THE MAN WHO CAME ❤️
*KADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER TWENTY-EIGHT: 28*
*THE MAN WHO CAME ❤️*
*JIDDAH BARKUM*
—————
Yaya Umar ya amsa da, “Aamiin,” yana bin Aliyu da wani kallon ƙasan ido wanda shi kaɗai ne ya san ma’anarsa, corridor ɗin asibitin ya sake komawa cikin wani irin yanayi na shiru mai nauyi da ratsa zuciya, shiru ne irin wanda ba wai don babu mutane a wajen ba ne, a’a, shiru ne na mutanen da kowannensu zuciyarsa ta cika makil da abubuwan da ba zai iya furtawa da baki ba saboda nauyinsu, Mommy Haleema tana zaune cikin sanyin jiki da sanyin gwiwa, hannayenta biyu a haɗe wuri guda, yayin da tasbihi yake ta yawo a yatsunta cikin tsantsar nutsuwa da roƙon Allah, Yaya Abubakar ya jingina bayansa da kujera, idanunsa a lumshe tamkar mai barci, amma a zahiri tunani ne ke ta faman damunsa, Adam kuwa ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa, Umar na ta jan nasa tasbihin a hankali, yayin da Faisal da Salim ma suka yi shiru suna kallon ƙasa, sai Khalil… shi ne yake yawan satar kallon Aliyu ta gefen ido lokaci zuwa lokaci, shi kansa Khalil ɗin bai san takamaiman dalilin da ya sa yake ta faman kallon mutumin ba, amma akwai wani ɓoyayyen abu da ke tattare da Aliyu, wani irin natsuwa na daban, wani irin kwarjini na tsatson gado, da kuma cikar haibar dattako, duk da kasancewar ba su taɓa ganinsa ba a rayuwarsu, sai Khalil ya ji a ransa kamar mutumin ba baƙo ba ne a gare su, Aliyu kuwa yana zaune a gefe cikin kiyaye mutuncinsa da tsantsar nutsuwa, ba ya nuna kansa, sai dai lokaci zuwa lokaci, idanunsa masu cike da damuwar ganin halin da Inteesar ke ciki sukan sauka a kan fuskarta, kuma duk lokacin da ya ga kumburin idanunta saboda tsananin kukan da ta sha, sai ya ji zuciyarsa ta matse da wani irin zafi, ba ƙaramin ciwo yake ji a ransa ba, domin tun da ya san Inteesar, bai taɓa ganinta cikin irin wannan raunin halin ba, Inteesar, kawarsa mai yawan dariya da walwala, mai saurin yin fushi, kuma mai saurin tsokana… yau kuwa, fuskarta babu ko digon walwala, idanuwanta sun yi jawur, fuskarta ta nuna tsananin damuwa, duk da ƙoƙarin da take yi na ɓoye baƙin cikinta, Aliyu ya san cewa zuciyarta na zubar da hawaye fiye da ainihin idanunta, cikin wannan yanayin ne sai ga ƙofar ɗakin da Daddy ke kwance ta buɗe a hankali, wata nurse ta fito riƙe da wasu takardu, nan take dukan idanuwan da ke corridor ɗin suka dawo kanta cikin fargaba, Mommy Haleema ta miƙe tsaye da sauri, muryarta na rawa ta ce, “Lafiya?” Nurse ɗin ta yi tattausan murmushi domin kwantar musu da hankali, ta ce, “Alhamdulillah, patient ɗin ya farka yanzu,” nan take wani nannauyan numfashi na sauƙi ya fita daga ƙirjin kowa a wajen, “Alhamdulillah!” Abubakar ya furta cikin tsantsar jin daɗi, Adam ya lumshe idanunsa yana godiya, har Mommy Haleema ta ɗaga hannayenta biyu sama ta ce, “Alhamdulillah, Ya