RU'UYAA (The dreams we never lived)

38. ...What we have...🖊️

by @autum17






Slowly ya sauke fararen ƙafafunsa saman farin carpet mai laushi dake gaban gadon shi ya miƙe tsaye yana stretching kafin ya shiga baye yayi wanka ya dawo gaban madubi...goge jiki yayi ya shafa mai a nutse,bayan ya gama yasa farar t-shirt da singlet da baƙin wando...ya gyara gashi ya fesa turaren mai daɗin ƙamshi sannan ya ɗauki waya ya fito daga ɗakin...a dining ya gansu suna breakfast ya isa wurin ya gaishe dasu...suka amsa warmly su Amnah suka gaishe shi bayan nan ya wuce kitchen ya haɗa ma kanshi breakfast,har zai zauna a kitchen sai kuma ya fito...the atmosphere around them was gentle...

****

Na ɗauka da Roman yayi tafiya zan kasance cikin baƙin ciki,inji na damu amma sai naga akasin hakan,naji daɗi sosai..dayake Khalil ya hana ni jin ko wane irin rashin jin daɗi,kullum muna tare bana gundura da kasancewa tare dashi kullum har alla alla nake safiya ta waye mu sake haɗuwa

ta waya nake faɗa ma Jay yanda nake ji game da Roman ya canja tace

'' dama ai ba son shi kike ba, Abunda kike ji game dashi ana kiranshi da infatuation...wani lokaci kiji kina son shi kamar zakiyi hauka,wani lokaci kiji baki damu dashi ba...nan da lokaci kaɗan idan kin dena son shi da gaskiya ta..amma idan har wucewar watanni yanda kike ji game dashi bai sauya ba toh da gaske sonshi kike!" 

Na jujjuya maganar ta a raina...ina fatan in dena sonshi gaba ɗaya Hmph!


Badaɗewa asabar tazo ranar zuwa gida kenan...Khalil sai marairaice min yake wai inyi zama na in bari sai wani sati

''hh,ai nayi kewar su Mama kuma suma suna so su ganni...''

'' idan kika tafi zan kasance cikin kaɗaici!" Yayi maganar yana turo baki...wannan Khalil ɗin..ɗauke fuska ta nayi gefe ina dariya '' pls kitten!"

'' kaxo mu tafi tare sai ka dinga kwana a baye'' zaro ido yayi yace

 '' kina so aljana ta aure Ni!" Na tuntsire da dariya...


Da yamma wurin ƙarfe biyar muka iso gaban gidan mu..yayi parking har zan fita naji ƙofar rufe...yake kallona ido can ciki '' yanzu dai tafiyar zakiyi ko?"

'' gashi ma har mun kawo''na bashi amsa ya girgaza kanshi...'' ai ranar Lahadi da yamma xan dawo!" Na sake faɗa..ya sauke ajiyar zuciya

 '' then,zaki dinga kirana kullum?"

corner bakina yayi sama duk da naso hana kaina murmushi...'' idan kana jin kaɗaici Diyaam zata raka ka!" Girgiza kanshi yayi murya ƙasa yace '' she's not Abeedah...'' 

Lumshe idona nayi ina jin kaɗaicin shi,ga Romo bai nan..dama kuma ko yana nan ba wani abun zai tsinana ba...na kwantar da murya nace '' ai na yau kaɗai ne gobe fa zan dawo..ka daina damuwa kaji?" Sai ya jinjina kanshi..yanda yake yi ɗin kamar yaron da mamarshi zatayi tafiya tabar shi nayi dariya '' bari in yi musu magana daga ciki sai ku gaisa...''

Da sauri ya riƙon hannu na '' idan nazo gobe .. I'm not properly dressed..'' kallon kayan Jikin shi nayi..ƙananun kaya ne.. toh meye matsalar? gyaɗa kaina nayi..

