70
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad Yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 7️⃣0️⃣
Bayan sun baro event ɗin gidan Ammi suka nufa, tun daga compound kaje jin guɗa nata tashi, kuma su mama safiya ne da wannan aikin
Fito da su akayi kowacce fuskar ta lulluɓe a cikin mayafi, part din Mommy aka kaisu wajen surukan Anisa (yau mommy ta koma suruka), albarka da nasiha iyayen dake dangin mommy suka musu tama Mommy ta ɗan yi nata sannan suka tafi part din Ammi
Wajen Amma aka fara kaisu, Amma baki har kunne dan murna, ita gaba ɗaya ma da aka ce ta musu nasihar ka sawa tayi sai kuka, ta kama su duk su biyun ta rungume tana saka musu albarka, su mama Maimuna da mama safiya ne suka ƙara musu wani nasihar ace a kai ko wacce wajen mahaifiyar ta su gana kafin a kai su ɗakin su
----
Ammi
Tana jin sanda aka shigo dasu, zuciyar ta ke ta azalzalar ta taje taga ɗiyar ta dan tayi kewar ta mutuƙa kawai kawaici ke sa ta nuna bata damu sosai ba ake ta shagulgulan biki, amma tana son ganin ta ko a yanzu ma ji take ta tashi ta fita parlourn ba sai ta jira sun kawo mata ita ba, tana a haka sai gashi an turo kofar Jalila da Leema riƙe da ita
Ai da sauri ta taso ta yo inda suke, ita ma ganin Ammin ta ta fashe da kuka ta rungume ta, itama Ammin kuka ta saka suka rungume juna suna tayi, Jalila da Leema ma saida suka share hawayen ganin su a haka
'' Allah sarki yau Allah ya kawo ranar da wannan beautiful souls ɗin zasu rabu da juna'' ta faɗa a ranta itama hawayen tausayin su na zubo mata
''Hayaty nah''. '' na'am Habibty, me ya faru''. Ta ɗago ta tana kallon fuskar ta, kasa cewa komai ta ƙara yi, sai hawayen da ya ƙara sulalowa ta idon ta tace
'' Ammi Abhie'' sai ta sake fashewa da kuka, itama Ammin kukan take yi, ta kasa ma ta taushe kanta bare ta taushi Anisan da ta daina kuka, a hankali taja hannun ta har gaban wardrobe ɗin ta ta ɗauko wani set ɗin awarwaro ta saka mata a hannu sannan ta kalle ta tayi murmushi tana share hawayen idon ta, sannan ta share hawayen idanun Anisan ita ma tace
'' Abhie will be very proud of his beautiful girl, yanzu ki daina kuka kiyi murmushi, baki ga yanda bangles ɗin suka miki kyau a hannu ba? Kin san wanda ya bani kuwa?''
Kai ta girgiza alamar a'a ba tare da tace komai ba kuka na sake cin karfin ta. '' Abhien ki ne ya samun su a ranar da aka kai ni gidan shi, kema gashi nan ki ringa tunawa kina da wani abu daga gurin Abhie ɗin ki'' ta faɗa wani kukan na sake cin karfin ta, kai Anisa ta jinjina itama kukan na sake cin karfin ta, suka ƙara rungume juna
Suma su Leema kukan suke, yau body and soul zasuyi parting, aure mai raba uwa da ƴa
Amma ce ta shigo ɗakin ta gansu a haka, itama kawai taji zuciyar ta ta karye sai kuka, Ammi ce ta ɗago ta kalle ta sai ta miƙa mata hannu da sauri ta ƙarasa wajen ta rungume su, ganin Jalila Ita ma sai kukan take Ammi ta mika mata hannu itama suka rungume juna su huɗu suna ta kuka