Rabbi!” Inteesar kuwa ta ji zuciyarta ta yi wani irin sanyi, ta runtse idanunta da sauri, inda sabbin hawaye na godiya suka taru a cikinsu, Alhamdulillah, Daddy ya farka! Ta yi wannan addu’ar a ranta, tana jin wani irin sauƙi ya mamaye zuciyarta, Mommy Haleema za ta taka ƙafar shiga cikin ɗakin kenan, sai Aliyu ya miƙe tsaye, tsayinsa na asalin Bafillatani ya bayyana sosai, a hankali, cikin tsantsar ladabi, ya kira sunanta, “Mommy,” ta juyo da sauri tana kallonsa, “Na’am?” Ta amsa tana ba shi dukkan hankalinta domin jin abin da zai ce, Aliyu ya ɗan sadda kansa ƙasa, ya yi shiru na daƙiƙa biyu kamar wanda yake auna ko ya dace ya faɗi abin da ke ransa, sannan ya ci gaba cikin muryarsa mai cike da kwarjini, “Idan ba matsala… zan so na shiga na duba jikin Daddy,” wajen ya yi tsit tamkar an dasa musu ƙafafu a ƙasa, Khalil ya ɗaga gira yana murmushi, Faisal ya ɗan dubi Adam, Adam ya dubi Abubakar, Umar ma idanunsa suka dawo kan Aliyu, har Inteesar kanta ta ɗago da sauri tana kallonsa, wani irin mamaki na daban ne ya bayyana a cikin ƙwayar idanunta, domin ko ita kanta ba ta yi tsammanin cewa Aliyu zai nemi izinin shiga ya duba Daddy ba, a tunaninta, idan kowa ya shiga, shi ma zai bi bayansu ne kawai, but Aliyu was different, Aliyu yana da nasa tsari, komai nasa a aune yake, kuma yana yin abubuwa cikin tunani da girmamawa, bai ɗauki kasancewarsa bako a wurin a matsayin damar yin abin da ya ga dama ba, Aliyu kuwa yana tsaye cikin daddadan nutsuwarsa, babu alamun tashin hankali ko fargaba a fuskarsa, babu nuna isa, sai tsantsar girmamawa kawai da ta shimfiɗe a tare da shi, Mommy Haleema ta kalli Abubakar domin jin ta bakinsa, Abubakar ya dubi Adam, Adam ya ɗan gyada kai a hankali alamun goyon baya, sai Abubakar ya dawo da kallonsa kan Aliyu ya ce cikin nutsuwa, “Babu matsala, ka shiga,” Aliyu ya ɗan risina, “Na gode,” Mommy Haleema da Inteesar suka shiga gaba, Aliyu kuma ya bi bayansu a hankali, yayin da suka isa daidai bakin ƙofar ɗakin, sai Aliyu ya tsaya, ya ɗan ja numfashi, sannan ya cire takalmansa ya ajiye su a gefe cikin nutsuwa, wannan matakin ya sa Inteesar juyowa ta kalle shi cikin mamaki, domin kowannensu ya shiga ne da takalma a ƙafafunsa, amma Aliyu ya ga dacewar cire nasa kafin ya shiga ɗakin da mahaifinta ke kwance, wannan ƙaramin abu ne a idon wasu, amma a wajen Inteesar, ya kasance wani babban alamar girmamawa, bai san Daddy ba, bai taɓa haɗuwa da shi ba a baya, amma duk da haka yana kula da shi kamar wanda yake girmama shi tun da daɗewa, Aliyu ya lura da yadda take kallonsa, sai ya yi mata wani tattausan murmushi mai sanyaya rai, ya ce mata a hankali cikin rada, “Marar lafiya yana buƙatar tsantsar nutsuwa,” Inteesar ta sauke idanuwanta ƙasa da sauri saboda wani irin nauyin kunya da ta ji, kuma ba tare da ta sani ba, wani sabon girmamawa ya ƙara cika zuciyarta game da shi.