Ya ciro kuɗi masu yawa daga gaban wurin ya miƙa min na ɗage gira '' idan kina buƙatar wani abu..''

zance ya barshi yayi saurin faɗin '' i won't take no for an answer!" Khalil ɗin nan yana kashe min zuciya...'' okay Nagode sosai!" na jefa kuɗin cikin ƙaramar purse ɗin daya siyamin akan hanya

Na buɗe motar na fita yayi ƙasa da glass ɗin gefen wurin '' ji nake kamar in jawo gobe..'' ya faɗa suddenly...

'' Nima...'' maganar ta fito ba shiri da sauri na rufe bakina ya washe baki '' ashe kina sona har haka?" 

Da sauri nabar wurin bakina ya kasa rufuwa..ina jiyo dariyar shi daga baya na

'' Assalamualaikum masu gida ana sayen kayan miya...'' na faɗa da murmushi bayan na kawo tsakiyar gidan...Anaam dake riƙe da pepopin jarabawar mu ta zubar tayo kaina... Asma'u dake wanki ta miƙe tsaye da murmushi a fuskarta 

'' Abeedah!!!!!!" Anaam ta jefar dani su Mama suka fito daga ɗakinsu

'' maraba maraba da TUWO!!!" Inna sarai ta fincike Anaam daga jikina ta miƙar dani na faɗa jikinta na ƙanƙameta ina dariya 

'' kada ki karya Ni...'' inna sarai ta jaye ni daga jikinta tana dariya itama...purse ɗin data faɗi sanda Anaam ta jefar dani ta ɗauka,wasgewa Anaam tayi daga hannun inna sarai kuɗin da Khalil ya bani suka faɗi waya ta ma saura kaɗan ta faɗi...idonsu duka suka buɗe

Mama dake tsaye sharply ta iso wurin ta karɓi komai daga Anaam tana min kallo fuska a matuƙar murtuke kamar ba ita take murmushi ba yanzu... Asma'u ma ta ƙaraso tana duba wayar tace 

'' ke Abeedah wannan tsadaddar wayar da ake yayi daga ina kika samu?" Sai kowa yake jiran amsa daga gare ni..yanda Mama take kallona ya sanyaya jikina...

'' waya baki wannan wayar da kuɗin?" Ta tambaya a kausashe tana min kallo mai ma'ana..hakan ya karya zuciya ta hawaye suka ciko idona

'' abi ahankali yaya...'' Inna sarai ta faɗa ta dawo gefe na..'' tambayar ki nake!!!" Mama ta maimaita da ɗaga murya naji zuwa gidan ma ya fita raina...yanzu... taune leɓena nayi da na fahimci abinda Mama ke tunani....


'' Khalil!" Na furta kai ƙasa...zaro ido Anaam tayi'' Khalil dai daya zo nan ya kawo abinci sanda kika tafi gidan su Jadeedah?" na gyaɗa kaina ina share hawayen da suka zubo da sauri wasu nabin wasu...sai expression ɗin ta ya ɗan sassautu amma bai canja ba

'' me kika yi mashi daya siya maki waya kuma ya baki wannan kuɗin?"

'' ko kuma ina ma kuka haɗu?" Asma'u ce ta jefo tata tambayar bayan Mama...duk muna tsaye bayan yanzu nazo...anya nan gidan mune kuwa


'' wayar da kika bani ce ta faɗa cikin ruwa..shine yasa!" Inna sarai daga gefena ta shafa kafaɗuna ta sigar lallashi...


'' a gidan su nake aiki!" Naba Asma'u dake shirin ƙara tambaya ta amsa...naga shock a fuskar ta...kasa haƙura nayi na kalli Mama '' yanzu Mama....kina tunanin...zanyi...'' ban ƙarasaba ...naga yanayin ta ya koma na rashin jin daɗi...

Na jaye jikina daga na inna sarai na shige ɗakin mu na faɗa saman gado ina kuka sosai..harda abinda ya kusa faruwa dani yasa nake kuka ba kawai abinda Mama take ayyanawa a ranta ba duk da nata ɗin yafi min ciwo....

