OMRI HAYATII

8

by @asmybaliyu

OMRI HAYATII 

by
Asmy b Aliyu 

8....
murmushi abba yayi Yana Kara jin kaunar Yaran nasa na cika masa zuciya.numfashi ya sauke ya kalli fareeda Cike da so da kulawa yake fadin "idan Zasu tafi shopping din tazo ta karbi card dinsa,rungume Abbanta tayi tana yimasa godiya
shafa kanta kawai ya iyayi Yana sakin murmushi.
a daren ranar ma ba wani bacci yayi cikin natsuwa ba duk fushin da mami keyi ya damesa.haka bai damu da wayarsa da take a Kashe ba duk da malaak tana manne a ransa yasan Kuma xatayi ta nemansa.Kara ya fara shawo kan Mami
kafin ya tunkari malaak din.

####
duk yadda mum dinta ta sakata a gaba da rarrashi akan taci abinci da ya'r aiki ta jera a agabanta kusan Kala biyar kin taba komai tayi har wata rama tayi haka idanunta sunyi zuru -zuru tamkar mai wata cuta duk yadda hajia zainab din ke jin takaicin ya'rtata dannewa tayi saboda tana yiwa ya'yannata wata irin masifaffar soyayya duk abunda sukeso shi takeso,
idan Kuma abu yakai bango duniya Xata iya zuwa ta samosa dan ta mallaka masu shi."bani nayi maki alkawarin zanje gobe har gidan nasu ba na dibo maki halin da ake ciki,meyasa kike da kafiya ne malaak??"
da sauri malaak ta riko hannayen uwar 
cikin rawar murya take fadin"wallahi mum tun ranar da na baro gidansu zuciyata batada natsuwa bansan meyasa nake jin wani iri ba har yanxu wayarsa a Kashe mum."ta fada da wani daci a muryarta,
"komai zai zama daidai
mum ta debi abinci a baki ta Kai bakin malaak din wacce ta bude baki ta fara ci a hankali haka mum din ta rika feeding dinta
tamkar ya'r shekara biyu.sai da taci fiye da rabi ta fadawa mum dinta ta koshi
kafin hankalin mum din ya kwanta 
haka ta saka mai aiki ta fita da sauran abincin....

maleeka dake zaune a falon da waya a hannunta tana dannawa shekarunta bazasu wuce 28 ba a duniya ta daga Kai ta kalli mum din tasu da ta karaso cikin falon damuwa bayyane cikin fuskarta.maleeka din ta aje wayar hannunta tana kallon mum din take fadin "taci  abincin?"
mum taja wani numfashi tana saukewa take fadin nasamu taci ,dan tabe baki Maleeka tayi kema mum kin San rigimar malaak dan taga kina biye matane shiyasa take iskanci daya daya.ta riga ta mutu akan mu'azzam din nan.na lura Banda tsinannen girman Kai da yake dashi.
ji dai malaak din yadda take binsa kamar Xata xauce akansa.mum ki fadamun ga wata so nawa kike ganin mu'azzam a gidan nan yazo wurin malaak??'"dan shiru mum din tayi tana juya maganar maleeka aranta.

gobe dai koma menene zanje gidan nagani da idona kin San itama uwar tasa tsinannace. kin manta inda yayi gadon fadin rai,inbanda malaak ta mutu akansa 
tayaya zaayi na rika bin Aisha ,ai kema kin San Sai dalili mai Karfi tarenmu ma kamar ana mata dole.nadai samu malaak ta auri danta sai tayi mugun raina kanta wallahi."dan murmushi maleeka tayi tana gamsuwa da bayanin mum din tata. 
dan itama auren da tayi sai da aka bi ta karkashin kasa ta samu abunda takeso
dan itama babban mutum ne ta aura wani babban dan siyasa,wanda duka rayuwarsu da suke A Abuja suke yinta Yana da wata matar itace ta biyu ,amman matarsa shigowar maleeka farook rano cikin rayuwarsu ya sauya kowa da komai
dan nan take tarihin uwar gidan ya shafe tamkar babuta cikin duniyar mijinta maleeka kawai yake gani a gabansa,
haka daman hajia zainab keso ya'yanta su zama wasu a gaban mijin su xasu rika juya mazajensu basune Zasu rika juyasu ba,
kusan kullum maleeka tana a kaduna wurin uwar kullum cikin yawo take,
mijin Sai yadda sukayi dashi.....

washegari ya samu mami ta dan sake masa.har tayi masa tayin breakfast,
Rabin damuwarsa yaji ta sauka 
ganin Mamin ta sauka Shima ya shirya wuraren 12 ya nufi clinic dan ragewa kansa damuwa.har lokacin Kuma yaki yadda ya kunna wayarsa,Yana isa clinic ya wuce office dinsa Kai tsaye ya murza key
batareda ya nemi kowa ba kafin ya shigo
Sai da ya tabbatar kowa yazo nemansa Kar abari ya shigo ace kawai bayanan,
natsuwar zuciya dama kwakwalwa yake nema a wannan lokacin....

