QADDARARREN AURE

EP_________ 3️⃣

by @swrites22

🕊️ DESTINED MARRIAGE 🕊️



*HAUSA EDITION*



🕊️ QADDARARREN AURE🕊️



          SWRITES 
              A-K-A 
     YOUNG WRITER✍🏻 




EP_________ 3️⃣




Ko da Faryal ta shige ɗakin nasu, wanka ta fara yi sannan ta gabatar da sallar Isha'i, kafin ta fito neman abin da za ta ci, dan ta san mutanen gidan nasu sun riga da sunyi dinner ɗin su tun kafin ta dawo.

Bayan ta gama cin abinci, wurin mahaifinta ta shiga ta gaida shi sannan ta musu sai da safe ta fito ta koma ɗakinta.

 Wayarta ta dauka, ta shiga WhatsApp, ta aika wa Hamdan saƙon, "Heyyyy". Gani tayi datar sa a buɗe saboda alamun tick biyu da ya nuna mata, dan haka ta shiga tiktok ta hau kalle kalle kafin ya dawo mata da amsa.

Tana a haka har lokaci ya ja sosai ba tare da ta sani ba. Kafin ta ankara, har ƙarfe 10:27pm. Buɗo kofar ɗakin akayi, Hadiyyah ta shigo, ɗauke da shopping bags.

"Faryal, ashe kin dawo?". Hadiyyah ta faɗa tana murmushi.

 "Eh, tun ɗazu na dawo ai. Maama ta ce min kina falon baqi tare da baƙo". Faryal ta amsa tana kallon Hadiyyah data zube shopping bags ɗin akan gado.

"Abubakar ne fa". Hadiyyah ta amsa.

Cikin sigar tsokana Faryal tace, "Keee Hadiyyah, ki ji tsoron Allah! Me kuke tattaunawa ne ke da Abubakar ɗin da duk lokacin da ya zo sai kun shafe awa huɗu zuwa biyar? Bari ma in tambaye ki, kin yi sallar Magariba kuwa kafin ki fita wurinsa?".

Hadiyyah ta fashe da dariya, tana rage kayan jikinta, ta wuce ta ɗauko rigar bacci doguwa ta sauya tana faɗin, "Ke dai bari, ko na miki bayani ma ba lalle ki fahimta ba tunda ke dai baki yi dacen saurayi ba ballatana ki san irin yadda ake ji in ana tare da masoyi. Dan wannan Hamdan ɗin dai da kike kira naki, ke kaɗai kike kidanki kike rawarki a kansa".

Faryal ta haɗe fuska. Kafin ta ce, "Mind your own business Hadiyyah! Me ya shafe ki da rayuwata da har za ki tsoma min baki a cikin lamarin soyayyata, Ehh?".

Taɓe baki Hadiyyah ta yi, ta wuce bathroom ba tare data sake cewa komai ba saboda ganin yadda Faryal ɗin ta hassalo mata dan kawai ta faɗi gsky.

Kwafa Faryal taja kafin ta janyo wayarta ta sake dubawa, saidai har yanzu babu wani message daga Hamdan ɗin. Tana shirin ajiye wayar sai kuma ta yanke shawarar kiransa. Haka wayar ta karaci ringing ɗin ta bai daga ba.

Ajiye wayar tayi a gefe, ta san dole zai biyo bayan kiran shiyasa bata kai ta da nisa ba dan ma kar ya kira ba ta ji ba. Ta karanto addu'o'in kwanciya bacci ta shafa, kafin ta gyara ta kwanta.

A lokacin da Hadiyyah ta fito daga bathroom ɗin already Faryal ta yi bacci. Fita tayi daga ɗakin, ba jimawa ta dawo ɗauke da plate ɗin abinci da robar ruwa, domin itama a lokacin da su Maama suke yin dinner ɗin tana ɗaki tana kwalliya.

