WHEN JOY MET SORROW!
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER TWENTY-FIVE: 25
WHEN JOY MET SORROW!
JIDDAAH BARKUM
———-
Alhaji Kabeeru ya ja numfashi, ya sake kallon fuskokin iyalinsa da ke kewaye da shi a ɗakin asibitin, sannan ya ci gaba da magana cikin muryar da ke nuna tsantsar ƙauna:
“Washegari, Fateema ta tashi kamar babu abin da ya faru a daren jiya. Tana ta walwala da fara’a tare da yaranta maza, abin da ya faranta mini rai ba kaɗan ba. Na ji kamar duk nauyin da ke zuciyata ya sauka.
Wajen la’asar, suna zaune a falon ƙasa, ita da amintacciyarta Haleema, suna hira cikin natsuwa. Haleema tana zaune a gefenta tana ɓare mata dafaffiyar gyaɗa, tana ba ta tana ci. Amma duk da hirar da suke yi, yanayin Fateema ya nuna cewa ba ta cikin hayyacinta sosai. Lokaci zuwa lokaci sai ta ɗan yatsine fuska, ta runtse idanunta na wasu daƙiƙu kafin ta sake sakin fuskarta.
Haleema, wadda ta ƙware wajen lura da ita, ta fahimci akwai wani abu da ke faruwa. Ta dubi Fateema cikin girmamawa ta ce, ‘Uwar ɗakina, lafiya dai ko?’
Fateema ta juyo, tana cije baki cikin dauriya, ta ce, ‘Wallahi, na ji kamar naƙuda ce ke shirin farawa. Tun safe fa nake jin abubuwa suna canzawa, ina ta daurewa ne kawai saboda Habibi da kuma yaran, kar hankalinsu ya tashi. Amma yanzu ina ganin haihuwar ta zo.’
Cike da damuwa, Haleema ta ce, ‘Toh, uwar ɗakina, ai bai kamata mu zauna ba. Mu fara shirin zuwa asibiti kafin wani abu ya faru, tunda kin ce tun safe kike ji. Bari na ƙarasa shirya akwatin kayan asibiti, sai mu jira abin da Ubangiji zai yi, ko?’
Fateema ta gyaɗa kai da ƙyar, sannan ta ce, ‘Toh, ba komai. Ki shiga ciki ki ƙarasa shirya kayan.’
Alhaji Kabeeru ya kalli Khalil da Abubakar da ke asibitin, ya yi murmushi mai sanyaya rai, sannan ya ci gaba:
“Tana zaune a falon bayan Haleema ta shiga ɗaki, sai ga su Adam sun shigo. Adam, wanda shi ne babbansu a cikin yaran, ya shigo tare da ƙannensa duka bayan sun dawo daga masallacin la’asar. Dukkansu suka zauna a falon kusa da mahaifiyarsu.
Khalil, wanda shi ne ɗan ƙarami a cikinsu, ya taho da gudu da niyyar hawa kan cinyarta kamar yadda ya saba. Cikin sauri, Abubakar ya dakatar da shi cikin faɗa a hankali:
‘Kai! Meye haka? Ba ka ganin halin da take ciki ba, sai ka zo ka hau cinyarta?’
Nan take Khalil ya turo baki, ya fara shirin yin kuka. Cikin tsantsar soyayyar uwa, Fateema ta miƙa hannu ta kamo hannunsa, ta ce, ‘Babana, rabu da Yaya. Me ya faru?’
Sauran yaran suka kalli juna, yayin da Khalil ya lafe a jikinta, yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Fateema tana zaune tana shafa kansa cikin rarrashi, ta ɗago kai ta dubi dukan yaranta maza bakwai da ke zaune a gabanta. Ta jefa musu wani tattausan kallo mai cike da soyayya, sannan ta ce:
‘Allah Ya yi muku albarka, Ya sa ku gama da duniya lafiya. Allah Ya kawo mini ƙaninku ko ƙanwarku lafiya cikin sauƙi. Babban burina guda ɗaya ne… Ina fatan Ubangiji Ya haɗa mini kanku gaba ɗaya, Ya cire shaiɗan a tsakaninku, ku zama tsintsiya ɗaya madaurinki ɗaya.’
