SHIELDS OF LOVE❤️
*KADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER TWENTY-SEVEN: 27*
*SHIELDS OF LOVE ❤️*
*JIDDAH BARKUM*
—————
Suna fitowa daga ɗakin asibitin, Inteesar ta ji dukan jikinta ya yi sanyi, ƙafafunta sun mata nauyi, da ƙyar take iya ɗaga su, ta kasa yarda cewa Daddy ya ɗauki tsawon shekaru yana ɓoye wannan gagarumin sirrin a ransa, tun tana yarinya ta san cewa Hajiya Fateema ce mahaifiyarta ta jini, sannan Mommy Haleema ce ta raine ta, amma ba ta taɓa sanin cewa yayyenta maza ba ’yan jinin Alhaji Kabeeru ba ne, haka kuma, ba ta taɓa tunanin cewa Daddy ya ɓoye wannan babban sirrin tsawon shekaru ba, a lokaci guda kuma, ta fara tuno dukkan abubuwan da suka faru a rayuwarta ta baya, ta tuna yadda yayyenta suka nuna mata tsantsar soyayya da kariya tun tana ƙarama, ta ji wani sabon girmamawa da ƙauna gare su ya mamaye zuciyarta, a yanzu ne ta ƙara fahimtar irin girman soyayyar da suke mata, da kuma yadda suka ɗauke ta a matsayin ƙanwarsu ta jini, ba tare da la’akari da gaskiyar da ta ɓoye a tsakaninsu ba, ta juyo da sauri ta kalli Mommy Haleema, ta kasa daurewa, ta faɗa kan ƙirjinta ta rungume ta tana kuka mai ban tausayi, “Mommy… nagode, wallahi, ban san yadda zan rayu ba da babu ke,” Mommy Haleema ta sa hannunta ta ƙara ƙanƙame ta, tana share mata hawaye a hankali, “Ke ɗiyata ce tun ranar da na karɓe ki daga hannun Daddy, kuma za ki kasance ɗiyata har na koma ga Allah,” kalaman Mommy Haleema suka ƙara karya zuciyar Inteesar, ta ƙara manne wa jikinta, tana kuka kamar ƙaramin yaron da ya tsorata da yiwuwar rasa mafakarsa, a gare ta, Mommy ba kawai macen da ta raine ta ba ce, ita ce mahaifiyarta a kowace ma’ana ta kalmar, a gefe guda kuwa… Abubakar na zaune kansa a sunkuye, tunani kala-kala suna masa yawo a zuciya, Adam ma ya jingina da bango, yana kallon ƙasa cikin shiru, Salim kuwa ya haɗe hannayensa wuri guda, idanunsa a lumshe, kamar yana ƙoƙarin sarrafa motsin zuciyarsa, Umar ya jingina da kujera, yana jan tasbihi a hankali, bakinsa yana motsi da addu’o’i marasa sauti, sai Khalil… shi kaɗai ne yake yawan ɗaga kai lokaci zuwa lokaci yana kallon Inteesar, duk lokacin da ya ga sabbin hawaye sun sake zubowa daga idanunta, zuciyarsa sai ta yi masa ciwo, Princess ɗinsu ce, tun tana jaririya, tun lokacin da yake ɗaukar ta yana zagayawa da ita a kafaɗarsa, tun lokacin da take bin sa tana cewa, “Yaya Khalil, carry me,” yanzu kuma… ga ta nan, babbar yarinya, amma har yanzu, idan ta yi kuka, zuciyarsa tana jin kamar lokacin yarintarsu ne, a wurinsa, girman Inteesar bai taɓa rage matsayinta na ƙaramar ƙanwarsu mai buƙatar kulawa da kariya ba, Abubakar ya matso kusa, ya kalli Inteesar cikin sanyin murya ya ce, “Intee, Daddy ya faɗi gaskiya, ba mu taɓa kallon ki a matsayin ’yar rabin jini ba, we will protect you no matter what. (Za mu kare ki ko da me zai faru),” Adam ma ya gyada kai, ya dafe kafaɗarta ya ce, “Ke ƙanwarmu ce wacce