Wayarta ta ɗauka ta koma kan rug ta zauna, tana cin abincin tana amfani da wayarta ta har ta gama, ta ɗauki plate ɗin ta fita ta kai kitchen sannan ta dawo ta cigaba da chatting din ta har wurin 1am.

Washegari kuwa ko da suka idar da sallar Asuba, ba su koma bacci ba. Haɗuwa sukayi a falo dan yin karatun Alƙur'ani kamar yadda suka saba har saida gari yayi haske.

Faryal ita ce babba. Ta kammala karatunta a fannin Business Administration, wato harkokin kasuwanci, following her fathers footsteps. Mahaifinta hamshaƙin ɗan kasuwa ne wanda ya ɗauki kasuwancinsa da muhimmanci sama da komai including his family.

Da kansa ya damƙawa Faryal ragamar kula da kamfaninsa na Agro commodity company a lokacin data kammala degree ɗin ta. Saidai itama a lokacin tana da nata business ɗin da takeyi tun kafin ta gama makarantar wato event planning and decorations, kuma ALLAH ya sawa abun nata albarka, ako da yaushe sunan brand ɗin ta ƙara fita yake, dan yanzu daga maƙota garuruwa ma ɗaukan su ake.

A ɓangaren iyayensu na wajen uwa kuwa, mixed heritage ne su. Kakansu ɗan asalin Indiya ne, yayin da kakarsu wato Daadee ta kasance asalin Shuwa Arab.




*** *** ***




Bayan sun kammala karatun Alƙur'ani, ita da Hadiyyah suka fara gyaran gidan. Suna gamawa kuma suka wuce kitchen dan girka breakfast.

Bayan sun kammala girkin, ta bar wa Hadiyyah aikin gyaran kitchen ɗin, ita kuma ta wuce ciki da sauri dan shiryawa, kasancewar Juma'a short day ce.

Wani cotton lace ta sanya marar nauyi ɗinkin doguwar riga, ta yi daurin dankwalinta simple. Ta kawo red lipstick ɗin dake kara haskata ta goga, sannan ta ɗauki medicated glass ɗinta ta maqala, wanda ya ƙara fito da kyawunta.

Ta fito da black Handbag, veil da takalmi. Ta ɗauki wayarta, ta cire tsohuwar pouch ɗin, ta sanya wata red me adon golden stones kafin ta fice daga dakin.

Wato Faryal in dai wanka ne to a bar mata kayanta, dan tana amfani ne da skin colour ɗinta wurin zaben colour ɗin kayan da take ado dasu, shiyasa komai nata very unique. Ina ma ace masu karatu za su iya ganinta a cikin wannan perfect combo din, da sun fahimci ainihin ma'anar fashionista.

A falo ta tarar da Maama wadda ke taimaka wa Beta wajen ƙarasa shiryawa dan wucewa makaranta.

Ajiye Handbag ɗinta tayi a falon tana gaishe da Maaman, kafin ta wuce dinning area. A gurguje tayi breakfast ɗin kafin ta dawo falon tana faɗin, "Maama, Appa yana gida ne?". Saboda tayi tunanin ko already ya fita ne, kamar yadda ya saba.

"Yana ɓangaren sa". Maama ta amsa. Kafin ta ɗaura da faɗin, "Ya ce ma yana son ganinki kafin ki fita, dan yau zai yi tafiya zuwa Kano".

 "Okay Thom". Ta faɗa tana daukan hanyar barin falon ta nufi ɓangaren Mahaifin nata.

A falonsa na ciki ta tarar da shi yana waya. Zama tayi tana jiran ya gama, lokaci zuwa lokaci tana kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunta.

Ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da ta ji yana sallama da wanda yake wayar da shi.

 "Appa, ina kwana?". Ta faɗa bayan ya ajje wayar a gefensa.

Da Murmushi akan fuskarsa ya amsa kafin ya ɗaura da faɗin, "Duk inda Faryal zata shiga, ko ba'a tambaya ba, an san jinin Hafiz Zanna ne yake gudana a jijiyoyinta. Kina da wani muhimmin abu ne a Company da ya sa kike ta wannan saurin haka?".

