Page 12
by @oumamani
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 12
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Dagowa yai ya kalli fuskar ta yaga ta wani zuba masa ido tana masa wani kallo, hade rai yai ya mike tsaye ya dafa table din yace "karatu kika zo ko kuma tallan jikin ki kika zo min"
Da sauri ta dago ta kalle sa ganin yadda ya hade fuska yasa ta cikin inda inda tace "uhm uhmm sirr"
Tsaki yai ya nuna mata kofa yace "get out"
Zata sake magana ya daka Mata tsawar da bata son lokacin data kwasa a guje ba tafita.
Zama yai yana sauke ajiyar zuciya yana tunanin mafitar da zai dauka don gaskia bazai iya daukar wannan Risk dinba....
*********
Ina shiga gida da sallama na shiga palourn mu ganin Umma bata nan yasa na kalli Aisha dake assignment nace "Aisha ina Umma"
Dagowa tai d a fara'a tace "Maman hidaya ce ta haihu Ya batul shine Umma ta shiga itada Mimi, Nima da zan bisu sai Umma tace na zauna in kin dawo ma shiga tare"
Cikin murna nace "Kai don Allah Maman Hidaya ta haihu mai aka samu"
Murmushi tai tace "Namiji aka samu, kar kiso kiga Mimi da aka fada mata kamar zata yi hauka da kyar ta Jira Umma don da tace ita wallahi baxa ta Jira umma ba zuwa zatai taga baby"
Dariya nai nace "Allah ya raya sa, amma ALLAH ya shirya min Mimi wallahi ko meye na zumudin"
Dariya ita ma tai tace "Ai ya Batul Baki sani ba rige rige suke ita da Hidaya wai duk Wanda ya fara daukar babyn toh babyn sane kin san su ai da son girma"
Girgiza kai kawai nai nace "mai aka dafa ne don ina Jin yunwa"
Sai da tayi dariya tace "jallof din taliya ce tana kitchen"
Mikewa nai naje na zubo na zauna ina ci muna hira da Aisha har na gama, ina bata labarin Asma'u yau nayi kawa dai finally.
Sai wajen magrib Umma ta dawo ita kadai, kallon bayanta nai bayan na gaishe ta nace "Mimi fah Umma"
Tabe baki tai tace "taki dawowa wai bata gama ganin babyn ba ni kuwa na kyale ta tunda zaku shiga sai ku dawo tare"
Daga kai nai nace "dama mu jiran ku muke amma mun shirya bara mu shiga kafin Abba ya dawo"
Hijab dina na gyara muka fita nida Aisha zuwa gidan Maman hidaya, acan muka sami Mimi kuwa ta kankame ita da Hidiya sun kafa sun tsare duk wanda ya dau babyn sai sunje sun makale shi suna leka babyn.
Zama mukai bayan mun gaisa ina wa Maman Hidaya sannu, karbar babyn nai ina kallon sa Allah ya zuba min son Yara sosai a zuciya ta, murmushi na saki na dago na kalli Mimi data zubawa yaron ido itama.
Dagowa tai ta kalle ni tace "Maa Nima ki siyo min baby irin wannan"
Kallon ta nai gabana yana faduwa yanzu kullum zan kalli Mimi sai fuskar Mr Wicked ta fado min a rai, dan murmushi nai nace "ba ga shi ba Maman Hidaya ta siyo muku"
Make kafada tai tace "Maa wannan brother din Hidaya ne kinga maman tace ta siyo mata kuma a gidan su yake, nima ki siyo min nawa sai ya ringa kwana a gidan mu kina goya min Shi"
Aisha dake sauraran mu tayi dariya tace "Ya batul sai ki shirya siyo ma shalelen ki baby don tunda ta fara wannan maganar nasan kullum sai ta ishe mu akan zancen baby"
Banxa nai musu na maida hankali na gurin maman hidaya muna hira, muda muka ce zamu tafi da wuri sai gamu har 9, sallama mukai Mata bayan munyi maganar ni zan Mata snacks da drinks na suna.
Koda muka koma gida Mimi cika ma Abba kunne tai da labarin sabon baby, marairaice wa tai ta kalli Umma tace "Umma nace Maa ta siyo min baby tace baza ta siyo ba toh ke ki siyo min kawai"
Dafe kirji Umma tai tace "ni kuma Mimi da tsufana"
Daga kai Mimi tai tana mar mar da ido tace "Uhm Umma kawai ke ki siyo min zan dinga ma babyn wasa"
Kallona Umma tai tace "tab wannan aikin sai dai Maa din taki amma bani ba, ita dai zaki sa gaba ko zata maida hankali ma ta fara kula manai manta"
Hade rai nai na kalli Abba nace "Abba kaji Umma zata fara koh"
Murmushi Abba yai yace "gaskia take fada miki Batul, ni kaina maganar da mukayi da Yakumbo kenan yau tace ya kamata ki maida hankali a kan masu zuwa neman auren ki, kullum girma kike sake yi"
Kokarin maida hawayen nake nace "Abba ni bazan yi aure ba, bazan rabu da Mimi ba kuma bana son tai agolanci azo ana mata gori"
Salati Umma ta saki tace "kice so kike ki tsufa a gida muna goga kafada, in an shigo a rasa wace matar gidan wace yar gidan koh Batul, wai yaushe zakiyi hankali ne maganar Mimi dama wani yace zai raba kune"
Abba ne ya karba da fadin “kuma baga Yusuf ba yaron nan ya yadda da Kaddara yace Shi ahaka yake sonki kuma zai rike Miki Mimi kamar Shi ya haife ta amma kinki sauraran sama gaba daya"
Cikin rawar Murya nace “Abba taya zan saurari Yusuf shin kun manta waye Yusuf Abba, saurayin.....” Sai kuma na fashe da kuka ina rungume Mimi a jikina, sosai nake kukan wanda hakan yasa Mimi fashewa da kuka itama tana rungume ni sosai......
Kuyi hakuri da wannan na fita ne kawai na muku typing nema😊
***