muke tsananin ƙauna, and we are ready to go to any lengths for you. (Kuma a shirye muke mu yi duk abin da ya dace domin kare ki),” Khalil ɗin da ke tsaye ya ɗan matso kusa yana kallon fuskarta, ya yi narai-narai da ido cikin sigar tsokana, don ya sa ta ɗan manta da baƙin cikin da take ciki, sannan ya ce, “Princess ɗinmu ce, our little babygirl, yanzu dai dry those tears. (Share hawayen nan.) Ko na miki video kina kuka na ajiye, har jikokinki sai sun gani,” kalaman Khalil suka sanya Inteesar yin wani ɗan gajeren murmushi mai haɗe da kuka, murmushin ya kasance ƙarami, amma ya isa ya sa sauran ’yan uwan nata su ɗan ji sauƙin nauyin da ke kan zukatansu, kowa a wajen ya ɗan share hawayensa na juyayi, duk da cewa gaskiyar da suka ji ta girgiza su, soyayyar da ke tsakaninsu ta kasance tamkar garkuwa da ba za ta bari wannan sirri ya raba su ba, a daidai wannan lokacin, sai wayarta ta fara ruri a hannunta, ta kalli wayar, sauran ’yan uwan ma duka suka kura mata ido, sunan Aliyu ne ya bayyana a kan allon wayar, ta ɗan haɗiye yawu, tana kallonsu ta ƙasan ido, ganin sun ɗauke hankalinsu daga kanta, sai ta ɗaga kiran cikin sanyin murya, nan take Aliyu ya gane cewa kuka take yi saboda yadda muryarta ta canza, “Intee? Me ya faru? Kin yi kuka ko?” Ya ƙara tausasa muryarsa cikin kulawa, “How is Daddy now?” Ta daidaita numfashinta, sannan ta gaya masa cewa jikin Daddy ya ɗan yi sauƙi, Aliyu ya sauke ajiyar zuciya, “Alhamdulillah, Allah Ya ƙara ba shi lafiya,” daga yanayin sautin da ke tashi a bayanta, Aliyu ya lura cewa tana cikin asibiti ne, sai ya tambaya, “Wane hospital ne?” Inteesar ta ɗan goge fuskarta ta ce, “Me za ka yi da sunan hospital ɗin?” Aliyu ya amsa mata kai tsaye cikin muryar dattako, “Ina son zuwa na ga Daddy, duk da ban taɓa haɗuwa da shi ba… ina so na zo na duba jikinsa, don Allah, kada ki ce a’a,” Inteesar ta yi mamaki matuƙa a ranta, saboda ba ta taɓa tsammanin cewa Aliyu zai damu da lamarin iyalanta har haka ba, wani irin daɗi ya gauraya da mamakinta, duk da cewa ba ta san yadda za ta fassara wannan kulawar tasa ba, cikin sanyin jiki ta gaya masa sunan asibitin, Aliyu ya ce mata, “In Sha Allah zan zo, ki kula da kanki, kuma ki daina kuka, Daddy zai samu lafiya,” Inteesar ta yi shiru na ɗan lokaci, tana jin yadda kalamansa suka shigo zuciyarta cikin natsuwa, ko da yake bai yi mata doguwar nasiha ba, yadda ya nuna damuwarsa ya isa ya sa ta ji cewa akwai wanda yake tunanin halin da take ciki, bayan kamar minti arba’in (40 minutes), sai wayar Inteesar ta sake ruri a hannunta, ta ɗaga kiran da sanyin murya, with a soft, tired voice, “Hello,” daga can ɓangaren, Aliyu ya amsa cikin nutsuwa da daddadan sauti, “Intee, na ƙaraso, ina waje a yanzu haka, zan iya shigowa ciki babu komai ko?” Inteesar ta juyo a hankali ta kalli yayyenta maza da Mommy Haleema da ke zaune a corridor ɗin, ta ɗauke idanunta daga kansu, sannan ta gyada kai kamar yana