Page 14
by @oumamani
*TASWIRAR KADDARA*
DijahAM(Oum Amani)
Page 14
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Sai da gabana ya buga da karfi amma na tattaro nutsuwa ta nace "ina kwana Ya Yusuf"
Ina Jin sautin murmushin Shi cikin nutsuwa yace "Lafia qalau ya jikin, Baba yace min baki da lafia"
Ajiyar zuciya na sauke nace "da sauki Alhamdulillah"
"Masha Allah, Allah ya kara sauki yasa kaffara ne"
A hankali nace "Ameen"
Shiru mukai dukan mu, shine ya ce "sai anjima tohm Allah ya kara sauki kiyi saving number ta kinji zan Kira anjima ln shaa Allah"
"Toh" kawai nace na kashe wayar dagowa nai idona suka fada cikin na Umma da ke tsaye a kofar dakin su tana kallona, marairaice fuska nai amma tai banza dani ta wuce kitchen.
Kwana na biyu bana zuwa makaranta saboda ciwon kan dake damuna, saukin tama duk abinda a kai Asma'u tana turo min kuma tana min attendance, a kwana biyun nan kuwa Yusuf ya taso ni gaba da Kira, don jiya ma sai da yazo dubani nidai ban fita ba kwanciya nai nayi lambon bacci sai Aisha ce taje ita da su Kamal suka gaisa ya basu leda Mai dauke da kayan kwalam su bani.
Yau da wuri na shiga makaranta kasancewar jikin nawa da sauki sosai, a hankali nake tafiya ina sanye da hijab dina kamar kullum dark blue na rataya jaka a kafada ta, cikin sanyin jiki nake tafiya nayi nisa a tunani kawai naji na bangaji mutum, da sauri na dago ganin waye na bangaja a tare kirjin mu ya buga.
Zuba mata ido yake yana kallon ta kwana biyu kenan baya ganin ta, tun shekaran jiya daya shiga musu lecture har yai ya fita bata zoba kuma jiya ma yana lura da abokin ta Shi kadai yake yawo a school Banda ita hakan ya tabbatar masa da cewa bata zoba kenan don da tazo da zai gansu tare.
Nima zuba mishi ido nai ina kallon sa sai kuma na turo baki na kauda kaina gefe, ciki ciki nace "Good Morning Sir"
Maimakon ya bani amsa sai jinai yace "mai yasa baki zo school ba?"
Da mamaki na dan saci kallon sa sai kuma na juya ina matsa hannuna nace "Banda lafia ne shiyasa banzo ba sir"
Kankance idon sa yai yana kallon ta yace "amma baki rame ba"
Turo baki nai nace "na rame mana"
Gira daya ya daga yace "really"
Dagowa nai bansan ya akaiba na maka masa harara, ware idonsa yai akan fuska ta yace "ni kike ma rashin kunya"
Da sauri na girgiza kai nace "sir ba haka bane sorry idona ne a haka sometimes sai yayi kamar ina harara"
Dan kallon gefen sa yai ganin mutane suna kallon su yasa shi yin kasa da murya yace "in kika Kara min wannan abin sai na tsone Miki ido". Raba ni yai ya wuce da kallo na bisa kafin na tabe baki na juya Zan wuce. Shan gabana naga anyi da sauri nadan ja baya ganin saura kadan mu hada kirji da wata.
Cikin Huci Zuby tace "mai kika tsaya yi keda Mr Azlan, Mai yake ce miki? ke har kin isa ki tsaya kusa da Mr Azlan dina kina masa magana kina wani yanga?"
Dan kallon ta nake a kaikaice ina kokarin fahimtar mai take nufi ganin tana hakikan cewa yasa ni fadin "akan wa wai kike wannan hayaniyar"
Zagi Nana ta kutuntuma tace"Zuby lallai yarinyar nan bata da mutunci ji yar iskar yarinya ta maida mu mahaukata, tambayar ki muke mai kuke fada keda Mr Azlan"
Kankance ido na nai cikin rashin tsoro na tako ahankali har gaban ita wacce ake cewa zubyn nace "mai zai hana kije ki tambaye sa mai muke cewa"
Cikin masifa tace "ni kike fadawa haka kinsan ko wace ni kuwa a fadin makarantar nan?"
Saida na juya idona nace "kece mana student data zo neman ilimi kamar yadda nake student dana zo neman ilimi nima"
Ina fadin haka na juya nai wuce wata ina jan tsaki a raina ina fadin banza mara aji ta rasa akan wa zatai fada sai akan Mr Wicked.
Kasa magana Zuby tai sai bina da kallo kawai tai, Nana ce ta jata zuwa wani guri suka zauna tana cewa dole su Nemo ko wace ni don su koya min hankali.
Yinin ranar sukuku nai sai duk bani da kwarin jiki, har Asma'u itama ranar duk wani iri tai ta don nidai ko fita daga hall dinmu ban ba dama kuma period nake ba sallah zan ba.
Ina komawa gida wanka nai na shiga kitchen na dora mana abincin dare ina cikin yi Yusuf ya kirani, kamar bazan dauka ba sai kuma na dauka, ai kuwa nayi nadamar daukar wayar don ya fada min sakon daya bata min Rai cewar yana zuwa bayan sallar magrib.
Umma na fadawa bayan na ajiye wayar, nan da nan fara'a ta mamaye fuskar Umman ta shiga tambaya ta mai za'a tare sa dashi, Dan sassauta yanayin fuska ta nai kodan saboda fara'ar dana gani a fuskar Umma.
Nidai bance komai ba sai Aisha ce ta shiga kokarin ganin ta sa masa cake da doughnut din da nake a wani bowl na tangaran ta rufe ta kuma dauko zobo ta juye a jug tasa a fridge wai yadda in yazo sai dai kawai a dakko a basa.
