LOKACI CHAPTER 24
by @fulani32
***
⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI
YOTA
Team Yota's Amazing Pen's.
FULANI
***
PAGE2️⃣4️⃣
Zay'd bayan ya bar ƙofar gidan, kai tsaye gida ya nufa, da sam ba zai iya komawa restaurant ba, tuƙi yake a hankali, kamar wanda baya son zuwa inda zai je, abin da ta yi masa ya taɓa sa sosai, yana zuwa gida kai tsaye part ɗin Ammie ya wuce.
Ta na zaune, Princess a kusa da ita, duk a tare suka ɗago suna kallonsa, da gudu ta taso ta rungumesa, kanta ya shafa ya riƙe hannunta suka ƙarasa wajen Ammie.
"Yaushe ka dawo Babban mutum?" Ta tambayesa fuskarta cike da jin daɗin ganinsa.
"Ɗazun Ammie"
Ido ta zuba masa na ƴan daƙiƙu, tasan wanene shi, gane halin da yake ciki baya mata wahala, daga shigowarsa ta karanci damuwa a tare da shi.
"Lafiya kuwa?"
"Alhamdullah Ammie me kika gani?"
Kai tsaye ta ce "ban yarda ba"
Murmushi ya yi "babu komai fa Ammie"
Shiru ta yi, hannunta ta ɗora a kansa " nasan akwai damuwa Zay'd, kawai dai ba zaka faɗa min ba, Allah yayi maka maganin koma menene"
Ƙasa ya yi da kansa.
"Princess kawo masa ruwa da abinci"
Badan zai ci ba yayi shiru, sai dan kar ya ɗaga mata hankali.
Kusa da shi ta koma ta zauna bayan Teema ta bar wajen "ko a wajen aiki ne da matsala? Ko kuma dai maganar restaurant ɗince har yanzu?"
"Dagaske fa Ammie babu komai, kawai gajiya ce, na gaji shiyasa, wanka ma nake son naje nayi"
Kallonsa tayi na ɗan lokaci, ta san ba gaskiya yake faɗa mata ba, ita kuma ba zata matsa masa ba, hannunta ta ɗora a kansa "Allah ya shiga lamarinka Muhammad"
Sunkuyar da kansa ya yi ya sumbaci hannunta, sannan ya miƙe "zan je part ɗina Ammie"
Sallama yayi mata ya wuce, da ya shiga rigar jikinsa ta sama ya cire ya ajiye akan kujera, sannan ya zauna akan cussion, hannunsa ɗaya ya cusa cikin gashinsa yanata faman hargitsawa, idonsa a lumshe, fuskarta ce ta bayyanar masa.
"Me na yi miki da zafi haka Besty?"
Ya tambayi kansa, ba haka ya tsara haɗuwarsu ba, ya yi tunanin za ta nuna farin cikin ganinsa, sannan ta faɗa masa yanda tayi kewarsa, amman sai ya ga saɓanin haka, bai taɓa tunanin zata nuna masa abin da ta yi masa a yanzu ba, lumshe idonsa yayi.
"Falmata.." ya kira sunan a hankali.
Jin wayarsa nata ringine ne, ya sa shi ya buɗe idonsa, wayar ya kalla, manager ya ga tarin misscalled ɗinsa, sai dai ba tashi yake ba, kamar ba zai ɗaga ba, ya ɗaga ba tare da ya yi magana ba.
"Barka da yamma Sir"
"Uhm" kawai ya ce masa.
"Daman akan ordern ne, an kai musu an ƙarasa tun ɗazu, sai dai suna ta tambayarka, sannan kuma..."
Gyaran murya ya yi, hakan yasa shi yayi shiru, rufe idonsa ya yi na ɗan lokaci, a da duk abin da ya shafi Zay'd restaurant baya wasa da shi, amma yau yaji bai ma damu da duk abin da zai faru ba, abin da yake gabansa yafi ƙarfin wannan.
"Ka yi duk abin da ya dace" ya basa amsa a taƙaice.
"Okay Sir amma akwai.."
Ƙitt ya katse wayar tare da sakata a silent, ajiye ta yayi a gefen sa, ya mayar da idonsa ya rufe...
★★★★
Ta na kwance a kan gado, idonta akan silin na ɗakin, ciwon marar da take ya ɗan ragu, amman zuciyarta har yanzu tana cikin wani irin yanayi da ta kasa fahimta, jin wayarta na ringing ne ta ɗago dan ganin me kiran, tana da true caller, take sunansa ya bayyana, ajiye wayar ta yi gabanta yana faɗuwa, ko a ina ya samu number ta, ta yi wa kanta tambayar da itama bata da amsarta, a hankali ta tashi zaune, idonta ne ya sauka akan unifoam ɗin da ta cire ɗazu kafin ta yi wanka.