ganinta ta cikin wayar, ta ce, “Ehh, ka shigo,” “Okay,” ya amsa mata a taƙaice kafin ya datse wayar, Inteesar ta kafe ƙofar da za ta sada mutum da ainihin corridor ɗin asibitin da idanuwanta, tana jiran ganinsa, zuciyarta ta ɗan fara bugawa da sauri, ba don wani dalili da ta fahimta ba, sai dai kawai saboda tunanin ganin Aliyu a wannan yanayin, kafin ta ankara, ta fara hango shi yana takowa cikin takunsa na tsantsar nutsuwa da kwarjini, sanye yake cikin farar shadda mai matuƙar kyau da tsada, wacce ta ƙara fito da ainihin haibarsa, kamalarsa da cikar siffarsa ta ɗan Fulani—his undeniable Fulani aura, Aliyu fari ne tass, fatar jikinsa mai haske ta ƙara fito da kyawun fuskarsa, dogo ne sosai na ƙarshe, a true giant, domin idan Inteesar ta tsaya a gabansa, ko tsakiyar ƙirjinsa ba ta kaiwa saboda tsayinsa, ga shi kuma yana da ɗan kauri madaidaici na jiki, wanda ya ƙara nuna cikarsa da kwarjinin da yake da shi, idanuwansa farare ne tass, masu ɗauke da baƙar ƙwayar ido da ke cike da kwarjini, yana da dogon hanci madaidaici wanda ya zauna daidai da kyakkyawar fuskarsa, kansa babu hula a lokacin, hakan ya fallasa ainihin gashin kansa kwantacce, lafiyayye irin na Fulani, duk da cewa ba wai ya tara suma mai yawa ba ne, akwai ɗan gashin da ke kansa wanda ya ƙara masa kyau da kamala, a ƙiyasin Inteesar, Aliyu zai iya takawa zuwa shekaru arba’in da bakwai ko arba’in da takwas a duniya, domin a zahirin yadda yake ganuwa, ta san sarai cewa ba yaro ba ne, he is a mature, distinguished man, daga yadda yake da nutsuwa da cikar kamala, babu shakka Aliyu ba saurayi ba ne, yana da haibar dattako da kwarjinin manyan maza, irin mutanen da ba sa buƙatar ɗaga murya domin a lura da kasancewarsu, dukan wannan ƙurullar kallon, Inteesar ta yi shi ne a cikin abin da bai fi daƙiƙa biyu ba, kafin ta ji takunsa ya tsaya daidai a gabanta, yana mata wani tattausan murmushi mai sanyaya zuciya, “Intee…” Ta ɗago ta sake kallon fuskarsa da sauri, kafin ta sunkuyar da kanta ƙasa cikin jin kunya da girmamawa, ta ce, “Sannu da zuwa, ina yini?” Aliyu ya ɗan raba idanuwansa a kan fuskarta, ya kalli corridor ɗin asibitin da kyau kafin ya amsa mata cikin sanyin murya, “Lafiya alhamdulillah, ya mai jikin yanzu?” “Alhamdulillah, da sauƙi, yana ciki,” Inteesar ta amsa, muryarta tana rawa, “Inteesar…” Aliyu ya kira sunanta da wani daddadan sauti mai cike da sanyaya rai, ta ɗago idanuwanta da suka sha kuka suka koɗe gaba ɗaya, fuskarta ta yi jawur saboda tsananin baƙin ciki da kukan da ta sha na fitar rai, Aliyu ya kalli fuskarta, nan take yanayin nasa ya canza, fuskar ta nuna tsantsar damuwa da tausayawa, ya sake ƙasa da muryarsa ya ce, “Haka kika yi kuka? Mun yi magana fa ba za ki yi kuka ba, za ki yi wa Daddy addu’a kawai… and you broke the promise, why?” Inteesar ta ji nauyin kalamansa da yadda ya furta su cikin kulawa, ta kasa ce masa uffan, sai ta sauke idanuwanta ƙasa tana wasa da gefen