NUFIN ALLAH

72

by @anisamuhammadyah897


💕 NUFIN ALLAH 💕 
      By
Anisa Muhammad Yahaya 

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Wannan page ɗin sadaukarwa ce ga FATIMA ABDULLAHI SABO🥰🥰❤️‍🩹❤️‍🩹 (Anty Tatee🥰🥰). Ina godiya da duk taimakawa da guiding Dina da kika yi, thank you so much for all your support and encouragement, ban ma san da wani irin baki zan gode miki ba, haɗuwar novel group but kinyi supporting ɗina, I took you more than a stranger ko wata wadda muka haɗu online, ina jin ki kamar wata babbar sister thank you so much 🥰🥹🙏🙏🙏


Page 7️⃣2️⃣


Ko da asuba da suka tashi da kyar ta iya yin sallar a gaban shi saboda tsananin kunya, tare suka yi jam'i suka yi sallah dan be iya ma fita masallacin ba tsayawa yayi ya kula da ita kamar wata kwai, 

Suna idar da sallah ta kwanta a kan darduman ta dunƙule kafin ma ya juyo dan bata burin su ƙara haɗa ido, ji take ina ƙasa ta tsage ta shige, ganin haka ya saki wani kayataccen murmushi da tun a daren jiya ya kasa barin shi, wani irin farin ciki ne da tsantsar sonta dake ƙara shigar sa ke ƙara ratsa zuciyar sa, shi yasa yake ta tarairayar kayar sa, dan shi ya gasa ta da daddaren ya sake mata wanka ya ɗauko ta suka kwanta, ya manna ta ajikin sa

Duk abubuwan da ya mata idanuwan ta a kulle amma taji daɗin jikin ta da ya gasa ta saidai wani irin muguwar kunyarsa da ta mamaye ruhin ta, a zuciyar ta kam tana tunanin baza ta ƙara iya ido huɗu dashi ba, har wani zazzaɓi ma take ji amman jikin ta da ya haɗu da nashi ya fara ɗan rage mata zazzaɓin saboda yanda fatar sa mai laushi da ƙamshi ta haɗu da nata ga sanyin fatar nashi sai ta sa mata wani nutsuwa har ta samu ta iya komawa sai yanzu da suka taso da asuba


Wuraren 11 ya farka, fuskar ta dake a ƙirjin sa ya kalla, hannu ya kai ya shafa baby face ɗin nata wani murmushin na sake zuwar mai, a hankali ya kai hannu sa kan bakin ta da suka sha wahala sosai jiya, har yanzu basu sace daga kumburin da suka yi ba, ji yayi duk tausayin ta ya mamayi shi 

A hankali yanda baza ta tashi ba ya zame jikinsa ya gyara mata kanta akan pillow sannan ya rufe ta ya fita kitchen

Breakfast ya haɗa musu ya sa a warmers ya kai dining sannan ya gyara kitchen ɗin ya koma ɗakin

Bakin gadon ya je ya sunkuyo saitin kanta, bargon yayi kokarin janye wa amman ta riƙe gam taƙi ta saki, wani murmushi ya saki sannan yace
'' ashe kin tashi, to sauko mu fita'' 

Kai ta girgiza a cikin bargo tana ƙara matsewa
'' tunda baza ki fito ba shikenan bara in je in cewa su Ammin su tafi kin ce baza ki zo ba'' 

'' A'a na fito'' ta faɗa da sauri tana mike wa, da kallo yake bin jikinta dake bayyane, gaba ɗaya ta ƙara rikita mai lissafi, ganin ya kafe ta da ido yasa ta bin inda ya ƙure da ido a hankali ta kai idon ta kan ƙirjin ta, wani irin kwantawa tayi ta ƙara jan bargo tana kuka 

Dariya yayi me sauti ya ɗago ta, bargon ya nami ya cire amma taƙi yarda dan wani irin kunyar sa take ji
'' ni da naga abinda yafi wannan jiya, to me kike ɓoye mun bayan ba iya...'' be ƙarasa ba ta fasa wani ihu haɗe da kuka, da sauri ya janyo ta jikinsa yace 

