RU'UYAA (The dreams we never lived)

39. ... Attractions...🖊️

by @autum17


Jay d ta zuba ma Khalil abincin ta ajiye a gabanshi,baki washe ya ɗauki cokali kamar ranar a cikin kitchen ya fara caccakar ɗan waken...daga gefe suna ta dariya... haka haka har yaci rabi yabar sauran...

Anaam tace '' kasan ranar wannan ɗan uwan naka bai kawo mu har gida ba wallahi cikin ruwa ya ajiye mu!" Khalil ya zaro ido bayan ya goge bakin shi

'' da gaske?" 

'' eh mana...hm..ai ka fishi mutunci!" 

Daga cikin ɗaki Abeedah tace '' har da kyau ma!'' 
Khalil yayi ƙasa da kanshi yana dariya 

'' Sha'awanatu da Abeedah kunci gidan ku!" Mama ta faɗa daga cikin ɗakinsu...

Anaam bata sake cewa komai ba,Jay d ce take jan Khalil da hira.. he was so down to earth.. sosai ya birge ta,taji inama ace shi Abeedah take so



da sauri na shirya cikin doguwar rigar atamfa,na tsane gashina na shafa mai harda kwalli a ido..ban san dalilin dayasa nake so inyi kyau a wannan lokacin ba,amma dai ba kwalliya nayi ba

🍁🍁: anya kuwa? naga harda powder da ɗan ƙaramin jan baki...


Abeedah: nifa bana son sa'ido...farar ƙasa ce na shafa ba powder ba. 

Nayi kyau sosai na ɗaura ɗan kwali na fesa turaren su Anaam dake saman wurin...

Anaam ta shigo ta sauya hijabi har takai ƙofa nace '' ina zaki ne?"

''.wurin baba Saminu mai sharare zan tafi in bashi takardun jarabawar mu ya bani sharare...'' 


'' ki jira mu sauke ki...'' ta wani share min kallo sama da ƙasa '' sannu masu mota!''

Nayi mata gwalo...ta fito ta shiga ɗakinsu Mama bayan tafito tace '' Jadeedah mu tafi ki rakani..!"

Leƙowa nayi '' wai ban gane ba...''
'' Meye baki gane ba?" Anaam ta Harare ni

'' yaushe kuka zama ƙawaye ne har haka?" Na naɗe hannu a ƙirji

'' Tun kafin mu haɗu muka zama ƙawaye!" Anaam taban amsa


Kallon Jay d nayi tace '' ai kema kin san keta dabance...babu me maye gurbi...''

'' Hmph!!" Na saki labulen da sauri bayan idona ya haɗu dana Khalil dake kallona ko ƙiftawa bai yi...yanda zuciya take bugu ina gudun kada ta katse ta faɗa cikin ciki na..


''kishi har na Innalillahi!" Anaam ta furta tana hararar labulen...Khalil dai tunda yaga Abeedah notikan kanshi suka fara zarewa what was that? ya tsare ƙofar ɗakin da kallo 

ganin su Jay d na kallon shi sai ya ɗan shafa ƙeyarshi yana murmushi da kallon gefe 

Jay d da Anaam suka fara dariya da tsokanar shi


Fitowa nayi saye da farin hijabi na tsaya gaban shi amma ban kalli fuskarshi ba dan kunyar shi nake ji sosai '' ka gama cin ɗan wanken? Yayi daɗi? Mu tafi da sauran?" Na jero mashi tambayoyin yana gyaɗa kai...


Kitchen na shiga na ɗauko sabuwar kula na juye sauran ciki...wanda ya ajiye gefe na ɗauka na zauna can gefe ina ci...


Yake bina da kallon nan nashi.. murmushin shina ƙara faɗaɗa...ban kalli inda yake ba...