A hankali suka tura ƙofar suka shiga ciki, Alhaji Kabeeru yana kwance a kan gadon, fuskarsa cike da alamun gajiyar rashin lafiya, sai dai idanunsa biyu a buɗe suke, da ganin Inteesar, wani tattausan murmushi ya bayyana a leɓɓansa, “Princess ɗina,” Inteesar ta ƙarasa kusa da gadon da sauri, ta kama hannunsa tana jin wani irin sanyi a ranta, “Daddy,” muryarta ta fito a hankali, cike da soyayya da damuwar da har yanzu ba ta gama fita daga zuciyarta ba, Mommy Haleema ta matso ta gyara masa pillow ɗin da ke bayansa, sai a lokacin Alhaji Kabeeru ya lura da cewa akwai wani mutum da ke tsaye a bayansu, ya ɗan lumshe idanunsa, ya sake buɗewa yana kallon Aliyu, Aliyu kuwa bai tsaya yana nuna wa tsohon kansa a tsaye ba, nan take ya ƙarasa gaba, ya durƙusa kusa da gadon, ya risina cikin tsantsar ladabi har ya sadda kansa ƙasa, sannan ya ce cikin muryar ƙasa-ƙasa, “Assalamu alaikum, Daddy,” Alhaji Kabeeru ya amsa cikin sanyin murya da ke fita da ƙyar, “Wa alaikumus salam,” Aliyu ya ɗago kansa kaɗan, amma idanunsa na ƙasa, ya ce, “Sunana Aliyu, na zo ne domin na duba jikinka, Allah Ya ba ka lafiya, kuma in Sha Allah za ka tashi lafiya, Allah Ya sanya wannan rashin lafiyar ta zama kaffara a gare ka,” Inteesar da Mommy Haleema suka amsa a tare, “Aamiin, Ya Allah,” Alhaji Kabeeru ya zuba masa idanuwansa, yana nazarin tsantsar nutsuwar mutumin, ladabinsa, da kuma yadda yake fitar da kowace kalma cikin girmamawa ta musamman, sai wani tattausan murmushi na gamsuwa ya bayyana a fuskarsa, ya ce cikin muryar ƙasa-ƙasa, “Na gode, ɗana, Allah Ya saka da alheri,” Aliyu ya ɗan ƙara sunkuyar da kansa, “Ameen, Daddy, Allah Ya tashi ƙafadunka,” a hankali Alhaji Kabeeru ya ɗaga idanunsa daga kan Aliyu, sai suka sauka a kan Inteesar wacce ke tsaye a gefen gadon tana kallonsu cikin sanyin jiki, sannan idanunsa suka sake dawowa kan Aliyu, kafin su koma kan Inteesar a karo na biyu, sai Alhaji Kabeeru ya sake yin wani tattausan murmushi a hankali, murmushin da babu wanda ya fahimci ainihin ma’anarsa ko ɓoyayyen saƙonsa a cikin ɗakin, sai shi kaɗai a cikin ransa, a hankali ya ɗaga hannunsa, alamar gamsuwa, sannan ya ce, “Allah Ya saka da alheri, ɗana,” Aliyu ya sake risinawa sosai cikin girmamawa, muryarsa ƙasa-ƙasa, “Ameen, Daddy, Allah Ya tashi ƙafadunka lafiya,” Mommy Haleema ma, wacce ke tsaye tana kallon nutsuwa da ladabin Aliyu, ta dube shi cikin karamci da sanyin rai ta ce, “Mun gode ƙwarai, Ubangiji Ya bar zumunci,” Aliyu ya ɗan sadda kansa ƙasa, cike da kamala ya amsa, “Babu komai, Mommy, Allah Ya ba shi lafiya, Ya sanya kaffara ne a gare shi,” bayan ya gama faɗin haka, ya ɗan ja da baya a hankali cikin nutsuwa ba tare da ya juya musu baya ba, “To, Mommy, zan wuce,” ya faɗa cikin tsantsar ladabi, Mommy Haleema ta gyada kai tana masa fatan alheri, “Allah Ya kai ka lafiya, Ya tsare hanya,” Aliyu ya sake yi wa Alhaji Kabeeru sallama, kafin ya juya cikin takunsa na natsuwa ya fita daga ƙofar ɗakin, Inteesar ma ta ɗan kalli Mommy, sannan ta bi bayansa a hankali, ko da suka fito ainihin corridor ɗin asibitin, su Yaya Abubakar da sauran yayyenta maza duk suna