Murmushi tayi kafin ta ce, "Eh, Appa. Ina da meeting da wasu baƙi ne by 9am, kuma ina da buƙatar duba wasu documents kafin mu shiga taron".

"That's My daughter! Ina alfahari dake. Kici gaba da ƙoƙarin da na sanki dashi ako da yaushe, kinji ko? Ki mai da hankali sosai a kan burikanki da duk abin da kike son cimmawa". Jinjina masa kai tayi kafin ta amsa da , "In sha ALLAH Appa".

"Yauwa, ya batun kayan da kuke shirin fitarwa zuwa Ghana?".

"Eh, Appa, muna kan shirye shiryen tukunna. Amma batun customs duties fa...?"

Katse ta yayi da faɗin, "Kada ki damu, zan kula da komai. Za mu ƙarasa maganar ko da a waya ne, dan yau zan wuce Kano, kuma zan yi kamar 2-3 weeks haka. Duk abin da kike buƙata, ki yi shi kawai ba sai kin nemi izinina ba, kin ji ko?".

"To, Appa. Allah Ya dawo da kai lafiya".

"Amin ya Allah. So, akwai wata matsala ne?".

"A'a, Appa".

"To, shikenan. Za ki iya tafiya. Allah Ya miki albarka".

Faryal ta amsa da, "Amin". Tana miqewa ta fice.

Ko da ta dawo falon nasu, har lokacin Maama na zaune tare da Nasar da Beta.

"Maama, ni zan wuce". Faryal ta faɗa.

"Yauwa Faryal. Da Allah ki wuce ki sauke Nasar da Beta a makaranta, saboda Malam Yusuf yana da uzuri yau, matarsa ce ba lafiya. Hadiyyah kuma tana wanka, kinsan yanayin shirinta kafin ta gama zasu iya makara". 

Dafe goshinta tayi, kamar zatayi kuka ta ce, "To yanzu Maama in na kai su wa zai dawo da su?".

"Hadiyyah mana. Ai yanzu ma dan ta riga ta shiga wanka ne da itan zata kai su".

Faryal na shirin sake magana, Maama ta katse ta da faɗin, "Ki yi haƙuri mana! Kina sake bata muku lokaci ne fa tsayuwar da kikeyi".

Waje ta nufa tana turo baki, Nasar da Beta biye da ita. Maama ta bisu da addu'ar Allah ya tsare.

Suna hawa titi Faryal ta sake take accelerator, saboda ganin time da tayi wanda ya nuna mata 8:05am.

Tana yin parking a Kofar makarantar. Nasar ya dafe goshinsa kamar wanda yayi mantuwa kafin ya ce, "Ohh sh**t. Look at the mess you have made. Kinsa na manta kuɗin break ɗi na".

Kallon gefen ido Faryal ta masa dan Beta tuni ta buɗe motar ta fita sunyi shigewarsu ita da wata kawarta da drivernsu ya sauketa a lokacin itama.

"Ji dan Allah, ko kunya bakaji, wai kuɗin break, da girmanka".

"To Alhamdulillah dadin ta, ba ke kike ba ni ba".

"Au to, me ya sa yanzu kake faɗa min? Ai da sai ka bari sai kaje wurin wadanda suke ba kan".

"Amma ai ke kika sa na manta da kuɗin saboda yadda kika gaggauta mu. Dan haka, dole ki ba ni".

Tsaki Faryal taja kafin ta buɗe glovebox ta zugo dubu biyar ta wurga masa. "Ɗauka ka fitar min a mota. Marar kunya kawai".

Karɓa yayi yana dariya ya ce, "Allah Ya kiyaye ki Yayata. Allah kuma ya dawwamar da soyayyarki da Hamdan". Ya ƙarashe yana ficewa daga motar. Ya rufo mata ƙofar.