mayafin abayarta cikin rashin sanin abin da za ta ce, ta san cewa ya damu da ita, amma ba ta san yadda za ta bayyana masa cewa abin da ta ji a yau ya wuce abin da kalmomi za su iya bayyanawa ba, sai kuma a hankali ta daidaita muryarta ta ce, “Muje ka gaisa da Mommy da yayyena, gansu can a gaba,” ta faɗa tana ɗan kallonsa ta gefen ido, Aliyu ya juyar da kansa ya kalli inda ta nuna masa, ya ga mutanen gidan duka a zaune cirko-cirko, fuskokinsu cike da alamun jimami, ya dawo da kallonsa kanta, ya ɗan matsa gefe guda cikin tsantsar ladabi da girmamawa ya ce, “Ladies first, bismillah,” ta yi gaba tana takowa a hankali, shi kuma yana binta a baya cikin natsuwa, inda dukan idanuwan yayyenta maza da Mommy Haleema suka dawo kansu, Aliyu ya ƙaraso gaban inda suke zaune cikin takunsa na takamaiman kwarjini da cikar zati, ko da ya isa daidai gaban Mommy Haleema, bai tsaya a tsaye kawai ba, ya risina sosai har ya kai ga tsugunawa, ya sadda kansa ƙasa alamun tsantsar ladabi da girmamawa, sannan ya ce cikin muryar ƙasa-ƙasa mai natsuwa, “Mommy, ina yini? Fatan kun tashi lafiya, ya jikin Daddy? Allah Ya ƙara masa lafiya, Ya sanya wannan rashin lafiyar kaffara ne a gare shi,” Mommy Haleema ta ɗago fuskarta da ke cike da damuwa da alamun gajiyawa, ta ɗan kalle shi kaɗan, kafin ta daidaita muryarta da ke rawa ta amsa cikin karamci, “Lafiya alhamdulillah, jiki kam da sauƙi, mun gode wa Allah, muna godiya ƙwarai da zuwa, Allah Ya saka da alheri,” Aliyu ya sunkuyar da kansa cikin girmamawa, “Amin, Mommy, Allah Ya ƙara ba shi lafiya,” bayan ya gaishe da Mommy, Aliyu ya miƙe tsaye ya juyo ya kalli su Yaya Abubakar da Yaya Adam da ke zaune a kujerun wajen, kowannensu fuskarsa babu annuri saboda juyayin rashin lafiyar Daddy, ya matso kusa da su, ya miƙa musu hannu yana ɗan risinawa domin su gaisa cikin salonsa na girmamawa, su Yaya Abubakar suka sa hannu suka gaisa da shi cikin sanyin jiki, amma a lokaci guda, idanuwansu duka gaba ɗaya suna kansa, suna auna shi tun daga sama har ƙasa cikin mamaki, suna musabaha da shi, amma a can ƙasan zukatansu, kowa cike yake da tarin tambayoyin da suka rasa amsa, wannan kuma fa? Daga ina yake? Kuma a ina Inteesar ta samo babban mutum haka? Inteesar ta lura da yadda yayyenta suka zuba wa Aliyu ido suna binciken kowace gaba ta jikinsa, hakan ya sa ta fitar da wani nannauyan numfashi, ta sunkuyar da kanta ƙasa cikin tsantsar jin nauyi da fargaba, ta san cewa ba za ta iya hana su mamakin ganin Aliyu ba, a ganinsu, wannan mutumin da ya zo da irin wannan kwarjini da ladabi ba wanda suka saba gani tare da ƙanwarsu ba ne, Aliyu kuwa, a matsayinsa na gogaggen namiji, bai nuna ya lura da yanayin kallon da suke masa ba, ya sake juyawa ga Umar cikin nuna halin dattako, ya ce, “Ya ya jikin Daddy?” Bai jira amsar Umar da ke binsa da kallo ba, ya ɗora da cewa, “Allah Ya sa kaffara ne, Ubangiji Ya tashi ƙafadunsa, Ya ba shi lafiya cikakkiya.”