Nidai ina kallon su ni kadai nasan yadda nake ji, zuwan da zaiyi yau kuwa na tanadi tambayoyin da zan masa ko Allah zai sa ya dawo cikin nutsuwar sa ya tuna da babban cin amanar daya ke shirin yi.
Ana Magriba Umma ta sani a gaba wai nai wanka duk kaurin girki nake, kamar zanyi kuka na sake wanka amma ina fitowa Mai kawai na shafa na zira rigar bacci ta na zumbula katon hijab har kasa ash colour sabo ne ban taba sashi ba, turare na dan fesa kadan na kalli wayata dake ringing, cikin sanyin jiki na dauka na Kara a kunne, a hankali cikin nutsuwa y sanar min da karasowar sa, Nima banyi wani hauka ba sai cewa danai gani nan zuwa kawai na kashe wayar.
Gurin Umma naje kamar zanyi kuka nace "Umma wai yana waje"
Mikewa tai tace "toh Masha Allah sannun sa da zuwa jeki Maza bara na bawa Khalil dadduma ya kawo muku zuwa anjima sai a kai masa abin tabawar koh"
Nidai ban mata magana ba sai kaina dana sunkuya kasa idona na cikowa da hawaye, kallona Umma tai ta tabe baki tace "zaki wuce ne toh ko kuma tsayawa zakiyi anan"
Ban mata magana ba na fita cikin sanyin jiki, a waje na gansa tsaye kusa da dakalin kofar gidan mu ya jingina da motar sa Yana sanye cikin manyan kaya, Yusuf kyakkyawa ne don bakin bafulata nine yana da rufin asiri daidai gwargwado don yana aiki, bashi da makusa mutum ne shi mai fara'a da barkwanci sam bashi da damuwa.
A hankali na karaso ina dan sassauta yanayin fuska ta nace "ina wuni yasu Mama"
Murmushi ya min yace "lafia qalau Batul yasu Mimi dasu Umma"
A hankali nace "Alhamdulillah"
Shiru nai ban sake magana ba sai maida kallona gurin Khalil danai daya ke tahowa dauke da dadduma, yana zuwa shinfida mana yai aka dakalin dayake yana da dan girma ya gaishe sa ya juya ya koma cikin gida.
Kallona yai yace "Bismillah zauna"
Ajiyar zuciya na sauke na zauna daka can karshen dakalin, murmushi yai ya girgiza kansa dama yasan Batul zata iya abinda yafi haka ma.
Zama yai shima ya dan yi shiru kafin yace "nasan zaki ji wani iri a bisa ra'ayin auren ki dana nuna Batul, in har kin amince Zan aure ki kuma xan rike Mimi na Miki alkawarin baxan taba banbanta ta da yayan da zan Haifa ba"
Kallona yai yaga kaina a kasa yake ina jujjuya wayar hannuna ya cigaba da fadin "baxan takura kiba Batul kina da damar da zakiyi rejecting dina, in har ban kwanta Miki ba kar kiji komai ki fada min don Allah"
Ajiyar zuciya na sauke nace "Ya Yusuf baka jin kunyar wannan cin amanar da kake so nayi ko ka manta Kai din saurayin waye?"
Zuba mata ido yai kafin ya girgiza kai yace "Batul ban manta ba amma ynxu gare ki nazo ina neman amincewar ki, kuma ba cin amana bane Batul bata inda mukai cin amana"
Kallon sa nai da mamakin Jin cewa wai ba cin amana yake shirin samu yiba tab lallai ma Yusuf, na bude baki zanyi magana kenan Kamal ya fito daga gida hannun sa dauke da tray gefensa Mimi ce tana sanye da kayan bacci kanta sanye da hular sanyi kasancewar garin dakwai sanyi.
Karasowa gurin sukai ajiye tray dn Kamal yai a tsakiyan mu, Mimi kuwa kallon sa take tana son zuwa gunsa amma tana kallo na don na hanata zuwa gurin ko wanne namiji in basu Kamal ba sai kuma cilla bayan haka ma Mimi bata da saurin sabo da mutane, Murmushi Yusuf ya sake Mata yace "Mimi baki gane niba"
Turo baki tai tace "na gane Ka Uncle Ina wuni"
Dariya yai yace "lafia qalau Mimi yasu Umma da Hidaya"
Sai lokacin tayi dariya tace "Hidaya Mummyn ta ta siya Mata baby, Nima nacewa Maa ta siyo min tace baxa ta siyo ba kuma fa nace mata baxan dinga dukan babyn ba wasa kawai zan na Mata"
Kallona yai yana dariya yace "gaskia ya kamata ki samo Mata baby itama tana so ko Mimi"
Sunkuyai da Kai nai kunya na kamani ita Mimi yarinya ce bata san ya ake samun babyn ba ni kuwa ai da wayo na na sani, ina kallon su suna hira sai biyewa shirmen ta yake hakan yasani jin wata nutsuwa tana shigata, tun ina kallonsu har nima na fara sa baki anayin hirar dani.
Sai wajen 9 muka shiga gida bayan ya bawa Mimi ledar kayan cwt sai murna take tana tsalle, sallama nai masa ina murmushi na shige gidan.
Ranar Umma kamar zata goya ni ganin banyi complain ba na saki raina ina hidima ta har lokacin kwanciya yai.
Koda muka zo kwanciya sai daya kirani, mun dan dade muna hira kuma ba laifi na saki jiki ba kamar kwanakin baya ba sai da na fara jin bacci sannan nai masa sallama na kashe wayar......
***