Faryal ta yi ɗan murmushi, tana girgiza kai ta ce, "Nasar, Nasar! Yaron nan ba zai taɓa canzawa ba". Juya kan motar tayi ta nufi Company.

Tana shiga secretary ɗin ta Aysah ta miqe tana gaisheta haɗi da mata sannu da zuwa, ta karbi jakarta suka nufi office ɗin.

"Have you seen My Mail Aysah?".

"Eh, ma'am. Har ma na kammala duk abubuwan da kika umarce ni".

"Alryt". Faryal ta faɗa tana tura ƙofar office ɗin suka shiga. "Ki kawo min record na ayyukan jiya. Sannan game da mutumin nan da ya ce yana da tons goma na riɗi, ki cewa marketing manager in ya samu lokaci ya kawo min sample ɗin kayan in gani". 

"Okay ma'am". Aysah ta amsa, kafin ta ajje mata jakar ta juya ta fice.

Jona wayar computer ta tayi a jikin socket, kafin ta zauna ta fara aiki. Ba jimawa Aysah ta dawo ɗauke da files ta ajiye mata akan table ɗin tana faɗin, "Na isar da sakon ki Ma'am, amma na barshi tare da mutane inajin sai ya sallame su zai kawo miki".

Jinjina mata kai tayi kafin ta ce, "You can go". Sai da ta ɗan risina kafin ta nufi kofa ta fice.

Janyo files ɗin tayi ta shiga buɗewa tana dubawa ɗaya bayan ɗaya a nutse. Agogo ne ya buga ƙarfe tara wanda yayi daidai da knocking ɗin ƙofar office ɗin da akayi. Ba tare data ɗago ba ta ce, "Come in". 

Aysah ce ta shigo tana faɗin, "Ma'am, lokaci ya yi. Baƙin namu sun samu isowa, yanzu haka mu kaɗai ake jira" .

Numfashi Faryal ta furzar, kafin ta miƙe tsaye tana dan lankwashe yatsunta suka yi ƙara. Ta gyara zaman medicated glasses ɗin ta sannan ta ɗauki wayarta, ta nufi hanyar fita daga Office ɗin. Biyo bayanta Aysah tayi, suka fita sannan ta kulle mata office ɗin suka nufi hall ɗin da zasuyi meeting ɗin.

Suna shiga meeting hall ɗin, hankalin kowa ya koma kanta. Despite kasancewarta matashiyar budurwa me kananun shekaru, but her confidence and demeanor commanded respect. Su kansu baƙin ba su yi tunanin ita ce CEO din ba sai da suka ga kujerar data zauna akai.

Bayan gaisuwa, suka fara tattaunawa kan abinda ya tarasu. Kuma Alhamdulillah an gudanar da taron cikin nasara, dan Faryal ta yi farin ciki da matsayar da suka samu.

Bayan sun sallami baƙin nasu, ta yanke shawarar zagaya Company tare da Aysah domin duba yadda ayyuka ke gudana.

Sun ɗauki tsawon lokaci suna zagayawa haɗi da duba ayyukan da akeyi, har sai da ta ga rana ta fara takewa sannan ta sallami Aysah ta koma office ɗin ta.

Zama tayi ta kira Hamdan, duk da cewa ba ta so kiran nasa saboda abin da ya yi mata a daren jiya, amma ta kasa haƙura, dan zuciyarta ce ke ingiza kan ta kira taji ko lpy yake. Haka dai ta bi zuciyarta ta kira, saida kiran ya kusa katsewa kafin ya ɗauka cikin muryar bacci.

"Karka ce min bacci kake yi?". Faryal ta tambaya cikin takaici.

Hamma ya yi kafin ya ce, "Eh whl, yanzu na farka. So nake ma in tashi in yi wanka in shirya zuwa masallaci, sai kuma ga kiranki".

"Anyway, Ya kake?".

"Lafiya kalau. Ke fa?".

"Ina lafiya in dai har mijina yana lafiya". Ta faɗi hakan a tausashe, kafin ta ƙara da faɗin, "Ya Umma?".