Ammi da Amma kukan nasu sai ya koma daga kukan farin cikin yau zuwa na tuna rayuwar su ta baya, ashe duk tsanani na tare da sauƙi, ashe akwai sanda ƙarshen wahala zai zo, a lokacin da suke kallon kamar komai bazai taɓa wucewa ba, kamar a ƙangin wahala da azabtar war kishiyar uwa zasu dauwama, yau ina take, kamar a lokacin idan ta aura mata wanda take so baza ta taɓa samun farin ciki ba, kamar idan sanda suka rasa Papi baza su ƙara zama cikin farin ciki ba, kamar sanda ta rasa Abhie shikenan ta gama rasa duk wani gata kulawa da farin ciki na har abada
Juna suka kara rungume wa an rasa mai tausar wani acikin su, ita ma Leema kuka take yi a lokaci ɗaya tana dariyar wannan beautiful bond ɗin nasu, wayar ta ta ɗauko ta musu video, Anty ce ta shigo ɗakin jin su shiru idon ta itama jawur, dan cewa aka yi Amma ta ƙira su a fito da Anisa dan akai su dare na ƙara yi
Wani hawayen suka saka ta tana tu no sanda suka wahala a hannun mahaifiyar ta, duk da irin wahalar da suka sha su ba su wahalar da nasu ƴanuwan ko sun yada su ba, sai kara janyo su da suke yi kullum a jiki suna ƙoƙarin mantawa da irin abubuwan da suka faru a rayuwar su ta baya masu ɗaci, suka maida komai ba komai ba, ƙarasawa tayi inda suke ta ɗaura hannunta a kan bayan Amma da Ammi ta bubbuga a hankali
'' tace Adda ya isa haka kuyi hakuri, duk tsanani na tare da sauƙi, abinda ya wuce ya wuce duk yanzu sai labari''. Dan a yanda taga suna kukan nan ta san ba iya kukan auren bane harda raɗaɗin da suka ji na baya ne ya taso musu
Ta ƙara cewa '' lokaci na ƙurewa za'a tafi kai su yanzu''. Da jin haka Amma ta sake su, ita ma Jalila ta sake su, ita ma Ammin janye wa tayi amma ina Anisa taƙi ta kyale ta sai kuka da ta ƙara saka wa tana cukwikuye Ammi tana kuka tana girgiza kanta
'' kiyi hakuri Anisa kin ji ai baku rabu ba, ki zo muje lokaci ne ke tafiya'' Anty ta faɗa zuciyar ta cike da tausayin su duka
'' Anty na fasa auren danAllah abar ni wajen Ammi na danAllah''.
Zuciyar Ammi ce ta ƙara karyewa ita ma ta rike ta suka cigaba da kuka
'' haba Adda ya zaki ƙara biye mata kiyi hakuri''. Amma ta faɗa duk da ita ma hawayen be daina zubo wa daga idon ta ba
Ganin dai baza su iya su kadai ba Amma ta fita ta ƙira su mama Maimuna dan sun ƙi sakin junan su, sai da suka zo da ƙyar aka raba su suka fito, zama Ammi tayi kan gadon tana ta kuka dan idan ta fita baza ta iya bari su tafi da ita ba, ji take yi ta bisu akai ta da ita ko kuma a dawo mata da ƴar ta, amma ya zata yi, ƴar ta tace ta girma lokacin rabuwar su ne ya zo
-----
Suna fitowa taga Nabila a zaune a kan 2 seater tana ta kuka Fareedah zaune a gefen ta itama hawayen take yi, suna fitowa suka tashi suma, wajen su tayi ta rungume su hannun ta riƙe a cikin na Jalila, itama rungume su tayi suna ta rizgar kuka, yau Allah ya kawo ranar da zasu yi parting, a kullum suna tare barin ma su uku, their bond is beyond na cousins jin su suke yi sun wuce blood sisters ma jin su suke yi kamar quadruplets, kamar rana ɗaya aka haife su a ciki ɗaya, yau gashi kan su ya rabu aure mai yankan ƙauna
Eyya pookie, pickles, pixie, Peebles na tausaya muku,masu karatu toh, jikina ya mutu mu haɗu a next page
Follow me on arewapen for more updates 🥹🥰🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
______________________
By
Anisa Muhammad Yahaya 🌺
***