Duk muryoyinsu suka haɗe wuri guda suka amsa, ‘Amin.’
A daidai lokacin ne nima na turo ƙofa na shigo gidan daga masallaci. Dukkansu suna gabana. Da muka haɗu a falon, ni da nake da masaniya game da yanayinta, nan take na lura da yadda fuskarta ke canzawa da kuma yadda numfashinta ke fita. Na fahimci cewa naƙuda ta taso da ƙarfinta na gaske. Wannan ba lokacin wasa ba ne.”
Muryar Alhaji Kabeeru ta ƙara yin ƙasa, hawaye suka zubo a fuskarsa yayin da yake kallon Inteesar.
“Ban ɓata lokaci ba. Na sallami yaran da sauri, suka fita. Sai na kwala wa Haleema kira da ƙarfi:
‘Haleema! Sauko da akwatin nan da sauri tare da hijabinta, mu wuce asibiti!’
Muna isa asibiti, sai aka tabbatar cewa naƙudar ta yi nisa tun a gida, har buɗewar mahaifa ta kai 8cm. Likitan da kansa ya ce da ba don mun ƙaraso da wuri ba, da sai dai ta haihu a gida.
Ba mu yi minti talatin da isa asibitin ba, ta haihu cikin sauƙi da amincin Allah. Ta haifi sanyin idaniyata… Inteesar.”
Alhaji Kabeeru ya ɗora idanunsa masu cike da hawaye da tsantsar ƙauna a kan fuskar Inteesar, wadda take rungume da hannunsa tana kuka mai ban tausayi.
Ɗakin asibitin ya sake ɗaukar wani nannauyan shiru, tamkar ruwa ya cinye dukan mutanen da ke ciki. Kowa yana kuka, kowa jikinsa ya yi sanyi da jin irin wannan tarihi da ya haɗa wannan iyali.
Alhaji Kabeeru ya ɗan lashe busassun leɓɓansa, ya dubi babban ɗansa Adam, ya ce cikin muryar rauni:
“Adam… ba ni ruwa na sha.”
Kafin Adam ya kai ga takawa, nan take sauran yaran mazan suka fara rige-rigen ɗaukar robar ruwan da ke kan tebur. Kowa yana son shi ne zai ba mahaifinsu ruwa, a matsayin nuna tsantsar soyayya da girmamawa ga mutumin da ya zama jigo a rayuwarsu.
Bayan Alhaji Kabeeru ya kurɓi ruwan da ƙyar, ya miƙa wa Abubakar a hankali. Ya gyara kwanciyarsa, ya kalli Mommy Haleema da ke gefensa, sannan ya ci gaba da ba da labarin cikin muryar da ke rawa:
“Farin cikin da muka shiga ni da Haleema a ranar, ba a iya misalta shi da baki. Bayan likita ya fito da albishir cewa, ‘Masha Allah, an samu kyakkyawar yarinya,’ farin cikina ya zama ba shi da masaka. Bayan tsawon shekaru ina jiran haihuwa, ina kuka a asirce, sai ga shi Allah Ya amsa addu’ata. Ban san lokacin da na zube a ƙasa na yi sujjadar godiya ga Allah ba, ina kuka na tsantsar murna, tears of pure joy.
Cikin hanzari na ɗauki waya na kira Adam. Muryata tana rawa na shaida masa haihuwar ƙanwarsu, na ce masa, ‘Adam, ku ɗauko mota ku taho asibiti yanzu haka, amma don Allah ku taho a hankali.’
Ban gama magana ba, na jiyo sautin ihun murnar sauran yaran ta cikin wayar. Kowa yana murna zai ga ƙanwarsa mace. Ba a daɗe ba kuwa, asibitin ya cika da ’yan uwa da abokan arziki da ke ta zuwa taya ni murnar samun sanyin idaniyata… Inteesar.”