'' to ba zan sake ba, fito muje mu gaida su Ammi ko ba kya so'' a hankali ta buɗe fuskar ta tana cuno baki fuskar ta dagaje dagaje da hawaye, dariya ta bashi yace ''to taso'', kai ta girgiza da sauri tana riƙe bargon jin yana neman yaye wa tace

'' A'a nidai ka fita in sa kaya to''. '' ba inda zan je idan kuma na fita to zan je ne ince wa su Amma ba kya son ganin su su juya su tafi'' 

'' A'a nidai kar kayi haka amma gaskiya nidai ka fita'' murmushi yayi yace '' to shikenan, amma ni fa na kasa gane maisa kike ta wannan ɓoye ɓoyen haka, bayan na gama ganin su tun jiya kuma yau ɗin ma dai a jikina suka kwana'' 

Pillown dake kusa da ita ta je fo mai tana kuka, kunya kuwa kamar zai kashe ta a wajen, '' wai daman haka Yah Umar yake, baida kunya bata sani ba sai yau'' ji take ina ƙasa ta tsage, daba dan Ammi yace ba da ba inda zata je, ji take ƙafafuwan ta uwa zasu cire daga gangan jikinta, a haka ta daure ta tashi ta dauko kaya a akwatin ta da ba'a kawo gidan bikin ba, direct nan gidan su aka kawo da ita da Nabilan 

12 pieces ne masu bala'in kyau, hamshaƙe da kaya ƴanuban su, Amma ce tace bata son a kai gida dan kar a ma daukar musu wani abu a kawo musu gidan su, in yaso idan sun zo sa bawa ƙawayen su da kansu
 
Les ta saka blue colour da mai flowers ƙananu farare, ɗauri tayi mai kyau ta fesa turaren ta na channel Coco mademoiselle ta fito ɗas abin ta, juyowa tayi ta ganshi jin gine a bakin kofa ya zuba mata ido, baki ta turo tace

'' amma wai Yah tun yaushe kake tsaye a wajen''
Ajiyar zuciya ya sauke ya tako har inda take ya manna ta a jikin sa, yace 

'' tun kina shiryawa, har abinda ba'a so in ƙara gani saida na gani''
Ɗan bugar ƙirjin sa tayi ta tura kanta jikin sa dan kunya, murmushi me sauti yayi dan yau gaba ɗaya nishadi take saka shi, hannun ta ya kama suka nufi parlourn 

Suna zuwa taga bata ga kowa ba, ba alamar ma wasu sun zo gidan, kallon shi tayi tana ɓata rai, cike da shagwaba tace
'' Yah ina su Ammin da kace sun zo, ba ma alamar kowa yazo ''

'' ai so nake daman ki taso muyi breakfast, nasan idan kika san ba su zo ba wahalar da zaki bani sai ta fi haka, ke da ganin mutane a gidan nan sai nan da wata ɗaya dan nace wa su Amma bana buƙatar kowa zan kula da matata, ko su Jalila bana buƙatar ganin su sai na gama cin amarci na'' ya faɗa yana lakace dogon hancin ta, baki ta cuno tana kwaɓe fuska kamar zata yi kuka 

'' kin san kika cigaba da cuno bakin nan sai na tsotse shi'' da sauri ta sa hannu ta rufe bakin ta juyar da kanta gefe, hannun ta ya ja har dining sai da ya ja kujera ya zauna, tana ƙoƙarin jan wani kujerar yayi saurin ɗaura ta a cinyarsa, zaro ido tayi tace

'' ni na fi son zama a kan kujerar''
'' ga babbar kujerar ki nan''. Ganin dai ba sarki sai Allah tsakanin ta dashi, yasa ta janyo warmers din, da sauri ya amsa yace ''wannan ba aikin ki bane nawa ne ke sarauniya ce yau sai abinda kika ce, ba za kiyi aiki ba'' 

'' serving ai ba aiki bane''. '' to ni aiki ne a gurina'' ya faɗa ya janyo warmers ɗin yayi serving a plate ɗaya, kallon sa tayi wai a plate ɗaya yake son su ci, spoon ya ɗauka ya nufi bakin ta dashi, fuska ta marairaice, tana ƙoƙarin yi mai kuka





Follow me on arewapen for more updates 🥹 🥰 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 



_____________________
By
Anisa Muhammad Yahaya 🌺 
0705982249