Anaam ta shigo ciki ta zauna gefe na..ko ta lallashe ni sai ta buɗe wayata da babu password tana wasa da ita saboda rashin wayo

Inna sarai ta shigo ɗakin ta zauna daga gefe na '' yanzu Abeedah akan abinda baki da tabbaci akan shi kike kuka? Waya faɗa maki zargin ki take?" Inna sarai ta tambaya

'' baki ga yanda take kallona ba...hakan yayi min ciwo sosai..'' na tashi zaune

'' sai kuma kike kuka?"

'' ai Abeedah wata irin baby ce,abu ko bai kai ya kawo ba sai tayi ta kuka! Hawayen take dasu shine yasa!" Inji Anaam tana jan tsuki

'' tashi kibar wurin nan!" Inna sarai ta kore ta daga ɗakin...amma maganganun ta sun tsaya min arai...meyasa nake da saurin kuka har haka? Ko abu bai kai ya kawo ba sai inji ya soki zuciya ta koda da wasa ne...meyasa baxan iya zama mai taurin rai ba inƙi kuka?

Khalil...shima idan ina mashi kuka haka yake tunani? 

Kasa tsayawa hawaye na sukayi...kamar an buɗe famfo...inna sarai tana ta lallashina koda aka ce a zubo min abinci kasa ci nayi...

'' to ki cire hijabin ki huta mana!" Inna sarai ta tayani cirewa...Mama ce ta shigo..idon mu na haɗuwa...na koma yar gidan jiya..sum sum ta zauna can gefena

'' Haba Abeedah bada gangan bane kinji kiyi haƙuri...kin san na damu dake shine yasa...ba wai ina zargin ki bane kinji!!'' turo baki nayi ina share hawayen da suke suntiri itama tana taya ni...

 Asma'u ke tafiya kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki ta zauna can gefe...


Anaam ta ɗago daga kallon wayata ta zuba tagumi ta kafe ni da ido '' wai jama'a kuna ganin abinda nake gani kuwa?"

Kowa aka juya ana kallonta'' toh uwar tsegumi me kike gani damu Bama gani?" Inna sarai ta harari Anaam


Ɗaga hannunta Anaam tayi fuska taɓe ta cigaba da wasa da wayata

'' wai saratu kin gane min ƙirjin Abeedah kuwa...ciko kika fara?" Mama tambayar tana ƙoƙarin leƙa rigata..da sauri na dafe wurin....''kai innalillahi Mama...'' na furta da tsananin kunya '' ke bari mugani mana!"

Inna sarai take ƙoƙarin cire hannu na suna dariya,da sauri Anaam tayo wurin mu '' bari in taya ku ƙasa da rigar...!"

suka wani tararmin wai so suke su gani..'' wallahi kuwa iyye Abeedatuwoooo yan mata!" Mama tayi maganar tana riƙe baki...sun ban dariya da kunya '' kai Mama...'' 


'' to bazaki bari mu gani ba?" Anaaam ta furta tana jaye hannuna da ƙarfi inna sarai ta sakar mata duka a hannun ta sake ni tana yarfi fuska kamar an kwaɓa rogo..

Su Mama sai dariya suke.. can Anaam ta jaye ɗan kwalina..nan ma ana ta santin gashina sai zolayata suke wai gidan masu kuɗi ya karɓe ni...kowa na farin ciki banda Asma'u data zauna gefe tana binmu da ido..ban ce komai ba


'' amma shi Ibrahim ɗin akwai wani abu tsakanin kune?" Inna sarai ta tambaya..ban san dalilin da yasa blush ya mamaye fuskata ba daga jin wannan tambayar..na rufe Fuska ina dariya...wacce bani da control akai..kawai taxo ne...

'' Uhmm,da akwai kenan!" Mama ta faɗa...Anaam ta zauna gefe '' gaskiya auren mai kuɗi kin huta Abeedah...'' 

'' Mama babu wani abu tsakanin mu..kawai dai yana min mutunci sosai!"

'' shikenan inkin ce...'' Mama ta faɗa da murmushin manya...'' na kasa yarda Abeedah ce ta girma haka..ji pimples ɗin sun ragu..harda wani kyau da fresh ta ƙara!"

Anaam ta riƙe haɓa can ta ƙara faɗin '' ko in zaki koma in biyo ki mu tafi?" 