"Lafiyarta kalau, Alhamdulillah".

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce, "Ka faɗa min cewa ba za ka ƙara yin hakan ba, amma ga shi ka kuma. Ka ce min jiya zan ganka a online, amma sai gashi ka sake barina ina jiran gawon shanu".

"Eyyerh, yi haƙuri dan ALLAH Faryal. Umma ce ta aike ni wani wuri whl, to nayi dare ne kafin na dawo shiyasa ma ban bi takan wayar ba dan nayi tunanin ma kinyi bacci".

"To shi kuma kiran da na ma fa?".

"Kai, an ya kuwa. Ban ga kiranki ba gsky. Ai kin san da na ga kiranki, ba zan ƙi ɗagawa ba".

Shuru Faryal ta yi tana doubting akan kiran amma sai wani ɓangare na zuciyarta yake gaya mata kawai yana ƙoƙarin kare kansa ne. Amma still zuciyarta ta ƙi yarda ta ɗauke shi a me laifi. Katse tunanin nata tayi da faɗin, "To, shikenan dai Hamdan. Bari in bar ka ka shirya, kada ka rasa salla". Da haka sukayi sallama ta kashe.

Ajje wayar tayi akan table ɗin gabanta, a hankali ta shiga lila kujerar da take kai tana tunanin dalilin da ya sa Hamdan ya ƙi amincewa da tayin aikin da ta yi masa, bayan kuma bashi da wani abun yi. Ta kuma bashi shawara kan fara business nan ma ya yi mata kunnen uwar shegu, dan har cewa tayi zata hada shi da baqin su ya dinga saro kaya daga wurinsu sai ya kawo Company su ya shigar amma ya doje. Tambayar kanta ta shiga yi ko dai da gaske ɓata lokacin nata kawai take a kan Hamdan, dan a yadda abubuwan ke tafiya, ba ta yadda za'ayi su yi aure cikin irin wannan yanayin.

Tana cikin wannan tunanin ne aka ƙwanƙwasa ƙofar office ɗin. Kafin ta yi magana kuma ƙofar ta buɗe, Manira ce ta leƙo kai tana faɗin, "Gafara dai. Zan iya shigowa ko kuwa sai na jira an bani izini?".

Tsaki Faryal taja kafin ta ce, "Wane irin wulaƙanci ne wannan? Ko dama kin zo ne ki kunyata ni a gaban ma'aikatana?".

Shigowa Manira tayi tana faɗin, "Guess what?".

Sake haɗe rai tayi kafin ta ce, "What?".

Buɗe Ƙofar gabaɗaya Manira tayi tare da furta, "Surpriseeee!".

Da sauri Faryal ta miƙe, tana kai tafukan hannuwanta baki cikin mamaki, kafin ta fashe da dariyar farin cikin ta nufi matar da ke tsaye a bakin ƙofar da gudu, suka rungume cikin tsananin farin ciki.

Daƙyar Faryal ta sake ta tana bin ta da kallo ta ce, "Bestie! Yaushe kika shigo Nigeria ba sanarwa ba?".

Matar da Faryal ta kira da Bestie ta yi mata kallon gefen ido, kafin ta ce, "Haka kike barin baƙo a office ɗin naki tsaye kamar mabaraci?".

Riqo hannunta Faryal tayi, suka nufi 3 seater sofa ɗin dake karshen office ɗin. Suka zauna.

"To, ni da ba'a maraba dani ai sai in koma". Manira ta fada.

"To, ki koma mana, da wa ya kawo ki? Ai ba a maraba da ke a nan dama". Faryal ta faɗa hankalinta akan kawarta ta.

"Shegiya kaza! To, ba dan ni ba wa zai kawo miki Shenal ɗin?". Manira ta faɗa tana tahowa da sauri ta zauna kusa da Faryal ɗin tana tureta. Ta ce, "Dan baƙin ciki sai dai ya haɗiyi heart!".