Kayan ta zubawa ido, a hankali ta miƙa hannunta ta ɗauki rigar ta riƙe a hannunta, kallonta take, sai kuma ta ɗorata akan cinyarta, tunani ta fara akan yadda abubuwa suka dinga faruwa, tun kafin lokacin da ta fara aiki a Zay'd Signature, a hankali tunanin yanayin da ta dinga ji tun kafin ta shiga wajen ya dawo mata, yadda ta kasa samun nutsuwa, da kuma yanda ta ji kamar wani abu zai faru da ita, sai dai bata taɓa tunanin haɗuwa da Best friend a wajen ba.
Ta ya akai ma ya koma Zay'd bayan Muhammad ta san shi da shi, a yanzu dai koma menene shine mai jagorantar wajen aikinta, anya zata iya? Ta tambayi kanta.
"Ya rabb ya zanyi ni yanzu"
Ta ce ta ɗora hannunta akan goshinta kamar zata yi kuka, ta san dai ba zata iya ci gaba da zuwa wajen aikin ba, tunanin abin da hakan zai haifar sosai yake ɗaga mata hankali, ta na son aikin dan yana da muhimmanci a wajenta, ta sha wahala kafin ta kai inda ta kai a yanzu, ta jure abubuwa da yawa, ciki harda maganar mahaifiyarta da ta mutane, amman ba zata iya jure aiki a waje ɗaya da shi ba, dan ita kaɗai tasan abin da hakan zai iya haifar mata da shi kansa, numfashi ta sauke mai nauyi.
Cikin nutsuwa ta miƙe, ajiye unifoam ɗin ta yi a cikin wardrobe, ba ta jin zata iya ƙara komawa shiyasa ko tunanin wanke su ba tayi ba, jakarta ta buɗe ta ɗauki littafi da biro, farar takarda ta ɗauka, zama tayi a ƙasa, ta daɗe tana kallon farar takardar, ita ta yanke wa kanta hukunci, amman ta rasa ta ina zata fara, da ƙyar ta rubuta kalmomi guda biyu a saman takardar.
*LETTER OF RESIGNATION*
Dakatawa tayi da rubutun, saboda yanda hannunta yake rawa, lumshe idanunta tayi, dogon numfashi ta ja, sannan ta ci gaba da rubutun, bayan ta kammala kallon takardar ta yi, ta haɗiye wani abu da ya tsaye mata, tana jin an buɗe ƙofar ɗakinta amman bata juya ba, Salmah ce ta shigo inda take ta nufa Kai tsaye, sai dai tun kafin ta zauna ta ware idanunta cike da mamaki.
"Big sister.." sai ta rasa abin da zata ce mata, sai takardar da ta ɗauka tana karantawa. "Me ya sa zaki ajiye aikin da kika wahala a kansa?" Ta tambaye ta har lokacin mamaki ya kasa barin ta.
"Ba zaki gane ba Salmah, da dai na ci gaba da zama a inda yake gwara na haƙura da aikin gaba ɗaya"
Kasa magana Salmah ta yi sai ido ta zuba mata kamar ta samu tv, tunanin irin ƙalubalen da ta ringa fuskanta akan aikin kawai take, kuma duk ta jure, amman yanzu wai zata ajiye akan mutumin da ita kanta batasan laifin da yayi mata ba.
"Nidai a iya labarin da kika bani banji in da kika ce yayi miki wani abu, me ya yi miki da zafi haka dan Allah?" Ta tambayeta cikin sanyin murya.
Kanta kawai ta girgizawa Salmah, "Hmmm Autah inda ace nayi aure na haɗu da Best friend, ni kai na bansan wani irin farin ciki zanyi ba, ko yanzu ina cikin farin cikin ganinsa, sai dai tsorona da fargaba sun danne wannan farin cikin, Autah Best friend ya na da kafiya, indai ya ce zai yi abu wallahi babu wanda ya isa ya hanasa, indai ina son zaman lafiya dole ne na nisanta kaina da shi"
Gaba ɗaya kan Salmah ya ɗaure "me ya sa zaki nisanta kan ki da shi toh? Wani abin zai miki dan baki aure ba?" Salmah ta tambayeta tana kallonta.