tsaye, Aliyu ya matso daidai gabansu, ba tare da wani fariya ko jallabin girman kai ba, ya miƙa hannunsa na dama ga Yaya Abubakar cikin tsantsar girmamawa, Abubakar ya sa hannu suka yi musabaha mai ƙarfi, ya ce cikin nutsuwa, “Mun gode sosai,” Aliyu ya ɗan yi tattausan murmushi da ya ƙara fito da cikar haibarsa, “Ba komai, Allah Ya ba Daddy lafiya,” daga nan ya juya wajen Yaya Adam, shi ma suka yi musabaha cikin mutunci, sannan ya miƙa wa Faisal, sai Salim, sai Umar, har ya zo kan Khalil da ke tsaye yana jiran nasa layin, Khalil ya yi wani ɗan gajeren murmushi, yana ƙara kallon tsayinsa da cikakkiyar haibarsa a kusa, ya ce, “Mun gode sosai,” Aliyu ya ɗan girgiza kansa a hankali, “Please, kar ku ce haka, dukkanmu addu’a za mu ci gaba da yi wa Daddy,” Khalil ya gyada kai, “In Sha Allah,” bayan ya gama gaisawa da su duka, Aliyu ya sake juyowa ya yi musu sallama cikin mutunci, “Assalamu alaikum,” “Wa alaikumus salam,” suka amsa masa gaba ɗaya cikin haɗin baki, Inteesar kuwa tana tsaye a gefe guda tana kallon kowane motsi na Aliyu, wani irin sabon natsuwa da kwarjinin mutumin ne yake sake burge ta, a fili da ɓoye, babu nuna isa, babu son a yaba masa, babu surutun banza, komai nasa a aune yake, cikin tsari da lissafi, da ta ga ya juya zai tafi, sai ta tsinci kanta da yin saurin bin bayansa, “Bari na raka ka,” ta faɗa cikin muryar rada, Aliyu ya ɗan juyo da kansa ya kalleta, sai ya yi mata wani kyakkyawan murmushi, “Bismillah,” a tare suka fara tafiya cikin dogon corridor ɗin asibitin, Yaya Umar ya bisu da kallo, sannan ya sauke idanunsa ƙasa, wani irin shiru mai daɗi ya mamaye tsakaninsu, sai kawai sautin takun takalmansu da ke fita jifa-jifa, da kuma sanyin iska mai ratsa jiki da ke fitowa daga na’urar AC ta asibitin, ba wanda ya fara magana da farko, Inteesar kuwa tana tafiya a gefensa, tana ƙoƙarin daidaita tunaninta, duk da cewa zuciyarta na cike da damuwa game da Daddy, kasancewar Aliyu a kusa da ita ya ba ta wani irin kwanciyar hankali da ba ta iya bayyana ma’anarsa, suka sauko daga matakala har ƙasa, daga nan suka nufi babban parking lot na asibitin, motarsa tana can a fake a gefe guda, ƙarƙashin inuwar wata doguwar bishiya, baƙar mota ce mai matuƙar kyau, tsada, kuma mai tsarin gaske, da suka isa daidai jikin motar, Aliyu ya tsaya a hankali, sai ya juyo gaba ɗaya ya fuskance ta, a karon farko tun zuwansa asibitin, ya ba ta cikakken hankalinsa, ya tsaya yana kallon fuskarta, ya lura da yadda idanunta suka kumbura saboda kuka, ya lura da yadda fuskarta ta nuna gajiya a cikin ’yan awoyin nan, da kuma yadda daddadan muryarta ta rasa kuzarin da ya saba ji a cikinta, “Inteesar…” Ya kira sunanta cikin wani tattausan sauti mai ratsa jiki, ta ɗago idanunta a hankali, “Hmmm?” “Ki kula da kanki,” ya faɗa cikin sanyin murya da ke cike da kulawa, “Kada ki sake yawan kuka haka… kin ji?” Ta yi shiru, sai ya ci gaba da magana cikin muryar lallashi, “Na san kina son Daddy, kuma na san kina jin tsoron halin da ake ciki, amma ba kukanki Daddy yake buƙata ba a yanzu, addu’arki yake buƙata, In Sha Allah zai samu lafiya, kuma komai zai wuce,” Inteesar