'' da naji daɗi!" 

'' kodai daga ni har ke ɗin a koro mu ba!" Ta furta tana taɓe baki...


Nasha tambayoyi da yawa game da Khalil...Anaam ta shiga pictures tana zaƙulo hotunan da muka ɗauka kwanakin baya a kitchen sai santin haɗuwar kitchen ɗin take

'' wannan ba Diyaam bace?" Ta tambaya tana nuna min wani inda Diyaam na zaune Khalil a bayanta yana nuna mata wani abu

'' itace... gidan take!" Na bata amsa...ta zaro ido...

Nayi farin cikin dawowa gida sosai..da daddare bayan sallar Isha'i mukayi waya da Khalil..sai lokacin na fahimci ashe nayi kewarshi sosai...

Har lokacin Asma'u bata wani sake dani ba kuma ban san dalili ba...bayan na gama magana da Khalil nida Jay d muka shiga chatting sai wurin ƙarfe tara na wanko baki na canja kaya zuwa wasu daga cikin kayana dake gidan ina kallon gashina ta cikin madubi daya saukor har kafaɗa Anaaam ta shigo ta zauna bakin gadon mu

'' wai Abeedah kin koga yanda kika canja sosai..kamar wacce tayi shekara! ashe makaranta kallon tsoro muke maki!" tayi maganar da alhini

'' Ni banga canjawar da nayi ba!" Na faɗa da gaskiya 

'' kalla hips da bayan ki...kalla ƙirjinki...da kina nan gidan mata kamar allo,amma yanzu jibi yanda kika zama yan mata yar shafal shafal duk da ba wai sun girma can can bane amma dai yafi da!" Tayi min dogon bayani harda zagi...juya idona nayi

'' ko fuskar ki ta canja kin ƙara kyau..kai ban taɓa kishin idonki ba sai yau...waih..wayyo Allah nima ina son ido ruwan toka!" Dariya nayi da wannan dramar na Anaam na dawo na zauna gefen ta 


'' ke wai kin san gayen nan ɗan uwan Khalil..'' 

'' Romaniya?'' hararta nayi '' Roman fane sunan shi...baki gan shiba kyakkyawan gaske fari sol ashe ɗan Italiya ne,gashin shi har gadon baya baƙi mai laushi!" 

'' dan Allah?"

'' wallahi...ɗan rainin wayon bai taɓa murmushi ba ..ɗaya daga cikin kwanakin baya yayi tafiya zuwa Abuja!" na bata amsa ta saki baki da hanci

'' amma dai Khalil yafi shi mutunci ''

'' nesa ba kusa ba!" Na bata amsa ina tuna abinda yayi min ko haƙuri bai bani ba

'' wai Asma'u ko magana!'' wani kallo ta jefa min ɗaɗɗage daya sa na taɓe baki nida Anaaam muka cigaba da hirar mu...sai ƙarfe goma muka kwanta...

Wayata tayi ƙara alamun shigowar message,ɗauka nayi na duba '' good night kitten..Kiyi mafalkina kinji!" Saƙo ne daga Khalil juya idona nayi...bakina yaƙi rufuwa Anaam ta zuro min kanta

'' Goodnight kitten Kiyi mafalkina..'' ta karanta message ɗin a fili... ture kanta nayi..sai ga Asma'u ta zuro nata itama...ban damu ba..na tura mashi emojin '🙄' juya ido dana murmushi


Da sauri reply ɗin shi ya shigo '' i can feel your blush!" Yar ƙaramar dariya nayi na manta da Asma'u dake kusa dani na cigaba da texting ɗin shi...ina jin bacci gashi messages ɗin shi nata shigowa kawai sai na miƙa mata wayar ...da sauri ta karɓa suka cigaba da hira.. nikam nayi bacci...

