66
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad Yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 6️⃣6️⃣
'' A'a dai Abida baza ayi haka ba, Malam ayi yanda nace tunda dai yaran namu zasu samu su shiga ai shikenan daga baya a fitar da su ta ƙarfin tsiya''
'' Amman dai Adda da anyi yanda nace''
Mama zata yi magana malam yace
'' na duba duk aciki za su yiwu amman ɗaya yafi hatsari kuma kun ce bikin yanzu bai fi kwanaki uku ba to hanya biyu ne, riƙe wannan mu ga''
Ya tura musu carbin hannun sa yace '' kowacce acikin ku ta zaɓa guda ɗaya sai mu ga hanyar wa za'a ɗauka wanne zai fi yi kamar yankan wuƙa''
Da rawar jiki suka riƙe hannun Mama har wani rawa yake dan bala'i, duk da tana tsoro dan ta daɗe bata bi malamai ba tun sanda Ummah ta bata wani magani har aka kamata, sai yau da son abin duniya ya rufe mata ido, ta tambaye wata kawar ta da suke yawon tare a da ta nuna musu wannan malamin
'' ku sake'' suna sakewa ya kama inda suka riƙe, wanda Mamee ta rike ya fara mur zawa yana kulle ido yana surutai, ƙasar gaban sa ya janyo da ɗayan hannun idonsa a kulle yana wasu zanuka a ciki, yana gamawa ya ɗago ya kalle su yace
'' to idan hanyar da ke Abida za'a bi sai anyi sadaukarwar hantar sauro guda biyu, an samo baƙin alade mai gemu a tsakar ka an tsigi guda biyu, sai an samo jaki mai ƙaho a tsakiyar kwakwalwar sa guda biyu, sannan a yanka ƙuda mai ido ɗaya a sadaukar da jinin sa saboda shine wanda zai baku damar raba auren, baza a ƙara tada maganar za'ayi auren da wasu ba bayan yaran ku ba, kuma hakan zai iya ɗaukar kusan kwana huɗu,dan haka bara in duba ɗayan hanyar''
Bayan ya gama gwalan gwalan ton shi yace
'' shi kuma wannan hanyar, a ranar auren ma za'a haɗa da yaran ku ba zai ɗauki kwana 1 zuwa 2 ba idan kun yi abinda ake buƙata''
'' me ake buƙata kenan Malam'' har suna hada baki dan zumuɗin jin abinda zai ce, dan a maganar sa ta farko jikin Mamee yayi la'asar, bata san haka ake ayyuka ba gaskiya malamin nan yasan abinda yake ashe shiyasa wani aikin yake kamar yankan wuƙa wannan abubuwan daya lissafo bata taɓa jin su ba, ita in ba yau ba bata taɓa zuwa wajen boka ba ko wani malami
Kallon su yayi yace
'' a gaskiya na kara dubawa dole se dai abi hanya na biyun nan dan auren nan ba fashi sedai za mu iya ƙullin da za'a haɗa harda naku yaran''
'' malam ayi duk wani mai yiwa kawai''
Kai ya jinjina duk da bai fito ya faɗa musu zahirin abin da ya gani ba, gwara ya ci kuɗin su ko yaya ne dan yasan ba yanda auren da suke son kullawa ya yiwu
'' sai an nemi idanuwa jajaye guda biyu na mage mai farin gashi ba ɗugon ko wani kala kwalli ɗaya a jikin ta sai gashin bakin da za'a same ta dasu baƙaƙe, sai kwan salwa baƙi ƙirin kamar bayan miciji jikin sa zai kasance guda biyu, sai furen tumfafiya guda huɗu, wannan bazai yi wahala ba, sai kuma jinin mahaukaciyar tsutsa da za'ayi sadaukar war dashi''
'' tsutsa fa malam??kuma ma mahaukaciya, daman akwai mahaukaciyar tsutsa??''
'' ba'a katse mana hanzari idan muna magana''
'' tuba take yi malam bazata sake ba'' Mama ta faɗa da itama jikinta duk ya mutu jin abubuwan da yake ta lissafa wa
Cigaba yayi da magana
'' sai tsuliyar kifi sabon haihuwa, makwallaton bushashshen matacciyar giwa''
'' to malam mu duk a ina za mu samu wannan abubuwan da kake lissafa wa''
'' ai kuɗin kawai zaku bayar aljanu za su muku hidima, dan duk wannan abubuwan sadaukar war su za'a ba, idan aka ce a jira ku samo wasu zama a iya shekara baku san inda zaku nufa ku samu ba, amma aljanu ana basu suke samowa, awa ɗaya ya ishe su ko mintinan 30, ke har a minti 10 ma''
''to shikenan malam mun gode''
'' ai indai zaku biya kuɗi ku sake Naira to ku tabbatar da aikin nan kamar yankan wuƙa dan yana buƙatar a sake kuɗi da yawa''
''in Sha Allah malam baza kaji kunya a wajen mu ba zamu yi duk abinda kace, indai aiki ze yiwu''
'' ai kusa a ran ku kamar anyi an gama kuje kawai kuma a fara shirin biki da ku, ga wannan a ringa wa amaren turare kafin babban aikin ya kammalu''
Godiya suka ringa mai kamar zasu kifa suka bar wajen cikin wani maɗaukakin farin ciki a bayyane a fuskar su da zukatan su
Follow me on arewapen for more updates 🥹 🥰 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏
______________________
By
Anisa Muhammad Yahaya 🌺
***