ta ji wani irin sanyi na daban ya ratsa dukkan ƙofofin zuciyarta, duk da cewa gagarumar damuwar da take ciki ba ƙarama ba ce, kalaman Aliyu suna da wata irin asirtacciyar nutsuwa da ke sanyaya zuciya a take, ta sauke wani nannauyan numfashi a hankali, sannan ta yi wani gajeren murmushi a karon farko tun bayan fitowarsu daga ɗakin Daddy, “Na gode,” Aliyu ya ɗan ɗaga girarsa guda cikin sigar tambaya, “Saboda me?” Inteesar ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa cikin jin kunya, “Saboda ka zo… Na gode da ka zo ka duba Daddy, ban yi tsammanin za ka damu da lamarinmu har haka ba, gaskiya, wallahi, na yi farin ciki sosai da zuwanka,” Aliyu ya zuba mata kyawawan idanuwansa, yana kallon yadda take fitar da kowace kalma da gaskiya gaba ɗaya daga cikin zuciyarta, sai ya yi wani tattausan murmushi mai cike da natsuwa, “Me ya sa ba zan zo ba?” ya tambaya cikin muryar ƙasa-ƙasa, “Duk da ban taɓa haɗuwa da Daddy ba a baya… na san irin gagarumin matsayinsa a zuciyarki, saboda haka, duk abin da ya dame ki…” Ya ɗan dakata na daƙiƙa guda, yana kallonta kai tsaye, “…ba zai taɓa zama ƙaramin abu a wurina ba,” Inteesar ta ji zuciyarta ta yi wani irin mugun bugawa! Wani sabon jiri na daban ya ziyarce ta, sai ta sauke idanuwanta ƙasa da sauri cikin tsantsar jin kunya da fargabar kalamansa, a daidai wannan daddadan lokacin ne wayar Aliyu da ke cikin aljihun shaddarsa ta fara ringing cikin ƙara mai ƙarfi, ya zaro wayar daga aljihunsa cikin nutsuwa, da ya kalli screen ɗin wayar, sai ya ɗago ya kalli Inteesar, ita ma a daidai lokacin ta ɗago idanunta suka sauka cikin nasa, sai kuma a hankali ta sake mayar da su ƙasa tana wasa da yatsunta, Aliyu ya mayar da idanunsa kan wayar hannunsa, ya ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu yana kallon sunan da ke bayyana a kan screen ɗin, sannan ya ɗaga kiran ya kai wayar a kunne, “Assalamu alaikum,” daga can ɓangaren kiran, wata daddadan muryar mace mai cike da tsantsar sabo, shagwaɓa da kusanci ta daki kunnen Aliyu, har sautin muryarta yana fitowa ta cikin speaker yadda Inteesar za ta iya jiyo wasu kalamanta, “Wa alaikumus salam, sweetheart, kana ina ne wai? Wallahi, tun ɗazu nake zaune ina jiran ka fa, ka manta ne cewa ka ce za ka zo mu tafi unguwa tare yau?” Ta ɗan yi shiru, kafin ta ƙara da muryarta mai zaƙi cikin alamun shagwaɓa, “Muna nan muna jiranka, Ayaan har ya yi barci fa,” Aliyu ya ɗago ya kalli Inteesar, a daidai lokacin ne ita ma ta ɗago idanunta tana kallonsa, sai dai… nan take murmushin da ke shimfiɗe a fuskarta ya dusashe a hankali, tamkar girgije ya rufe rana, idanuwanta suka sauka gaba ɗaya a kan ƙasa, ta daskare a wajen kamar dutse, wani irin abu mai zafi da kaifi ya soki tsakiyar zuciyarta, har ta ji kamar numfashinta zai ɗauke, ta kasa ɗaga kanta, ta kasa kallon Aliyu, ta kasa ma fahimtar dalilin da ya sa kalaman matar suka yi mata wannan tasirin, sweetheart? Wace ce wannan matar a gare shi? Sai wata tambaya mai nauyi ta fara yawo a cikin zuciyarta, tana ƙara mata tashin hankali da baƙin ciki da ba ta fahimci inda suka fito ba, dama… dama yana da mata kenan???