"Ke dai kika sani". Faryal ta faɗa. Nan suka shiga hirar yaushe gamo, kowacce na bada labarin abinda ya faru bayan rabuwarsu.

(Saadah Shenal shi ne sunanta. Ta kasance ƙawarsu tun yarinta, har zuwa secondry school. Bayan sun kammala karatun secondry, results ɗin su ya fito. Faryal da Manira suka wuce University, a yayin da Shenal tace ita sai ta huta tukunna. Sai da Faryal da Manira suka shiga 200 level, kafin Shenal ta wuce Cyprus domin ci gaba da karatunta. Haka suka rabu cike da kewar juna ba dan sun so ba. Tun daga lokacin da Shenal ta tafi kuma, ba ta sake dawowa Nigeria ba ko da hutu, har sai yanzu da ta kammala karatunta ta dawo a matsayin ƙwararriyar likita). WANNAN KENAN.

Ko da lokacin salla ya yi, a bathroom ɗin dake office ɗin suka ɗauro Alwala sannan suka gabatar da sallar tare sannan suka cigaba da hira.

Da misalin 2pm, akayi knocking ƙofar office ɗin.

"Waye?". Manira ta tambaya a kasalance, tana me kishingiɗe a kan sofa tana kora drink.

"Wai miye haka ne? Ji abinda kikeyi kamar wata yar kauye. Abun kunya ma whl". Faryal ta faɗa tana harararta.

Banza da ita Manira tayi tana cigaba da faɗin, "Idan dai namiji ne, ki tashi ki je ki same shi a waje. Karki kuskura ki shigo mana da gardi cikin office ɗin nan, yww".

"Eh saboda falon faza ne ko?". Faryal ta fada a hasale.

Shenal ta fashe da dariya, tana kallon su duka biyun kafin ta ce, "Ikon Allah, wato har yanzu dai ba ku daina wannan halin naku ba ko?".

"Gata nan uwar neman tayi". Manira ta faɗa tana nuna Faryal data tashi ta koma kan kujerarta, tana bawa me knocking ɗin izinin shigowa, dan already ta riga ta ga waye a CCTV camera ɗinta.

Aysah ce ta shigo da sallama amma bata Ƙaraso ba, ta tsaya daga bakin ƙofar tare da faɗin, "I'm sorry ma'am. Hope I don't bother you with your guest".

"No problem Aysah. They are my sisters".

Ɗan murmushi Aysah tayi kafin ta gaishe dasu Manira, wanda bata san lokacin da suka shigo ba. 

Ƙarasawa tayi gaban table ɗin Faryal ta fara mata bayanin kayan da aka shigo dasu yanzu, sannan ta ƙara da faɗin logistics manager ya buqaci ta zo ta ga kayan idan tana da lokaci.

"Ai ko kema in kin gani ya wadatar Aysah. Amman jira ni a waje, ina zuwa".

"Okay, ma'am" . Aysah ta amsa, sannan ta juya ta fita.

Faryal ta miqe tana kallon Shenal ta ce, "Shenal, mu je in zagaya da ke, kiga Companyn mu ko".

Manira ta katse ta da faɗin, "Ni kuma saniyar ware ko oho".

"Kanki ake ji". Faryal ta faɗa tana gyara mayafinta ta dauki wayarta sukayi waje.

Su ukun suka fito daga Office ɗin, Aysah ta jagorance su har zuwa wurin da aka Parker trailers goma na kayan.

Saida Faryal ta duba motocin ɗaya bayan ɗaya, ta tabbatar da komai daidai kafin su bar Aysah tare da su logistics manager su wucewarsu.

 Zagayawa ta shiga yi da Shenal da Manira a cikin Companyn. Tana nuna wa Shenal sassa daban daban haɗi da yi mata bayanin yadda kowanne sashe yake aiki.

Sun ɗauki lokaci mai tsawo suna zagayawa, kafin daga bisani su koma office ɗin Faryal ɗin.