Daddanna wayarshi ya shiga bayan wani lokaci...sai kuma ya ajiye yana kallona yace '' shall we?" 

ajiye plate ɗin nayi na sha ruwa,sannan na shiga ɗakinsu Mama na faɗa masu zamu tafi...

 suka sake fitowa su biyun suna ta suburbuɗa ma Khalil Godiya da addu'a...shima yana amsa a girmame kanshi ƙasa...ya tashi ya fita bayan nan


Anaam biye dashi tana surutu kamar yanda ta saba...ina jiyo sanda take tambayar shi wai idan ya taɓa cin sharare..na girgiza kaina..


Mama ta bani dubu biyar cikin kuɗin dana kawo jiya duk da nace bana buƙata...inna sarai ta haɗani da kaninfari riga-kafin infection...

Karɓa nayi ina miƙa tawa godiyar...su Mama suka ƙara min da nasiha gajeruwa mai ratsa jiki...

na jisu sosai kuma zanyi amfani da abinda suka faɗa... sanda na fito Asma'u kaɗai ce tsakiyar gida...ko kaɗan ban son yanda abubuwa suke tsakanin mu tayi min murmushi a karo na farko tunda nazo gidan '' mu tafi in raka ki...'' nima baki washe kamar sabuwar amarya na dinga jinjina kaina...


Muka fita daga gidan...nayi mamakin ganin su Jay d cikin motar...bakin ƙofa Asma'u ta tsayar dani zata koma nace tazo mu tafi tare sai su dawo...da ƙyar ta yarda...gaban motar na zauna ita kuma ta zauna dasu Jay d a can baya...sannan Khalil ya tada motar muka bar wurin...


Cikin motar babu abinda muke sai hirar baya...harda Asma'u naji daɗin yanda ta saki ranta ana hirar da ita... daga lokaci zuwa lokaci mutumin nan ke kallon sashe na...na samu kaina da jin nauyin shi fiye da koda yaushe


Parking yayi muka fito... directly wurin baba Saminu muka isa...mutane sun gane Khalil dan haka yau mutanen da suke bamu abubuwa kyauta sun fi na ranar yawa... Asma'u tace '' dama kun taɓa zuwa wurin?"

'' yeah...and it was the best day of my life..thanks to kitten!" Khalil ya bata amsar yana kashe min ido...su Jay suka zage ita da Anaam suna ta cin komai aka kawo...sai wurin shida da rabi har rana ta faɗi sanyin marece ya sauko muka bar wurin...Jay d muka fara ajiye wa a gidansu ta sauka tana ma Khalil godiya tace '' in the future,idan kazo neman auren Abeedah nida Anaam mune gaba gaba ko Anaam?"

'' hakane yar uwa...'' Anaaam ta amsa murya sama...Khalil yayi dariya bai ce komai ba sai kallona da yayi...bye bye tayi mana sannan ta wuce gida...



Ya rage saura Asma'u da Anaam... hirar ta koma tsakanin mu uku... badaɗewa ba muka iso gida...su Anaam suka sauka...tace '' toh Allah ya kawo mana ranar da za'a zo ɗaukar amarya..yayan mu!" 

'' Ameen!" Khalil ya amsa...yaban mamaki da kunya...yace '' Asma tunda ba zaki yimin sai da safe ba,Ni kam sai da safe...'' Asma'u ta tsaya ta juyo da murmushin yaƙe a fuskarta tace '' sai da safe... Allah ya kiyaye...'' 

Ya amsa da Ameen ya tayarda motar muka bar wurin

bin bayan motar da kallo Asma'u tayi sanyin marecen na ratsata fiye da normal zuciyarta na narkewa da soyayyar Khalil at the same time tasan yayi mata nisa...hawaye suka taru a idonta..duk sanda ya kira sunanta kamar yana goga gishiri a ciwon dake wurin ne...she wants him...

Anaam ta tsaya daga gefenta..amma yau babu baƙar magana..sai ma Hawayen data shiga goge mata...'' kiyi addu'a kinji?" Gyaɗa kai Asma'u tayi suka shige ciki



Cikin motar yayi shiru bayan fitarsu...babu abinda ke tashi sai sanyin A'c da kuma ƙamshin turaren Khalil...daga lokaci zuwa lokaci nakan saci kallon sashen shi...