#####
malaak ce tsaye akan mum dinta dake amsa waya cikin isa da wata irin izza,
malaak duk ta kagu mum dinta subar gidan tanayi tana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta , fitted gown ce ajikinta wanda akayi dinkin daidai da jikinta kayan sun zauna ajikinta Sai simple dauri da tayi sai wani dan yololon mayafi data dora akan kafadarta mai shege da atamfar Sai uban kamshi ke tashi ajikinta 
kallo daya zakayi mata kaga kyakkyawar macce tana da kyau daidai gwargwado 
baa sakata a layin masu tsayi haka baa sakata a layin guntaye tsaka tsaka 
kalar fatarta chaculate colour 
Wanda skincare dinta take amfani dasu
ya hade da hutu ya saka fatar tata har wani sheki take .daganin yanayin jikinta kudi take kashewa bana wasa ba.......

bayan mum ta gama wayar ta daga Kai ta kalleta da mamaki .kafin tayi magana malaak din ta rigata mum na shirya kefa nake jira.........baki bude mum din ke kallonta.yanxu da tsakar ranar nan Zaki ce kin shirya mu tafi waike meyasa bakida hankali ne.??"mum kwana biyu banji muryarsa ba mum kamar zan zauce nake ji
mum bakiji zuciyata ba kamar an dora mata katon dutse.....malaak ki dawo hankalinki idan xaki dawo baa nunawa namiji irin wannan kalar so 
gaskiyya kin bani mamaki da kunya
dan ni dai bani kika gado ta wannan bangaren ba.kina ganin bana rawar jiki akan mahaifinku Sai dai shi yayi rawar jiki akaina.
kinga me ya sameni"saboda ban dorawa Kaina wahalar mugun sonsa ba,
wlhi ba baki nake maki ba ki rage wannan shegen son da kike nunawa wannan yaron 
idan ba haka ba a gaba ke xakiyi nadama."

"mum please!!!"
malaak ta fada a mugun fusace tana jin zuciyarta na mugun tafasa kamar Xata kama da wuta wani irin zafi da radadi zuciyarta keyi mata.Shima Yana sona ya damu dani. ni nasan akwai dalilin da yasa bai nemeni ba hankalina bazai taba kwanciyya ba Sai naji wannan dalilin."
nidai baxan fita a yanxu ba bakuwa zanyi
yanxu tana hanya idan xaki iya jira tazo 
idan ta tafi Sai mu fita idan bazaki iya jira ba ki kama hanya kiyi tafiyarki."ganin tayi mum din tabar falo ta nufi up stairs zuwa dakin baccinta dan idan ta cigaba da zama a falo malaak din bata mata rai kawai xatayi.ba yadda malaak din ta iya haka ta juya ta koma zuwa dakinta duk ranta a dagule bazata yafewa mu'azzam ba wannan wahalar da ya sakata da dama mata duk wani lissafin dake cikin kanta.

bakuwar mum din bata bar gidan ba Sai kusan 4 .malaak ta cika tayi fam kiris take jira ta fashe koda suka fito an fara kiran sallar la'asar daga uwar har ya'r basuyi tunanin yin wata sallah ba malaak ta jasu a mota suka nufi gidansu mu'azzam din dake cikin (Unguwar Rimi)

maigadi Yana ganin motar malaak ya bude Mata get ta shige da motar tayi parking 
inda aka tanada dan parking mota,
lokaci daya suka fito itada mum,
daidainan fareeda ta fito itada Ayusherh 
kowace cikin turkish abaya Ayusherh kalar black fareeda kalar maroon,sunyi kyau har Sun gaji da fara'a fareeda take gaishesu
mum ma ta amsa cike da fara'a tana fadin"Yammatan mami Ina xaaje haka akaci wannan gayu.?"fareeda tayi murmushi tana fadawa mum shopping Zasu tafi ,nan take mum ta bude jika ta ciro rafar Yan naira dubu rafa biyu ta miqawa fareeda tace ta Kara tayi shopping 
da sauri fareeda ta girgiza Kai tana fadin"mum kibarsa dan Allah Abba ya bamu wallahi."hade rai mum tayi tace lallai Sai ta karba haka babu yadda fareeda ta iya ta karba .yau tasan idan Mami taji Zata sha fada,dama Ayusherh tana gaishesu bata jira Sun amsa ba tayi gaba ta tsaya gun motar Mami wacce cikinta driver xai kaisu,bayan Sun wuce
mum ta rike baki tana fadin"Aisha Akwai
karambani da kininbibi ,haka kawai ta hada ya'r aikinta da yarta Sai ka rantse Yarinyyar nan ba ya'r aiki bace.
kadan ma kika gani mum Sai kin ganta acikinsu yadda take walwala kamar Sun hada jini daita,ni wallahi na tsani Yarinyyar nan,ga shegen tsinannen girman Kai 
na masifa."dan tabe baki Mami tayi Suna nufar entrance din shiga falon gidan,
daman tun da suka shigo malaak ke bin motocin gidan da kallo haka bataga motar mu'azzam a wurin ba kenan bayanan."wata zuciyar ta fada mata,

babu komai a fuskar Mami tayiwa 
mum din sannun da zuwa,tasa dayan mai aikinsu wacce take zuwa tana Yini ta kawo masu drinks da abun motsa baki banda danna wayarta babu abunda malaak din keyi bayan ta gaisheda Mami,
kwana biyu Aisha tunda baki zumunci nace ni bari nazo mugaisa."murmushi kawai Mami tayi tana fadin kin San abubuwan dayawa."kullum haka kike fada Shima mu'azzam kwana biyu na daina jinsa ko a waya.murmushi Mami tayi
tana fadin"ai danki ne kunfi kusa."
daidainan wayar Mamin ta fara ring,
ganin mai Kiran Mami ta kalli mum 
tana fadamata tana zuwa bari ta amsa waya.da haka Mamin tabar falon.....



#OMRI HAYATII 
#LOVE/FATE
#BEST LOVE
#BEST STORY 
#MALAAK FARUK RANO 
#MU'AZZAM MARAFA
#ASMY B ALIYU 
#***