Da safe wurin ƙarfe goma Jay d ta iso...gidan ya ɗauka ita da Anaam suka haɗu suna min shaƙiyanci.. Asma'u tana daga gefe..'' wai, yar gidan Khalil bada kanki a sare kije gida kice ya faɗi'' na ɗauke kaina gefe...zama tayi saman gadon ta ajiye hijabinta gefe aka buɗe sabon shafin hira...'' ke wai baki da hoton Roman ɗin nan ki nuna min?" Ta tambaya

''nidai a iya sani na ban dashi amma duba ki gani!'' na bata wayar...sai lokacin na tuna da ƙaramar wayar da Khalil ya bani yace inba Mama...tashi nayi na kai ma Mama wayar su kuma sai hayaniya suke wurin neman hoton Roman

'' hmm,nidai wannan abu da walakin goro a miya!" Inna sarai ta faɗa...''.kai inna sarai '' na turo baki


'' mai za'a dafa mashi da yamma kin ce zai zoko?" 

'' ɗan wake!" 

'' har kin san abinda yafi so!" Inna sarai ta are ta yafe...tashi nayi na fita daga ɗakin ina ƙunƙuni.. Inna sarai tana ta dariya


Da sauri ranar ta wuce yamma taxo su Jay d duk haushi ya kama su akan rashin ganin hoton Roman a wayata...koda akwai dana goge...


inna sarai da kanta ta dafa ɗan waken su Jay d daga cikin ɗaki suna jiran zuwan Khalil... Anaam ta ƙudira a ranta sai ta faɗa mashi cewa Roman bai kai mu gida ranar ba...


Ruwa na ɗiba na shiga Baye ina wanka naji wayata tana ringing..kafin into magana har wani ya ɗauka...



''.kitten!" Muryar Khalil ta shiga kunnen Asma'u.. wani irin lumshe idonta tayi saura kaɗan ta faɗi..da sauri tayi balancing kanta Allah yasa ba kowa ɗakin..

'' I'm outside your house...'' ya katse kiran kafin Asma'u tace wani abu...ajiye wayar Asma'u tayi ta ɗauki hijabi tasa ta fito tsakar gida '' Mama wai yazo yana ƙofar gida..'' ta faɗa ma su Mama dake zaune a baranda...da sauri suka tashi suna kalkamta barandar

'' kije ki shigo dashi!"Mama ta amsa,ita da inna sarai suka shiga ɗakin su... Jay d da Anaam suma suka wuce ɗakinsu...


Tsayawa Asma'u tayi zaure taja dogon numfashi zuciyar tana tsananin duka sannan ta fito...daga nesa take jiyo ƙamshin turarenshi, hakan ya ƙara ma zuciyarta bugu...


Fitowa tayi tagan shi tsaye jingine da motarshi saye da shadda olive green...data sha guga ɗinkin yayi mashi kyau sosai ya zauna jikinshi...hannunshi saye da wai agogo mai bala'in kyau.. Asma'u taji kamar ana ƙara kwaranyo soyayyar shi a zuciyarta wannan lokacin...

Bata san tsawon yaushe take kallon shiba,kawai ganin Anaaam tayi tazo ta wuce ta '' wayyo Allah kayi kyau sosai...kai!!!" Juyowa Khalil yayi ya kalli Anaam sai kuma ya saki murmushi

'' Anaam!" Ya kira sunanta

'' ashe ka tuna?" Ta dafe kumatun ta 

'' in manta ne...''

'' kai ai..sanin sunana shine sadakin aurenka da Abeedah idan ka manta shikenan!" Khalil ya gyara hularshi yace 

'' bari in ƙara haddace sunan da kyau da kyau!" Su biyun sukayi dariya Asma'u tayi tsaye baki sake fuskarta tayi duhu wane irin abune Anaaam take yi haka? How dare she steal her moment...taune leɓenta tayi tana jin haushin ta sosai


'' oh wai ka shigo ciki fa!" Anaam ta faɗa bayan sun gama gaisawa da Khalil tana gaba yana biye da ita...