Shiru kawai tayi mata, ƙarshe ta tashi tabarta a wajen....
★★★
*BAYAN SATI ƊAYA*
Tsawon sati bata je wajen aiki ba, duk da ta warke, kamar ma batai rashin lafiya ba, ga takardar da ta rubuta, ta kasa kai wa kuma ta kasa tura musu, tun lokacin kuma wayarta a kashe take, saboda kira da massage ɗin da yake tura mata, hakan yasa ta zaɓi haƙura da wayar dan ya fi mata kwanciyar hankali.
Tsakar gida ta fito, riga da wando ne a jikinta, kanta a tsefe ta saka ribbom ta ɗauresa a tsakiya, sosai tayi kyau a cikin kayan, ba zaka taɓa kallonta kace takai shekara 35 ba, kitchen ta shiga, bata jima ba ta fito da tea a hannunta.
"Zahra"
Mahmah ta kira sunanta.
"Na'am Mahmah" ta amsa mata ba tare da fargaba ba, ganin yanzu Mahmah ta dena hantararta, ko kuma tayi mata wani abu na rashin jin daɗi.
"Me ya sa bakya zuwa aiki ne?" Ta tambayeta ba tare da ta kalleta ba.
Dum gabanta ya faɗi, dan tambaya ce da bata taɓa tunanin jinta daga bakin Mahmah ba, shiru ta yi ta rasa abin da zata ce mata, gashi Salmah tana makaranta bare ta ƙwace ta, ganin irin kallon da take mata ne, yasa ta buɗe bakinta a hankali ta ce.
"Daman na dena aikin ne Mahmah"
"Kamar ya?"
Shiru ta sake mata.
"Hmm Zahra kenan!"
A tsorace ta kalli Mahmahn jin a yanda tayi mata magana, gashi gabanta sai faɗuwa yake, saboda a take taga fuskarta ta koma mata ta waccan Mahmahn sak.
"Burinki ya cika ba'abin mamaki bane dan kin dena zuwa" ta ce bayan ta saka idonta a cikin nata.
"Mahmah..."
"Eh burinki ya cika, a lokacin da na ce kar kiyi tun kafin ki fara kin saurareni ne? Baki ji ba, kinyi abin ki, sai bayan kin gama ɓata min suna, kin saka mutane sun gama zagina, da jifana da maganganu kala_kala, zan wuce ana nuna ni ana zunɗena, akan ƴata taƙi aure, sai dai yawo, wanda nima nasan yawon kike, duk na jure shine yanzu zaki ce kin dena zuwa aikin, burinki ya gama cika ai na ɓata min suna, dan haka toh wallahi baki isa ba, ki shirya gobe ki tafi wajen yawon aikin naki, idan kuma ba haka ba, wallahi wallahi wallahi sai kinyi danasanin kasance wata mahaifiya a wajenki"
Tana gama maganarta ta shige ɗaki ta bar Zahra a tsaye a wajen tana wani irin kuka mai cin rai.
Ta jima a wajen kafin ta shige ɗaki, bayan ta ajiye tea ɗin dan ba za ta iya sha ba, kwanciya tayi kukan ma ya ɗauke mata sai wani irin zafi da zuciyarta take mata, ya zamar mata dole ta koma aiki, saboda Mahmah, amman zuciyarta ta fara raya mata wani abu, tana ganin gwara kawai ta zama ƴar iskar da Mahmah take yawan jifanta da shi, idan ya so sai ta ce tana yawo da hujja, ta gaji da mugayen kalaman nan da ake jifanta da su, gwara kawai ta zama idan yaso sai su tabbatar, su dena zarginta.
A zuciye ta buɗe wardrobe ɗinta ta fara watsi da kayan ciki, tana neman unifoam ɗinta dan ta wanke, can ta ganosu a wanke a goge, gaba ɗaya tama manta Autah ta wanke mata, zama tayi tana karkaɗa ƙafarta, Salmah ce ta shigo da sallama, ko kallonta batayi ba bare ta amsa mata.
"Big sister na gaji"
Idan ta amsa mata gadon da take kai ya amsa mata. A take ta sha jinin jikinta, musamman ganin yanayin fuskarta, a tsorace take mata magana, har ta fidda rai da zata mata magana, kamar daga sama taji ta ce mata.
