiye wayar, tana jin kamar amsar da ta aika ba ta wadatar ba. Ta so ta ƙara masa wani abu, amma ba ta san abin da za ta ce ba.
Nabila wadda take kallon ta ta yi murmushi a ɓoye.
“pixie, idan kin gama wannan saƙon, ki taimaka mana mu zaɓi kayan bikin.”
wayar ta yi saurin ɓoyewa tana cuno baki, tasan halin su koda basu an kara da abinda take yi ba tunda Nabila tayi magana zasu iya sai sun ga me take yi.
“Na gama mana!”
Fareedah da Jalila ne suka saka dariya Nabila tace
“Allah ya kyauta miki kekam”
Cinyar ta Anisa ta daka tana juyar da kanta dan kunya bata ce komai ba
Da daddare, bayan ta koma ɗakin su, lokacin basu riga da sun shigo ba, ta sake buɗe saƙon Ya Faruq.
Ta karanta shi a karo na huɗu, sannan ta rungume wayar a ƙirjin ta na ɗan lokaci kafin ta yi saurin sauke ta, kamar wani ya gan ta.
“Ya Allah, me ke faruwa da ni ne?” ta furta a hankali zuciyar ta na matsewa
Ba ta san amsar ba ko ince ta ƙi yarda da abinda zuciyar ta ke faɗa mata.
Abin da kawai ta sani shi ne, a hankali, Ya Faruq yana zama wani ɓangare na rayuwar ta da ba ta son ta rasa, har yanzu ita kanta ba ta shirya yarda da wannan gaskiyar ba.
Jama'a baku tambaye ni su Mamee ba ace har sun hakura da wuri haka?? Mu dai je zuwa.
Karku manta kuyi following ɗina a arewapen for more updates 🥹🥰🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
______________________
By
Anisa Muhammad Yahaya 🌺
***