'' nayi maki kyau ne?" ya ɗage gira yana cigaba da kallon gaban shi...lashe lips ɗina nayi ƙasa da idona '' You look beautiful!" He whispered..wani irin butterflies naji a cikina..bakina ya kasa rufuwa can nace '' akwai... is there a possible way to thank you?" 

'' yeah...if you'd kiss me!" Ya furta daidai muna shigowa cikin gidan... idona waje har yayi parking ya juyo side ɗina 

'' wanna try?" Da sauri na ɗauki ledar dasu Mama suka bani na fita daga motar gudu gudu sauri sauri...kamar xan kife


'' wasa nake fa!" Naji Muryar shi daga baya amma nikam banko juyo ba...ban tsaya ko ina ba sai ɗakin mu

Na jingina da ƙofar hannu na dafe da ƙirjina ina dariya...what was that?


Ajiyar zuciya na sauke..na ajiye abubuwan dake hannu na saman gado na ƙwanƙwasa ƙofar toilet bayan na tabbatar ba kowa na faɗa ciki...wanka na sake yi na fito nasa kaya marasa nauyi...


Na sauka ƙasa na ɗauko wata gora na zuba kaninfari da yawa ciki na xuba ruwa na rufe kamar yanda Inna sarai tace...


Wurin ƙarfe tara muna kallo nida wasu masu aiki Hansa'u da Fauziyya suka shigo a tare...kallon banza suka bini dashi ban damu ba na cigaba da kallo tare da sauran...fim ɗin yayi min kyau sosai...


Da ƙarfe goma dukan mu muka shige ciki...nake kallon saman gadon Hansa'u amma dai nayi nisa cikin tunanin Khalil...meyasa nake tunanin shi? Meyasa nake murmushi idan na tuna abubuwan da mukayi tare? Meyasa nake son kasancewa dashi? 

' yana da kirki!" Wani sashen na zuciyata ya faɗa...a haka har bacci yayi gaba dani...

wurin ƙarfe biyu Hansa'u ta sauko daga gadon ta tana kallon Abeedah maliciously kafin tayi ƙwafa ta isa wurin ƙofa ta buɗe... Fauziyya ta shigo saye saye da baƙin hijabi suna magana ƙasa ƙasa tsakanin su

Kafin Fauziyya ta ciro wani ƙoƙo daga ƙasan hijabinta mai ɗauke da wasu baƙaƙen ƙwari suka isa wurin kan Abeedah suka zazzage mata ƙwarin akai...ƘWARƘWATA ne aciki... 


Suka kalli juna da murmushin mugunta sannan Fauziyya ta fita Hansa'u ta rufe ƙofar ta dawo ta haye gadonta ranta fess...


Washegari na tashi a wani irin yanayi..kaina sai ƙaiƙayi yake kamar abubuwa da yawa namin yawo a kai amma kona duba babu abinda nake gani yasa ban damu ba can can...

Na tsaya gaban madubi ina ƙara kallon gashina da yayi tsawo sosai...ina gode Allah dukda dai bai yi kama da irin na turawa ba...yananan da texture ɗin shi irin na Africa...

Wurin Diyaam na tafi muka yi karatun jarabawar mu ta gaba,muna zaune Khalil ya shigo bayan ya ƙwanƙwasa mun bashi izini

Can gefe ya zauna..sau ɗaya na kalle shi nayi ƙasa da kaina...yana ta murmushi '' gudu na kike ko?" Ya tambaya can

'' a'a ba haka bane fa!'' nayi maganar da buɗe ido...ɗauke kanshi yayi yana taunar leɓenshi '' hmmm,shine baki zoba?" 


