68
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad Yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 6️⃣8️⃣
Tun bayan suka gama take jin ta cikin walwala amma tun ta tuna wani abu gaba ɗaya fara'ar ta ta ɓace, duk suka kasa gane kanta, banda kuka ba abinda take yi idanuwan ta sunyi jajir, duk sun tusa ta a gaba har Nabila da itama dai gata nan gata nan sai kallon ta suke, har sun gaji da tausar ta da tambayar ta dan banza tayi ta ƙyale su, amman basu tashi sun barta ba, suna tunanin kewar Abhie ne ya saka ta kuka
Wuraren bayan la'asar Momma da yaya Saudat (ƴar gidan Mama ta uku) da kaɗan ta girme musu, daman ita ba ruwan ta tun bikin kwana uku ta taho abun ta jin shiriritar da Mama da Mamee ke neman yi, wai su a lallai harda Amra da Zulaiha za'ayi aure, shiyasa ta tattaro yanmatan kafafun ta kafin su kunya tata
'' har yanzu Anisa baki daina kukan nan ba, kiyi hakuri mana, zo to ki faɗa mun me ke damun ki kin ji ƴa ta''
Ta rungume ta ajikin ta tana bubbuga bayanta, itama rungume ta tayi tana kara jin zuciyar ta na karye wa, cikin muryar kuka tace
'' Momma a kaini naga hayaty na, ina son in ga Ammi na'' ta faɗa dan tasan ita kaɗai zata fahimci irin abinda take ji ko da ba ta furta mata ba kuwa
'' to kiyi shiru tukuna, Flight ɗin ku na 5pm ne dan haka akwai kusan one hour tashi ki shirya ki goge hawayen ki indai da gaske kina son ganin Ammi''
Kamar ƙaramar yarinya ta gyaɗa kai tana goge hawaye
'' yauwa that's my girl, Saudat ku shirya su nasan kafin ku gama dai ai 4:30 zai wuce sai driver ya kai ku airport, mu ma taho daga baya''
'' eyya Momma ba tare zamu tafi ba?'' Jalila ta tambaya tana kwabe fuska
'' a'a ni sai na jira Jamal yace yana hanya tare za mu taho da sauran mutanen a mota, ku ku fara gaba tunda za kuyi attending wani event din kafin a kai su''
'' naso tare za mu tafi amman dai shikenan '' ta faɗa muryar ta a karye
'' Adda Saudat amman ke dai ba Momma za ki jira ba koh?''
'' ai ƙafa ta ƙafar ku Fareedah muna manne tip da tyre''
Dariya sukayi gaba ɗaya Momma ta fice ta bar musu ɗakin, Nabila ce ta kalla Anisa duk da bata da ita ma wani kuzari tace cikin zolaya
'' Leema ko dai ango ne be kira ba yasa take ta mana kukan shagwaba''
'' nima dai ina jin haka, wannan kyan ta shi zaki kira ki tusa a gaba ki ta mai wannan kukan ba mu ba duk kin cika mana kunne''
Hararar su tayi ta juyar da kanta gefe Yaya Saudat tace
'' gaskiya a daina ta kura wa ta kusa da ran haka, ku kyale mun ita ta sha iska, duk kun ma bi kun zagaye ta kamar wacce ta ci muku bashi''
'' yaya Saudat ai ta kusa da ran taki ita ce auta a cikin mu dole mu zagaye ta tana mana shagwaba'' Jalila ta faɗa tana ɗaga wa Anisa gira
Baki ta cuno bata ce komai ba amma kukan ya fara tsayawa
'' ai saboda autar ce ta ke mana yanda take so, ohhh Ya Umar zega abu'' Fareedah ta faɗa duk suna kwashewa da dariya
'' uhmm kinga bara dai muyi serious muyi abinda ya dace kafin mu makara flight din mu''
-------------
''Wani zancen banza nake ji haka, wai nufin ku shikenan an kammala ɗaurin aure ko me? Ban gane ba naga kuna shigowa ba tare da naji an kira sunan Amra ko Zulaiha ba, kai Hafeez me hakan yake nufi?''
Mama ta faɗi tana zare ido wani uban gumi na yan kowa tunda ga ƙasan gashin ta har tafin ƙafafuwan ta take jin su
Baba ne ya kalle ta a ɗage yace
'' daman an tsara za'a ɗaura da ɗaya daga cikin su ne da zaki ce hakan?''