"Gobe zan koma aiki"
Bata iya ce mata komai ba, sai kanta data gyaɗa mata, dan wani irin tsoron Zahran ne ya dirar mata, ɗakin Mahmah ta shiga, itama kallo ɗaya tayi mata ta fito, bata buƙatar ƙarin bayani daga yanayin gidan ta fuskanci wani abu ya faru, kuma a kan aikin Zahran, dan haka sai ta kama kanta, ɗakinta ta shige dan ba zata iya zama tare da Zahra ba.
Wayarta ta ɗakko har zata danna kira sai ta fasa ta fara rubutu a wajen massage.
"Barka da yamma Yah Zay'd, gobe Big Sister zata koma aiki" ta tura masa tana murmushi.
Ko minti ɗaya ba'ayi ba, sai ga reply na sa.
"Kin tabbata Autah?"
Tabbaci ta bashi, sannan ta goge maganarsu, dan da zarar sunyi magana take gogewa, gudun tonuwar asirinta.
Washe gari da wuri ta tashi, babu wani abu da tayi da ya shafi aikin gida, cikin unifoam ɗinta ta shirya ta fito, kai tsaye hanyar fita ta nufa, har ta kusa fita daga gidan gaba ɗaya, sai taji zuciyarta tana mata rawa, ji take ba zata iya abin da ta ƙudurci niyyar aikatawa ba, a hankali ta dawo da baya, knocking tayi a ɗakin Mahmah, bayan an bata izinin shiga, ta shiga da sallama, gaishe su tayi, daga haka ta juya ta fice daga gidan gaba ɗaya.
Ta fuskanci babu abin da zata iya sai dai haƙuri da fatan Allah ya kawo mata mafita, dan haka sai ta fara ƙoƙarin cire komai a ranta, ta hanyar addu'a har taje wajen aikinta.
Kasa shiga tayi sai zubawa wajen ido da tayi, yanayin da ta baro shi yana dawo mata a rai, iska ta busar daga bakinta mai zafi sannan ta shiga, fuskarta a kame, kamar yanda ta saba tayi musu sallama, suka gaisa sannan ta nufi kitchen, tana jin yanda ake magana ƙasa_ƙasa amman ta nuna kamar bata ji ba, daga yanayin kallon da suke mata tasan suna mamakin ganinta a restaurant ɗin suke ba wani abu ba.
Ƙoƙarin tattara hankalinta take waje ɗaya, saboda ta samu damar yin aikin dake gabanta cikin nutsuwa, duk da ba ta cikin nutsuwar, saboda yanda zuciyarta take bugawa da ƙarfi, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ci gaba da aikin gabanta.
Jin an buɗe ƙofar kitchen ɗin ya sa ta dakata da abin da take, saboda ƙamshin da hancinta ya shaƙo mata, duk da yanda ƙamshin abinci yake tashi a kitchen ɗin, hakan bai hana ƙamshin shi kai wa hancinta ziyara ba, ƙoƙarin ci gaba da aikin take, duk da babu abin da take fahimta.
Duk da ya saba zuwa kitchen ɗin, ya duba sosai zuwansa na yau ya bawa ma'aikatan mamaki, saboda tun ranar da suka samu labarin abin da ya faru tsakaninsa da Zahra, basu ƙara ganinsa ba, duk da har yanzu basu san cikakken labarin abin da ya farun ba.
Sanye yake cikin suit army green mai duhu sosai, wadda ta fito da ainayin hasken fatarsa, fuskarsa cike da nutsuwa, a bakin ƙofar ya tsaya na ɗan lokaci, yana duba ma'aikatan da suke ciki ɗaya bayan ɗaya, a hankali idonsa ya sauka a bayanta, da sauri ya janye idonsa, saboda abin da suka gano masa.
A jikinta taji kallon da yayi mata, jikinta ne ya fara rawa a hankali, tana jin tsoron yayi wani abu da zai nuna sun san juna ita da shi a gabansu, katse mata tunaninta yayi da muryarsa cike da umarni.
"Kowa ya fita" ya ce ba tare da ya ƙara kallonsu ba.
Tsayawa sukayi suna kallonsa cike da mamaki.
Idonsa ya ɗago ya kallesu " i said everyone out now!!" Yayi maganar da ɗan ƙarfi.
Ɗaya bayan ɗaya, suka fice suna satar kallon sa, wasu kuma suna satar kallon Zahra.
Kanta ta sunkuyar tana addu'ar Allah yasa kar abin da take tsoro ya faru, ganin duk sun fice itama sai ta ɗauki hanyar fita.
"Ban da ke"
Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba, matsawa yayi ya rufe ƙofar, sannan ya jingina da ƙofar ya zuba mata idanunsa.....
FULANI
***