'' karatu muke shine yasa...kasan mun kusa gama jarabawar...'' na kalli Diyaam dake gyaɗa kanta idonta manne da littafin dake hannunta,na lura tunda ya shigo bata sake buɗe page ba kamar tana bitar wurin bayan kuma ko minti ɗaya batayi a page idan muna karatu har nake tunanin kodai kawai kallo take ta wuce

'' hmm..'' yayi shiru bayan haka yana latsa wayarshi...can ya tashi nabi shi da kallo '' zan tafi wani wuri ne...'' yayi min bayani

'' a dawo lafiya '' nida Diyaam muka haɗa baki

'' Ameen..'' ya amsa...

Har tsawon kwanaki ƙaiƙayin kaina bai dena ba...

Ranar Alhamis da safe muna tsaka da breakfast dukan mu,ƙaiƙayin ya taso min fiye da koda yaushe

'' wai anya yarinyar nan ba ƙwarƙwata gare taba?" Rasheedah take kallona fuska yamutse

'' kwata gareni ba ƙwarƙwata ba!" 

jaye min ɗan kwali Hansa'u tayi.. wasu manya manyan ƙwari suka biyo suka faɗi saman table....kowa ya tashi daga kusa dani kamar inada wata cuta


'' dama nasani! Ƙwarƙwata ce da ita shine take ƙoƙarin shafa mana!"

'' babbar buta cike da ruwan zafi!! Wallahi sai dai ai mata aski...baza ta shafa mana ƙwarƙwata ba!" 

Almakashi Hansa'u ta ciro daga aljihun wandon ta,cike da mugunta suka fara rufewa a kaina...ina ja baya ..su Aina'u ko sunyi ƙoƙarin taimako na bazasu iya ba...Mama Asabe ma ba sauraren ta suka yi ba...


'' ku barni in fita wurin Khalil!" Na faɗa cike da tsoro hawaye fal a idona.


'' inaaa! Babu wani Khalil da zaki wurin shi...''

Suka damƙoni ina kubce kubce ina kiran Khalil suka shiga katsemin gashi...


Da gudu Waleeda ta fita daga sashen mu zuwa babban gida,amma wa'yannan mutanen sun gama cimin zarafi...inaji ina gani gashin danake tsananin so...na daɗe ina tattali...na zubar da hawaye akai suka yanka tashi guda batareda sun ƙifta ido ba...aski suka min fa....


Babu abinda hawaye na suke sai zuba duk sunbi sun daddanne ni.. Fauziyya ce riƙe da almakashin...naji kamar sun zare min rayuwa....hawaye suka rufe min ido...dama Nasan basa sona bantaɓa tsammanin tsanar su takai har haka ba... wasu daga cikin yan aikin suka fara min dariya Mama Asabe tana ta sallallami

'' MEYA KE FARUWA ANAN!!!!" Khalil ya daka masu tsawar data sa lokaci guda suka sauka daga jikina suna rarrabar ido

Ƙarasowa yayi a inda nake kwance da gaggawa ya ɗagoni zuwa jikinshi...na ɓoye fuskata a ƙirjinshi ina kuka sosai

''Khalil...gashina...wayyo Allah na...sun kashe ni...wayyoooo!!! '' sukayi tsuru tsuru da ido suna kallo...wasu har suna ja baya dan su samu wurin ɓoyewa


'' waya baku izinin taɓa ta?'' ya sake daka masu tsawar idonshi sunyi jajur 


'' yallaɓai tana da ƙwarƙwata kuma...''


'' SHUT UP!!!!!" jijiyoyin kanshi sun fito..nida nasha wahala kafin na iya son kaina..yanzu taya zan iya kallon kaina a madubi?


'' wait for your turns...'' ya ɗauke ni muka fita daga sashen...


Bayan tafiyar su Abeedah masu aikin suka juyo suna kallon juna...cike da tsoron abinda zai biyo baya ..


Hansa'u ta matso kusa da Fauziyya '' koma meye ai munyi maganin yar iskar...''

'' eh,amma baki ga yanda yallaɓai Khalil yake ji da ita ba? Na tsani yarinyar nan!" Zuciyar Fauziyya ke tafasa kamar dutse mai aman wuta 

Suna tsaka da magana sai ga wasu maza sun shigo wurin daga ka gansu kaga ma'aska...baji ba gani suka shiga kamo ma'aikatan suna yi musu aski


Babu abinda ke tashi sai na shiga uku.. da sauran su...