Alhaji Kabeeru ya runtse idanunsa da ƙarfi, wani nannauyan numfashi ya fita daga ƙirjinsa, sannan muryarsa ta karye gaba ɗaya:
“Amma ashe farin cikinmu na ɗan lokaci ne. It was short-lived. Bayan wasu lokuta kaɗan, sai ga likitan ya sake fitowa daga ɗakin haihuwa. A wannan karon, fuskarsa ba ta da alamun farin ciki ko kaɗan. Cike take da baƙin ciki da damuwa.
Ya matso kusa da ni, ya fara faɗar kalmar da ta girgiza rayuwata gaba ɗaya, ta canza komai:
‘I’m sorry… Mun yi iya ƙoƙarinmu, amma ba mu samu nasarar ceton mahaifiyarta ba. Hawan jininta ya tashi da ƙarfi lokacin da take naƙuda. Ku yi haƙuri, Allah Ya karɓi abarsa.’”
A nan ne Alhaji Kabeeru ya yi shiru na ɗan lokaci, hawaye masu zafi na zuba daga idanuwansa ba kakkautawa. Ya kalli Inteesar cikin tsantsar tausayi, ya ce:
“A ranar da aka kawo mini farin ciki mafi girma a rayuwata… a ranar ce kuma aka karya zuciyata gaba ɗaya.”
Maganarsa ta girgiza dukan ɗakin asibitin. Mommy Haleema ta fashe da kuka mai sauti, yayin da tunanin ranar da duk abin da ya faru suka dawo mata daki-daki.
Dukan mazan gidan—su Abubakar, Adam, Faisal da sauran yayyenta—su ma suka kasa daurewa, suka fashe da kuka na tsantsar juyayi, suna tunawa da ranar da suka rasa mahaifiyarsu Hajiya Fateema, uwar da ta nuna musu soyayya tun suna ƙanana.
Ita ma Inteesar, kuka take yi da dukan ƙarfin jikinta, tana shaƙewa cikin wani irin tashin hankali da firgici. Zuciyarta ta rabe gida biyu, saboda ta gane cewa zuwanta duniya ne ya zo da rasuwar mahaifiyarta. Wannan babban sirri ya bar ta cikin tsantsar baƙin ciki da raɗaɗi.
Alhaji Kabeeru ya ƙara matse hannun Inteesar cikin nasa, idanunsa masu cike da hawaye suna kallon fuskarta da ta jike da hawaye. Ya daidaita muryarsa da ke rawa, ya ce:
“Kin zo mana da farin ciki mai girma, Princess ɗina.”
Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, yana ƙoƙarin haɗiye wani abu da ya tokare masa maƙogwaro saboda tsananin tunawa da baya. Sannan ya ci gaba da cewa:
“Amma Allah Ya karɓi mahaifiyarki a ranar da kika zo duniya.”
Jin wannan furucin ya sa hawayen Inteesar suka fara zuba da sabon ƙarfi. Tana kuka mai ban tausayi, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Ganin haka, Alhaji Kabeeru ya ƙara matse hannunta cikin nasa, ya dube ta cikin tsantsar tausayi da ƙauna, ya ce:
“Kada ki taɓa ɗaukar kanki a matsayin sanadin rasuwarta. Saboda idan akwai kyautar da Fateema ta bar mini a gidan duniya… ke ce.”
Ya juyo a hankali, ya bar idanunsa a kan fuskar Mommy Haleema da ke tsaye tana kuka, sannan ya ci gaba da cewa:
“Kuma idan akwai wata ni’ima da Allah Ya yi mini bayan rasuwarta… Haleema ce.”
Nan take Mommy Haleema ta kasa jurewa, ta fashe da wani sabon kuka mai motsa rai da kuma dumbin godiya ga Allah.
Yayyenta maza da ke tsaye a cikin ɗakin asibitin su ma suka kasa riƙe hawayensu. Kowa jikinsa ya yi sanyi gaba ɗaya, suna kallon irin girman tsarin Ubangiji a rayuwarsu.
Sai Alhaji Kabeeru ya yi wani tattausan murmushi mai cike da godiya ga Allah, ya kalli dukan iyalinsa, ya ce:
“Allah Ya ba ni mata ta gari sau biyu a rayuwata. Fateema ta ba ni ke… Haleema kuma ta raya mini ke, cikin amincewar Ubangiji.”