Asma'u ta juya da sauri ta koma ciki '' waccan ba Asma'u bace!?'' Khalil ya tambaya '' itace fa!" Ta bashi amsa

suka shigo gidan tare...yake bin ko ina da kallo...su Mama da inna sarai suka fito nan da nan Khalil yakai ƙasa yana gaishe dasu cike da girmamawa..suma su Inna sarai suka durƙusa daga inda suke suna amsawa da kuma yi mashi godiya akan abinda yayi ma Abeedah


Bayan sun gama gaisawa ya zauna saman daddumar da aka shimfiɗa mashi saman tabarma ya tanƙwashe ƙafafun shi kanshi ƙasa...abinci aka ajiye mashi da ruwan gora yake kallon ɗan wanken,dasu cabbage da sauran abubuwa sosai ya biyo mashi a rai...amma kafin nan idonshi sai neman Abeedah suke

'' wai ina Abeedah?" Inna sarai ta tambaya ganin yanda yake kallon ko ina...


'' Mama a ƙaro min ruwa...ruwana sun ƙare...yaji ya shigar min ido...'' suka jiyo Muryar Abeedah daga Baye

''.ashe wanka take..ƙazamar yarinya!" Inji Anaam..da sauri Jay d ta fito ɗakin su Anaam ta ɗauki bokiti ta ɗebo ruwan sanyi takai mata a bakin ƙofar bayen '' ga ruwan ki buɗe ki ɗauka!" Ta furta 


'' ina Mama?" Ta tambaya daga ciki bayen

'' Mama wai Abeedah kizo ki taya ta wanka!" Anaam ta kware baki daga inda take zaune...Khalil yake murmushi ƙasa ƙasa..tace '' Abeedah Mama ke mata wanka bata iya wanka ba ..bokiti gudan data shiga dashi na ruwa ya ƙare..yanzu na tabbatar idan ta fito aka duba sai anga inda bata wanke ba!" 


Jay d ta talle ma Anaam ƙeya '' suda uwar surutu!"..ta tsaya can gefe ta gaishe da Khalil '' Asma'u bazata zo mu gaisa bako?" Ya tambaya da murmushi

'' bari in kirata..!" Anaam ta tashi ta shiga ɗakin,samun Asma'u tayi laɓe da bango tana sauraren abinda ke wakana a waje...

Idonsu na haɗuwa Asma'u ta ɗaure fuska Anaam ta taɓe baki...'' iska na wahalar da mai kayan kara...ai ni dama na daɗe da sanin son bawan Allah'n nan kike... maimakon ki fito fili ki faɗi sai laɓe laɓe kike...ki tsaya kallon ruwa kwaɗo ya maki ƙafa!'' bangaje Anaam Asma'u tayi ta fito da hijabin data sa ɗazu daga bakin ƙofar ɗakin ta duƙa cike da kunya tace '' ina wuni...''


'' a'a ni bazan amsa ba,sai dana roƙa...'' da wani irin siririyar murya Asma'u tace '' ba haka bane wallahi...'' Anaam da Jay d suka kalli juna suna gimtse dariya...'' ya karatu?"

'' Alhmadulillah...'' 


Fitowa nayi daga bayen saye da hijabi..duk budurin da ake ban sani ba...ajiye bokitin nayi tare da tsalle na kamo igiya na shanya pant ɗin dana wanke,ina waƙa ina murya sama ina juya kaina 


🎶 One kiss is all it takes... falling in love with me...🎶

...naji idanu da yawa a kaina yasa na kalli baranda...

Saura kaɗan zuciyata ta fito ta baki da ido na ya sauka ana Khalil !!!... jaye idonshi yayi daga cikin nawa a wani irin luuu ya sauke su akan pant ɗin...ba shiri na kamo igiyar na warce pant ɗin na ɓoye cikin hijabina...duk jikina yayi zafi bayan da ruwan sanyi nayi wanka,naso in ɗaure fuska inyi kamar babu abinda ya faru sai dai na kasa ɗago idona in kalle shi

Anaam da Jay d suka saki dariya...banda Asma'u... Khalil baice komai ba..na taune leɓena 

Sum sum hannu gaban hijabi na raɓa su na shige ɗakin mu...na faɗa saman gado,sai kuma na tashi na fara safa da marwa !!! meye haka?

 🌹 ❤️📖✨



***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin ***..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️