****

Sanda muka bi ta falon,ƙara ɓoye fuskata nayi a ƙirjinshi saboda yanda yan gidan sukayi mana caaa da ido...


'' Bray me kake yi da namiji a ƙirji?" Farzan ne yayi tambayar shida bai san abinda ya faru ba..su Seraphina da suka sam abinda suka aikata suka saki dariya
'' wannan yarinyar cefa!" Ɗage gira Farzan yayi suka cigaba da dariya suna min shaƙiyanci...

Na shiga uku ni Abeedahtuwo...ya zanyi da raina ne... A parlon shi ya sauke ni Hawaye na sun kasa tsayawa....ruwa ya miƙo min cikin cup na karɓa na shanye batareda nasan nayi hakan ba Saida ya sauke min cup ɗin,yanda ƙirji na ke ciwo har ina gudu kada in kamu da ciwon zuciya 


Ƙasa nayi da kaina ina taunar leɓena...tare da damƙe rigar dake jikina a hannu na...duk da ba askin ƙwalƙwal suka yimin ba...amma banida maraba da namiji...hakan yasa na sake fashewa da kuka...jikina na tsuma...zuciyata na ƙuna...


Durƙusawa Khalil yayi gabana tare da riƙo hannu na a nashi '' Kitten!" Ya kira a tausashe daya ƙarasa zuciyata karyewa...

'' su...n..yim..as..i''maganar ta fito a rarrabe daga bakina..taya zasu min haka?

basu san irin hawaye da baƙin cikin da nayi akan wannan ba...shine rana guda ba ƙifta ido zasu kwashe min gashi...


riƙo fuskata yayi a hannunshi '' look at me...'' ɗaura hannayena nayi a nashi dake riƙe da fuskata na kasa kallon idonshi..kunya duk ta dabaibaye ni.. na tabbatar kyau'n dasu Jay suke cewa nayi..ya ɓace yanzu nafi da muni...

'' nayi...muni ..sosai na sani...baza...sake..kallon madubi ba...'' na sarƙe da kalamaina...hawaye wasu nabin wasu kamar dam ɗin daya karye

'' no you're not ugly...''


'' na...'' matso da fuskar shi ya sumbaci gefen bakina...dayasa naji wani irin zirrr! a duk ilahirin jikina hawayen suka tsaya kamar anyi ruwa an ɗauke...idona suka haɗu da nashi dake kallona with a deep gaze 

'' listen to me...keba Mummuna bace regardless of what they did to you...''

 ya faɗa da murya mai zurfi..ya haɗe goshina da nashi babu abinda zuciya ta take sai lugude,jikina ya ɗau zafi like never before

'' ke kyakkyawa ce...'' ya furta ƙasan maƙoshi... numfashin muna fita lokaci guda da sauri sauri

'' I'm not saying it to make you feel better Abeedah..I mean it!'' lumshe idona nayi kamar wacce aka yima sihr..yake shafa fuskarshi a tawa...and I wasn't even resisting it...

Ya ƙara sumbatar idona da hawaye ke gangarowa daga ciki,da tsinin hancina... zazzafan numfashin shi ke sauka a fuskata...har lokacin na kasa buɗe idona kuma na kasa hanashi...his lips were almost touching mine...for a split second na ɗauka sumbata ta zaiyi...much to my disappointment yaja baya....ya riƙo hannayena instead ya sumbata...


'' you're not ugly at all... you'll always be beautiful in my eyes...'' ya furta yana kallon cikin idona...naji daɗin kalaman shi amma...


🍁🍁: you're disappointed the kiss didn't happen

Abeedah: wai ma 😳,inji wa?

🍁🍁: meyasa kike blushing harda turo baki..You look annoyed yunno 


Abeedah: that's cuz you're annoying 🤬🤬...

  🌹 ❤️📖✨



***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin ***..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️