'' Adda amma ai ba haka muka yi da Malam mai carbi dubu ba, ba cewa yayi yau ko ana ha maza ha mata sai anyi auren nan ba''
Mamee ta faɗa cikin fitar hayyaci dan duk kuɗaɗen da take tarawa na auren yaranta ko wani babban abu idan ya taso mata ta haɗa ta bayar ita kuma Mama gold ɗinta da ta a dana ta dauko ta siyar aka cika suka ba Mai carbi dubu,
'' kenan a banza ko me? Wallahi ba zata saɓu ba sai kin biyani kuɗi na Shaheeda '' Mamee ta faɗa ta yo kan Mama da ta tsaya sandandan kamar an kafa ta a wajen, ba abinda take tunani sai wannan gold din, a banza ta siyar dashi dan tana buƙatar kuɗin amman ace wai yanzu haƙar su bata cimma ruwa ba, '' kai ina da sake wai anyi wa mai dami ɗaya sata, ai bama a isa ba su za'a cuta''
Mutanen wajen kuwa da kallo suke bin su Zulaiha ce da ƙwaƙwalwar ta ta gaza daukar komai tun bayan da ta gama jin wannan mugun jin da tashin hankalin ta kurma wani uban ihu ta fara zage zage tana wa su Abba Allah ya isa,
Abubuwa take kamar mara kai aikuwa bata ida gama zagunan da take yi ba Amma ta kai mata wani mahangurɓa a baki, cikin takaici da ɗacin rai tace
'' Shaheeda tattara muƙarraban ki kuyi waje kafin in muku abinda baza ku taɓa mancewa da rana me kamar ta yau ba har ku gama da duniya, salin alin ku bar nan gidan dan kema kin san hauka na idan ya tashi yafi naku duk ku huɗun, idan kuma shi kuke buri da fatan gani kuma mu zuba ni da ku''
Har Mama zata sake magana Anty ta tari numfashin ta tace
'' Anty danAllah ku fita kubar gidan nan dan ko ni sai na rufe ido na sa kwallin rashin mutunci, naga muke son kulla abin arziki da ku amman ku da sharri kuke son biyo bayan mu, ban taɓa tunanin za ku iya wuce gona da iri ba irin haka, kuje dan kanku''
Mamee ce cike da takaici ta baro inda take zata fara magana kuma da alama hannu take son kaiwa yasa Mommy da ta lura da hakan ta matso tana tare gaban ta tace
'' ja jiki kanzo bamu da ruwan riƙa ki anan kije can ki samu na yin ki ba wanda ke buƙatar jin tsamin bakin ki ku tattara ku koma Allah raka taki gona tunda ku ba'a kusantar ku da alkhairi sai kun saka da sharri''
Guiwa a sanyaye haka suka fice daga gidan kafin ma su ƙarasa fita suka kaure da da dambe, dan Mamee nunawa tayi bata san zance ba sai Mama ta biya ta kuɗin tarin ta, itama Mama tana ji da nata jimamin tace
'' to Abida ki danne ni ki kwata sai kace ni ba nawa kuɗin a ciki''
'' wannan ke ta shafa ai ke kika kawo shawarar dan haka wallahi sai kin biya ni''
'' akan maganganun bazar nan da kike yi kawai ki sa mun duka tunda naga kamar hannu kike son kai mun''
''ai dole Mamee tayi magana haba Mama kin san cewa aikin nan ba zai yiwu ba amma zaki Kaita wurin shi, ni ina ganin ma haɗin baki sukayi ita da malamin dan su ki kuɗin mu''
'' ke Zulaiha uwar ta wa kike wa rashin kunya''
'' ai da bata yi ba baza a mata ba'' Mamee ta ba Amra amsa a madadin Zulaiha dake galla mata uban harara kamar idanuwan ta zasu zubo kasa
'' ke Zulaiha ni Sa'ar ki ce da ina magana da uwar ki kike saka mun baki, ke kuma Abida kina jin abinda ta faɗa madadin daukar mataki saidai ki goyi bayan rashin kunyar da ta mun''
''ai ke kika bada kofar hakan, nan idan kuna zancen ku da manya idan mun sa baki sai ku ce daidai ne dan haka ba rashin kunyar da na miki idan ma nayi ke kika ja wa kanki ''
'' akan banzan kuɗin sata kike ma uwata rashin ta ido wallahi sai na dakaki a wajen nan, gwara mu ajjiyayyen kudi ne aka taɓa kuda na sata ne daga ke har uwar take Abida kuke tarawa mu kuwa fa kuɗi ne na halal malak mallakin mu dan haka kika kara kuskura kika ce wani abu akan uwata sai kin yaba aya zaƙinta''
Nan fa dambe ya kaure, tun jin hayaniyar tayi yawa, Mama Maimuna ta dauko Mp din dake ɗakin Ya Ahmad ta kure volume tace ƴanmatan dake cikin gidan su ta so su danse itama ta girgije abinta suka share hayaniyar su dake tashi
---------
Airport su Momma suka raka su saida flight din su ya tashi ma sannan suka koma
Tun suka taso zuciyar ta ke bugawa da sauri da sauri barin ma da suka sauka taga motocin ƴan gidan su, harda su angwayen aka zo daukar su, suna fitowa kuwa suka yi ido biyu dashi sai murmushi yake sakar mata
Kasa tayi da kanta zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri fiye da da, gefen mayafinta ta kama ta ringa wasa dashi itama murmushin da take yi ya gaza ɓoyuwa, dan kar ma ya ankara ta ɗan ja veil ɗin ya rufe gefen fuskar ta ta ɓarin da yake
Aikam murmushin a kan idon sa, wani farin ciki ne shima ya ratsa zuciyar sa fiye da farko da suka fito
Tako wa yayi har inda take ya rike hannunta yana ƙoƙarin su haɗa idonsu waje ɗaya, ita kuma tayi saurin ƙara sunkuyar da kanta duk kunya ta rufe ta ganin tarin jama'ar dake wajen amman ba kunya ya zo har inda take
Follow me on arewapen for more updates 🥹 🥰 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏
______________________
By
Anisa Muhammad Yahaya 🌺
***